← Book details Gimbiya Balaraba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 80

Sashe 19

Gimbiya Balaraba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Matasan dake tsaye a gurin ne suka rufa masa baya suma cikin rashin tarbiya suke cewa"bari muje muga wane dan iska ne,yanzu mu kaddamar masa"!

Maddibo yana hangen zuwansu gurinsa sai ya gyara tsayuwarsa, har suka karaso gurin,suka tare Salmanu, cikin tsageranci Walidi yace"kai ina zaka ne? me wancan guy yace maka"?

Jiki na rawa Salmanu yace"Cewa yayi in kira masa Gimbiya ta gidanku"

"Kai!! dan uwarka wacece Gimbiya a gidanmu"?
Walidi yafada yana dukan kafadar yaron.

" Balaraba fa yake nufi"
Salmanu yafada jikinsa na rawa domin wani irin tsoran Walidi yake ji
Cikin tsawa!Walidi yace "kai! kauce daga nan dan uwarka ko in yaga ka, yanzunan"

Da gudu Salmanu ya bar gurin,

Cikin wata irin tafiya Walidi ya karasa kusa da maddibo ya tsaya yana masa wani irin kallo, duk da cewa a kwai duhu a gurin bai hana shi ganin irin kallon da yake masa ba.

"Kai waye ya baka izinin shigo mana lungu ehe,! mufa duk inda mukaga bakuwar fuska babu yadda, gurin wace Gimbiya kazo a lungun nan"
Dariya ce taso takama Maddibo ganin yadda yaron yake wani ciccije baki yana wani tangadi tamkar zai kai masa duka, gashi sai warin ganye suke dukkaninsu, girgiza kai yayi gami da gyara tsayuwa yace"Sannuku "yan samari, ni bak'on alkairi ku kwantar da hankalin ku, Gurin Balaraba nazo"

Walidi ya gyara tsayuwar gami da zira hannu cikin aljuhun wandonsa ya fito da wata wayarsa wacce duk ta sha dauri ka da kyaure sabuda tsabar ganin duniya,ya kunna fitar wayar cikin sigar rashin mutumci ya dallare fuskar Maddibo da ita,
Sai wayar ta kusa faduwa sabuda razana da yayi, ganin Fuskar Sarki!Almansor da yayi, sabuda Maddibo suna dan yanayin kama da Sarki!amma ba sosai ba, sai dai duk inda jininka yake za'a ga kama ko yaya ne"
Bakinshi na rawa yace"ranka ya dade, kace Balaraba kake son gani"?

"Kwarai kuwa"
Maddibo yafada fuskarshi a sake,

Washe baki Walidi yayi yace"ai kuwa bata dade da dawowa daga kasuwa ba, wallahi ai yaya ta ce, bari in shiga in kira maka ita"

Fuska a sake Maddibo yace"Ok nagode Abokina, kace"mata Yusuf ne"

"E ai insha Allahu zan yi mata bayani"
Walidi yafada gami da juyawa da sauri!
Maddibo yace"jimana"

Walidi ya dawo da sauri ya zube kasa bai sani ba,
Maddibo yace mike tsaye mana Abokina"
Cikin yake Walidi ya mike tsaye sam ya kasa hada ido da Maddibo sabuda tsabar kwarjin da yayi masa,
Hannu ya zira cikin aljihu ya fito da kudi daurin "ya dari-dari guda uku ya mika masa, Hannu na kyarma Walidi ya karba yana ta zabga godiya,
Gyaran murya yayi yace" ka dauki dauri daya ku raba da kai da abokanka, sauran dauri biyu ka bawa mutanan gida"
Godiya kawai Walidi yake bakinshi yaki rufuwa,sauran matasan dake gurin suka sanya ihu!suka bi bayan Walidi da gudu,
Shamsiyya ta dago kanta tana kallonsu har suka karaso gurin basu bar ihun murna ba, ranta a bace! tace"kai wannan wane irin iskanc......kafin ta karasa maganar tata Walidi yazo yayi fatali da kaskon suyar awarar wanda yake cike taf da mai gami da awara cikin kwai, da sauri! ta dauke kafafunta tana kurma ihu! sabuda yadda mai duk ya zuba a kafafunta, kafin ta dawo hayyacin ta Walidi ya daki! Katuwar rubar dake cike taf!da awara an soya ta gwanin sha'awa, duk ta watse a gurin cikin kasa da tarkacan kazanta, ihu! ta kurma ta mike da sauri tayi kan Walidi tana dura masa ashar! ba ta sani ba ta tsumbula kafarta cikin kaskon awarar wanda ke dauke da ragowar mai da bai karasa zubewa ba, durkushewa tayi a gurin tana rike kafarata sosai ta kone, a kafafun da hannunta guda.

