Sashe 32
Gadar Tsautsayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kai tsaye ta ce "eh,nima É—an'uwana musulmi na aura,don sai da na tabbatar da cewa Arnold ya musulunta sannan na aure shi"
Kai tsaye Diego ya girgiza kai ya ce "Arnold bai musulunta ba,kuma ba zai taɓa musulunta ba,asalima babu abin da ya tsana kamar addinin Musulunci, lokacin da ya nuna mana yana sha'awar auren musulma dariya muka yi ta yi masa saboda mun san yadda ya tsani musulunci,sai ya ce mana so yake yi ya mayar da ke addininmu na Christianity,amma kuma sai na fuskanci ba haka bane daga gare ki,don kamar ke ce kika rinjaye shi
Sai dai Arnold bai fasa bin addininsa na Christianity ba,don......"
"Dakata! Diego dakata min!!
Me kake cewa ne?
Ƙarya kake yi, Mubarak ba zai yaudare ni ba,don......"
"Kira shi da sunansa Arnold,kuma ko kin yarda ko ba ki yarda ba addinin iyayensa yake bi ba na matarsa ba,idan ba ki yarda ba kuma za ki iya yi masa dukkan gwajin da kike ganin za ki gamsu,na bar ki lafiya "ya miƙe ya fice ba tare da ya sake saurarenta ba
Wani irin tashin hankali da firgici irin wanda bata taɓa samun kanta a ciki bane ya ziyarce ta,kai wannan maganar ma ƙarya ne, Mubarak ɗinta ba zai taɓa yi mata haka ba
Gumi ne ya rinƙa karyo mata,ta miƙe ta kama safa da marwa,wani irin tashin hankali yana sake rufe ta
Eh tabbas ba abin mamaki bane idan ya kasance Mubarak yaudararta ya yi da sunan ya karɓi musulunci don ya aure ta,na farko bai damu da duk irin shigar da ta yi ba idan zata fita,wani lokacin ma shine yake zaɓar mata kayan da za su nuna surar jikinta, Sai dai idan ita ce ta sauya,na biyu kuma sam bai damu da ibada ba,sallar asuba ma sam ba ya tashi,duk haƙurinsa da yadda yake sonta idan ta tashe shi faɗa suke yi,a dalilin haka ma ta daina tashinsa
Share gumi ta yi tana samun waje ta zauna,ai yau azumi ya rage saura kwanaki biyar a fara shi,don haka zata gani idan zai yi ko ba zai yi ba
Tana nan zaune har ya shigo gidan,ta É—aga kai tana kallonsa,ya yi murmushi, cikin harshen Spanish ya ce"na yi kewar kyakkyawar matata,ya jikin,kuma ya É—an jaririnmu?"
Ɗaurewa ta yi ta ƙaƙaro murmushi ta ce"kewarka yake yi,ya karaso inda take ya rungume ta yana kissing goshinta,ya zauna a kusa da ita ya ce"ya dai?
Na ga kin zama wani iri"
Ta kwantar da kanta a jikin kujerar da take zaune ta ce"bana jin daɗi ne"janyo ta ya yi jikinsa ya rungume ta ya ce"ya kamata ki kwanta ki huta hakanan"bata yi masa magana ba ta miƙe ta shiga banɗaki
Alwala ta É—auro ta zo ta yi sallar maghriba da isha'i da ta kubce mata,yana zaune yana kallonta, sannan ta kwanta ta lumshe idanunta tana sauke ajiyar zuciya
Daga lokacin bata sake cewa ya yi sallah ba,tana kallonsa kawai,ba zai hana ta ba, Sai dai ya yi ta bin ta da kallo,duk da cewa zuwa yanzu ta fara gano wannan kallon ma yana da manufa
Lokacin da azumi ya zo ta sanar da shi,amma sai ya birkice kan cewa ba zata yi ba, saboda cikin jikinta,ita kuma ta dage kan cewa sai ta yi,hakan ya haifar musu da gagarumar rigima, cikin fusata da rufewar idanu ya ce"haka addinin naku yake babu tausayi?da ciki ma sai kin yi azumi?
