← Book details Gadar Tsautsayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 51

Sashe 18

Gadar Tsautsayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka nake son gani!na tabbata idan ta ganki zata yi burin aiwatar da mummunan ƙudurinta"sai kuma ta yatsina fuska ta ce"na kasa gane abin da mata suke buƙata a jikin ƴan'uwansu mata,da har suke jin za su iya illata wani akan wannan mummunar ɗabi'ar tasu

Daga yau ina buƙatar a cire mata sha'awar ya mace a rayuwarta har abada,ina buƙatar ta ji a duk duniya babu abin da ta tsana sama da wannan dabbancin,in other hand kuma ina buƙatar ta ji tabbas Roxy ta wuce tunaninta,tafi"babu musu Azeema ta ɗauki abayarta ta ɗagawa Roxy hannu,ta fice daga dakin tana ƙoƙarin saka abayar

Itama Roxy miƙewa ta yi ta fice daga ɗakin, a ranta ita kaɗai ta san wutar fansar da take ruruwa a cikin zuciyarta

*KANO STATE*

*HAISAM*

Da sauri-sauri yake fitowa daga sashensa,don a rayuwarsa ba ya son ɓata lokaci ko kaɗan, musamman a irin abin da ya shafi aiki

Nimra ya gani a raɓe a jikin bangon parlourn,ta narke idanu ta langwaɓar da kanta,a cikin zuciyarsa ya furta

"Kai!inna lillahi wa inna ilayhi rajiun!

Wannan wacce iriyar masifa ce?"

Katse masa tunani ta yi, cikin yauƙi take faɗin

"Good morning sweetheart!"

A taƙaice ya amsa da"morning!"

Lumshe kyawawan idanunta ta fara yi tana buÉ—ewa cikin sigar jan hankali, Haisam ya É—auke kanshi, zuciyarsa tana zafi

"Can we go now?

Za mu iya magana?"

Ba shi da zaɓin da ya wuce cewa"okay! bismillah "duk da cewa yana da abu mai muhimmanci da zai yi,ya juya ya koma cikin parlourn, ta biyo bayansa

Yana zaune ya zuba mata idanu ganin bata da niyyar yi masa magana,gashi shi kuma yana da abu mai muhimmanci da zai yi, cikin ƙosawa ya dube ta ya ce

"Nimra kin san yadda aikina yake, kuma a kowanne lokaci kusan na ce miki ina bakin aiki ne,idan kina da magana mai muhimmanci then let's talk,is not proper ki zuba min idanu kina kallona bayan kin ce min kina da magana,nima kuma ina da inda zan je, don akwai aikin da zan yi"

Shagwaɓe fuska ta yi,ta ce"kenan yanzu baka da lokacin iyalinka sai na aikinka kenan?"

Kanshi tsaye ya ce"kusan haka!"

Ya faɗa ne don ta ƙyale shi, amma a maimakon haka sai ta kama murmushi tana faɗin "You must be joking my friend!

Whatever,ko ma dai haka ne ni nan zan sauya yanayin aikin nan da yake cinye haƙƙin mutane,ka ba ni time, shima aikin ka ba shi,for now dai,a yi maganar a yanzu,anan, yaushe za ka tura magabatanka gidanmu?idan ba za ka iya magana ba ni zan yi wa daddynka magana,idan ya so sai su je can wajen abbana "

Shi abin ma dariya ya ba shi,amma ya ɗaure fuska ya ce"ba sai kin gaya masa ba,idan na samu time zan yi masa magana, yanzu dai kina gani na da shiri aiki zan fita "juya ƙwayar idanunta ta yi ta ce"alright babu matsala,sai na ji ka,amma kar na ji shiru Please "ya jinjina kai kawai yana miƙewa,ta miƙe itama ta rufa masa baya suka fito har wajen motarshi

Sunkuyar da kanta ta yi daidai windon motar tana kallonsa tana narkar da idanu yadda ta saba idan tana son ta ja hankali, ɗauke kanshi ya yi daga kallonta yana yunƙurin tayar da motar,da wata iriyar sexy voice ta ce"safe trip sweetheart!

