Sashe 28
Gadar Tsautsayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da sauri ta kalle shi cikin tsananin mamaki,ya jinjina kai cike da ƙwarin gwiwa,ya ce"soyayyar da nake yi miki zan iya sadaukar miki da komai,ciki har da addinina ma"
Ihun murna sosai ta yi tana godewa Allah, cikin tsananin farin ciki ta ce"na yi maka alƙawari,muddin ka musulunta ni kuma kai ne zaɓina,kaine komai nawa,ina sonka,ina matuƙar sonka Arnold"shima murmushi ya yi jikinsa a sanyaye,ta gyara zama ta ce"wanne suna za ka koma idan ka musulunta?"
Kai tsaye ya ce"duk wanda kika zaɓa min a shirye nake na karɓe shi "Shaheeda ta miƙe tsaye tana murmushi ta ce"tukunna dai, akwai wani course mate ɗina,yana karantar da mu addini sosai,zan kai ka ya ba ka kalmar shahada zuwa anjuma in sha Allah, welcome to the religion of peace sweetheart!"ta karasa faɗa tana murmushi, sannan ta miƙe tsaye,ya raka ta har bakin hostel ɗin su,sai murmushi suke yi cikin tsananin farin ciki
Muyassar ta fara sanarwa da cewa Arnold zai musulunta,bai nuna mata komai ba a wayar,ya yi masa fatan alkhairi kawai, sannan ya sanar mata da zuwansa zuwa gobe don ya mayar da ita gida
Bayan magriba da kanta ta zo har garden ɗin makarantar inda ɗalibai masu nacin karatu suke yawan zuwa,inda Arnold ya saba zama,ta ja shi suka tafi wajen Sheikh Mukhtar,wani course mate ɗinta ɗan asalin ƙasar Oman don a laƙanawa Arnold kalmar shahada
Da kanta ta yi wa Sheikh Mukhtar bayani, shi kanshi ya yi mamakin yadda Arnold ya yarda zai musulunta saboda Shaheeda farat É—aya,don ya san su Arnold iri su ne waÉ—anda suke da tsananin tsauri a addinin kiristanci
Hakan bai hana shi farin ciki ba, ba tare da ɓata lokaci ba ya karantowa Arnold kalmar shahada, Arnold ya maimaita, aka ɗauki kabbara cikin farin ciki
Daga nan kuma aka tambaye shi sunan da yake so a saka masa,tana murmushi ya nuna Shaheeda, wadda take jin kamar an yi mata gafara saboda tsananin farin ciki, Shaheeda tana murmushi ta ce "a sanya masa suna MUBARAK!"
Murmushi ya yi yana kallonta, Shaikh Mukhtar ya cigaba da yi masa bayanan abubuwan da suke Shari'a ne,bayan ya gama ya dubi Shaheeda ya ce"malama Fatima za ki iya ƙarasa yi masa sauran bayanin,don na san kin san abubuwa da yawa, Allah ya saka miki da alkhairi"Shaheeda ta yi murmushi, Sannan ta yi musu sallama suka tashi ita da Arnold suka tafi
Har bakin hostel É—in su ta kai shi tana murmushi,shi ma murmushi yake yi,ta ce"I'm proud of you Mubarak!
Kuma ina tare da kai duk runtsi,na san tarihin soyayya ba zai manta da mu ba"Mubarak yana dariya ya ce"na san sai an sake updating Romeo da Juliet,kuma mu za mu zama updated ones É—in"dariya ta yi sosai,suka yi sallama,ta tafi shi kuma ya shiga hostel É—in su
Washe gari tun safe suke a tare,tana sake wayar masa da kai akan abin da ya shafi addinin Musulunci, kasancewar ya saka kanshi sai gashi yana ganewa sosai
Ko da Muyassar ya zo don tafiya da ita kiri-kiri ta shaida masa ita ta fasa tafiya,ba zata koma Nigeria yanzu ba,da ya tambaye ta dalili kai tsaye ta ce "yaya ka ga Mubarak jiya ya karɓi musulunci,yana buƙatar koyon al'amuran addini sosai,kuma ka ga ni ya sani,ya kamata na zauna na koya masa"
A kufule Muyassar ya ce "Shaheeda yarinta tana damunki wallahi!
