← Book details Gadar Tsautsayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 51

Sashe 42

Gadar Tsautsayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ni sunana AZEEMA,ni da mijina daga wani ƙauye muke a can Ghana,bamu da kowa a nan"Shaheeda ta jinjina kai ta ce"Ni kuma sunana Fatima,mijina ya rasu babu jumawa,gashi bani da kowa"Azeema cikin jimami ta girgiza kai ta ce"Allah sarki! Allah ya ji ƙanshi ya yi masa rahama "Shaheeda ta lumshe idanu kawai bata ce komai ba

Wat guda da tariyar Shaheeda,gaba É—aya damuwarta a yanzu ta kau, saboda Azeema da mijinta RABI'U sun É—auke ta tamkar Æ´ar'uwarsu, musamman da ya kasance mijinta ya rasu,kuma bata da kowa,su ma kuma ba su da kowa sai kansu,sai kuma ita da Allah ya kawo ta rayuwarsu

Shaheeda ta kula da yadda talauci ya ci jikinsu sosai,wani lokacin ma abin da za su ci sai sun yi da gaske suke samu,amma duk da haka in dai sun yi girki ko yaya ne sai sun É—ibar mata

Karamcin mutanen yana matuƙar burge ta,har ta ji a ranta ya kamata ta zama wata itama don ta taimake su watarana

Tun daren jiya take ta fama da matsanancin ciwon mara,amma kasancewar bata taɓa haihuwa ba sam bata kawo naƙuda take yi ba,sai da abin ya tsananta,tana durƙushe tana fama da kanta Azeema ta shiga da sallama

Ɗagowa ta yi idanunta suna chanja kamanni tana kallon ta, Azeema ta ƙaraso da sauri tana faɗin "me ya faru?

Ba ki da lafiya ne?"

Murya ƙasa-ƙasa ta fara faɗin "bayana!marata!!ji nake yi kamar zan mutu"gaban Azeema ya faɗi,a tsorace ta ce "ko dai haihuwa ce?"gaban Shaheeda ya faɗi,a tsorace ta ce"ina ga ita ce"Azeema ta miƙe a tsorace tana safa da marwa,bata san yadda zata yi mata ba,itama Shaheedan bata san yadda za'a yi mata ba,gashi ba su da kuɗin motar da za su tafi asibiti,gashi Rabi'u baya nan,yana wajen aikinsa na gini da yake yi idan ya samu

Haka Shaheeda ta wuni ta malelekuwar azaba,tun tana kuka Azeema tana taya ta,har bakin ya mutu

Sai daf da magriba Allah ya yankewa Shaheeda ta haifi ɗanta,sai dai kallo ɗaya Shaheeda ta yi masa,duk bata san yanayin jariri sabuwar haihuwa sosai ba, kasancewar Ummeey bata haihuwa,kuma matan gidansu ko sun haihu sai ta ga dama take shiga,kuma ba sa ba ta ɗan,amma a haka ta gane nata jaririn ba shi da ƙoshin lafiya, musamman yadda numfashinsa yake fita da yadda yake kuka a wahale

Azeema ce ta yi ƙoƙarin ɗaukarsa ta goge masa jiki, ta yi masa wanka,don dama ita ta iya kula da jariri kasancewar ta taɓa haihuwa ɗan ya rasu bayan ta gama shirya shi sannan ta fita maƙobtansu,akwai wata tsohuwa,ita ce ta taimakawa Shaheeda ta yi wanka ta gyara jikinta

Sai da suka nutsu, Shaheeda tana cin abinci sai ga Rabi'u,ya yi murnar ganin Shaheeda ta haihu lafiya,amma ya yi ta yiwa Azeema fadan meyasa ko maƙobta bata shiga ta aro waya ta kira shi ba, Azeema ta ce ta sha'afa ne, saboda yadda suka gigice a lokacin

Ya ce"ki dai rinƙa kulawa, yanzu dai alhamdulillah,amma duk da haka sai mun je asibiti an sake duba ta,ga wannan kuɗin ki adana"ya miƙa mata dubu biyu,ya ce"wannan kuma"ya nuna mata kuɗin da za su iya kai wa biyar zuwa sama ya ce "sai a duba ta da yaron ko?"

