← Book details Gimbiya Balaraba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 80

Sashe 56

Gimbiya Balaraba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jin motsin Leda yayi yawa a tsakar gidan,yasa Lantana rarrafowa ta futo, domin taji sallamar Maburuka tabbas tasan ta kawo kayan dad'i, ilai kuwa tana futowa tayi arba da wata k'undumeniyar kaza gasashiya taji k'uli-kuli da tumatur da albasa,Uwa sai k'okarin kaiwa bakinta take. Lantana ta dunga washe baki tana fad'in Allah yasa banyi bacci kam,tun d'azu bacci yake so ya kwashe ni,Allah bai nufa ba"

Zam tayi gefan Maburaka tana tai mata banbad'anci Mabaruka ta ciro cinya da hak'arkari ta bata, sannan ta bata robar yoghot guda d'aya, tace"Shikkenan na sallame. Ki tashi kije ki kwanta"

Lantana ta mike tana. Fad'in "Ai ko baki fad'a 'yan nan, Allah ya bamu alkari"

Babu wanda ya kulata a cikinsu duk suna can suna rubibin cin gasashiyar kaza me maik'o☺

Sai da suka kusa cinyewa sannan suka tuna da Sallau, Uwa! Tace"Wannan ragowar k'ashushuwan sai ku barwa babanku ki"?

Shamsiyya tace"Wallahi ni har na manta ma dashi"

Tab'e baki Uwa! Tayi ta mike tsaye tana niyar shiga d'akin take fad'in kin manta dashi ko na manta dashi, ummm".

D'akin ta shiga,Mabaruka ta mik'e da Sauri,jiri yasa ta dafe bango sai da tayi minti biyu sannan ta d'an dawo dai-dai, cikin yanayin maye ta k'arasa bakin rijiya ta ja ruwa ta zuba a buta ta shiga band'aki.

Lokacin da suka gama alfashansu da saurayin batayi wanka ba,ko da yake a cikin motarsa suka yi komai, babu gurin wanka dole sai ta dawo gida.

***************
Yau sati biyu da rasuwar su Fiddausi mutuwar me Martaba kuma ta kasance sati uku,, Waziri ya saki jiki sosai kullum yana zama a fada sai dare yake tashi sosai ya jinjinawa Mak'asudu domin da yarjewarsa ya samu nasara, tun bayan mutuwar su Fiddausi Mak'asudu bai k'ara tsotsewa wani jini ba,ya bari ne k'ura ta lafa, amma yana sane da iya adadin mutanan da akai masa alk'awari.

Komai yana tafiya dai-dai ta b'angaran Hajiya Kulu ita da yaranta, biyu daga cikinsu ma sun kaso auransu sun dawo gida, kullum sai su shirya su futa basa dawowa gida sai dare can,wani lokacin ma a can suke kwana. Hajiya Kulu kuwa kullum tana tare da k'awayenta "yan duniya sosai suke shek'e ayarsu Hajiya Kulu ta zama k'umgurmar " yar lesbian, sosai take jin dad'in harkar shiyasa take ganin babu wani dalili da zai sa ta tadaina more rayuwarta yanzu ta fara, k'awarta Hajiya ta Masu, itace take kawo mata "yan mata zuguda-zuguda. Sai ta biya ta kudi masu tsoka.

Kuma duk abunda ta tacewa Sarki! Ya aikata sai ya aikata shi,domin baya tsallakewa umarnin ta.

******

Yau saura kwana uku d'aurin auran Sarki! shine dalilin da yasa gidan ya hautsine da shirye-shirye b'angaran Mama Fulani ma haka bayi sai shige da fuce sukeyi, Mama Fulani taso Sarki! Ya d'aga lokacin d'aurin auran sai bayan futarta daga takaba. Yace tayi hakuri kawai a d'aura yanzu burinsa kawai a d'aura auran ya wuce gurin domin sunyi magana da governor maganar zama a fada yace sai bayan auransa wannan zai fara zama domin shine cikar mutum, wannan magana da Sarki! Yayi itace ta kashe masa jiki, yasa ya hak'ura kawai,amma sam baya kaunar ganin Waziri kan kujerar mulki domin sam bata dace dashi ba.

