Sashe 12
Gadar Tsautsayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mintuna kaÉ—an ya fara magana"Awwal!gata nan mun haÉ—u,mun yi magana,kuma da alamu ma ba zata yi turjiya mai yawa ba za mu samo kanta,be ready, kowanne lokaci daga yanzu zata iya shiga hannu"Awwal ya sara masa a cikin wayar ya ce"best of luck Sir"
Bayan barazanar da ta yi masa na ƙwace wayar drivern Amna Haisam ya sauya taku na bincike akan ta,da kanshi, ba tare da sanin ƴan team ɗin nashi ba ya gano cewa tana shirin barin ƙasa zuwa Spain,sam bata san jirgi ɗaya suka hau da shi ba
Sai dai shi a maimakon Ibiza kai tsaye Barcelona ya nufa,ya cigaba da bincike a sirrance ta hanyar wasu yaran Roxy É—in da ya ba su wasu kuÉ—aÉ—e
Tsawon kwanaki shida ya É—auka yana tattara bayanai akan Roxy,sai dai har zuwa yanzu bai samu cikakken tabbacin daga inda Roxy ta fito ba,ya dai samu sunanta,da kuma tabbacin ita É—in Æ´ar Nigeria ce
Ya samu nasarar bincikar inda ya sauka a Ibiza,ya cigaba da bibiyarta,ta yi harƙalla da su Alejandro,asalima abin da ya kawo ta Spain kenan,inda ta damƙa kayan maye danginsu cocain waɗanda darajar su zata kai ta dala miliyan biyu a hannunsu
Ya kwashi wasu kwanaki yana bibiyarta,har sai da É—aya daga cikin yaranta, wadanda suke yi masa aiki a sirrance suka sanar masa kwanaki uku ya rage mata a Spain sannan ya tunkare ta bayan fitowarta daga Pacha Ibiza club
Wannan kenan!
💫
Washe gari tun da safe Haisam yake ta cuku-cukun yadda zai yi ya samu kan Roxy, wadda zuwa yanzu ya san sunanta,sai dai ba shi da guarantee akan komai da ya sani daga gare ta,kuma yana fatan bata san shi ba, ballantana hakan ya ba shi matsala,don ya tabbatar sai ya kama ta da ikon Allah
Da yamma ya gama shirinsa tsaf, yana jiran dare don tafiya club ɗin da suka haɗu da Roxy,ko a cikin boat ɗin da ya tsallakar da shi zuwa Balearic Island bincike da nazari yake yi, don ya san wacece wannan yarinyar wajen kaifin basira da iya taku, shekaru biyu ta ɗauka tana jijjiga hukumar tsaro,babu yadda za'a yi mutum mara basira da fikira ya iya yin hakan saboda ƙwarewa da sanin makamar aiki ta jami'an tsaron Nigeria
A inda ya saba gano ta ya ganta,tana zaune tana busa hayaƙinta na shisha kamar yadda ya saba, gefenta yaronta David ne,sai Oga boss,sai ƴarinyarta Hanna da suke ta yin hira suna shewa,amma ita hankalinta yana kan shishar da take zuƙa,sai wayar da take dannawa lokaci lokaci
Kai tsaye wajenta ya nufa yana faÉ—in "hi! Hermosa!"
Dukkansu É—agowa suka yi suna kallonsa kusan a tare,ban da ita,da ta É—ago daga baya hankalinta a kwance,ya yi murmushi yana faÉ—in "Barka!
Sorry za ki ga ina yi miki magana da Hausa,na fi son na rinƙa jin daɗin mu'amala da ɗan ƙasarmu da yaren ƙasarmu"
David da yake bin shi da kallon raini ya ce"wanene kai?"
Kai tsaye Haisam ya ce"ka bari mu gana da uwar É—akinka,ku ba mu waje"
Kusan a tare suka kalli Roxy wadda ta ja hayaƙin shisha ta fesa shi a fuskar Haisam da take kalla kai tsaye, kafin ta ce
"Ku ba mu waje,mu ji da me ya zo"babu musu suka miƙe suka bar wajen,shi kuma ya samu waje ya zauna yana fuskantar ta
"Beunas tardes!"(Good evening in Spanish)
Kallonshi ta yi, kamar ba zata yi magana ba sai kuma ta yi murmushi ta ce "ka gaji da yin yaren naka ne?sai ka ari na wani?"
