Sashe 30
Gadar Tsautsayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Babu jumawa sai gashi ya zo,bata yi wata-wata ba ta faÉ—a motar,ya ja da gudu suka bar makarantar
Kai tsaye daga nan airport suka nufa,komai ya zama ready,amma jirgin su da zai tashi zuwa Lagos,sai nan da awa ɗaya zai tashi,daga Lagos ne za su yi boarding jirgi na gaba zuwa Madrid,ita dai tana zaune ƙirjinta yana ta bugawa,gaba ɗaya ta ji ta sare tana jiran ko ma me zai faru ya faru
Har jirginsu Shaheeda ya tashi cikin iska jikinta bai daina rawa ba, lokaci guda kuma hawaye ya wanke mata fuska,a ranta tana jin wai ita ce wannan Fatima Shaheedan dai, favourite É—in abbanta,amma a yau an wayi gari saboda namiji ta bar abbanta da ya nunawa duniya bashi da kamarta,ta bar Ummeenta, wadda ita kaÉ—ai Allah ya ba ta, wannan wanne irin abu ne?wacce iriyar makauniyar soyayya ce?
Rushewa ta yi da kuka, Mubarak da yake gefenta ya yi maza ya riƙo ta cikin tashin hankali yana tambayarta abin da ya faru,ta girgiza masa kai tana faɗin "babu komai"
Ya ce"ki gaya min,bana jin daÉ—i, zuciyata zafi take yi idan na ganki a cikin damuwa, please Fatima"
Ta yi É—an murmushi tana goge hawayenta ta ce"kewar iyayena na fara yi ne,ina son su sosai,kuma ina tausayin halin da za su shiga idan bana nan"
Mubarak ya ce"very soon za mu dawo gare su mu nemi afuwar su,na san za su yafe mana ko?"ita dai ta yi shiru tana kwantar da kanta a gefen kafaÉ—arshi,ya rungume ta sosai yana sauke ajiyar zuciya
Awa É—aya da rabi ne ya É—auke su daga Kano zuwa Lagos,kuma suna sauka kai tsaye ya kama musu hayar É—aki a hotel É—in da take kusa da airport É—in
A ranar Mubarak ya bincika babu jirgi mai zuwa Madrid,dole sai dai su bari zuwa washe gari,don haka dole suka haƙura da tafiyar yau ba don sun so ba
Sai dai a wannan daren suka biya bashin soyayya na tsawon lokaci,suka fanshe tarin wahala da fargabar da suka sha,a wannan dare Mubarak da Shaheeda suka zama abu guda,suka kasance cikin shauƙin soyayya da ƙaunar juna
Sosai ya yi ta tattalinta musamman da yakasance har yanzu Shaheeda yarinya ce ƙarama,don duka-duka shekarunta har yanzu sha takwas da ƴan watanni, sannan kuma ya same ta a cikakkiyar mace kamar yadda ya yi tsammani,dama ya sani Shaheeda bata da kule-kulen maza
Washe gari Shaheeda ta tashi da zazzaɓi,ga kukan da take ta yi,hakan ya tilasta masa kai ta asibiti don a duba lafiyarta
Shaheeda tana ganin likitan sai da gabanta ya faɗi,don ta gane shi,El-muaz Adam,class mate ɗin Muyassar ne a secondary school, saboda yadda Muyassar yake ji da ita ya sa su manyan abokansa ma suke ƙaunarta,amma yadda ta nuna bata gane shi ba shima haka, musamman da ya ganta tare da wanda yake da tabbacin mijinta ne,idan suka nuna sanayya a tsakaninsu bai san yadda zai ɗauki abin ba,don ma da gani ba bahaushe bane,kuma babu alamun yana jin Hausa,sai dai abin da ya ba shi mamaki yadda ya ganshi Sam bai yarda da tarbiyyarsa ba, musamman ganin tattoo ɗin da ya yi a wuyansa
Amma ya yi mamakin yadda aka yi auren ƙanwar Muyassar amma bai sanar masa ba
Hakan bai hana ya yi attending É—inta ba,ya ba su magunguna suka wuce hotel É—in da suka sauka
A ranar sai da suka sake kwana saboda yanayin jikin nata,washe gari suka bi jirgin ƙarfe takwas zuwa Birnin Madrid
💫
Roxy tana zuwa daidai nan a labarinta ta yi shiru kanta a ƙasa sai sauke ajiyar zuciya take yi,da alamu ta zo wata gaɓa mai ciwo wadda ta kasa mantawa da ita a rayuwarta, ciwon har yanzu yana taɓa mata zuciya,a hankali Haisam ya ɗago yana kallonta, cikin sanyin murya ya ce"kin yi kuskure Shaheeda!kin tafka kuskure a rayuwarki,tun a wannan gaɓar na fuskanci yadda kika kassara rayuwarki,why?
