Sashe 31
Gadar Tsautsayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"What!"El-muaz ya faɗa yana zama a gigice,ya ce"ɗazun nan ta bar asibitina ita da wani Guy da nake tunanin cewa mijinta me, don da alamu ma ya je mata a yadda nata saba ba take zazzaɓi ya kawo ta na duba ta, don't tell me cewa wannan saurayinta ne Muyassar"
Muyassar da wani irin tashin hankali ya lulluɓe shi,yana sharce gumi ya ce"ka gaya min gaskiya El-muaz,you know that girl is my life,my happiness,my everything,ka daina gaya min ta ba wa wani namiji kanta,na san ba za ta yi haka ba"El-muaz ya katse shi da faɗin"I'm sorry to say abin da na gani na gaya maka,sai kusan yadda za'a yi a ɗauki mataki, I'm sorry dude!"ya kashe wayarshi yana nadamar kiran Muyassar, zuciyarshi cike da tausayinsu
Shi kuwa Muyassar yana sauke wayar ya hau sharce gumi yana faɗin"no!no it can't be possible, Shaheeda ta kasance da wani namiji ba ni ba a ƙarƙashin inuwar aure,nooooo!
Why?why Shaheeda? please are you okay?"
Dariyar da ya ji a bayansa ya sa ya waiga da sauri, Arfa da ya gani ya sa jikinsa ya fara rawa,don ya san ta ji komai, wayarshi da El-muaz ma babu mamaki ta ji, saboda wayar tana speaker
Ƙasa magana ya yi sai rawa da jikinsa yake yi, Arfa ta kalle shi sheƙeƙe ta ce "ka ce ba ni da tarbiyya ko?
To ga ma'asumiyar da kake so nan,ga halin da take ciki nan,sai anjuma ko"ta juya ta fice daga sashen
#Nusy_bee
Page 25
Da kallo ya bi ta har ta fice daga parlourn,a cikin ranshi yana jin wani irin tashin hankali,babu wanda yake tausayi kamar Ummeey,duk da irin soyayya da kulawar Abba a gare ta,yana nan a zaune sai ga Ummeey ta shigo cikin tsananin tashin hankali,ɗan kwalinta ma a hannu,a bayanta kuma Hajiya Ruƙayya, Hajiya Atika da Hajiya Sa'adatu ne da ba su juma da zuwa ba ita da aunty Salma da Hajiya Zaituna matar uncle Rufa'i
A gigice Ummeey ta nufi inda Muyassar yake zaune kamar wanda aka dasa yana kallon komai, har yanzu ji yake komai kamar almara,sai Shaheeda ta bi wani sun gudu,har ma ta ba shi kanta,inaa! wannan ba mai yiyuwa bane, Shaheedansa ba haka take ba,kamilar yarinya ce mai riƙo da tarbiyyar da aka yi mata
Yana cikin wannan tunanin ne su Ummeey suka shigo,kan Ummeey ko ɗan kwali babu,zaninta ma yana kwancewa tana gyarawa,ta shiga wani irin tashin hankali irin wanda bata taɓa tunani zata shiga ba a rayuwarta,tana zuwa ba tare da wata-wata ba ta fara jijjiga kafaɗarshi tana faɗin "me ka sani game da Shaheeda don Allah?
Da gaske ne abin da Arfa ta faÉ—a na cewa Shaheeda saurayi ta bi?kuma ka sani?don Allah ka gaya min! Inna lillahi wa inna ilayhi rajiun!!!"