ÆŠan murmushi ya yi shima,ya ce"kin san bahaushe ya ce idan mutum ya je gari ya ga kowa da jela,shima sai ya samu É—an zirin tsumma ya É—aura"ta jinjina kai tana faÉ—in"kenan kai ma É—aurawa ka yi dai ko?"
Ya É—an jinjina kai ya ce"kusan haka"
Ta ce"well!
Lafiya dai ko? menene dalilin da ya sa kake bi na?"
Kai tsaye ya ce"kasuwanci nake so mu yi,ina son na shigar da kaya zuwa Nigeria amma na gagara, saboda wahalar da hakan yake ba ni
Shine na zo na nemi alfarmar hakan daga gare ki,idan ma kina da wani connection É—in ko dabarar hakan I'm ready ki ba ni,don bana jin daÉ—in yadda ake kama min kaya,gashi kuÉ—aÉ—e da yawa nake asara"
#Nusy_bee
Page 10
Da kallo ta bi shi har ya gama jawabinsa ba tare da ta ce uffan ba,sai hayaƙin shishar da take cigaba da zuƙa tana fesarwa,sun kwashi kusan mintuna biyu cikakku a haka,bata yi magana ba,ta zuba masa idanu kawai tana cigaba da shan hayaƙinta,shi kuma ya yi shiru yana jiran amsarta
Zuwa can ta dube shi,kallon ƙasan idanu,ta ce"menene dalilin da ya sa ka fara business ba tare da kana da dabarun yin hakan ba?"
Murmushi ya yi yana gyara zama,ya ce"ai da ni da ke bambancin ya kai tsawon sama da ƙasa ranki ya daɗe
Ku ne manyan yan kasuwa,ku ne iyayen gidanmu a wannan harkar,why not ki yi min jagora,i bet za ki iya tsallakar min da kaya na"
ÆŠauke kai ta yi daga kallonsa tana jinjina kai,a hankali ta ce"yaushe ka shirya fita da kayan?"
Kamar mai jira ya ba ta amsa a É—okance"duk lokacin da kika tsara, yanzu feedback daga gare ki nake jira,ki gaya min maximum abin da za ki É—aukar min da abin da zan biya"
Miƙewa ta yi ba tare da ta kalle shi ba ta ce"mu yi magana next time, David zai karɓi phone number ɗinka,za ku yi magana da shi,akwai gidana na sirri da nake ganawa da baƙi, za'a kawo ka zuwa gobe, because I'm leaving this country in less than 48 hours "
Murmushin fuskarsa ya faÉ—aÉ—a,ya ce"alright, thanks very much ma!"bata kula shi ba,ta yi hanyar ficewa daga club É—in,ya bi ta da kallo yana murmushi, kafin ya fito da wayarsa
David ne ya ƙaraso inda yake, ba tare da ya yi masa magana ba ya miƙa masa hannu yana galla masa harara, Haisam ya miƙa masa complementary card ɗinsa ba tare da ya kalle shi ba, sannan ya miƙe ya nufi hanyar fita daga club ɗin
Washe gari tun da sassafe yake dakon kiran wayar Roxy,amma shiru babu wanda ya kira shi,har wajen sha É—aya na safe,a lokacin ya gama magana da su Awwal,sun yi shiri cif
Sai wajen ƙarfe biyu wayarshi ta yi ƙara,ya ɗaga yana duban wayar, unknown number ya gani,ba tare da damuwa ba ya ɗaga wayar
David ne a daƙile ya ce"kana ina ne?"
Kallon restaurant É—in da yake ya yi,ya ce"ina wani restaurant ne"
"Ya sunan restaurant É—in?"Haisam ya gaya masa
David ya ce "okay to yanzu ka fito zuwa bakin titi,ka bi hannunka na dama bayan ka tsallaka titi,ka yi doguwar tafiya,za ka same mu,sai mu karasa wajenta "
"Okay babu damuwa "ya faɗa yana miƙewa don ficewa daga wajen
Yana fita,ta cikin earbuds da suke kunnensa, ƙasa ƙasa ya furta"get ready Men!"suka amsa kusan a tare "yes sir!"