Why Shaheeda? meyasa kika zaɓi ki jefa kanki a cikin wannan mummunan halin? wanda har ki bar duniya tabon ba zai bar ki ba?
Meyasa za ki yiwa kanki tabo irin haka?kai!!?"ya dafe kai yana murza goshinshi,da alamu abin ya taɓa shi sosai
Ƴar dariya mai ciwo Roxy ta yi tana kallonsa, kafin ta ce "ka fara tausayawa halin da nake ciki right?
To kar ka yi gaggawa,don har Shaheeda ta bar ƙasar a lokacin tana cike da farin cikin auren masoyinta,bata san illar da hakan ya ƙunsa ba,sai a gaba take gani
A taƙaice ma dai,a yanzu babu wata Shaheeda a duniya,don himma, soyayya da hazaƙa,gami da mutuntakar da Shaheeda take da su duk sun mutu a yau, zafi da raɗaɗin da suka rage su kaɗai ne a tare da Shaheeda, babu abin da ya rage wanda take tunawa da shi a duniya ta samu nutsuwa sai ɗanta Mubarak "
Haisam yana kallonta ya ce"to ina mijinta Mubarak?"
Roxy ta jinjina kai ta cigaba da labarin;
💫
Tafiyar awanni goma ta kai su zuwa birnin Madrid,don sai da suka fara tsayawa a Casablanca babban birnin marocco,gaba É—aya jikin Shaheeda a sanyaye, duk da yadda take farin ciki da auren masoyinta da yadda yake ta taraiyayarta,hakan ne ma ya rage mata raÉ—aÉ—in da zuciyarta take yi
Kai tsaye gidan da ya kama musu haya suka nufa, gidan ya yiwa Shaheeda kyau sosai,don irin wanda take so ne ya kama
Zamansu ya miƙa cikin matuƙar farin ciki da ƙaunar juna,cikin ɗan lokaci kaɗan Shaheeda ta sake,ta manta da wata kewar mahaifanta da kuma ƙasarta,batun karatu kuwa tuni ta daɗe da watsar da shi
Kusan duk lokacin da yake gida ta kan taimaka masa da ayyukansa, kasancewar course iri ɗaya suka karanta,a dalilin haka ma ya yi mata alkawarin ware mata wani kaso a albashinsa, don tuntuni ya fara aiki a ƙasar, kasancewar yana da connection a ƙasar ya sa bai wani sha wahala ba,ga result ɗinsa ta yi kyau sosai
Kusan duk weekend ya kan É—auki Shaheeda su zaga birnin Madrid,su ne duk wasu manyan parks da ke cikin garin Madrid,har ma da wajensa, Shaheeda mai son yawace-yawace har Allah-Allah take yi weekend ya zo don su zaga gari
A cikin watanni biyu da aurensu sun murje sun yi kyau hankalinsu ya kwanta, kuma a wannan tsukin ne Shaheeda ta fara laulayin ƙaramin ciki, wanda shi kansa Mubarak da kanshi ya gano da cikin,amma sai da suka je asibiti aka sake yi mata gwaji aka tabbatar da cikin
Dukkansu sun yi farin ciki,duk da cewa Mubarak ya so su ɗan ƙara ɗaukar lokaci kafin samuwar cikin,amma sai ya bi ra'ayinta,suka yi farin ciki sosai,a ɓangare guda kuma ya sake zage dantse don ba ta kulawa da nuna mata soyayya
💫
A gida kuwa tun lokacin da Shaheeda ta saba dawowa daga makaranta ya wuce hankalin Ummeey ya tashi,ta fara kiranta a waya amma shiru,bata samunta, Shaheeda bata kashe waya, wannan abu ne wanda kowa ya sani a gidan, Sai dai idan wani dalili ne mai girma,don haka kai tsaye ta kira Muyassar ta sanar masa da cewa don Allah ya je makarantar su Shaheeda ya duba mata ko wani abin ne ya tsare ta, Muyassar yana jin haka sai da gabanshi ya faÉ—i,amma hakan bai hana shi zuwa makarantar ba
Hankalinsa ya tashi sosai lokacin da ya samu tabbacin cewa ta fita a wata mota da ta saba fita,kuma dukkan alamu sun gwada cewa motar wannan matsiyacin yaron ce,a cewarsa,gumi ya shiga karyo masa da tunanin ina ya kai masa ƙanwa?