To sai kin ajiye azumin!dole ma ki bar addinin nan,don tabbas ba zai yiwu ki illatar min da ciki saboda addini ba"
Wani kallo Shaheeda take yi masa bakinta yana rawa,ta ce"Mubarak!no Arnold!!!
Dama ba ka koma musulunci ba?da gaske yaudara ta ka yi don ka aure ni?"
#Nusy_bee
Page 26
Shiru ya yi ba tare da ya ba ta amsa ba, cikin É—aga murya ta ce"tambayarka nake yi Arnold!dama yaudarata kake yi?ba musulunta ka yi ba dama?
Har ka da na aure ka?ka bani amsa!"
Kallonta ya yi ya watsar ba tare da ya yi magana ba,sai kuma ya miƙe zai bar wajen, cikin gushewar hankali Shaheeda ta shaƙo masa wuya tana faɗin "ka cuce ni,ka cutar da ni,ka halaka min rayuwata,ka mayar da ni inda ka ɗauko ni,ba zan sake kwana da kai a cikin gidan nan ba,na tsane ka,na tsane ka...."hankaɗe ta ya yi,ta yi baya taga-taga, amma kafin ta faɗi ya yi saurin riƙo ta, cikin idanunta yake kallo,a hankali ya furta "a tsawon watannin da muka ɗauka muna rayuwa tare da ke a cikin farin ciki a gidan nan kowa yana bin addininsa ne,don haka yanzun ma za mu iya cigaba,kowa ya cigaba da bin addininsa,amma tabbas na aure ki don ina sonki,kuma zaman aure yanzu muka fara da ke,ya rage naki ki karɓi addinina ko ki cigaba da bin naki,amma zama da ni yanzu kika fara"ya zaunar da ita a gefen gadon dake ɗakin sannan ya juya ya fice daga ɗakin
Cikin tashin hankali mai tsanani ta bi shi da kallo,kukan ma da take yi tuni ya tsaya sai sauke ajihar zuciya da take yi,a hankali hawaye suka zubo mata,tana tuna maganar yayanta Muyassar
"Ya musulunta ne don Allah ko ya musulunta ne don zai aure ki?"
Ya yaudare ta kenan?in dai haka ne ai babu aure a tsakaninsu yanzu,tuni kuka ya kubce mata,take ta fara wata iriyar nadama,ta gudu ta bar abbanta da yake bala'in sonta,ta bar Ummeenta da ita kaɗai ta mallaka,ta bar masoyi na ƙwarai Muyassar ta biyo maƙaryaci, mayaudari, munafiki kuma azzalumi,to yanzu ya zata yi?
Da wanne ido zata kalli iyayenta a lokacin da ta koma gare su?
Da wanne idanu zata kalli Muyassar masoyinta, wanda ya so ta so na gaskiya,ya ƙaunace ta,ya zama gatanta?
Take ta fashe da kuka sosai, ta jinginar da kanta jikin bango tana rera kuka zuciyarta cike da nadama da danasani
Bata sake saka Arnold a idanunta ba,sai bayan kwana uku,a lokacin da aka É—auki azumin farko,tana idar da sallar la'asar ya shigo yana bin ta da kallo
Kallonsa take yi itama,bata yi mamakin kwanakin da ya ɗauka baya nan ba, dama wani lokacin idan aiki ya riƙe shi a company yana yin waɗannan kwanakin,amma su kan yi waya,sai dai wannan karon ba su yi wayar ba saboda ta kashe tata wayar
Kallonta yake yi cikin kulawa yana murmushi,da alamu ma ya manta abin da ya faru kafin ya fice ya bar gidan
Cikin kulawa ya ce"ba ki da lafiya ne?ko dai baby ne yake wahalar min da ke?"banza ta yi masa,bai yi fushi ba ya miƙe ya tafi kitchen,jum kaɗan sai ga shi ya dawo hannunsa riƙe da Plate mai ɗauke da wani nau'in wainar kwai da dankali,yana zuwa ya ajiye a gabanta,ya sa cokali ya ɗiba ya kai bakinta
Kallon abincin ta yi ta ɗauke kai, murya ƙasa-ƙasa ya ce "ki ci abinci mana,kin san ya kamata ki rinƙa yawan cin abinci fa"
Tana kwance kai tsaye ta ce"na gaya maka azumi nake yi"
"Azumi?