Hawaye suka zubowa Muyassar babu shiri,ya dafe kanshi yana jin Ummeey tana cigaba da roƙonshi tana kuka mai tsuma zuciya, Hajiya Atika ce ta yi guɗa tana faɗin "Allah buwayi gagara misali! Allah ya ɗauke mana damuwar da ta addabe mu a gidan nan ta sigar da ta dace,an yi walƙiya dai a ƙarshe an ga kowa, Allah ya shirya mana zuri'a"ta ja hannun ƴarta Malika suka fice daga sashen
Ita kuwa Ummeey a take ta yanke jiki ta faÉ—i,aunty Salma ce ta yi saurin É—auko ruwa ta zuba mata,amma ina,ko alamun zata farfaÉ—o babu
Tilas ta yiwa driver magana, Muyassar ya ɗaga ta da ƙyar ya fita da ita ya saka ta a mota,sauran mutanen dama tuni sun kama gabansu
Gwajin farko da aka yiwa Ummeey aka gano jininta da ya yi mugun hawa, hankalin Muyassar ya tashi, tilas ya kira Abba ya shaida masa dukkan halin da ake ciki, dama tunda Shaheeda ta ɓata bai sake barin Kano ba
Cikin tashin hankali ya iso zuwa asibitin,anan yake samun mummunan labari daga bakin ƙanwarshi Sa'adatu mahaifiyar Muyassar,a labarin nata ma har da ƙarin cewa dama Shaheeda ta daɗe tana lalacewarta da kafirin yaron da aka gansu tare,yanzun ma da alamu ciki ne da ita shiyasa suka gudu,har ya kai ta ta ga likita
Shima dai a take Alhaji Yusuf ya yanke jiki ya faɗi,shima babu shiri aka shiga da shi, Hajiya Sa'adatu sai ihu take yi tana tsinewa Ummeey da yarta da ta kira annoba,tana iƙirarin idan ɗan'uwanta ya mutu sai ta yi Shari'a da Ummeey,tunda ita ta haifo musu bala'i a dangi
Awanni shida Alhaji Yusuf ya É—auka Kafin ya dawo hayyacinsa,shima dai jininsa ya yi mugun hawa
Ita kuwa Hajiya Zainab sai da ta yi kwanaki uku kafin ta dawo hayyacinta,ta rame ta zabge ta lalace kamar ba ita ba
Tsawon kwanaki biyar aka É—auka a gidan Kafin abubuwa su fara daidaita,don a waÉ—annan kwanaki biyar É—in gidan komawa ya yi tamkar na mutuwa
A lokacin ne Alhaji Yusuf Maliya ya tara kaf ahalin Maliya family sannan ya tambayi Muyassar ya faÉ—i gaskiyar abin da ya sani game da Shaheeda
Muyassar bai ɓoye komai ba ya sanar da Abba,sai da Abba ya nisa sannan ya saukewa Muyassar wani gigitaccen mari,rai a ɓace ya ce "ba ka cuce ni ba Muyassar!kanka ka cuta!! tunda har ka kasa sanar da ni halin da yarinyata ke ciki har sai da mai afkuwa ta afku
Amma ku shaida,daga yau,Ni YUSUF AHMAD MALIYA,na cire Fatima daga cikin Æ´aÆ´ana,idan ta sake amfani da wani abu nawa,ko da sunana ne sai na yi Shari'a da ita!ku shaida hakan!ku tashi ku tafi na sallame ku"Ummeey ta kasa jurewa ta fashe da wani kuka mai gunji,babu wanda ya kula ta,sai Hajiya Sa'adatu da take yin wani murmushi na farin ciki ta ce "to sai mu ce Allah ya raka taki gona
Sannan magana ta gaba, tunda ita ta zaɓi hanyar da take so nima na zaɓarwa ɗana mata,zan aura masa Arfa, ƙanwar Hajiya Ruƙayya "
Hajiya Ruƙayya da Hajiya Atika tuni suka washe baki, Hajiya Atika faɗi take yi "Masha Allah!