Kamar yadda David ya gaya masa,babu ɓata lokaci ya bi hanyar da ya kwatanta masa ba tare da tunanin komai ba,yana tafiya yana bin hanyar da kallo,don babu mutane
Daga can nesa ya hango David yana ɗaga masa hannu,kai tsaye ya miƙe don isa gare shi,amma me?
Kafin ya ƙarasa wani mutum da fuskarsa take a rufe ya dira a gabansa,kuma ba tare da ɓata lokaci ba ya hura masa wata powder a fuskarsa,babu ɓata lokaci ya sulale a wajen cikin fitar hayyaci, wanda shi kansa ba zai ce ga halin da ya shiga ba
Ba zai iya tuna lokacin da ya ɗauka a wannan halin ba, kafin Allah ya nufe shi da farfaɗowa,sai dai tun kafin ya gama wartsakewa ya ji shi a ɗaure gam gam, yadda numfashi ma sai da ƙyar yake iya yi
Dishi-dishi ya fara ganin mutane akansa,a hankali kuma ganinsa ya dawo tar-tar,ya ƙarewa kanshi kallo,inda yake ɗaure da wata ƙatuwar igiya, kafin ya kalli inda mutane suke
Su shida ne, Roxy da yaranta biyar, cikin su har da David da Hanna,sai kuma waÉ—anda ya biya kuÉ—i don su fallasa masa sirrin Roxy
Tasowa ta yi tana taku ɗaiɗai,tana murmushi,ta ƙaraso gabanshi ta durƙusa kusa da kanshi tana kallonsa tana sake waro kyawawan idanunta
"Hi!
Barka!!
Sunana Roxy,shahararriyar ƴar safarar miyagun ƙwayoyi daga ƙasa zuwa ƙasa, sannan kuma babbar ƴar yahoo, wadda jami'an tsaro suke nemanta ruwa a jallo
Yau dai gata ga jami'in tsaro, jami'in DSS"ta juya tana kallon su David tana murmushi,ya sunan nashi ma?"suka kusa haÉ—a baki"CSO Haisam Abdulmalik Madaka!"suka kwashe da dariya
Haisam dai yana kwance a ɗaɗɗaure yana kallonsu,gaba ɗaya ji yake yi ya muzanta,don tun daga yanzu ya fara ƙyanƙyaso cewa matar nan ta raina masa hankali ne,bai gama tunani ba ta cigaba da magana bayan ta miƙe tsaye tana aika masa wani irin kallo
"Na san jami'an tsaro suna nemana sama da shekaru,a tunaninka ni wawiya ce zan zuba idanu ina zuƙar shisha da fasa accounts ɗin mutane ina shagali?then you are mistaken dude!!
Yadda kuke bibiya ta haka nake bibiyarku. Tun lokacin da ka amshi wannan case ɗin,ka ce a ba ka wata guda don ka kama ni nake bibiyarka,gashi watan yana so ya ƙare,amma har yanzu babu labarin kama ni, infact,don ma na sa ka ji ka kusa cimma burinka ya sa na haɗa maka wannan trap ɗin
Na san kana cikin jirgin da na biyo zuwa Spain,amma da muka sauka a Barcelona kai sai ba ka biyo ni Ibiza ba, kafin ka ƙaraso izuwa Pacha Ibiza club ranar farko akwai yarana da suke kular min da shige da ficenka sun sanar da ni, lokacin da ka zo,muka haɗu a farko na saka an sake yi min bincike akanka,har yaran da ka zo da su, Finally, lokacin da kake waya kana communicating da naka yaran na yi hacking wayar, na ji komai,don haka na bari ka gama shirinka, sannan nima na zo da nawa shirin, wanda ya fi naka
Yarana da suka ba ka hint akaina don ka kama ni ni na ba su umarnin su yi hakan,don ka haƙa ramin da zan jefa ka da kanka,kuma gashi a ƙarshe na yi nasara
I repeated proudly N-
O-