Sashe 41
Gimbiya Balaraba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cike da karsashi,da jarumta ta durfafi inda suke fuskarta a had'e tamkar wacce bata tab'a dariya ba, tana zuwa tafara yunk'urin fuzge hannun Sadiya daga cikin nasa, a nutse ya d'ago kanshi tare da zuba mata idanunsa,ya bud'e tar! Gabanta ya buga! sai kace mai lak'ani a idonsa, duk gwiwarta ta sage! kanta ta sunkuyar k'asa domin bazata iya jurar k'alon k'wayar idonsa ba, amma duk da haka bata fasa k'okarin fuzge hannun Sadiyar ba saboda k'arfin Hali, rik'e hannun yayi tsaf! da tazo zata k'wace sai su had'a hannu, sai ya had'a da hannun nata ya matse,ganin abun nasa harda iskanci, yasa ta fuzge hannunta tana zabga masa harara, batare da tabari ya gane gazawar ta ba,ta kalli Sadiya,cikin fad'a tace"zan kama ki,wallahi tunda kike barin maza suna rik'e miki hannu" barin gurin tayi a fusace,ta kama hannun Usuman suka haura sama.
Kallo ya bita dashi, fuskarsa d'auke da murmushi, girgiza kai yayi kawai yana mamakin k'uruciyar ta, yanzu ya gane itama yarinya ce, sakin hannun Sadiya yayi dake zaune tana mayar da k'walar da ta taro a idonta,saboda tasan halin masifar yayarta
Yace"kwantar da hankalin ki kinji ko Halimatu, duk abunda tayi miki in mun had'u zan rama miki, tashi kije" mik'ewa tayi jikinta a sanyaye, ta haura sama
Sai sannan ya mai da hankalinsa kan Halisa dake tsaye, tana cika tana batsewa duk wani abu da ya faru tsakanisa da Balaraba ta gani mussaman had'a hannu da suka yi"
B'ata fuska yayi kad'an yace'' kin zama dogariya ne,wai duk gurin zaman nan bai miki ba sai dai ki tsaya a kai na"
Cikin fushi tace"ai banga fuska ba, tunda ka kawo wacce kakeso har gida,ita kuma wannan mai sifar karuwan fa"
Hararata yayi yace"ki iya bakin ki wallahi ranki zai mugun b'aci a kan wannan yarinyar matar Moddibo ce in sha,Allahu"
Wata dariya ta shek'e da ita,ta nemi guri ta zauna, cikin jin dad'i tace" gaskiya Ya Yusuf ya iya zab'e tsaf wannan zata yi masa wayo dubi idonta,don Allah,wai me ma ya kawota shashen ka ne, kuma meyasa har ka zauna da ita da k'anwarta guri guda"
ta k'arasa maganar da damuwa!
"Sai ki bari sai ya zo sai ki tambaye shi,amma yanzu ni bani da lokacin baki wannan amsosin naki"
Mik'ewa yayi daga gurin ya barta zaune,babu shiri ta mik'e tana bin bayansa har ya zauna kan wata kujera me cin mutum d'aya, ta zauna a wacce take fuskantar sa, wata k'aramar drowar ya jawo k'asan kujerar ya futo da wani k'aramin littafi irin na addini yafara dubawa, tunda taga yayi wannan zaman tasan ba zai saurareta ba, duk abunda zatayi kuwa,dole ta jira ya kammala tukkuna, mintuna goma ta gaji da zaman gurin sai ta mik'e ta fa kaici idonsa, ta hau sama tana laluben inda Balaraba take, cikin sa'a ta ga wani d'aki a cikin d'akunan dake barandar a bud'e,kai tsaye d'akin ta nufa cikin k'asaita ta tura k'ofar da k'afarta,ta shiga babu sallama, Balaraba na zaune gefan gado ta cire hijab d'in, tana sanye da doguwar riga,cotton mai taushi,tana da yankakken hannu, sai tayi amfani da k'ara min hijab me hula, irin na Larabawa, tayi mugun kyau,kamar wata balarabiyar k'asar Oman, Halisa sai da Gabanta ya ganin ciki da k'asaitar Balaraba,fata luwai sai kace me rayuwa a kasar waje,ko ita albarka,ita da take rayuwa a cikin jin d'adi.