Halisa na keb'e a wani guri, a cikin gidan dai, Madabo da sauran " yan uwansu suna kula da ita tare da gyara mata jikinta sosai domin Madabo tace "yar baza tayi boranci ba,dole sai tafi sauran matan da zai aura shiyasa tasa ake had'a ta sosai

To itama Azima tunda aka fara hidamar bukin ta tafi garinsu domin ta shirya tsaf, duk da yake ita kullum cikin shiri take Mamanta ma ba a zaune take ba.

Su Shahid da Shatima ne suke fad'i tashi tare da shige da fuce, ganin ko wacce a bata hakkinta a kwatuna iri d'aya suka siyo irin me sha biyu nan, duk a bubuwan dake cikin d'aya a kwai a cikin d'aya,Kai dai-dai da kayan bacci iri d'aya suka zuba musu, takalma mayafai gasu nan birjik,gaskiya sun had'a musu kaya kamar hauka.

Mama taji dad'in k'okarin dasu Shahid sukeyi domin in ta Sarki! Ne sai dai a d'aura auran babu lefe sam taga bashi ne a gabansa ba.

" Yan uwa da abokan arzik'i Mama ta kira suka mik'awa ko wacce nata Balaraba dai nata suna gaban Mama,inda tayi-tayi da ita tazo ta duba kuma ta d'ibi wanda take so a d'inka mata Balaraba kunya duk ta hanata, haka Mama ta hak'ura ta kira Jakadiya Shafa'atu ta d'ibar mata atamfofi da lesuka masu kyau da tsada a ka kaiwa masu d'inki.

Yanzu Balaraba bata futowa falo sosai, kullum tana d'aki a kulle indai ba Mama CE take kiranta ba bata futowa saboda wata irin kunyar ta da take ji,Su Sadiya kuwa ai sun zama "yan gari sun saba da Mama sosai hakanan Jakadiya Shafa'atu in zata wani guri sai ta tafi dasu domin suga gari.

Shi kansa Sarki! Ya kwana biyu bai sanya ta a idonsa ba, daurewa kawai yake amma kwanakin nan yana yawan jin fad'uwar gaba idan ya tuna da ita,kasancewar shi mutum ne Wanda baka ganin damuwarsa sai ta kai ta kawo shiyasa lokaci guda baza ka fahimci halin da yake ciki ba.

*********

Misalin hud'u da rabi na yamma Balaraba na zaune gefan gado tana duba wani k'aramin littafi irin na addu'oi, tana sanye da wata doguwar riga mai uban kyau da tsada rigar taji stone masu shek'i wuyanta da hannuta tayi amfani da k'aramin hijab irin me hulan nan fari k'al dashi, dai-dai kafad'arta ya tsaya, fuskarta tayi fayau sai annuri ne yake sauka, dama can ita wannan kwaliye-kwaliyen bai dame ta ba,ko Wanka tayi k'ark'ari ta shafa mai sai hoda,da kwalli sun ishe ta, amma fa akwai son k'amshi jidin jikinta na k'amshin turare.

Sadiya ce ta shigo da saurinta tana fad'in "Yayarmu kizo inji Mama,wai zaki kaiwa Magajin Sarki! Abunci yana zazzab'i"

Balaraba gabanta ya fad'i jin abunda Sadiya tace, tace"Wai ke ba na hanaki rashin kamun kai ba, don Allah dube ki sai wani rawar jiki kike yi"

Sadiya ta sunkuyar da kanta tana jin tsoran fad'an yayar tata.

"Karki k'ara shigowa babu sallama kuma ki daina wannan gudun da kikeyi"

Sadiya tace "To"

Ajiye littafin tayi kan gadon ta mike tsaye tana gyara zaman hijab din nata,tace"Yana ina ne Magajin Sarkin"?

"Yana shashensa tare da abokansa,muma bamu dad'e da dawowa ba ni da Usuman tun d'azu muna can"

Ita fa bata son zuwa shashensa gudun abunda ka iya zuwa ya dawo ta lura wani irin mutum ne shi, me saurin tab'a jikin mace ko haka yakewa sauran matan oho shi dai ya sani, amma dole zata kiyaye ta daina sakar masa jikinta.

