← Book details Gimbiya Balaraba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 80

Sashe 18

Gimbiya Balaraba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wata Muguwar shadda ya dauko wagambari blue coulor anyi mata ire-iren dinkin da ake masa, wanda hausawa suke kira"yar shara, wani irin aiki akayiwa rigar da zare kalar shaddar, gaba da baya,in banda maiko babu abunda take, ya dauki agogo na zallar azurfa ya daura a hannunshi, bayan ya fesa turaranshi na ka'ida, kai tsaye inda takalmanshi suke jere ya nufa.
Anutse ya sanya wani takalmi shima mai bue colour duk jikinshi gashi, samanshi a rufe, duk dai ka na gani kasan na masu mulki ne,

Cikin nutsuwa ya fiti falon inda Maddibo yake zaune yana sauraron fitowarshi, ya kalli agogon hannunshi yace"ka kyauta tun misalin karfe takwas da minti biyar ka shiga ciki, sai yanzu ka fito dubi time, fa"
Yafada yana nuna masa wani dan kareran agogo dake manne a bangon dakin, ya cigaba da cewa"yanzu har yaushe mukaje mu ka dawo,ka zauna kana wani feleke a daki sai kace wani mace"
Fuskarshi ya shafa yana sosa Gemunshi,cikin sigar Zolaya yace"mutumin da zashi zance gun budurwa ai dole ya kimtsa duk da dai ni a matsayin dan rakiya zanje, kuma mai gabatar da kai kaga dole in tsaya in shirya sosai domin kada budurwar taka ta rai na mu, duba ka ganka dan Allah, duk kabi ka wani susuce, ni da zan maka jagora ma watakila in fika mutumci a gurunta"
Da sauri Maddibo ya kalli jikinshi yana so yaga inda ya kakare wanda har zai sa Balaraba, tayi masa mummunan kallo,
Shi kanshi sai da ya bawa kanshi dariya, ganin jallabiya ce a jikinshi tun ta dazu da safe, shaf ya manta da ana wata kwalliya in za'aje gurin budurwa shi dai burinshi kawai yaje yaga mutuniyar shi,
Dariya yasa, sosai Sarki! yana taya shi, yacr"kasan Allah na manta da cewar wannan rigar ce a jikina,in banda ka tuna min,bari in shiga in canza kaya yanzu in fito"
Tsaki!Sarki ya ja yana kokarin zama kan kujera, yace"Wallahi har na ka gara inje in ga yarinya nan da ka rude a kanta,
ka dai yi sauri lokaci yana tafiya"
"Yanzu zan fito insha Allah"
Maddibo yafada yana kokarin shiga bedroom din domin shiryawa.

*Comment*
*Vote and Share*
[01/07, 17:43] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻

∆∆∆∆∆∆
_*GIMBIYA BALARABA*_
∆∆∆∆∆∆
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻

_*Na*_
_BINTA UMAR ABBALE_

*MARUBUCIYAR*
```Nana khadija```
```Yaro da kudi```
```Gimbiya Balaraba```

Zamani Writes Association🤝🏻

```Bisimillahir rahamanir rahim```

*🅿35*

Tsaf Maddibo ya fito cikin wani yadi mai santsi anyi masa wani irin dinki a gaban rigar ya dora falmaran ita ma duk jikinta surfani ne, ire-iren kayan Sarki! kenan, wannan ma da Maddibo ya sa sabbi ne dal,a ledarsu, kafarshi sany da takalmi kwatankwacin na kafar Sarki! yayi kyau babu laifi,amma bai kai Sarki!Almansor ba, haka suka fita daga farlon suna hira,cike da kasaita Sarki!yake tafiya, yayin da hadiman gurin suke zubewa suna kwasar gaisuwa.
Direba shi ne ya taso da sauri ya nufi wata katuwar mota cikin jerin motocin dake aje a gurin a je motocin ya je ya bude yana sauraron karasowar su,
Zubewa yayi kasa hannushi a dunkule yace"ranka shi dade barka da fitowa,Allah yaja zamanin ka, Sarki!me jiran gado"
"Barka kadai Haladu, ya aiki"?
Yafada yana kokarin shiga motar,

" Alhamdulilahi ranka ya dade"
Haladu ya fada yana kallon Maddibo yace"barka da fitowa yallabai"
Maddibo ya mika masa hannu cikin barkwanci da wasa da dariya suka gaisa,sannan ya shiga mota ya zauna kusa da mutumin nashi,

