Sashe 23
Gadar Tsautsayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Aunty ba ki ga irin wulaƙancin da Muyassar ya yi min ba saboda waccan tsilar koɗaɗɗiyar yarinyar
Har zagina fa ya yi ya hankaÉ—a ni waje, gaskiya ni ba zan iya lamuntar wannan rashin mutuncin ba"
Hajiya Ruƙayya ta ce"a'a dole gaskiya a ɗauki mataki kam,kuma ke ma ai sai da na ce ki bar komai a hannuna,za mu tattauna da uwar amma kika ƙi,idan kuma kika cigaba da zuwa yana ci miki mutunci ni babu ruwana"
"Amma aunty kin san irin son da nake yi masa,kuma shima ba ga alamu yana so na,kawai wani ƙulumboton waccan tsinanniyar yarinyar da uwarta suka yi ya guje ni"
"Idan ma ƙulumboton ne ni na san yadda zan yi ai
Yanzu ki kwantar da hankalinki,da kaina zan yi masa magana in sha Allah,idan kika ga bai aure ki ba to sai dai idan mutuwa ya yi,amma in sha Allah aure tsakaninku kamar an yi an gama ne
Ki daina damuwa da wannan ƙwailar yarinyar, saboda ko da ace sonta yake yi kamar yadda kike zargi ni na san Mahaifiyarsa ba zata taɓa bari ya aure ta ba"
Wata wawiyar ajiyar zuciya Arfa ta yi,ta ce"ko aunty?
Amma menene dalilin?"
Kai tsaye Hajiya Ruƙayya ta ce"babu jituwa tsakanin Hajiya Zainab da Hajiya Sa'adatu ne,shine dalilin
Shekarun baya da Hajiya Sa'adatu ta zauna anan Alhaji ya fifita matarshi akanta, shine ya sa take jin haushinta "shiru Arfa ta yi tana taɓe baki
Daga lokacin babu wanda ya sake shiga harkar wani tsakanin Shaheeda da Arfa, musamman da Muyassar ya samu Shaheeda ya yi mata faɗan duk abin da Arfa zata yi mata kar ta sake tayar da kai ta kalle ta, murmushi dai kawai Shaheedan ta yi masa a lokacin,amma ta gama ƙudurcewa a ranta duk lokacin da Arfa ta sake shiga harkarta sai ta ganar da ita kurenta, don wallahi sai ta yi mata duka a tsakiyar gidan,sai dai komai zai faru sai ya faru daga baya
Sai kuma aka yi sa'a babu wanda ya sake shiga harkar juna a cikin su biyun,asalima kwanan Arfa biyu da zuwa ta koma gidansu
Tafiya ta miƙa, lokaci ya yi ta ƙaratowa na tafiyar Shaheeda zuwa Belgium, murna da farin ciki kuwa a wajen Shaheeda ba'a magana,ji take yi babu ya ita a farin ciki,ga Muyassar mai sake zuga ta
Sai dai a matan gidan babu wadda take farin ciki da wannan tafiyar,amma babu halin bayyanawa,duk da cewa Shaheeda ta san da cewa ummeey bata son tafiyar Tata amma ko a jikinta
Kwana biyu ya rage jirgin su Aneesa ya ɗaga zuwa garin Ghent da ke ƙasar Belgium inda zata fara karatunta na course ɗin software engineering,idan Muyassar yana kiranta da software engineer har wani blushing take yi
Yau zata koma kasuwa don siyan kayan tsarabarta kafin ta saba da Belgium,dangin su chaculate da biscuits da suka zama sune farin cikinta, Muyassar baya nan,yana gidansu,don haka ta kira shi a waya,kai tsaye ya ce ta biyo ta gidansu sai ya kai ta
Driver ne ya kai ta har bakin gate É—in,ta kalli drivern ta ce"baba Nuhu kawai ka tafi, babban yaya zai dawo da ni idan mun gama"
