← Book details Gadar Tsautsayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 51

Sashe 17

Gadar Tsautsayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abin haushi, yarinyar da criminal ce, nemanta ake yi ruwa a jallo amma zata yi min haka, sai na tona mata asiri a wajen yan sanda wallahi"Hassy dai bata ce komai ba, Amra ta cigaba da faffaɗar maganganu, saboda ranta a tsananin ɓacin rai da take ciki

*ROXY*

A hankali take buɗe idanunta da take ganin dishi-dishi,ga jikinta ta ji ya yi sanyi babu ƙwari ko kaɗan,amma hakan bai hana ta yunƙurin tashi zaune ba tana sauke numfashi da ƙyar

Ji ta yi an riƙe ta,an mayar da ita ta kwanta,ta dubi matar Oga boss da take riƙe da ita tana murmushi ta ce"sorry Ma'am!

Jikinki babu ƙwari, ba'a juma da cire bullet ɗin da aka harbe ki ba, relax ma'am "

Kallonta ta yi ta ce"ina Oga boss?

A ina ya gan ni?"

Matar Oga boss ta ce"a gefen hanya,da ƙyar muka gano ki,mun yi yawo sosai,sai kuma muka ganki a sume,shine muka dauko ki muka kawo ki nan,tun jiya da dare muka yi magana da likita ya zo ya duba ki ya cire miki bullet ɗin hannunki"Roxy ta kalli hannun nata ba tare da ta yi magana ba,ta sake dubanta ta ce"Azeema ina Oga boss?"

Azeema ta ce"yana parlour"

"Kira min shi"ta faÉ—a ba tare da ta kalle ta ba

Babu musu Azeema ta juya ta fice daga ɗakin don kiran Oga boss, Roxy ta zauna sosai,ta lumshe idanunta, komai da ya faru yana dawo mata ƙwaƙwalwa tiryan-tiryan

ÆŠan murmushi ta yi tana tuna cin amanar da Amra ta yi mata,ta girgiza kai kawai,a ranta ita kadai ta san me ta shirya mata

Tana nan zaune su Oga boss suka shigo ɗakin,da sauri ya ƙaraso yana faɗin"sannu ma'am!

Ya jikin?"

Kallonsa ta yi ta ce"Oga boss wani aiki nake so ka yi min,amma da Azeema za mu haÉ—a!"

Waje ya samu ya zauna yana faÉ—in"okay ma!

Wanne aiki ne?"

Lumshe idanu ta yi ta buÉ—e, sannan ta fara yi masa bayani a nutse,a razane Oga boss yake kallonta, ba tare da shakka ko tsoro ba ta ce"eh haka nake so

So nake na hukunta Amra,ina son a yau ta san wacece Roxy!"

Jinjina kai ya yi,ya dubi Azeema ya ce"za ki iya?"

Cikin bayar da tabbaci ta jinjina kai,ta ce"zan samu masu taya ni ma ranki ya daÉ—e

Ke ce fa kika ba mu sutura, kika ba mu dukkan farin cikin rayuwa,raina ne kawai ba zan iya ba ki ba"

Cikin kwantar da murya Oga boss ya ce"amma kuma akwai haÉ—ari a cikin wannan aikin ranki ya daÉ—e,ga na nakasarwa idan an samu matsala

Ba za'a chanja hukuncin da wani ba kuwa?"

Kallonsa Roxy ta yi, cikin yanayin ɓacin rai ta ce "ka san wacece Roxy,babu wanda zai gaya maka halina ko da ace David da muke tare kusan koyaushe

Ka san abin da na fi tsana,to me yasa Amra zata ci amanata?

Na san Amra cikakkiyar karuwa ce kuma Æ´ar lesbian,amma a haka nake tare da ita duk da ni bana ra'ayin hakan,amma meyasa dole sai ta yi forcing É—ina na yi abin da ban yi niyya ba?

Duk da cewa Amra bata cancanta ba amma ina girmama shekarunta,don na san ba ta kusa da sa'a ta ba ce,amma a ƙarshe ta zubar da ragowar girman da nake ganinta da shi ta ci amanata,amma kuma zan shayar da ita mamaki tabbas,na yi wannan alƙawarin!!