Cikin Ihu!da hargowa Walidi yq shiga gidan, sauran matasan dake biye dashi a baya suna tayashi,
Lantana ta mike da sauri! har sai da zanin jikinta ya sabule ya fadi kasa tayi saura daga ita sai dan tofi, Cikin gigita tace"shikkenan Walidi ya jawo mana musiba ooo ni Lantana!
Uwa! ma fitowa tayi daga dakinta kanta babu ko dankwali,gabanta yana mugun faduwa tace"kai Walidi menene kake mana ihu! ne"?

Banza yayi musu ya nufi dakin Balaraba da gudu, yana fadin" Aunty Balaraba Gimbiya ta gidan sarki! ki fito kinyi babban kamu, daga yau nine zan zama yaronki, Allah ya yanke min wahala"

Tana zaune kan dadduma hannuta rike da carbi idar da sallahr ta kenan, taji shi yafado mata daki yana mata sambatu,

Jin abunda Walidi yake fada yasa Lantana, bankada labulen dakin Balaraba da sauri ta shiga har tana kokarin faduwa, tace"kai Walidu me kunne na yaji kana fada ne"?

*Muje zuwa*

*Comment*
*Vote and Share*
[03/07, 14:29] +234 808 996 5176: 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻

∆∆∆∆∆∆
_*GIMBIYA BALARABA*_
∆∆∆∆∆∆
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻

_*NA*_
_BINTA UMAR ABBALE_

*MARUBCIYAR*
```Nana khadija```
```Yaro da kudi```
```Gimbiya Balaraba```

_*Zamani Writes Association*_🤝🏻

```Bisimillahir-rahamanir-rahim```

*🅿37*

_*Almuminu,Almuhaiminu ya Allah*_

Wani kallo Walidi yayi wa Lantana irin nasu na marasa tarbiya yace"kinga Lantana duk wani zancan bakin ciki da hassada ya kare, ni daga yau wallahi na dai na biye muku ku cuce ni, Balaraba dai Allah ya rufa mata asiri,dan Sarkin garin nan shine yazo gurinta gashi can a waje"
Lantana bata bari ta karasa jin zancan Walidi ba ta nufi hanyar waje tamkar zata kifa sabuda sauri,
Iya ce tayi sauri ta tari gabanta tace"ina zakije haka Lantana dubi jikinki babu zani daka ke sai dan tofi"

"So nake inje in ganewa idona zancan da Walidi yazo dashi"
Lantana ta karashe maganar tamkar wata zautacciya
Sadiya Matar Kawu tasa dariya tace"yanzu ke Lantana idan a kace ki futa haka sai ki futa,to in kin futa waje me zakiyi"?

Iya ta riko hannuta ta dawo da ita tsakar gida ta zaunar da ita kan tabarmar ta,sannan ta leka dakin Balaraba tace"me kike yi baki futo ba kije kiga ni ko waye"

A nutse tace"Iya babu inda zani ni domin ba muyi da wani zai zo gurina ba,sai dai idan wata Balarabar a ke nufi bani ba"

Walidi kamar ya dora hannu a ka yace"dan girman Allah aunty Balaraba kizo kije ku gaisa,kin san dai bazan miki karya ba, wallahi da gaske nake"

Shamsiyya ce ta shigo cikin gidan tana durawa Walidi zagi ta Uwa ta Uba, sai jan kafa takeyi, Mahaifiyar su ta gani tsaye bakin rijiya tayi shiru, kamar babu ita a gurin, cikin jin radadin zafin ciwo tace"Wallahi Uwa!yau sai nayiwa Walidi rashin mutumci, kinga yadda ya kona ni, yayi miki barna,gashi can duk ya zubar miki da awarar gaba daya"

Wani uban zagi Uwa!ta kurma tana kwalawa Walidi kira wanda yake dakin Balaraba yana tw zabga mata magiya kan ta taje gurin Maddibo.