Dukkaninsu k'ofa suka kalla jin a bugo da k'arfi an shigo, dogarewa tayi bakin k'ofa tana watsa musu kallo, ta kalli Balaraba a k'asan kan ce,tace"zo ki rufe min k'ofar nan,ke me kama da "yayan bayi"!!
D'as!d'as!d'as! K'irjin Balaraba ya fara buga jin furucin Halisa, cikin sigar izgili da nuna ke awa! kuma baki isa ba,tace" a matsayin ki na wa! da har xaki bada umarni abi,ki bari sai kin kai matsayin zama cikkakun mutane sai ki bada umarni,amma dai yanzu baki isa ba"
"Ke ni kike fad'awa magana,har kike k'okarin zagina,munafukar Allah, ta'alah macuciya, an ga gidan sarauta an lallab'o, to bari kiji,shi kanshi Moddibo baza ki same shi ba,balle kuma Sarki! Wannan nawa ne ni d'aya"
Halisa ta k'arashe maganar tana dungurewa Balaraba kai, abunda Halisa bata sani ba shine ba'a nuna Balaraba da d'an yatsa,komai girman ka kuwa sai ta nuna maka ruwa ba,sa'an kwando bane,
Wani ba hagon mari ta tsinkawa Halisa a fusace! Sam!ba tayi tunanin abunda zai je ya dawo ba.
Ihu Halisa ta kurma! tayi kan Balaraba da duka sai zaginta take,abinka da sabo da fad'a tuni Balaraba ta tare ta,su kafara kokawa abun mamaki, nan Balaraba ta yar,da Halisa a k'asa, saboda ita bata iya fad'a ba,ga jikin Hutu,babu k'wari, sosai Halisa taji ciwon fad'uwar ta k'asa, ko da mik'e bata daddara ba,ta k'ara yin kan Balaraba a karo na biyu, tayi nasarar fuzge mata hijab d'in wuyanta ta cire hular kan nata,ta tattaro gashin kan Balaraba ta rik'e sai ja take,tana gaya mata maganganu na b'atanci kuma sai ta d'aure ta,tunda ta sake tayi kokawa da ita, Balaraba kuwa k'okarin kwatar kanta takeyi hannuta ta kama ta murd'e! da k'arfi, Halisa ta saki ihu,babu shiri ta sakar mata, kai tana duba hannunta tana cije baki, ki take kamar wacce tayi targad'e, ganin sunk'i su dai na fad'an yasa,Sadiya sauka k'asa da gudu, domin taje ta fad'awa Magajin Sarki, yana zaune,a inda yake,kanshi k'asa yana duba littafin hannun sa, ya ga Sadiya gabansa tana zare ido,d'ago kai yayi yana rufe littafin hannusa, yace"dukan ki tayi kike haki! haka"?
Girgiza kai tayi cikin tsoro tace" Yayarmu fad'a suke yi da wannan da tazo gun ka"
Falon yake bi da kallo, cikin mamaki, ina Neman Halisa,
M'ikewa yayi kawai ya rik'e hannun Sadiya suka nufi sama,
Yana tura k'ofar yaga abun mamaki da d'aure kai, Balaraba ce, rik'e da wuyan Halisa ta mak'ure a bango,ita kuma Halisa duk tayi wujiga-wujiga,sai k'okarin k'watar kanta take,ta kasa,idanunta duk sun firfito waje, k'arasawa yayi ciki har inda suke, batare da yace,komai ba ya fara, k'okarin b'anb'are hannun Balaraba dake wuyan Halisa, sanyi da taushin Hannunsa,suka sa ta dawo hayyacin ta, kallonsa tayi da idonta wanda suka kad'a saboda b'acin rai!
Hannunta ya matse cikin nasa,shima ya zuba mata idonsa,kamar yarda tayi masa, dafin! dake nasa idon ya fi nata,dole tasa, ta risinar da idonta, ta zare hannuta daga nasa ta koma gefe guda tana huci!
Halisa kuwa zubewa tayi a gurin tana nufarfashi,na wahala! Dariya ce take cinsa ganin yadda Halisa tayi wurjanjan, cikin yanayin maganar sa yace"Halisa,da ilimin ki da komai kike kokawa sai kace a jahiliyya,in ita ta saba da dambe,ke sai ki biye mata,gwara ma da tayi miki duka"
Yafad'a babu damuwa a tare da shi.
Hawayen b'akin ciki ne ya fara zubowa Halisa,tace"abunda zaka ce kenan ko"?