#Nusy_bee

Page 14

Shiru Oga boss da Azeema suka yi suna kallonta, Roxy bata damu ba,ta koma ta kwanta saboda nauyin da ta ji kanta yana yi mata,a hankali ta ce"Azeema ki nemi masu taya ki É—in,zan tsara muku yadda za kuyi"Azeema ta rissina tana faÉ—in "noted ma'am!"

Roxy ba ta sake magana ba ta koma ta kwanta,su kuma suka fice daga É—akin

Hannun Azeema Oga boss ya riƙo yana faɗin "ke wai ba ki da hankali ne?

Ya za ki biye mata don tana cikin ɓacin rai da ciwo?

Kin san girman kasadar da kika É—auko kuwa?

Ko ba ki yi tunanin abin da kan iya kai wa ya dawo ba bayan aiwatar da wannan É—anyen aikin?"

Azeema ta yi murmushi tana girgiza kai ta ce"sanin kanka ne Roxy bata yin abu ya kwaɓe mata,bayan haka ka san bata juyawa baya akan ra'ayinta, sannan kuma abin da ta yi mana ba zai ba ni dama na juya mata baya ba,tabbas sai na cika mata burinta,sai na hukunta mata wannan azzalumar matar da ta yaudare ta ta cuce ta, karuwar banza kawai"

Oga boss ya jinina kai yana kallonta yana murmushi, kafin ya ce "to Allah ya bada Sa'a"Azeema ta shige É—akin da Roxy take kwance tana faÉ—in "Ameen"

*ROCKY ESTATE, KANO STATE*

"Barka da dawowa Alhaji!"juyawa ya yi yana kallon mai aikin Hajiya Mariya da take gyara dinning area,ya ce"Barka dai,ina Amna?

Ko ta koma wajen Nanny É—inta?"

Ta ce"Amna tana wajen Hajiya Nimra,suna sashenka"Haisam ya ji kamar ya ɗora hannu aka ya ƙwala ihu, ba tare da ya yi magana ba ya juya ya fice daga sashen

A parlourn shi ya samu Nimra da Amna a zaune suna kallo,kallo ɗaya ya yiwa Nimra da ta tsuke cikin kayan bacci,ta saki gashin kanta gadon bayanta,ya ɗauke kanshi,ta miƙe tana kwantar da Amna da take bacci,ta nufi inda take tana taku ɗaiɗai tana girgiza jikinta, cikin karairaya ta ce"welcome sweetheart!

Tun É—azu ina ta jiranka "

Kallonta ya yi ya ɗauke kai,ta ƙaraso tana daf da rungume shi ya kauce,ta tsaya tana kwaɓe fuska kamar zata yi kuka

Bai sake kula ta ba ya ɗauki Amna ya wuce da ita wajen Nanny ɗinta, Nimra bata yi zuciya ba ta bi shi,har ya ƙarasa wajen Nanny ɗin Amna,tana fitowa Nimra ta sake biyo shi

Tsayawa ya yi fuska a É—aure ya ce"ya dai?

I hope everything is fine"

"So nake mu yi magana"ta faɗa a shagwaɓe

"Sai da safe ma yi maganar"yana faÉ—a ya wuce don komawa sashenshi

"But you promise me za mu yi magana idan ka dawo"ta faÉ—a tana biyo shi da sauri

"Sai da safe" ya faÉ—a ba tare da ya kalle ta ba"

"Ai gobe ma fita za kayi ba tare da na sani ba"bai saurare ta ba ya shige sashen shi, amma kafin ya shiga parlourn ta biyo shi

Cikin ƙosawa ya kalle ta ya ce "ina haɗa ki da Allah ki yi haƙuri gobe za mu tattauna, yanzu kin ga akwai aikin da zan yi,idan kika zo kika yi interrupting ɗina za ki iya janyo min matsala,na yi Miki alƙawarin zan saurare ki mu yi maganar"

Ba a son ranta ba ta juya ta fice daga sashen,ya shige parlourn shi ya rufe ƙofa yana jan tsaki

Ya tsani naci,ita kuma wannan akwai ta da nacin tsiya

Yana zama ya fara kiran Saleem,babu jumawa Saleem ya É—aga kiran

"I'm sorry Saleem!