Allah ya dawo min da kai lafiya "ya jinjina kai sannan ya tayar ya fice daga gidan

Kai tsaye address É—in da Saleem ya tura masa ya nufa,sai gashi ya ya tsinci kanshi a gaban wani katafaren gida

Bin gidan ya yi da kallo yana sake duba address É—in da mamaki,amma da ya tuna wacece Roxy sai ya yi murmushi kawai,yana sake duba hotunan da aka tura masa

Ya kai wajen mintuna talatin a ƙofar gidan kafin ya samu yaron da zai aika gidan ya yi masa sallama da matar gidan,babu jumawa sai gashi ta leƙo,sanye da hijabi har ƙasa,autanta Habu yana riƙe da hannunta

Har ƙasa ya durƙusa yana gaishe ta,ta amsa da sakin fuska sannan ta ce"ka shigo ciki mana,sannu da zuwa"ya yi ɗan murmushi ya ce"a'a dama ba shiga zan yi ba, tallafin marayu ne aka ce na kawo muku"ya ciro kuɗi ɗaurin 100k guda biyu ya ce "gashi, Allah ya ji ƙan mahaifinsu ya albarkaci rayuwarsu"hannunta yana rawa ta karɓa tana faɗin "oh Allah!

To an gode an gode sosai, Allah ya saka da alkhairi, yadda kuke faranta mana Allah ya faranta muku, Allah ya kula da ahalinku kuma"É—an murmushi Haisam ya yi,ya ce"babu komai Mama, in sha Allah ina nan dawowa nan kusa,hi boy!"yaron ya É—aga kai a sanyaye yana kallonsa, tsananin kamar da suke yi da mahaifiyarshi ya sake tabbatar masa da zarginsa,kamar har ta yi yawa ma,ya kama hannun yaron yana yi masa wasa,duk da yadda ya nuna masa ba zai saki jiki da shi ba,amma saboda kayan biscuits da sweets É—in da ya kawo masa ya saki jiki da shi,har ya É—aga masa hannu da zai shiga motarshi

Sai da suka shiga gida ya É—aga waya ya kira Saleem, Saleem yana É—agawa ya ce"komai ya yi daidai Saleem, thanks very much for your effort "

Saleem ya rissina kamar yana gabansa ya ce"ka cancanci fiye da haka daga gare ni Oga, Allah ya ba da sa'a, Allah ya ba ku nasara akan maƙiya"Haisam ya kashe wayar yana murmushi

#Nusy_bee

Page 15

*ABUJA*

"Hajiya Hassy girman kujerarki!

Ga yaran na samo,ga su tsala-tsala,har sai sun fi Roxy garÉ—i ma"a cewar Amra a waya tana kallon su Azeema da ta saka suka cire after dress É—insu, kowacce ta zauna daga ita sai kayan banzan da ta saka

Daga ɗaya ɓangaren Hajiya Hasana, wadda aka fi sani da Hassy ta ce"alright gani nan zuwa,kin san mai gidana yana gari,ga yaran miji da shegen sa ido,bana son a ɗago ni,dama gashi sun dame ni da tambayar ina na ji ciwo, matsiyatan yara kawai"

Amra ta ce"maganinsu za ki yi kamar yadda kika yi maganin ubansu,ki kai su sama su ma a rufe bakin su daina saka miki idanu, suna uzzura miki da tambayoyi na babu gaira babu dalili,kamar waÉ—anda suke aurenki"

Hassy ta ce"mhm!

Gani nan zuwa dai,idan na zo sai mu ƙarasa maganar ko?"Amra ta ce"okay sai kin zo"suka kashe wayar

Abinci da abin sha Amra ta kawo musu,ta shimfiɗa ƙatuwar darduma ta ce"bismillah,mu zauna girls"babu musu suka sauko,ta yi serving ɗin kowa,itama ta yi serving kanta

Ba su juma da fara cin abincin ba kira ya shigo wayar Amra,wayar tana ɗakinta,don haka ta miƙe ta fice daga parlourn don ɗauko wayar

Da sauri Azeema ta ciro ƴar ƙaramar ƙwayar da Roxy ta bata ta jefa a cikin kofin Amra,suka cigaba da cin abincin su a nutse

Babu jumawa Amra ta shigo tana jan tsaki,don kiran da unknown number aka yi,kuma da ta É—aga shiru ta ji,har ta gaji ta kashe wayar

Kallo su ta yi tana murmushi,ta zauna tana faÉ—in"sorry ko?

