Sashe 8
Gadar Tsautsayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Gaba ɗaya ɗakin zubawa Amra idanu suke yi, wadda take ta masifa ko mayar da numfashi bata yi, banda Roxy da take zaune a kusa da shisha ɗinta tana cigaba da zuƙa tana fitar da hayaƙi, fuskarta babu alamun damuwa ko kaɗan, Oga boss ya dubi Amra cikin jin takaicin wannan abu da ta yi,rai a ɗan ɓace ya ce"wannan abu da kika yi sam bai yi ba Amra!
Ita ce shugabarmu,kin ɗaga mata murya saboda kuɗinta, wanda ta nemo da wahalarta, tana biyan mu albashi wanda ya ishe mu shan sharafinmu,tana ɗaukar nauyin duk wani abu da muke buƙata,ina ganin wannan hayaniyar ba ki yi ta a inda ya dace da wanda ya dace a yiwa ba,hakan butulci ne
Sannan kar ki sake yi mata gorin addini, saboda itama tana da nata addinin,kuma ta yarda da abin da take bautawa"
A fusace Amra ta dube shi ta ce"malam ba da kai nake ba,da uwar ɗakin da kake neman gindin zama a wajenta nake"Oga boss zai sake magana Roxy ta ɗaga masa hannu, har yanzu bata kalli sashen da suke ba, asalima zuƙar hayaƙinta take yi hankali kwance
Miƙewa ta yi tana tafiya kamar mai rangaji, har ta isa gaban Amra, wadda hantar cikinta ta kaɗa ganin yanayin Roxy, Roxy ta yi wani killer smile tana kallonta, kafin ta fara magana cikin izza yadda ta saba
"Me kika ce ma?
Wai.....na kai ki gidan talakawa na wukaƙanta ki na gaya miki magana bla bla bla!
Ina son na tuna miki asali da tushenki ne!
Yes!!!so nake na tuna miki ke ma ba kowan kowa ba ce,ba Æ´ar kowa ba, face yar gidan malam Namadi mai kayan miya a gefen kasuwa,kuma na san kin tuna da hakan, that's okay for me
Sannan da kike maganar kin yi min aiki,aikin da waccan matar da kike kallo a matsayin ƙasƙantacciya ta yi min aikin da ko makamancinsa ba ki isa ki yi min ba, sannan wannan kuɗi nawa ne,Ni na yi wahala na samo shi,ke ma idan za ki iya go ahead and get yours, best of luck Madam monkey!"ta ƙarashe maganar tana bubbuga kafaɗarta ta dama
Har ta juya ta sake juyowa tana kallon Amra wadda ta ƙame a waje ɗaya, ba tare da damuwa ba ta ce"yawwa sai Maganar addini,ke wanne addinin kike bi tukunna?"
Ba Amra ba,hatta su Oga boss sai da suka razana suna kallonta cikin tsananin mamakin wannan tambayar,da ƙyar Oga boss ya dube ta ya ce"musulma ce mana"
Kallonsa ta yi tana murmushi ta ce"really Oga boss?
To menene shaidarka na addinin nata?sau nawa ka taɓa ganin ta yi Sallah?ka taɓa ganin ta tana azumi?"
Shiru suka yi gaba É—aya, Roxy ta ce"to bata da addini,kar ta sake yi min gorin addini, otherwise kuma wani abu mara daÉ—i ya biyo baya, I can't take that nonsense"
Shiru wajen ya ɗauka,don da alamu ran Roxy ya ɓaci, sai da ta ɓata kusan mintuna biyar tana danna waya sannan ta kalli David ta ce"David ya batun aikin da na ba ka?"
David ya numfasa ya ce"ma na gano kusan komai da ya danganci jami'in
Sunansa HAISAM Abdulmalik Madaka,mai riƙe da muƙamin CSO a hukumar DSS,mutum ne mai matuƙar ƙwazo da ƙawazuci a aikinsa,idan ya saka abu a gaba to tabbas sai ya ga bayansa,sai ya yi nasara akansa
Haka tarihinsa ya zo Ma'am "
Jinjina kai ta yi ta ce"uhumm!
