← Book details Gimbiya Balaraba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 80

Sashe 75

Gimbiya Balaraba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Balaraba ta k'aware sosai gurin had'a dambun nama shiyasa sam bai bata wahala ba, nan ta had'a komai cikin abunda bai fi awa guda ba, k'amshi ne kawai yake tashi kicin d'in, zuba shi tayi cikin warmers ko wanne ta aje ta samu wani had'ad'an akushi irin na gidan sarauta ta cika shi da cake d'in da Dambu nama,wannan ta aje shi ne sai zasu tafi zata bashi, ruwa ta d'ora a wuta ta zuba kayan tea masu sa kamsh gahwa na'ana'a citta kanifari kimba da dai sauran su sai da ya gaja da tafasa sannan ta kashe gas d'in ta tace sosai ruwan tea d'in yayi kyau sai kamshi yake ta juye cikin fulas mai kyau. D'auka tayi ta kai falonta ta aje ta dawo ta gyara kicin din tas! Sannan ta dawo ta d'auki, d'auki abunda ta aje, kai tsaye part din shi ta nufa. Lokacin har su Shahid sun zo sun d'auko dashi k'asa yayi wanka shar dashi kana ganinsa kaga ango sosai yake walwala Shatima na tsokanar sa wai farin cikin me yake, shi kuma yana basarwa.
A nutse tayi sallama ta shigo, da sauri ya dago kanshi yana kallonta, saurin sunkuyar da kanta tayi, cikin mamaki ya bi hannuta da kallo, yana kallon yanayin tafiyar ta, Shatima ya amsa yana fad'in"Gimbiya sannu ki da zuw..... Katse shi yayi ta hanyar fad'in"Ka tsaya kana surutu ka karb'i abun hannuta mana,bata da lafiya" Balaraba tayi saurin kallonsa, cikin mamaki, da sauri ta wuce Shatima ya bi bayanta yana fad'in"Ayya! Gimbiya sannu da kokari kawo in aje miki daining d'in." Murmushi k'arfin hali tayi tace." Ka rabu dashi don ni lafiya talau fa." 'Yar dariya yayi yace." Ai naga alama gashi kin sha aiki domin ki faranta ran maigidan ki mybe yana so ki huta ne shiyasa Yace in karb'e ki" Shiru kawai tayi masa tana sunkuyar da kanta cike da kunya,wato Dole dai sai ya tona mata asiri gurin abokan shi,kome amfanin fad'a musu haka oho masa. Gyara gurin tayi sosai, Shahid ya kawo shi har gurin, idonsa a kanta yace." Wato nace kije ki huta shine kika wahalar da kanki ko." K'asa tayi da kanta kurum domin bata so tayi wata magar ya lafto wacce zai sa har su Shatima su gane. "Jimana" yafad'a yana tsare ta da ido, a nutse ta watsa masa wani kallo, Wanda ya shiga jikinsa,amma da yake ya saba karb'arsa sa'i da lokaci a gurin ta,sai ya dake! Yace." Bayan wahalar da kika sha jiya shine zaki na wahalar da jikin ki yanzu,wai ke bakya son hutu ne." ? Taikacinsa ya hanata cewa komai, sai aukin futo da warmers take, Shatima ya doki kafad'arsa yana fad'in." Kai kanai mata bak'in cikin ladan da zata samu ne, ina ruwan ka."? Shahid ya b'oye dariya yana fad'in"Lallai hausawa da sunyi gaskiya cikin karin maganar su, inda suke fad'in"Gurgu yafi...........Sarki! Ya galla masa harara! Dariya suka saka Shatima ya bashi hannu suka taga!Balaraba kamar ta nutse don kunya, simi-simi tabar gurin tana da ta sanin dawo da tasan tonan silili zai mata da bata dawo ba, dab da zata futa sai ga Mama ta shigo da jama'ar ta, sai ta tsaya tana murmushi , itama Mama murmushi ne a fuskarta, suka zauna cikin kujera Balaraba ta durkusa har kasa ta gaishe ta, cikin sakin fuska mama ta amsa tana tambayar me jiki, tace "Jiki alhamdullahi wallahi gashi yana k'okarin Mama muna sa ran samun nasara wannan tafiyar insha Allahu, Mama tace." Hakane dama babu abunda yafi k'arfin addu'a ai, jiya munyi waya da aminiya ta, Matar Sarkin Yalwa sosai mahaifinta dake Malami ne yasa yara 'yan makaranta na addu'a jiya an sauke al'kurani babu adadi"