Amma na ji daÉ—in wannan abu,dama me za'a yi da mara tarbiyya, Allah ya sanya alkhairi ya sa a yi da mu"
Shi kuwa Muyassar bakinsa ne ya kama rawa, hankalinsa idan ya yi dubu ya tashi,ba ya son wannan yarinyar Arfa,ya tsane ta ma,kuma har yanzu akwai soyayyar Shaheeda a cikin zuciyarsa, wadda yake jin har ya mutu da ita zai mutu, ko da a ce bai sake saka ta a idanunsa ba
Runtse idanu ya yi yana jin yadda ake cigaba da tsare-tsaren yadda za'a yi bikinsu,shi dai bai sake fahimtar komai ba har Alhaji Yusuf ya ba su izinin tafiya
Tsawon watanni biyu gidan ya kasance a haka, Ummeey bata da mai taya ta kuka,don ko da wasa ta yi wa Abba maganar Shaheeda sai ranta ya ɓaci,a ganinsa ai yaran kishiyoyinta ma ai nata ne,so shi bai ga abin damuwa da ɗorawa kai tension ba don Shaheeda ta gudu,haka ta zaɓarwa kanta,to ta je ta yi rayuwarta
Hakan ya ƙarawa Ummeey tension,har ta shiga depression,ga jinya tana fama sosai,amma bata da wanda zai fahimce ta a gidan
Hajiya jameela ce ta zo wajenta, wadda ta yi tafiya zuwa Canada na tsawon watanni shida,ta yi kuka sosai da jin abin da ya samu ƙawar tata,ta ba ta shawarwari sosai, waɗanda suka taimake ta har zuciyarta ta rage raɗaɗin da take ciki
Ummeey ta cigaba da rayuwa a gidan tana zaman haƙuri,don bayan abin da yake damunta na ɓatan yarta mutanen gidan suka sako ta a gaba da gori da shaguɓe akan Shaheeda,sai dai ba ta tankawa, musamman da ta fuskanci ana shakkar a yi mata a gaban Alhaji Yusuf,don haka itama ta cire komai daga ranta
💫
A ɓangaren Shaheeda kuwa tana rayuwarta cikin kwanciyar hankali ita da mijinta Mubarak tsawon watanni biyu,a lokacin ne wasu irin matsaloli suka fara ɓullowa waɗanda ta kasa gane musu
Da farko ankara da ta yi akan Mubarak bai damu da Sallah ba sam,idan za su wuni tare in dai bata ce masa ya tashi ya yi Sallah ba ba zai yi ba, maganar sallar asuba kuwa dama ba ya taɓa yi da asubar,kuma idan ba sharri zata yi masa ba zata iya cewa ba ya yi watarana ma,don sau tari ma cewa yake yi sai ya je wajen aiki zai yi
Sai matsala ta biyu,ta fara gamo sunansa Arnold har yanzu shi yake amsawa,ba ya amsa Mubarak,ita kaÉ—ai take kiransa da Mubarak, don ko abokansa na kusa da Arnold suka san shi
Da ta yi masa magana sai ya nuna mata ai saboda sabon da suka yi ne ya sa sunan ya kasa fita daga bakinsu, faɗin hakan da ya yi ne ya sa ta ƙyale shi
Duk wannan halin da suke ciki ya cigaba da koya mata abubuwa da yawa da bata iya ba wanda ya danganci computer, kama daga hacking security don gudun matsala, ɗora ƙaƙƙarfar security da sauran abubuwan da suka shafi software,kuma da yake tana da ra'ayi har yanzu ta mayar da kai tana ɗauka,don ma yanzu ciki ya saka ta a gaba da laulayi
A cikin abokansa akwai wani Diego,sam Diego bai yi mata ba,ta tsane shi saboda yadda ya kasance mashayi ne,gashi ɗan maye saboda ta'ammali da miyagun kwayoyi,babu yadda bata yi ba don Mubarak ya rabu da shi amma ya ƙi,don haka ta cigaba da nuna masa tsana a fili,shi dai Mubarak bai damu ba
Yau tana zauna tana shan lemon juice da take so saboda ciki, take yawan haɗawa yanzu ta sha,sai ga ƙarar intercom
Da mamaki take kallon ƙofar,ta san lokacin dawowar mijinta bai yi ba,amma sai ta yi tunanin ko wani abu ya manta,don haka ta miƙe ta buɗe ƙofar tana kallon wanda yake taɓa intercom ɗin da mamaki
Ba kowa bane sai Diego,ya yi mata wani murmushi ya gaisheta da harshen Spanish Wanda zuwa lokacin tuni sun bar Yaren dutch sun koma kanshi, saboda yanayin al'ummar da suke tare da su
A fizge ta amsa fuskarta a É—aure,yana murmushi ya ce"za mu iya zama mu tattauna?"
Sai ta yi É—an jumm sannan ta ba shi umurnin zama,suka zauna suna fuskantar juna
Diego ya fuskance ta sosai ya ce"Arnold ya tabbatar min da cewa ke musulma ce ko?"
Ba tare da ta yi magana ba ta jinjina kai tana kallonshi,ya ce "amma kuma kamar a addinin Musulunci mace bata auren wanda ba musulmi ba ko?"