ÆŠazu na ga kiranka,bana cikin yanayin da zan iya É—agawa ne"

Murmushi Saleem ya yi,ya ce"ba yawa yallaɓai,ai na san yanayin aikin

Na samo address É—in iyalan marigayi Malam tajo,dama shine abin da na kira na gaya maka kenan"

"Good job Saleem!tura min"

"Okay Sir "daga nan suka yi sallama

Ko da Saleem ya tura address ɗin Haisam ya daɗe yana mamakin inda ta luluƙa ta kai su,ya yi murmushi yana girgiza kai,a hankali ya ce"Allah sarki yarinya!

Ƙarshenki kuma ya zo kenan,sai dai na ce mu haɗu kawai nan gaba kaɗan "

*MALIYA ESTATE*

"Zan fita "É—aga kai ya yi yana kallon Arfa da take a shirye tsaf, rungume da Zuhra, cikin kwanciyar hankali tana sanar masa zata fita"

A fusace ya ce"a gidanku haka aka koya miki tarbiyyar tambayar miji idan za ki fita?sai da kika shirya kika gama komai sannan za ki wani tambaye ni za ki fita?"

"Wanne mentality É—in naka ne ya gaya maka tambayarka nake yi Muyassar?

Ai ba Ni kaÉ—ai ba ce aka yi missing koya min abubuwa da yawa a gidanmu,kai ma kamar ka samu lack of home training,tunda na ga baka san darajar aure ba,baka san darajar mace ba,asalima kai babu abin da ka sani sai tunanin karuwa da son kanka, don haka nima a bar ni na yi abin da na ga dama"

Muyassar ya girgiza kai, yanzu ya daina mamaki idan Arfa tana yi masa rashin arziƙi, saboda yadda ta samu cikakken goyon baya daga wajen wadda take faɗawa maganganu duk sanda suka samu matsala,wato mahaifiyarsa Hajiya Sa'adatu

Bai sake yi mata magana ba,yana kallo ta fice daga gidan,yana zaune bai tashi ba sai da ya ji ƙarar motarta, sannan ya miƙe jiki a mace ya ƙarasa jikin window yana leƙen waje

Shi mutum ne mai son hutu da kwanciyar hankali,yana son soyayya da kulawa,amma babu wadda yake samu daga wajen Arfa zai tsabar kishi da zargi,bayan haka bata iya komai ba

Ya rasa menene dalilin da ya sa mahaifiyarsa take matuƙar son su Arfa,don akan Arfa ba ƙaramin ci masa mutunci ta yi ba,sai da ya ji komai ya fice masa a rayuwa

Ga masifar soyayyar Shaheeda da take taso masa tana hana shi sukuni,ko a yau da zai ganta da wallahi sai ya aure ta,sai dai duk abin da zai faru ya faru,ba damuwarsa ba ce

Ya daɗe a wajen yana karanta wasiƙar jaki game da rayuwarshi da shaheedansa, kafin ya fice daga parlourn don barin gidan,a ranshi yana jin da yana da wani wajen da zai rinƙa zuwa yana yin zamansa ko ma ya kwana da ya je,ya huta da ganin Arfa, wadda har yanzu daidai da second ɗaya bai taɓa sonta ba

*ROXY*

Yau kwana biyu kenan da samun tsautsayin da ta yi, jikinta ya yi kyau sosai,har ma ta cigaba da yin kananan ayyukanta da system É—in Oga boss

Da kanta ta shiryawa Azeema yadda zata yi da zarar ta je gidan Amra,don tuni sun biya ta ƙungiyar su Amra ɗin,da ta tara manyan mata da yan mata,duk wadda kake so a kai maka,to an yi matuƙar Sa'a Amra ta buƙaci a kawo mata Azeema, wadda ta sauya suna zuwa star girl,dama tuni Roxy ta san irin matan da Amra take kwaɗayi irin su Azeema ne,don haka abin ya yi mata daidai ba tare da wata matsala ba

Cikin wasu tsinannun kaya Azeema ta shirya, Roxy tana daga zaune tana kallonta tana É—an murmushi, kafin ta ce"Good!
Chapter 17 · 0% Book details