"To me zan ce miki me ya kawo ki gurin ta,ko na aiko ne"?
Mik'ewa tayi tana gyara alkyabar jikinta,tace" zaka ce na fad'a maka wannan k'ask'antacciyar bata isa ta dake ni a banza,ba tana a matsayin baiwa ta,wallahi sai na wulak'antata"
Siririn murmushi ya saki iya leb'anshi ya d'an kalli Balaraba kad'an sai kuma ya kauda kansa,ganin ta babu hula,ga botiran rigar jikinta duk sun zube, saboda fad'a duk saman k'irjinta a waje, Ki yayi yanayin jikinsa na sauyawa, Matsalar shi kenan shi mutuk'ar zai ga wani shashe na jikin "ya mace shikkenan sai sha'awarsa ta motsa, ya cije leb'anshi na k'asa kad'an yace" Wannan tafi k'arfi ki Halisa,kika tab'a ta kin tab'a zuciyar Moddibo,ki bari zan mishi magana ya ja mata kunne"
Hannunta ya rik'e suka fara tafiya, domin barin d'akin,tace"wato ni ba zuciyar ka bace,kenan har zaka kasa d'aukar mataki a kanta dubi irin dukan da tayi min"
Kamar zai yi dariya, yace"muje k'asa in rarrashe ki, ko" mamaki sosai yake na k'arfin halin Balaraba, kizo har gida kina fad'a da masu gida, da alama dai yarinyar tana da aljanu.
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
^^^^^^^^^^^^^^^^^^
_*GIMBIYA BALARABA*_
^^^^^^^^^^^^^^^^^^^
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
_*NA*_
_BINTA UMAR ABBALE_
*®BINTUBATULA👄*
_*MARUBUCIYAR*_
```Nana Khadija```
```Yaro Da kud'i```
```Gimbiya Balaraba```
_*ZAMANI WRITERS*_
_*ASSOCIATION🤝🏻*_
_*DEDIGATED*_
*_TO_*
```RAHAMA ALIYU```
```BISIMILLAHIR- RAHAMANIR-RAHIM```
*🅿64*
Da harara Balaraba ta bisu dashi,har suka futa, Sadiya ta matso kusa da "yar uwarta tana wasa da hannuta tace" don Allah yayarmu ki daina fad'a da ita baki ga ita "yar Sarki bace,kar ki jawo a kulle mu,kinji tana cewa sai ta d'aure ki"
Ta k'arashe maganar tana sharar hawaye
Tsawa! ta buga mata tace"rufe min baki,duk bake kika jawo ba, wallahi duk sanda na k'ara ganin kinje gurin wancan mutumin sai ranki ya b'aci,ki ko kiranki yayi kar kije"
Kwanciya tayi kan gadon tana kuka,Usuman yana taya ta,ita kuma Balaraba sai fad'a take mata.
Ko da Sarki! suka sauka k'asa da Halisa, zamansa yayi a inda ya tashi,ta k'araci k'orafe-k'orafen ta,bai ce mata komai ba, haka ta mik'e tana niyyar tafiya ranta duk a b'ace! ya d'ago kai a tsanake yace"koma ki zauna zamuyi magana"
Komawa tayi ta zauna, ya aje littafin dake hannusa,fuskarsa babu yabo babu fallasa yace"kin san Gimbiya Azima,"yar Sarkin Yalwa"?
Gabanta ya fad'i! jin sunan wacce ya fad'a ita kuwa tasan Gimbiya Azima,domin abokiyar fad'anta ce, basa shiri ko k'adan dalili kowa yana ji da izza! gami da tak'ama.
Bakinta na rawa tace"Eh nasanta"
"Yawwa itace zata zama abokiyar zaman ki in Allah ya yarda"
Wani irin yarrrr! ta ji ajikinta lokacin da taji abunda yace mak'ogaron ta ya bushe k'amas, tace"ban fahimci abunda kake nufi ba"
Wani irin kallo yayi mata yace"kin San bana magana biyu, kije kiyi tunanin maganar dana fad'a miki"
Kuka ta fashe! dashi kamar wacce a ka aiko mata cewar uwarta ta mutu, tace"yaushe har a k'ulla wannan al'amarin ban sani ba,kuma mahaifiyata bata sani ba,Dan anga cewar ita macace shiyasa har ake abu batare da saninta ba,wannan ai yaudara ce"
Cikin kuka ta k'arashe maganar.