Ina jin ka, cigaba mana"
David ya gyara zama ya cigaba"sai batun iyalansa,ya yi aure shekarun baya,amma zaman shekaru uku kawai suka yi da matar sakamakon matsaloli irin na cikin gida,sun rabu yanzu haka, Æ´arshi guda É—aya Rasheeda Haisam makawa, wadda suke kira da Amna tana hannunsa"
ÆŠan murmushi ta yi ta ce"wow! that's is very interesting,ina jin ka, cigaba"
"Ba shi da yaya ko ƙani,bashi da uwa,ta rasu,yana rayuwa tare da mahaifinsa Alhaji Abdulmalik Murtala Madaka, wanda ya kasance ɗan kwangila ne,kuma cikakken ɗan kasuwa,amma harkokin kasuwancin nashi sun fi yawa a Abuja da Lagos,da matar babansa hajiya Mariya Madaka,ita kuma babbar likita ce da take riƙe da asibiti nata na kanta"
Roxy ta jinjina kai ta ce"good job David,a ina suke da zama?"
"Suna zaune a Rocky estate ne"ya bata amsa"Roxy ta ɗaga kafaɗa tana taɓe baki tana murmushi ta ce "good,ina phone number ɗin tashi da na ce ka samo min?"
David ya ce "na tura miki ta Whatsapp"babu musu ta miƙe ba tare da ta sake magana ba,ta fito zuwa compound ɗin gidan,tana kallon yadda gari ya fara wayewa,don an ɗan kwashi lokaci da gabatar da Sallar asuba
Kamar mai nazari haka ta fara bin compound É—in da kallo, kafin kuma ta É—auke kai ta nufi backyard É—in gidan kai tsaye
*MALIYA ESTATE, KANO STATE, NIGERIA*
A yau iyalan suna cike da farin ciki da kewa kuma duka a tare, saboda tafiyar su Iman izuwa ƙasashen da za su je karatu,ita dai Ummeey duk da yadda ta zama mujiya a cikin iyayen yaran hakan bai hana ta cigaba da kawo gudunmawa ta ko'ina ba
Kasancewar ta san suna son kayan zaƙi tuni ta saka an shirya musu dubulan da alkaki,sai cake,aka yi packaging ɗinsu a bokitai masu kyau
Da kanta ta yi sallama ɗakin Hajiya Ruƙayya, inda ake ta shirya kayan da za'a tafi da su, Hajiya Sa'adatu da take zaune ita da Saleem suna sake shirya kayan tafiyar ta su ta ɗago kai tana kallon Ummeey gami da amsawa
Tana murmushi ta ajiye bucket ɗaya da take riƙe da shi,itama mai aikinta da ta riko sauran biyun ta ajiye,tana murmushin ta dubi Hajiya Sa'adatu ta ce
"Hajiya ga su nan,na ga yaran namu akwai son kayan zaƙi,shine na saka aka yi musu, Allah ya taimaka ya bayar da abin da ake nema"
Surayya da take fitowa daga É—aki, kasancewar ta fi kowa raini a cikinsu ta dube ta ta ce"an gode Ummeey,amma da ba ki bayar an yi ba,mun riga mun karbo wanda aka yi mana already, Allah ya saka,amma da kin tafi da shi"
Kallonta Ummeey ta yi, duk da cewa ranta ya sosu amma sai ta yi murmushi, kafin ta kai ga magana Hajiya Sa'adatu ta riga ta
"Amma abin da mamaki Hajiya Zainab,na ga dai lokacin da Shaheeda zata tafi zuwa karatun nata kamar ba kiyi mata wannan hidimar ta kayan zaƙi ba, gashi na kasa yarda cewa kin fi son yaranmu akan yadda kike sonta,don dai babu munafunci mu dai mun fi son yaranmu akanta "
Hajiya Ruƙayya da ta shigo ta dubi Hajiya Sa'adatu da sauri, wadda ta mayar da hankali kan Hajiya Zainab tana kallon reaction ɗinta tana fatan ta tanka, Hajiya Ruƙayya ta ce"kayya!