Haladu ya kunna mota cikin nutsuwa suka fita daga gidan,

Hira suke irin ta abokansu wanda sukai yi karatu tare, Maddibo yace"kaga Harisu Galadima yaran shi uku kasan da mata biyu ya fara,jiya munyi waya dashi yake ce min daya amaryar tashi ma ciki gareta, zai na hudu, shi kuwa Yakuba Buba" dama kasan ya riga kowa aure yanzu in banyi karya ba sai in ce maka zai haifi yara biyar,duk da cewa matarshi daya"

A nutse yace"ka rabu da Harisu Galadima wannan ai mayen mata ne,ko ka manta lokacin muna skul yadda yakeyi in yaga mace,shege ji yakeyi kamar ya bita yayi mata fyade, in bai yi mace biyu ba me zai yi, muna nan da kai zakaji ance maka ya kara ta uku"
Dariya sukayi duk su biyun har da tafawa.
Maddibo ya gyara zama yana fuskantar Sarki! yace"kai ai ni in na samu wannan yarinyar nagama dacewa wallahi,nake gaya maka yarinyar ta cika mace ta ko wanne fanni, bazan iya yi mata kishiya ba"
Wani irin kallo yayi masa yace"yar towo-towo din ce kake wani cewa ta hada komai na mace wanda,kake so, kar fa ka mance cewar yarinyar "yar bakin kasuwa ce"
Shan kunu Maddibo yayi yace"Yasin zanyi maka rashin mutumci, wallahi Balaraba tafi karfin wulakanci a gurinka,kar ka kara ce mata "Yar bakin kasuwa"

Dariya ya sa har sai da dimful dinshi ya fito yace"Wallahi har ka tuna min da wata mara kunyar yarinya kwanakin baya, da sukayi saukar al'kurani,makarantar tasu ta kawo saukar gaban sarki, Sunanta Balaraba, bazan taba mantawa da kallon banzan da tayi min ba, kai in ka gani sai kayi mamaki, lokacin kana can Swiziland, abun ya bani mamaki, sosai"
Murmushi Maddibo yayi yace"nafada maka duk me wannan sunan ba karamar mace bace, mybe ka nuna mata halinka ne shiyasa ta nuna maka nasu halin"

Tabe baki yayi yana dan sosa sumar kanshi wanda hakan ya zame masa jiki in dai zai yi magana sai yw sosa kanshi yace"me ya dameni da ita,kasan ni mata basa gabana,wallahi, kai ni fa zan iya kare rayuwata batare da wata mace ba"

"Wannan kuma mahaukaci zaka fadawa wanda bai san wanene kai ba"

Dariya yasa ya dan sosa kai yace"Wallahi nake gaya maka yarinyar nan wai a na cewa gani na fito, ita ta riga kowa tashi domin ta ganni ina lure da ita, daga baya kuma ta fara yimin kallon banza,sai kace wani sa'an ta"
"Maddibo ya ce" ka ishemu da zan wata yarinya ko ka na ciki ne, dan ban taba ganin ka ka zauna zance wata ba,ko Halisa bata da wannan matsayin"
"Kai me zanyi da wannan yarinyar" yafada yana gyara fuska ya cigaba da cewa"kawai dai inai maka kwatance da ita ne, Allah yasa taka Balarabar ba irin halinsu daya da waccan din ba"

"Zamuje ka ganta ne ai sam tawa daban take da kowa"

"Ok Shikkenan, Allah yasa"

Nan suka cigaba da hira har suka karasa Unguwarsu Balaraba,

Maddibo ya kalli Haladu Direba yace"yi parking dai-dai can"
da sauri Haladu yayi parking din motar inda a ka umarce shi,

A nutse ya dago kanshi yana bin unguwar da kallo, Kallon Maddibi yayi yace"wannan wace irin unguwa ce ka kawo mu, guri duk tarkace da kazanta, ko ina kango,da kwatoci, kasan bazan fito ba wallahi,kaje kasa a kira maka ita"

Ajiyar zuciya Maddibo ya sauke domin yasan dole za suyi haka dashi, yace"kake maganar kango duk gidajan jama'a ne, duk babu wani kango a cikin nan unguwar, wannan tarkacen kuma da kake gani yaran unguwar ne suke sana'ar gwan-gwan"