Azumi kika ce?
Ba na gaya miki ba za kiyi azumin nan ba?
To ko ki ci abinci ko ranki ya ɓaci"
Kai tsaye ta dube shi ta ce"ɓacin rai kuma ai na gama tunda na aure ka,ka cuce ni ka yaudare ni kuma ka zalunce ni,ka tashi ka ba Ni waje kafin raina ya ɓaci na aikata duk abin da ya zo min kaina,tashi ka matsa nesa da ni"
"Duk abin da za kiyi ban hana ki ba,amma ba ki isa ki cutar min da É—ana na zuba miki idanu ba
Tunda kin nuna ba kya ra'ayina ba zan yi miki dole ba,amma za ki haihu ki ba ni É—ana sannan ki kama gabanki,a lokacin da kike É—auke da cikina ya zama dole ki kular min da É—ana har ya zo duniya
Don haka ki tashi ki ci abinci kar ki bar min É—ana da yunwa"
Ko kallon banza ba ta yi masa ba, hankalinta ma yana wajen tunanin yadda zata yi da wannan ƙaddarrarriyar masifar da ta gayyatowa kanta ta auren Arnold,shi kuwa Arnold ganin ta yi masa banza ya sa zuciyarsa ta yunƙuro,tun ba yanzu ba ta karantar da shi abubuwa da yawa a addinin musulunci,har da wanda yake karya azumi,don haka bai yi wata-wata ba ya afka mata a lokacin
Duk yadda ta so ta ƙwaci kanta hakan ya gagara,dama gashi ta galabaita,kuma ba ƙarfin su ɗaya ba,ya gama abin da zai yi ya ɗaga ta zaune,ya ce"ki ci abinci ki daina wannan kukan,amma na yi miki alkawarin duk lokacin da kika yi azumi sai na karya shi,sai anjuma "ya fice daga ɗakin ya koma parlour
Tun daga ranar bai sake barin ta ɗauki azumi ba,da kanshi yake zaunar da ita da safe ta ci abinci,idan ta ƙi kuma ya mu'amalance ta ta ƙarfi,ya sake ba ta abinci sannan ya fice daga gidan
Sai abu na gaba da ya ɓullo ganewa da Shaheeda ta yi yana shaye-shayen giya, ƙwayoyi da sauran kayan maye,shisha kuwa a parlourn yake baje ta ya yi ta zuƙar abinsa,bata taɓa damuwa ba,ko nuna masa ta damu da hakan
Akwai abin da ta fuskanta game da ƙwayar da Arnold yake sha,tana saka masa bacci sosai a duk lokacin da ya sha ta,kuma ko da a ce yana cikin damuwa ya sha yana kwanciya bacci idan ya tashi zai tashi zuciyarsa wasai,ya yi ta harkokinsa cikin farin ciki
Daga haka zuciyar Shaheeda ta kwaɗaita mata shan ƙwayar don ta samu ta yi baccin da damuwa take hana ta, sai ta kwashi kwanaki masu yawa damuwa bata bar ta ta yi bacci na cikakkun awa biyu ba,don haka kanta tsaye ta nufi inda yake ta ce
"Wannan ƙwayar da kake sha take saka ka bacci nake so ka ba ni"
Kallonta ya yi ya ce "ba kya samun bacci ne?"
Bata yi magana ba sai jinjina kai,babu musu ya ɗauko ya miƙo mata
Da farko ɗaya ta fara sha, ganin ta fara jin jiri ya sa ta kwanta, cikin ɗan ƙanƙanin lokaci bacci mai nauyi ya ɗauke ta
Daga lokacin Shaheeda duk lokacin da damuwa ta ishe ta sai ta ɗauki ƙwayar ta sha,tun ɗaya tana iya kwantar da ita har ta daina, ta koma shan biyu