Mama ta cigaba da cewa." Insha Allahu tanan zuwa itama,kin san bata samu damar zuwa gurin bukin ku ba tun dai da tazo lokacin mutuwar me Martaba." Balaraba tace." Kai angode sosai wallahi ai Mama alk'urani mai girma yana tattare da waraka ko wace iri ce ,mutukar mutum zai rike shi, to ya rike babban kundi." Mama tace." Haka maganar ki take Balaraba." Su Shahid ne suka k'araso gurin cikin nutsuwa suka tsuguna suna gaishe da ita, ta amsa musu da walwala a fuskarta tace." Ya mai jiki? Domin Ku zan tambaya." Shahid yace." Jiki alhamdullahi Mama kin ganshi zaune k'alau dashi,wannan kuma aikin Gimbiya ne ga tanan kusa dake." Cikin farin ciki Mama tace." Nasan zata aikata fiye da haka, k'okarin tura while chair d'in yake, da sauri Shatima yace." Kabari mana inzo." Ko saurarensa baiyi ba ya cigaba da turawa ya k'araso kusa dashi gami da kama while chair din yana fad'in"Da ka bari an turaka." "Akan me zan bari hannuna aikin me yake." Yafad'a ciki-ciki murmushi kawai Shatima yayi yana fad'in" Dama kai ai babu me iyawa da kai sai Balaraba."
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
_*GIMBIYA BALARABA*_
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻

~*NA*~
_BINTA UMAR ABBALE_
*BINTUBATULA👄*

*MARUBUCIYAR*

```NANA KHADIJA```
```YARO DA KUDI```
```GIMBIYA BALARABA```
```TSANTSAR BUTULCI```
```LADIDI K'WADAGA```

_*ZAMANI WRITES ASSOCIATON🤝🏻*_

_____________________
```We are here to educate motivate and entertain aur reades```
_______________________

*JAN KUNNE⚠*

_*Ban yarda a siyar min da d'aya daga cikin books d'in ba, duk mai buk'atarsu sai ya nemi numbar ta, ban yarda ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba kuma zamu tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha, ka nemi halak d'in ka yafi kaci da gumin wani, halak d'in ka shine mafi alkairi a gare ka.*_

