← Book details Gadar Tsautsayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 51

Sashe 27

Gadar Tsautsayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ni fa zuwa na yi don na gaishe ku na gaya muku na dawo,don kun san yanzu duba handout ma da tunanin assignment kawai ya isa ya sa na manta Allah ya halicce ku a duniya"

Arfa tana yi mata kallon banza ta ce "karatu dai,ni wallahi ban yarda karatun ake yi ba,na fi zargin wata baÉ—alar ake yi da sunan karatu ana raina mana hankali "

Dariya Shaheeda ta yi har tana kwarewa, kafin ta ce"to ai gwara ni,sai da na fake da karatun sannan ƴan iska irinki suke zargina,kar dai ki manta a gabana aka fito da ke daga ɗakin gardi,kar ki manta na san abubuwa da yawa,don haka ki yi rayuwarki nima na yi tawa,idan ba haka ba kuma allura ta tono garma"tana kai wa nan ta miƙe don ficewa daga ɗakin kafin ranta ya ɓaci a yi mara daɗi

Arfa ce ta yi wuf ta shaƙo ta,bata yi wata-wata ba ta sauke mata mari, sannan ta hankaɗe ta,ta fice daga sashen

Ko da ta koma sashen Ummeey ma bata sanar da ita yadda suka yi da matan uban nata ba,ta cigaba da harkar gabanta

Ta ji daÉ—i sosai lokacin da ta buÉ—e Whatsapp É—inta ta ga Arnold ya ajiye mata message,ta yi murmushi ta yi masa reply,bisa Sa'a yana online, suka cigaba da hira, wadda galibi ta karatunsu ce

Washe gari ma Ummeey ta ce ta je ta gaida kakarta innayyo,bata yi musu ba ta je,amma baya sauya zani ba,don yadda suka saba wulakanta ta yau ma haka suka yi mata,ta ja tsaki ta fice daga parlourn

Mummy ce ya finciko ta tana faÉ—in "ke!

Wa kike ja wa tsaki?"

Shaheeda ta yi murmushi ta ce"yi hakuri"sannan ta janye mayafinta ta fice daga parlourn

Ko da ta koma gida ma bata yi wa mahaifiyarta batun komai ba, kamar dai jiya,ta cigaba da sabgoginta

Tsawon kwanaki biyar da dawowarta kafin Alhaji Yusuf ya dawo,a tsakiyar gidan ta daka tsalle ta É—ane shi tana ihun murna,ya rungume ta cikin tsananin farin ciki da kewar Æ´ar tashi

Hannunta ya kama suka nufi sashensa,matansa da sauran yaran suka rufa musu baya,matan kowacce da abin da take wassafawa a ranta

Kamar yadda ya saba suka baje a babban parlourn shi da kuma yaranshi da matan ana hira,amma sai ya fi karkata akalar hirar ga ƴar gold ɗinsa Shaheeda, wadda ta taƙarƙare tana ta ba shi labarin karatunta da rayuwarta ta Belgium

Ba su juma sosai ba suka amshi tsarabarsu kowa ya tafi,amma ban da Shaheeda da take sake buÉ—e sabon topic na hira

Hajiya Ruƙayya da take da girki ranar ta dube su fuska a ɗaure ta ce"Alhaji ya kamata fa a ce ka sallami yarinyar nan, kowa ya tafi ita me take yi har yanzu?"

Kai tsaye Alhaji Yusuf ya ce"hira da ubanta mana"

Hajiya Ruƙayya ta ce"to sai ta tafi sai da safe ko?

Don gaskiya saboda wannan ƙatuwar yarinyar ba za'a shigar min lokaci ba,dama dai ƙarama ce sai na yi uzuri"

#Nusy_bee

Page 22

A kaikaice Shaheeda ta kalle ta, sannan ta ɗauke kai, Abba ya dubi Hajiya Ruƙayya fuska a ɗaure ya ce "kishi kike yi da ita?