Na bar ku jira, kuma ƴar'uwar tawa tana hanya bata ƙaraso ba"suka kalle ta,sai da dariya ta kusa kama Azeema ganin yadda take magana tana wani karairaya kamar tana tare da namiji

Ɗaya daga cikin ƙawayen Azeema, wadda ta fi ta iya bariki,ta yi fari da idanu ta ce"no babu komai baby,sai ta iso"Amra ta yi murmushi, Azeema da ɗaya ƙawar ta su suka kalle ta da mamaki jin ta kira ta da baby

Ai kuwa babu jumawa bacci ya fara fizgar Amra,suka cigaba da cin abincinsu a nutse suna kallonta suna murmushi

Mintuna biyar kyawawa ya ishi Amra faɗawa bacci mai nauyi,suka kalli juna suka yi shewa, Azeema ta miƙe ta fara laluben kitchen,su kuma sauran ƴan matan suka fara tuɓe mata kaya

Babu jumawa Azeema ta dawo hannunta riƙe da tafasasshen ruwa, tana zuwa bata yi wata-wata ba ta sheƙawa Amra a daidai saitin gabanta,duk da nauyin baccin nan da ƙwayar ta saka ta sai da ta yi wani ihun azaba, ba tare da damuwar komai ba suka tattara komatsansu suka fice daga gidan

Lokacin da za su fita daga layin a lokacin motar Hassy ta shigo layin,sai dai kasancewar babu wanda ya san wani a cikinsu ya sa suka wuce ba tare da sun tsaya ba ma,itama Hassy ta wuce gidan Amra zuciyarta cike da kwaÉ—ayi da É—okin haÉ—aÉ—É—un Æ´an matan da ta gani Amra ta tura mata ta Whatsapp

*MALIYA ESTATE, KANO STATE, NIGERIA*

"Muyassar menene yake faruwa ne?

A kwanaki biyun nan ƙararraki suna yin yawa akanka, mahaifiyarka ta kawo min ƙararka,haka zalika matarka,me yake faruwa ne?"

Kan Muyassar a ƙasa yana sauraren yayan mahaifiyar tashi ya ce"ban san akan me kake magana ba Abba"

Alhaji Yusuf ya ce"matarka ta tabbatar min da kana neman wata yarinya,har kana shiga lokacinta da sabgogin yarinyar , menene gaskiyar wannan maganar?"

Shiru ya É—an yi, kafin ya girgiza kai ya ce"a'a Abba,Ni ban san da wannan maganar ba gaskiya"

"Abba wallahi ƙarya yake yi,har cewa ya yi wai ya fi sonta da ni,kuma akanta ni ba mace ba ce,ya rinƙa ci min mutunci saboda ita, tukunna ma,don ka ga ina rufa maka asiri, wallahi Abba tsohuwar budurwarsa ce,wato SHAHEEDA!!"

Cikin wani Irin ɓacin rai Abba ya kalli Muyassar wanda ya yi ƙasa da kanshi kawai yana saurarensu, muryarshi tana tsaitsayawa ya ce"menene gaskiyar maganar matarka?

Menene gaskiya game da halin da kake ciki na neman waccan yarinyar?"

Kai tsaye Muyassar ya ce"ka gafarce ni Abba,na san dai har yanzu ina sonta,amma...."marin da Abba ya saukewa Muyassar ne ya sa ya yi shiru, cikin tsananin ɓacin rai ya ce"ko babu komai ka nuna min ni ba mahaifinka bane,ko da na ɗauki shekaru kana riƙe a hannuna,ka tashi ka ba Ni waje kafin na fusata na yi maka abin da ba za ka taɓa mantawa ba,tashi ka ba ni waje!'ya daka masa tsawa

Babu musu Muyassar ya miƙe tsaye, fuskarsa babu alamun damuwa,duk da cewa shi kaɗai ya san yadda yake ji a ranshi,ya fice daga sashen Alhaji Yusuf

Dubanshi ya mayar ga Hajiya Sa'adatu da ranta ya fi na Alhaji Yusuf ɓaci, cikin kakkausar murya ya ce"kina ina hakan take ta faruwa ne Sa'adatu?

Yaushe É—anki zai yi lalacewar bijirewa umarnina?
Chapter 18 · 0% Book details