Ina malamin da ya ba shi shahadar?ki kai shi wajensa mana,ko shi bai san yadda ake koyarwar bane?sai ke uwar iyayi da neman suna?"
Tana kumbura baki ta ce"ni dai yaya gaskiya ba zan tafi na bar shi ba,ba gaya maka yana buƙatar kulawata, sannan yaya ka daina ce min yarinya, I'm matured enough, eighteen years nake don haka don Allah a daina ce min yarinya"
Gaban Muyassar ya faɗi sosai, don ya fara hangen wani abu dabam,ya daure ya ƙaƙaro murmushi yana faɗin "da alamu dai baby sister ta kamu ko?"
"Yaya kamuwa kamar yaya?"ta jefa masa tambaya
Kai tsaye ya ce"kin kamu da soyayyar abokinki mana,gashi nan da yake ta karɓe ki har ƙiba kike yi abinki "
Ga mamakinsa sai gani ya yi tana murmushi sosai, ta ce"yaya soyayya akwai daÉ—i,kai ma ya kamata ka samu wadda zata dace da kai, you Will enjoy it ina gaya maka"
Tashin hankali! Muyassar ji ya yi kanshi yana juyawa,amma ya dake ya kalle ta ya ce"ai ni tuntuni na sami tawa sahibar zuciyar "
Shaheeda tana murmushi ta ce"wow!
A ina take yaya?tana da kirki?"
Kai tsaye ya ce"anan take,kai tsaye ma zan ce gata nan, ƙanwata,abar so na da alfaharina,farin cikin raina FATIMA SHAHEEDA!!!"
shiru ta yi na É—an lokaci tana bin Muyassar da kallo idanu waje kamar ta ga wata sabuwar halitta, kafin ta yi ta maza, murya a dashe"yaya ka san me bakinka yake faÉ—a kuwa?"
"Na sani sosai Shaheeda,ba ki sani ba ko?
To da soyayyarki na rayu,tun daga lokacin da na fara riƙe ki a hannuna kina jaririya a raina nake jin na samu matar da nake so, kowacce daƙiƙa ta rayuwata tunda kika zo duniya da tsananin soyayyarki nake bugun numfashi Shaheeda,ke ce farin cikina,ke ce ruhina,don haka Please Fatima, don't break my heart Please, I love you so much my Queen!"
#Nusy_bee
Page 23
Kamar wadda ake controlling da remote ta fara girgiza kai cikin sauri hawaye yana zubo mata,da ƙyar cikin in ina ta fara faɗin "a'a!
A'a yaya!yaya don Allah ka daina, yaya ta yaya za kace kana so na?yaya ka tuna,nice fa kanwarka wadda kake ji da ita,ka yi min alƙawarin za ka tsaya min a komai,yaya idan ka ce za ka aure ni ai ba za ka samu damar tsaya min ba,don Allah yaya kar ka yi min haka,yaya let's change this topic please,don Allah yaya!"
Muyassar ya ƙarasa inda take da sauri, cikin tashin hankali ya riƙo hannunta,muryarsa tana rarrabewa ya ce "Please Shaheeda!