"Wai me yake a cikin dakin waccan mutsiyaciyar ko tafara koya masa iskanci ne"
Shamsiyya tafada tana daga muryar ta dan Balarabar ta ji ta.

"Rabu da shashasha kwadayayye kawai,makarya cin banza da wofi wai dan Sarki ne yazo zance gurinta shine yazo yana yiwa mutane shirme"

"Kan Ubancan"!
Shamsiyya ta kurma wani uban zagi,ta cigaba da cewa" shine ya kona min jiki a kan waccan,wallahi bazan yadda ba,sai nayi musu wulakanci, wane dan Sarki kawai yace Farkanta ne ya biyo bayan ta meye ba mu sani ba"
ta karashe maganar tana buga cinyar ta

Lantada dake zaune kurum tun dazu bata ce uffan! ba tace"shiyasa ai nake so in futa in ci masa mutumci in koreshi, sabuda nasan babu wani mutum mai mutumci da zai zo gurin wannan lalatacciyar sai lalatacce, O ni Lantana,yanzu in da gaske ne dan Sarki ne yake son yarinyat nan ina zan sa kai na"
ta karashe maganar har da rike haba!
Sadiya matar Kawu tace"Ko wane irin miji Balaraba zata aura, duk mulkinsa da dukiyarsa gami da nasabar sa, Lantana baki isa ki hana abunda Ubangiji ya tsara a kan ta ba,Balaraba dai ta zama murucin kan dotse wallahi,bakin cikinku babu in da zashi a kanta"
Kuka Lantana tasa har da fyace majina tace"Ni kikewa rashin kunya Sadiya har kina kokarin zagina tsofai-tsofai da ni"

Uwa!ta tabe baki gami da cewa"muna furci dai dodo ya kanci meshi,ehe!! ai gashinan ke da kike daure mata gindi tana kokarin zaginki ,gaskiya naji dadin wannan abu"
Sadiya matar Kawu dakinta ta shige tace"gaskiya ce ba kyaso Lantana dole in fada miki"

Ganin Nacin! da Walidi yake mata ya ki karewa yasa ta mikewa tsaya har yanzu tana cikin hijab dinta har kasa ta kalleshi gami da cewa"muje shikkenan ai sai ka sakar min mara in sake"
Walidi ya washe baki gami da cewa"Yawwa matar Manya,aike yanzu kin zama kadara a gidan nan, ba irinsu wadancan "yan iskan ba"
Yana sane ya fada da karfi dan Shamsiyya taji,aiko ta ji shi, yana futowa ta dinga zaginsa, tana hadawa da Balarabar, shiru kawai Balaraba tayi mata,shi kuwa Walidi kallonta yayi shekeke!yace"mahaukaciya kawai a haka zaku shegu "yan iska, kawai" Da gudu Shamsiyya tabishi tana zaginsa, kamar wata "yar maguzawa, Balaraba tayi saurin kaucewa tabata hanya, tana mamakin ta tamkar wata dabba haka take ganin Shamsiyya sam!bata da nutsuwa balle kamun kai.
Tuni Walidi ya fuce daga gidan, sai ta tsaya bakin kofar gidan tana kalloshi yana tsaye can kusa Maddibo,ta dinga kurma masa zagi babu ji babu gani, sai da tayi mai isar ta sannan ta juya ta koma cikin gidan tana jan kafarta suka ci karo da Balaraba tana kokarin futowa,
Kaucewa tayi ta bata hanya a karo na biyu,ganin tana nema ta bangaje ta, tsayawa tayi ta na mata wani dan banzan kallo tace" Haka zaki kare,karuwa kawai"
Murmushi Balaraba tayi kawai ta raba ta gefenta ta wuce tabar ta tsaye a gurin,tana cizon ya tsa taso ta tanka mata suyi kokawa kamar yadda suka saba shekarun baya da suka wuce.

Can gefe ta hango Walidi tsaye da Wani mutum a tsaye,sabuda haka kai tsaye inda suke ta nufa cikin nutsuwa.
Chapter 19 · 0% Book details