Azeema ta ce"tabbas ka kawo dabara,don wallahi yaron magana ne kawai ban yi ba,amma kamar bashi da lafiya,ni kaina a tsorace nake wallahi, daÉ—inta ma uwar bata san yadda jariri yake ba da alamu,amma yaron nan ba shi da lafiya"

Da haka suka yiwa Shaheeda magana,bata yi musu ba ta bi su suka nufi asibiti

A can aka duba ta,ita dai babu wata matsala sosai, amma jaririn nata likitoci sun bayar da tabbacin cewa yana É—auke da larurar asthma, wadda alamu ya tabbatar da gadonta ya yi

Hankalin Rabi'u ya tashi sosai,ya koma ya same ta yana tambayarta da yi mata bayani, bata damu ba sosai,kuma bata yi mamaki ba,ta dube shi ta ce"tabbas haka ne, mahaifinsa ya tabbatar min da cewa nashi mahaifin an ce ciwon asthma ne ya kashe shi,babu mamaki don ya samu shima"Rabi'u ya jinjina kai cike da jimami ya ce"Allah ya ji ƙansu baki ɗaya

Kin tanadar wa yaron suna?"

Girgiza kai Shaheeda ta yi, Rabi'u ya ce"ya sunan babansa?"

Shiru Shaheeda ta yi, kafin ta yi shahada ta ce"Mubarak!"

Rabi'u ya ce"to ai kuwa za'a mayar masa da sunan babansa, Allah ya raya shi ya albarkaci rayuwarsa, Allah ya raya mana MUBARAK"

Kallonsa ta yi tana ɗan murmushin yaƙe, don bata so hakan ba,amma gudun kar asirin da ta binne ya tonu ya sa bata yi magana ba, Rabi'u bai kula ba ya ce"me za'a rinƙa kiransa?"

Shaheeda kanta a ƙasa ta ce"a kira shi da Mubarak ɗin sa,ya fi daɗi ma"

Ba su juma ba aka sallame su,bayan an É—ora Mubarak akan magani da ganin likita, sannan ga dokokin da aka kafawa Shaheedan akanshi

Ranar suna Rabi'u ya yi ƙoƙari, don hakika ya yankawa Mubarak banda kayan jarirai da suka yi ƙoƙarin shigowa masu sauƙin kuɗi duk da cewa itama Shaheedan ta siya,ya yiwa Shaheeda ɗinki mai kyau,aka yi taron suna daidai misali, wanda ya saka Shaheeda tsananin farin cikin da ta juma bata yi shi ba

Dukkansu daga Rabi'u har Azeema ba su ɗauke ta komai ba sai ƴar'uwa,sun riƙe ta da zuciya ɗaya,sun cike mata gurbin da ya yi mata saura, to ita kuwa me zata yiwa bayin Allan nan ta biya su?ko ta faranta musu?

Hakan ya sa bayan ta yi arba'in ta fara tunanin ta bi kamfanoni don neman aiki,amma kafin ta fara wannan yunƙurin sai da ta gayawa su Rabi'u

Dukansu sun goya mata baya tare da fatan Alkhairi, Azeema tana murmushi ta ce"ki ce mun kusa zama cele a garin nan,don masu aikin kwamfutan nan Allah kuɗi suke samu sosai,su ne fa za ki ga suna hawa jirgi suna barin ƙasar nan"

Ƴar dariya Shaheeda ta yi, Azeema ta ce"Allah da gaske,ko don ke ma watarana ko ba mu hau jirgi ba ai za mu gani, Allah ya kai damo ga harawa kawai"Shaheeda ta yi murmushi tana girgiza kai,da Azeema ta santa ai ba ma zata fara faɗar hakan ba

Cikin lokaci ƙanƙani ta fara neman aiki,da wani kamfanin software ta fara,bayan ta gama ganawa da Manager ɗin kamfanin ta sanar masa da abin da ta karanta, kai tsaye ya buƙaci ganin takardu

Idanunta suka yi ƙwal-ƙwal,a sanyaye ta ce"ban ƙarasa karatun ba ai, saboda matsalolin rayuwa da suka sha min kai,amma....."mutumin ya katse ta faɗin"ba ki da takardu kuma kike tunani za mu ɗauke ki aiki?"