Please!!don Allah kar ki yi min haka,ban san yadda zan yi ba idan kika rabu da ni"ta runtse idanu ta ce "ka tanadi yadda za kayi yaya,don wallahi bana sonka!bana son aurenka!! Mubarak shine abin da zuciyata take so kuma take muradi,yaya don Allah kar ka yi abin da zan tsane ka,yaya ina sonka,kai ɗin best friend ɗina ne,kar ka zama rival a gare ni, Please yaya!!!"tana kai wa nan ta fizge hannayenta daga na Muyassar ta ruga zuwa hostel ɗin su, wani irin tashin hankali da ɓacin rai kawai take ji,da gaske take jin sam abin babu tsari wai Muyassar yana sonta da aure, mutumin da ta ɗauke shi tamkar wanda suka fito ciki ɗaya
Arnold da yake zaune a gefe yana kallonsu,yana jin abin da suke cewa,amma kasancewar da Hausa suke magana ba ya fahimta,sai dai kuma ya fahimci cewa ko ma akan me suke magana ba mai daÉ—i bane
Muyassar ya bi Shaheeda da kallo cikin tashin hankali, kafin ya ɗauke kai,ya nufi inda Arnold yake zaune yana kallonsa, Arnold duk da ya fahimci Muyassar ba ya sonsa,amma ganin ya zo sai ya saki fara'a yana miƙewa don su gaisa,amma Muyassar yana zuwa ya nuna shi da yatsa, cikin harshen turanci ya fara magana
"Bana son na ji dalilin da ya sa kake tare da ƙanwata,amma bana son na sake yi maka kashedi akan ka rabu da ita,idan ka kuskura ka lalata min ƙanwata za ka gane bani da kyau, muddin ka yaudare ta sai na yi maka abin da za kayi nadamar zuwa duniya, ka je ka nemi daidai kai,amma ƙanwata ta fi ƙarfinka!"ya karasa faɗa yana hankaɗa shi
Hankalin Arnold ya tashi sosai,har Muyassar ya yi gaba ya zo ya sha gabansa kamar zai yi kuka yana faɗin "don Allah ka saurare ni,da gaske so nake na auri ƙanwarka,na musulunta ma ko ba ta gaya maka ba?"
Muyassar ya tsaya ya kalle shi cikin idanu ya ce"ka musulunta saboda ka auri ƙanwata ko?
To ka koma addininka na baya,amma ƙanwata ba zata taɓa aurenka ba"ya bangaje shi ya wuce, Arnold ya bi shi da kallo cikin tashin hankali
Abu Kamar wasa ƙaramar magana ta zama babba,don Muyassar kai tsaye da ya koma Nigeria ya sanar da Abba abin da yake faruwa, hankalin Abba da Ummeey ya tashi sosai, Hajiya Ruƙayya da labarin ya yi matuƙar yi mata daɗi tana murmushi ta ce
"Ai dama matsalar da ake samu kenan idan mace ta ce zata tafi ƙasar waje ba wani nata don ta yi karatu,to Allah ya sa ma ba su yi watsewarsu ba"
Abba ya kalle ta fuska a ɗaure ya ce"in sha Allah watsewa sai dai ki ganta akanki,ba akan Shaheeda ba"Hajiya Ruƙayya ta taɓe baki ba tare da ta sake magana ba
Washe gari Abba da kanshi ya je Belgium,a lokacin har Shaheeda ta yi kukan ta gama,sun sake komawa da Arnold wanda ya koma Mubarak, tare suke karatu,su yi hira tare,sai dai bai taɓa zuwa inda take ba,itama haka
Hankalin Daddy ya tashi sosai, saboda ya fuskanci soyayyar da take tsananinsu ta yi nisa sosai,kuma ta nuna masa kiri-kiri so take ta auri Arnold, wanda ya koma Mubarak yanzu
Tana kuka take faÉ—in "Abba saboda ni ya musulunta,ina sonshi sosai Abba,don Allah Abba kar ka raba mu"
Abba ya ja numfashi cikin damuwa ya ce "Fatima!na farko dai yaron nan ban yarda da tabbacin Musuluncinsa ba,don ya musulunta ne saboda ya aure ki,ba saboda Allah ba,na biyu ko da ace ya musulunta saboda Allah sai dai ya yi haƙuri, don na riga na yi alƙawarin aurenki ga Muyassar,don haka zan same shi mu yi magana,ba zan aura masa ke ba"
Ihun kuka sosai Shaheeda take yi tana roƙon Abba kar ya hana ta auren Mubarak, Alhaji Yusuf da Alhaji Aliyu da suka tafi tare hankalinsu ya tashi sosai,a ranar suka tattara Shaheeda suka mayar da ita gida, Alhaji Yusuf ya yi rantsuwa akan ta gama karatun
Kamar taɓaɓɓiya haka suka dawo da ita, Abba ya wuce da ita sashensa,tana kuka tana kiran don Allah a bar ta ta auri Mubarak
Duk yadda ya so ya yi mata bayani ya yi,amma hakan ya ƙi aiki,dama Shaheeda akwai kafiya,akwai ta da gardama da tsayuwa akan ra'ayinta,hakan ne ya fusata Alhaji Yusuf,ya sa aka ƙwace wayarta,aka rufe ta a sashen Ummeey