Drivern ya ce "to babu matsala Hajiya"Shaheeda ta fice daga motar ta kutsa kai cikin gidan
Hajiya Sa'adatu mahaifiyar Muyassar tana zaune a parlourn,tare da innayyo,kakarsu,ta daɗe da sanin su dukkansu babu mai ƙaunarta,amma ko a jikinta,tana ganin yadda mahaifiyarta take kuka saboda sun yi mata wani abin,amma ita gani take yi Ummeey bata yi niyyar ramawa bane,ta kan ce"gaskiya Ummeey wani lokacin gani suke yi kin cika yi musu shiru shiyasa suke yi miki abin da suka ga dama,amma wallahi da ni ce babu wadda ta isa ta taka ni ban murza ta ba,ko wacece kuwa, innayyo kawai zan iya ɗagawa ƙafa darajar auren ɗanta da nice ke"
Ummeey ta kan ce"ke ƴarinya ce Shaheeda,da kin gane da kin ɗauka, haƙuri shine komai, shine maganin komai,da sannu komai zai wuce, duniyar ma nawa take?"Shaheeda ta kan taɓe baki, wannan azancin na Ummeey ba wani gane kansa take yi ba
Sau uku tana yin sallama amma babu mai niyyar amsa mata,asalima cigaba da hira suka yi tamkar ba su san da Allah ya yi halittarta a wajen ba, Shaheeda ta taɓe baki ta ce"Allah ma ya gani na yi domin shi"ba tare da tunanin komai ba ta kutsa kai cikin falon ba tare da ta sake yin wata sallamar ba
A fusace Mummy mahaifiyar Muyassar ta É—ago tana kallonta kafin ta ce"mara tarbiyya uban wanene ya ba ki izinin shigowa cikin falon nan?"
Tana da abin faɗa,amma sai ta danne ta ce"yaya Muyassar ne ya ce na zo zai kai ni kasuwa,za mu ƙarasa siyayyar da za mu tafi Belgium "aunty Salma da ta shigo ta yi ƴar dariya tana faɗin "ai kuwa bakin naki ya iya faɗar Belgium ɗin!
Ke dai ubanki ya dage sai kin bar ƙasa,bayan ga makarantu nan masu kyau a Nigeria,to Allah ya bada sa'a,don Allah kar ki ba su kunya Shaheeda, kin ga dai uban kuɗin da ya kashe wajen nemar miki gurbin nan"ta karasa magana tana zama akan ɗaya daga cikin kujerun falon
Shaheeda ta yi murmushi,amma kafin ta yi magana a fusace Mummy ta ce"wannan tambaÉ—aÉ—É—iyar yarinyar dama kin daina bata bakinki Salma,amma ni ban ga alamun wani karatu da za'a yi anan wajen ba, sannan ki tashi ki fice daga gidan nan idan dai ba na ubanki bane"
#Nusy_bee
Page 19
Ƴar dariya Shaheeda ta yi tana faɗin "A'a fa Mummy,gida dai na ubana ne,kawai dai ba'a ciki yake ba ne,kuma ma,ni da na zo don na tafi?ai tafiya tawa ce"
Bin ta suka yi da kallo cike mamaki da takaici,sanannen abu ne cewa Shaheeda bata da kunya,shine dalilin da ya sa kaf matan ubanta babu mai ɗaga mata yatsa,amma ba su yi tsammanin zata iya kallonsu ta yi musu wannan wulaƙancin ba
"Ke Shaheeda!uwata da yayar tawa kike gayawa magana?ba ki da kunya?"
Yatsina fuska ta yi ta ce"aunty yi haƙuri"
Mummy cikin kufula ta ce"sai na yi maganinki mara mutunci matsiyaciya kawai!
Shegiya mara amfani"miƙewa ta yi tsaye tana mayar da wayarta jaka tana faɗin "a'a fa Mummy!ina da amfani wallahi"daidai lokacin Muyassar ya shigo
A kunnensa ta faÉ—a,don haka a kufule ya fara faÉ—in "Shaheeda mahaifiyata kike yi wa rashin kunya?"