*DEDICATED*
~*TO*~
*RAHAMA ALIYU*
~*ABUJA*~

_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_

*🅿114*

Shiru yayi masa har suka k'arasa kusa da Mama,ya fara k'okarin saukowa Mama tace." A'a kayi zaman ka kawai mu gaisa a haka lallai jiki yayi kyau,naji dadin ganin ka cikin walwala ubangiji Allah ya k'ara lafiya." Suka amsa da "Ameen" Cikin kauna irin ta d'a da uwarsa yace." Mama kin tashi lafiya."? Tace."Lafiya lau na tashi amma na kwanta da tunanin ka, shiyasa da na shigo na ganka cikin koshin lafiya naji dad'i kuma na godewa Balaraba." Sunkyar da kai kurrum yayi yana murmushi,tace." Ina fatan ka karya ko."? Balaraba tace." Ga kayan karin can kan daining." " To maza je ki d'auko masa in ga yaci a gabana." Kallon ta yayi yace." Mama sai kace wani k'aramin yaro." Murmushi tayi tace." K'aramin Yaro kake a gurina." Shahid yace." Wallahi hakane Mama mu yara ne a gaban iyayemu, Sarki! Shiru yayi yana kallon ikon Allah Mama tasa Balaraba ta had'a tea me kauri tace."fara bashi ya d'umama cikinsa." Balaraba ta mik'a masa kofin tae sai yak'i karb'a Mama tace." Ki cika ladanki mana." Sunkuyar da kanta tayi cike da kunya ta nufi bakinsa da cup d'in, a hankali ya bud'e bakinsa ya fara kurb'ar tea d'in, ji yayi sugar yayi yawa ga madara tayi yawa baya son k'arni, a hankali yace." Ki aje Wannan ki had'a min bak'i." Ajewa tayi kamar yadda yace ta fara had'a masa wani,hannu ya mik'a ya d'auki cake guda d'aya ya fara ci, sosai yayi masa dad'i a baki sai da ya cinye guda uku kafin taga ma motsa tea d'in yadda zai fi masa dad'i a baki ta fara bashi cike da kunya a idon Mama da su Shatima, Mama sam hankalin ta baya Kansu tana can tana magana da Jakadiyar ta, Su Shahid sai tsokanar sa suke yak'i tanka musu, a hankali ta dinga bashi yana kurba yana gutsirar cake d'in, sai da ya ci guda shida sannan ya d'aga mata hannu alamun ya ishe shi, tissue yake k'okarin yagowa, ta ya ciro masa mik'ewa tayi tana goge masa gefan bakinsa,ya tsura mata ido yana kallo, ita ko taki yadda su had'a ido dashi, Halisa da Azima ne suka shigo cikin wannan hali, turus sukayi ganin abunda yake faruwa kowacce jikinta yayi sanyi ga Mama a zaune ga uban tafiyar zaune cikin shiri Balaraba ta had'u sosai domin shigar ta ta yau tayi mata kyau, tana tsaye kusa dashi tana goge masa gefan bakinsa . Suka zazzauna jiki babu k'wari suna gaishe da Mama ta amsa musu a sake tana tambayar su me jiki, Azima da yake tafi Halisa wayo ta b'oye damuwar ta ta saki jiki suna hira dasu Shatima,har tana sa Balaraba a ciki kamar ba itace ta bangaje ta d'azu ba, ita ko Halisa sai shan kunu take tana hira da Mama kawai, cikin wannan hali me girma governor ya iso, suka gaisa da Mama cikin girmamawa, Halisa ta kalli Mama k'asa-k'asa tace." Mama ina gani tafiyar nan ayi ta dani domin yau girki na ne, kinga sai in kula dashi" Mama tace."aikuwa kin kawo shawara me kyau dama ya kamata a d'auki daya daga cikinku a tafi da ita, to amma kinga Balaraba bata futa daga lokacin ta ba, ina ganin da ita za'a tafi, in yaso in ya dawo sai ya sauka a dakin ki, kin gane ko"?

Halisa ta b'ata fuska bata ce komai. Me girma governor yaji dadin ganin jikin shi yayi kyau, sosai ba tare da wani b'ata lokaci ba, suka mik'e domin tafiya Shahid shine yake tura shi har suka futa harabar gidan jama'a a tsatstsaye Suna sauraron futuwarsu kowa na addu'a da fatan alkairi, tare da samun lafiya. Waziri na fada zaune shi da mutanan sa labari ya riske shi cewa gashi can an futo da Sarki! Zasu tafi Saudi'a sai ya kece da dariya yana fadin "Duk inda zasuje suje su dawo shida ya taka doran kasa da k'afafunshi to sai dai idan lahira yaje" mutanan sa suka ce "Wannan haka yake,takawar ka lafiya gyara kintsi dai!!!!!! Wani mugun dad'i ya rufe shi, jin yadda suke faman zuba masa kirari,abunda yake mutuwar so kenan a rayuwarsa.
Chapter 75 · 0% Book details