Ai yadda ta faɗa ɗin ne,ɗa na kowa ne,itama ai ƴaƴanta ne,ita ɗin mai iko da su ce, Hajiya, Allah ya amfana,an gode sosai, Allah ya bayyana Shaheeda "Hajiya Zainab ta yi ɗan murmushin yaƙe ba tare da ta yi magana ba ta juya ta nufi hanyar barin parlourn, ba tare da ta kula da kallon rainin da suka bi ta da shi ba
#Nusy_bee
Page 7
Da kallon banza Surayya ta bi ta, sannan ta dubi Hajiya Ruƙayya tana faɗin "Mamie wannan matar makira ce fa
Sai wani sumu-sumu take yi na munafurci
Duk abin da take yi da sanin Abba,ko ma na ce shine ya sahale mata,amma wallahi ba zata rinƙa taɓa Ni ina ƙyale ta ba"ta kalli buckets ɗin da Ummeey ta kawo ta yi fatali da ɗaya,alkakin da yake ciki ya zube,ta cigaba da sababi "yanzu haka ma wani barbaɗen ta yi a cikin wannan tarkacen da ta kawo kamar ana yunwa,ni wallahi komai da ta kawo min ma mayar mata shi zan yi,ta je ta bawa ƴarta, wadda mugun abin da take yi wa ƴaƴan mutane ya koma mata"
Hajiya Sa'adatu ta dube ta cikin kwantar da murya ta ce "kwantar da hankalinki Surayya,babu wanda ya isa ya yi muku wani mugun abu a duniya, yanzu ba sai anjuma zan mayar mata da kayanta,mu gaya mata ba ma bukata gaba É—aya,ki kwantar da hankalin ki"
Hajiya Ruƙayya ta dube ta ta ce"A'a Hajiya Sa'adatu!
Kar ta haÉ—a mu da alhaji,a maimakon haka gwara mu zubar a shara,idan ma wani mugun abin ta yi Allah ya mayar mata kanta, kamar yadda ya mayar mata wancan karon"
Iman da ta fito daga ɗakin ta taɓe baki tana cigaba da danna wayarta,ita yanzu lamarin matar nan ya daina ba ta mamaki ma
Tsam Saleem da yake kallonsu ya miƙe, ba tare da ya yi magana ba ya fice daga ɗakin,sauran suka bi shi da kallo, Hajiya Ruƙayya ta ce"ji shashasha!"
Iman ta ce"manta da shi Mamie,zai dawo hanya ne,na ga yana nuna cewa shi na Allah ne "
"Mu kuma na shaiÉ—an ne kenan?"a cewar Surayya tana watsa mata wani kallo
Dariya Iman ta yi ta ce"oh Allah!
Ni fa ba da ke nake ba,amma kin ga abar maganar,mu je mu ƙarasa shiryawa, jirginmu ya kusa ɗagawa"babu musu suka miƙe suka shiga don ƙarasa shiryawa
Bayan awa guda suka fito cikin shirinsu don tafiya, Ummeey ma ta fito lulluɓe da ƙaton mayafinta a kan tsadadden lace ɗinta,ta dube su tana murmushi, kafin ta ce"ƴan makaranta!
To Allah ya kai ku lafiya,kun yiwa drivern magana?"
Babu wanda ya kula ta,sai Saleem, É—a ga Alhaji Rufa'i ya É—ago yana kallonta, cikin girmamawa ya ce"ba driver bane zai kai mu Ummeey, Mummy ce,sai Mamie da zata raka mu"
Ummeey bata damu ba ta ce"to shikenan babu matsala,a wacce motar za mu tafi ne?"
Kai tsaye Hajiya Atika da ta zo wajen ta ce"a'a Hajiya Zainab,ba waje"ta dube su fuska babu walwala ta ce "ku wuce mu je ko?
Hajiya Zainab sai mun dawo mu kuma "
Jikin Ummeey a sanyaye ta ce"to Allah ya kai ku lafiya ya ba da abin da aka je nema,takwara, Allah ya tsare ya taimaka,a yi ta dagewa ko?
Allah ya kawo babban rabo na alkhairi"babu wanda ya sake kallon ta suka juya suka wuce suka bar ta a tsaye,har sun yi gaba Hajiya Sa'adatu ta dawo da baya,tana dubanta fuska a É—aure ta ce"au!