Babu tsoro ko shakka ta ce "cewa ta yi bani da amfani,ni kuma na san ina da amfani,ni gida ma zan tafi ba zan zauna a rinƙa tsine min ana kwashe min albarka ba,bayan uwata da ubana ba su kwashe min ba,sai anjumanku"ta wuce ta gaban Muyassar ta fice daga parlourn,suka bi ta da kallo
Shima bin ta ya yi ganin ta ɗauki hanyar gate,ya ce"Shaheeda dakata anan,idan kika fice daga gidan nan sai na yi mugun saɓa miki"babu musu ta ja ta tsaya fuska a murtuke
Mota ya koma ya É—auko,yana zuwa daidai saitin da take ta buÉ—e ta shiga tana kumbure-kumbure
FaÉ—a ya yi ta yi mata har suka isa super market É—in da za su je,sai huci take yi amma bata yi magana ba,shima daga baya ya gaji ya yi banza da ita
Duk da fushin da take yi hakan bai hana ta sakin jiki ta yi siyayyarta ba, Muyassar ya biya kuÉ—in suka kwashi kayan zuwa mota
Har cikin gidan ya shigar da motarshi,har suka shiga babu wanda ya yiwa wani magana,sai da ya tsayar da motarshi ya juya yana dubanta,ko kallonshi bata yi ba ta fara yunƙurin buɗe motar ta fita
Naɗe hannayensa ya yi a ƙirji yana kallon yadda take ta kokawa da mota, saboda bai cire lock ba,kuma ta san da hakan,amma saboda neman magana irin nata take ta kokawa da motar
"Zan fita,ka buÉ—e min motar"ta faÉ—a tana sake É—aure fuska
"Ba zan buÉ—e ba, ba kina da hannu ba? buÉ—e da kanki"
Tura baki ta yi,ya sauke numfashi sannan ya kira sunanta"Fatima!"
Tana kumburi ta ce "na'am!"
"Ba ni hankalinki my Teema"
Bata yi magana ba ta juyo amma bata kalle shi ba,ya fara yi mata nasiha cikin nutsuwa da kwantar da kai,ta yi shiru tana jin shi, duk da cewa jin shi kawai take yi,amma gaba É—aya nasihar iska take bi
Sai da ya ga alamu kamar bata tare da shi sannan ya ce"Shaheeda anya kina ji na kuwa?"
Gyara zama ta yi ta ce"ina jin ka mana,ka ce na daina faɗa manya suna faɗa ko?ko da ace sune suka yi min laifi na yi haƙuri"sai kuma dariya ta ƙwace mata, don maganar tashi gaba ɗaya a gwaranci ma take jin ta
"Au dariya ma na ba ki Shaheeda?
Ina magana kina yi min dariya?"
Girgiza kai ta yi tana murmushi ta ce"a'a,wani abu na tuna,na gode yayana "kallonta kawai ya yi yana girgiza kai,ya san halinta abu ne mai wahala ta sauya
Tana shiga part ɗin su kai tsaye ta wuce zuwa ɗakinta ta ajiye kayanta,ta fito tana ƙokarin kiran Ummeey, wadda ta san bata nan,tana gidan aminiyarta Hajiya jameela, wadda ta zama tamkar ƴar'uwarta uwa ɗaya uba ɗaya
Bugu biyu ta ɗaga,ta shagwaɓe fuska tana faɗin"Ummeey har yanzu ba ki dawo ba?"
"Ke bana son iskancin nan naki!ke ba yanzu kika dawo ba?kar ki ɓata min rai,ki ɗauki abinci ki ci, sannan ki ƙarasa gyara min kitchen ɗina,sai na dawo"ta kashe wayar
Shaheeda ta miƙe tana murmushi ta ce"wai abinci,sai ka ce wata cus!ga chaculate da yaya ya siya min me zan yi da wani abinci?"ta ɗebo chaculate ta dawo parlourn ta kunna TV tana kallo tana cin abinta
Da daddare bayan ta idar da sallar isha'i, tana zaune akan dardumar tana game a wayarta Ummeey ta leƙo,ta dube ta ta ce"Shaheeda sako hijabinki,ki zo abbanku yana son ganinki"babu musu ta miƙe,ta janyo hijabin da ta yi Sallah ta saka,suka fice zuwa sashen mahaifinta Alhaji Yusuf
Da sallama suka shiga parlourn abban nata, Shaheeda ta bi mutanen parlourn da kallo,bata yi mamaki ba,don ta san hakan zai iya faruwa dabam
Ummeey ce dai ta tsorata, saboda da ganin yanayin fuskokinsu ta san akwai abin da ya kawo su wanda ba mai daÉ—i ba, musamman da ya kasance Shaheeda ta je gidan nasu yau