Shiru ta yi jikinta a sanyaye, kafin ta ce"na iya aikin fa,ku gwada ni ku gani,ban damu ba ko da ace rabin kuɗi za ku bani ba,ni dai ina roƙonku don Allah ku ba ni aiki, ko yaya za ku biya ni zan yi"mutumin ya ƙare mata kallo, ganinta matashiyar yarinya mai jini a jika,kuma kyakykyawa sai ya gyara zama ya ce"to zan ba ki aiki a companyn nan,babban matsayi ma, amma da sharaɗi"

Cikin ɗoki tana murmushi ta ce"menene sharadi?"kai tsaye ya ce"za mu kwana tare,kuma duk sanda na neme ki za ki biya min buƙata,idan kika yi haka I'm ready"

#Nusy_bee

Page 34

Shaheeda dai ko zata ganta a bakin wuta ba zata taɓa canjawa daga Shaheeda ba,don haka ta dube shi a zafafe ta ce"idan karuwanci zan yi ba zan wahalar da kaina na zo nan ina roƙonka aiki ba,na san hanyoyi da yawa da zan yi karuwanci ba sai na wahala wajen wani aikin dabam ba,idan karuwa kake so ba sai ka bada aiki ba,ka san inda za ka same su"ta ja tsaki ta miƙe ta fice daga gidan a fusace

A ranar yini ta yi cikin ɓacin rai saboda abin da aka yi mata,amma hakan bai saka ta karaya ba, washe gari ma ta sake fita neman aikin

Haka ta yi ta yawon neman aiki a kamfanoni,amma rashin takardu ne yake yi mata cikas,na ƙarshe ma ce mata ya yi"ki nuna min wata shaida na cewa kin taɓa yin karatu a matsayin software engineer,na yi miki alƙawarin zan ɗauke ki aiki a kamfanin nan"jikinta a sanyaye ta tashi ta fice daga office ɗin,don dai a yanzu bata da wata shaida,bata sake nadamar banzatar da karatunta akan soyayya ba sai yanzu

Lokacin da take ba wa su Azeema labarin abin da yake faruwa idan ta je neman aiki daga ita har Azeema kuka suke yi, Rabi'u ne ya ja numfashi ya dubi Shaheeda ya ce"Fatima,akwai alamun cewa ba komai kika gaya mana game da kanki ba, lokaci ya yi da ya kamata ki faÉ—a mana komai,kin ga an zama É—aya,kuma ba mu san ta inda zai yiwu mu taimaka miki ba

Na gane kamar ke ba irinmu ba ce, ƴar ƙauye ko yar talakawa, saboda yanayin mu'amalarki da mutane da kuma wayewarki,don Allah ki gaya mana gaskiyar abin da ya same ki idan har kin ɗauke mu kamar yadda muka ɗauke ki"

Babu musu ta goge hawayenta,a hankali ta fara ba su labarinta tun daga tafiyarta karatu zuwa ƙasar Belgium har zuwa lokacin da ta kama haya a gidan nasu,ta ƙarasa cikin matsanancin kuka, saboda ita kaɗai ta san irin ciwon da take ji a duk lokacin da ta tuna mahaifinta ya yi disowning ɗinta,ya bar wa duniya ita, duk da yadda yake tsananin sonta,kuma itama take tsananin sonshi

Kafin ta kammala labarin Azeema ma ta yi kuka har da shiɗewa,shi kanshi Rabi'u sai da ya dake sosai ya hana kanshi zubar da hawaye, labarinta ya dake shi sosai, ya taɓa masa zuciya sosai,a haka ma ta yi juriya,da wata ce tsaf trauma zata jefa ta a cikin wani mawuyacin halin
Chapter 42 · 0% Book details