Saboda ba ke kika haife ta ba?"tsam Shaheeda ta miƙe, Abba ya ce "dawo ki zauna Fatima"

Shaheeda ta girgiza kai ta ce "Abba wani uzuri zan yi yanzu zan dawo"ta yi saurin ficewa daga parlourn don bata son rigima, kuma ta san halin Hajiya Ruƙayya,a kaf matan gidan ta fi kowa rigima

Tana zuwa bayan ta yi wanka ta yi shirin kwanciya kan gadon ta ta haye ta cigaba da chat da Arnold, wanda har yanzu take mamakin sabo da shaƙuwar da suka yi,kuma take matuƙar jin sa a ranta

Shaheeda ta cigaba da rayuwarta yadda ta saba a cikin gidan,ba ta shiga harkar kowa,amma duk wanda ya shiga tata ba'a rabuwa lafiya,kuma Abba ya goya mata baya sosai

A ɗaya ɓangaren kuma shaƙuwarsu da ta ƙara ƙarfi tsakaninta da Arnold, wanda har zuwa wannan lokacin babu wanda ya san da zamansa, Ummeey dai ta kula ta sake liƙewa waya,amma bayan haka babu abin da aka sake ganowa

Yawancin hirarrakin nasu akan abin da ya shafi course É—in da suke karanta ne,na software engineering,ya koya mata abubuwa da yawan gaske,wasu kuma yana gaya mata yadda zata yi

A haka ta cinye hutun session gaba É—aya,sau uku Muyassar yana dawowa a wannan tsukin amma gaba É—aya bata wani ba shi attention sosai

Ta cinye hutunta lafiya,sannan kuma ta koma don É—orawa daga inda ta tsaya

Ranar da zata tafi kowa ya yi mamakin yadda ta kasance cikin farin ciki da É—oki,amma babu wanda ya zargi wani abu, musamman yadda suka san Shaheeda take son karatun nan nata

Muyassar ne ya mayar da ita makaranta,abin da ya ba shi mamaki ganin mutumin da ya zo zai É—auke su ya kai su makaranta,ba kowa bane sai Arnold,kallo É—aya Muyassar ya yi masa ya É—auke kai,shima dai kallo É—ayan ya yiwa Muyassar É—in sannan yake tambayarta hanya

Tana murmushi ta ce"hanya lafiya ƙalau,mun dawo

Arnold ga yayana Muyassar,yaya Muyassar ga babban abokina kuma malamina Arnold"ta yi maganar cikin harshen turanci

Murmushi Arnold ya yi ya miƙawa Muyassar hannu suka yi musabaha, Muyassar ya daure ya miƙa masa,suka gaisa, sannan Muyassar ya dubi Shaheeda da take ta murmushi ya ce "to Shaheeda,ni dai zan wuce ko? tunda kin ga kin samu mai raka ki"ya karasa maganar yana murmushin yaƙe

Shaheeda ta ce"kai yaya!don Allah ka raka ni mana,mu je tare

Ka ƙarasa ladanka Please!"ta ƙarasa a shagwaɓe

ÆŠan murmushi ya yi kawai yana satar kallon Arnold da ya naÉ—e hannu yana kallon su yana lumshe kyawawan idanunshi,da hakan ya zamar masa kamar É—abi'a, sannan ya kalli Shaheeda ya ce "wani uzuri zan É—an yi ne,but I promise you zan zo nan da few hours"

Babu yadda ta iya ta jinjina kai,ya ce "to yayana,sai ka zo, Allah ya tsare min kai a duk inda kake"ya yi murmushi sannan ya tari taxi ya shiga ya bar wajen

Su ma motar Arnold suka faÉ—a suka wuce zuwa makaranta,suna zuwa Shaheeda ta sauka ta wuce hostel É—in su,shima ya wuce nasu

Da yamma Muyassar ya dawo kamar yadda ya yi alƙawari,suna zaune a wajen da ɗalibai suke zama karatu,suna ta kallon mutane da suke wucewa jefi-jefi Muyassar ya dubi Shaheeda ya jefo mata tambaya

"Shaheeda menene alaƙarki da wannan arnen?"