Ya mutse fuska yayi yace"gaskiya Maddibo baka da kirki, yanzu da kasan a irin wannan unguwar budurwar taka take ka gayyoto ni,kamar baka san halayyata ba, kai yanzu ya dace"kazo ka nemi matar aure a irin wannan guri"?
"Kaga bana son ka bata min rai dan Allah, kafito mu shiga ga lukon gidansu can,yanzu duhun dare ne babu wanda zai gane ka"

"Billahillazi, babu inda zanje nayi iya yi na, in ka damu kai ka futa ka kurawo ta sai mu gaisa,amma bazan fita daga motar nan ba,haka kawai kwalabe su fasa min kafafu,kan wata shashashar budurwar ka wai ita Balaraba"
ya karashe maganar yana gyara kwanciya cikin motar babu abunda ya dame shi.

Sanin halin taurin kai irin na Sarki! yasa Maddibo jan tsaki ya bude motar ya fita sabuda yasab duk nacin da zai masa bazai fito ba kamar yadda ya fada

Dariya Sarki! yasa bayan fitar Maddibo daga cikin motar yace"duk Abinda zakayi kayi amma bazan fita in cuci kai na ba"

Haladu Direba ya fito ya tsaya a bakin motar yana kalle-kalle, ganin fitowar Maddibo, yasa ya karaso Maddibo yace"ka tsaya kawai zan fito zan shiga gurin can"

"A fito lafiya yallabai"

Haladu ya koma bakin mota ya tsaya,

Ganin motar gidan Sarauta yasa yara suka fara, taruwa

*Comment*
*Vote and Share*
[02/07, 14:47] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻

∆∆∆∆∆∆
_*GIMBIYA BALARABA*_
∆∆∆∆∆∆
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻

_*Na*_
_BINTA UMAR ABBALE_

*MARUBUCIYAR*
```Nana khadija```
```Yaro da kudi```
```Gimbiya Balaraba```

Zamani Writes Association🤝🏻

```Bisimillahir rahamanir rahim```

*🅿36*

Kasancewar babu wutar nepa a unguwar shiyasa yara basu ankara ba sosai, dabi'ar yaran cikin gari kenan in suka ga bak'o cikin mota zasu zo su tsaitsaya suna kallo wasunsu kuwa har zuwa suke su dinga taba motar suna dariya suna rugawa gida da gudu,Sarki!yana kwance cikin motar yana bin unguwar da kallo, cikin zuciyarsa yace"yanzu haka jama'ar dake cikinta suke rayuwa, wasu gidajan gasu nan duk babu kofofi, wasunsu an sanya musu buhu an kare sabuda kar a gano cikin gidan, a fili yace"da gani gurin zai yi sauro sabuda tarin shirgi da datti da kazanta, dole a kawowa unguwar a gaji,
Shi kadai yake wannan sake-saken cikin zuciyarsa, gefe guda kuma ya zaku yaga wannan yarinya da Maddibo ya makance a kanta.

A nutse Maddibo ya kutsa kansa cikin lungun su Balaraba wanda yake dauke da tarkace iri-iri haka ya dinga tsallake kananun langa-langa da robibi har ya karasa kofar gidansu Balaraba,inda yara da matasa suke tsaye kan Shamsiyya wacce take ta faman soya awara da kwai,
Gefe guda ya ja ya tsaya ya kira wani yaro wanda yake tsaye kan Shamsiyya yana jira ta sallame shi,
"Kai Salmanu ungo awarar taka, in sallame ka in huta"
Shamsiyya ce ta dago tana wa Salmanu magana,kawai sai ta ganshi ya nufi gurin wani mutum can gefe, fitilar wayarta ta kunna ta haske fuskar Maddibo tana wani ya mutse fuska tace"wancan wanene a tsaye a can ne"
Da Sauri Walidi dake tsugune kusa da ita yana zukar wani abu a tsumma ya mike yana wani ciccije baki yace"yana ina ne yanzu in farde masa ciki"!
"Gashi can naga ya kira Salmanu ko uban me zai yi masa oho! je ka gani"

Walidi na tafiya yana hada hanya ya nufi inda Maddibo ke tsaye tare da Salmanu
Chapter 18 · 0% Book details