Allah ya kiyaye kar ya lalata masa ƙanwa,don bai ga alamun mutumtaka a tare da wannan yaron ba,gashi kuma ba Musulmi ba
Bai yi gaggawar sanar da Ummeey ba,don baya son ya É—aga mata hankali,ya gwada kiran layin Shaheeda da numbers mabanbanta,wai ko blocking É—in shi ta yi, amma amsar É—aya ce,layinta baya amfani
Hakan ya sa tilas ya koma gida,wani ƙarin tashin hankalin kuma a ranar Abba ya dawo daga Abuja,kuma yana zuwa kamar yadda ya saba ya buƙaci ganin sanyin idaniyarsa Shaheeda
Ummeey ce ta sanar masa halin da ake ciki,don Muyassar ce mata ya yi ya bincika bai same ta ba,kuma an tabbatar bata shiga makaranta ba, gudun kar a je a sake jin abin da ya ji, hankalin Ummeey ya yi ƙololuwar tashi,ta san wacece Shaheeda,bata zuwa ko'ina idan bata tambaye ta ba,ita yawo ma bai dame ta ba, ballantana ma su ba su da ƴan'uwan da za su rinƙa zuwa wajensu
Gaba ɗaya Alhaji Yusuf ya birkita gidan, faɗa kan mai uwa da wabi akan a fito masa da ƴarshi duk Inda aka kai ta, tamkar zai daki Hajiya Atika wadda suka fi samun matsala da Shaheeda,yana faɗin su ne suka ɓatar masa da ƴa, Hajiya Atika sai kuka take yi tana rantsuwar cewa ita babu ruwanta, Hajiya Ruƙayya ce mai cewa "haba Alhaji!ya za ka zarge mu da ɓatan ƴarka don ɗaukar alhaki?
Allah shaida babu abin da ya shafe mu da Æ´arka,amma idan ka cigaba da É—aukar alhakinmu kai da Allah"
Shi dai Muyassar bai yi magana ba,amma maganar gaskiya kowa a gidan ya ba shi tausayi, musamman ma Abba da Ummeey, wadda ita tun da ta fuskanci ƴarta ta shiga wani hali idanunta ba su huta da zubar da ƙwalla ba
Washe gari Abba ya saka cigiyar neman Shaheeda a gidajen Radio da television ta ƙasa, lokaci guda gari ya ɗauki ɗumi na ɓatan Yar CEO na Maliya groups of companies, Fatima Yusuf Maliya,tuni gari ya ɗauka, saboda yadda Alhaji Yusuf ya kasance mai tausayi da sanin ciwon ƴaƴa mata,ya sa gaba ɗaya gari ya ɗauka da tausayin tashi ƴar
El-muaz ne ya ga sanarwar,da yamma bayan ya koma gida ya huta,ya yi mamaki sosai,ya É—aga waya ya kira Muyassar
Bayan Muyassar ya É—aga El-muaz ya ce "Man kwana biyu ko neman mutane ba kwa yi"
Muyassar ya yi murmushin ƙarfin hali ya ce"ayyuka man,ya naka aikin?"
El-muaz ya ce "alhamdulillah, yanzu na ga sanarwar ɓatan ƙanwarka Shaheeda, menene gaskiyar lamarin?"
Muyassar ya yi ɗan shiru kafin ya dake ya ce"ta ɓata,amma ni na san ba ɓata ta yi ba,akwai wani saurayinta da ta bi,sai dai na kasa fitowa na sanar da iyayen nata"