_Niko nace Balaraba kenan maganar sakin jiki ta k'are tunda an kusa d'aura aure_
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
_*GIMBIYA BALARABA*_
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻

_*NA*_
_BINTA UMAR ABBALE_
*®BINTUBATULA👄*

```MARUBUCIYAR```

*NANA KHADIJA*
*YARO DA KUD'I*
*GIMBIYA BALARABA*
*TSANTSAR BUTULCI*

_*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*_

_________________________
```We are here to educate, motivate and entertain aur Reades```
_________________________

_*DEDIGATED*_
_*TO*_
_RAHAMA ALIYU_

_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR RAHIM*_

______________________
*Tsokaci*
______________________

*_Tun farkon farawa na fad'a cewa ban rubuta littafin Gimbiya Balaraba domin in ci zarafin wani ko wata ba, ku wani jinsi mutum me k'iba ko siriri, wannan labarin k'agaggene daga ni, Binta banga dalilin da zaisa kawai in ci mutum cin wani jinsi ba,kamar yadda wata "yar uwa ta fad'a min, Asali ma, wannan jinsin mutane da take magana akan su ina cikinsu to kun gani idan naci musu fuska har dani a cikinsu, Allah da kan shi ya hallici d'an Adam kuma ya karrama shi, duk a cikin hallitunsa ni Wacece da zanyi ciwa hallitar Allah fuska,, labari ne kawai saboda haka don Allah mu San abunda zamu dunga fad'a akan " yan uwanmu_*

*🅿89*

Mama Fulani na zaune a falo ita da Jakadiya Shafa'atu suna hirarsu cikin mutun ta juna.Balaraba ta futo a nutse ta k'araso inda suke ta tsuguna tana gaishe da Fulani.

Cikin "yar fara'a Mama Fulani ta amsa, tace" Dama nace Sadiya ta kira ki kaima Mutumin ki abunci yana can shashensa tare da abokansa su Shahid,watak'ila ya fi maida hankali yaci abuncin, tunda bashi kad'ai bane"

Cikin jin nauyi gami da kunya Balaraba tace"Mama Sadiya tace bashi da lafiya yana zazzab'i"?

"Ba wai bane, da gaske ne, yau ya tashi da zazzab'i amma dai yanzu nasan jikin da sauk'i tunda d'azu ma ya shigo mungaisa"

Balaraba ta mik'e tana fad'in Allah ya sawak'e, Mama ina abuncin yake"?

Can wani katafaran gurin cin abunci ta nuna mata tace "Kije ki had'a masa,amma yace nacin mutum uku za'a had'o in yaso in kika gama sai ki kira d'aya daga cikin " yan matan dake aiki a waje ta d'aukar miki'

Balaraba tace"To ta mik'e ta nufi gurin cin abincin.

A nutse ta had'a masa komai yadda yace d'in, Mama tasa Sadiya ta kira wata baiwa me suna Lahira ita tazo ta d'auki kwandon abincin suka futa tare da Balaraba.

Tun washe garin rasuwar Maddibo rabonta da b'angaransa shiyasa yanzu da ta shigo taji gabanta yana fad'uwa tunowa da tayi da rayuwarsu da Moddibo wasu hawaye ne masu zafi suke k'okarin zubo mata, ta fara k'okarin mai dasu,,.

Wasu k'yatattun takalma ta gani a bakin k'ofar shiga falon, kuma tana d'an jin magana a ciki, sai ta gyara yanayin ta,ta koma Balaraban ta ta asali, cike da jarumta tayi sallama ta shiga falon, Rahila na biye da bayanta.

Yana kishin gid'e cikin wata shirgegiyar kujera,me kamar k'aramin gado da wasu k'ananun fililluka a kai, daga shi sai boxar da k'aramar shart me k'aramin hannu,abunda yasa yayi wannan shigar saboda jin jikinsa ya d'auko zafi gumi sai zuba yake,dalili yasha maganin zazzab'i shikkenan gumi sai karyo masa yake ko ta ina,shine fa yayi Wanka ya sanya k'ananun kaya,yazo ya ware AC har suna rigima da Shatima saboda k'arfin AC d'in yayi yawa,shi kuma yace ya rabu dashi haka yake so.
Chapter 56 · 0% Book details