"Wanne arne?"ta faÉ—a tana kallonsa da fuskar mamaki

Ya ce"yaron da ya É—auko ki a airport É—azu "

"Oh!wai Arnold?shine arne?

Kawai abokina ne fa,kuma yana koya min karatu, shikenan fa"

"To amma ko ma dai yaya ne ya kamata ki san irin mu'amalar da za kuyi da shi,ko da a ce shi É—in musulmi ne, bana son wannan mu'amalar da take tsakaninku ta wuce misali Please"

Shaheeda ta ce "yaya na san me nake yi fa,babu abin da zai faru sai alkhairi in sha Allah"

Muyassar ya ce"to Allah ya sa"ta amsa da "Ameen"sannan suka sauya hira

Kwanan Muyassar biyu a Belgium ya koma UK, Shaheeda kuwa ta cigaba da karatunta cikin kwanciyar hankali

A hankali rayuwa take gungurawa Shaheeda a makaranta,tana cigaba da karatunta cikin kwanciyar hankali,a gefe guda kuma ba tare da ta ankara ba, soyayya mai tsananin ƙarfi ta sarƙe tsakaninta da Arnold,wanda zuwa lokacin hatta mamanshi ta san Shaheeda,don tana yawan kawo musu ziyara har makarantar

Muyassar yana iya bakin ƙoƙarin sa na ganin Shaheeda ta rabu da Arnold don tuni ya fara ƙyanƙyaso kamar akwai soyayya tsakaninsu,hankalinsa ya tashi sosai,amma kuma da ya tuna babu aure a tsakaninsu sai hankalinsa ya kwanta

Inda tashin hankalin yake shine lokacin da Arnold ya kammala karatunsa, Shaheeda ta tabbatar da cewa tafiya zai yi,sai kawai ta fashe masa da kuka

Da ƙyar ya lallashe ta, cikin karsashi ya ce"ki kwantar da hankalinki, yanzu lokaci ya yi da ya kamata iyayenmu su san halin da muke ciki,mu sanar da su, saboda kin ga lokacin karatunmu yana ta ƙarewa,ni na gama nawa ma, saura naki"

Kallonsa ta yi da sauri,ta ce"ba zai yiwu ba,aure tsakanina da kai ba zai yiwu ba Arnold"

Gabansa ya buga,ya zauna a kusa da ita a É—an rikice yana kallonta, kafin a hankali ya ce"meyasa? menene dalilin da ya sa kika ce haka?

Ko kin daina so na?"

Kai tsaye ta ce"soyayyarka na tabbatar da ita zan bar duniya,sai dai aure tsakanina da kai ba zai yiwu ba, saboda bambancin addini da yake tsakaninmu da kai"

Shiru Arnold ya yi yana kallonta, kafin ya lumshe idanu a hankali ya buÉ—e ya sake zuba mata su , cikin sanyin murya ya ce"

"To me zai hana ni da ke kowa ya yi addininsa tsakaninmu?

Ni ban damu ba ma,ko haifar yara muka yi su bi addininki babu matsala,ni dai ina sonki"

Shaheeda ta girgiza ta mayar da kan nata jikin kujerar da take zaune tana sauke numfashi,a hankali ta ce"hakan ba mai yiyuwa bane Arnold,a addinina bai halatta na aure ka ba,alhali kai ba musulmi bane"

Arnold ya ce"amma akwai wata ƙawar mahaifiyata da ƴarinyarta ta auri musulmi"

Shaheeda ta ce"ai dama ga mu mata ne,ga maza kuma babu matsala sosai"

Arnold ya girgiza kai cikin ƙunar zuciya ya ce"kenan a musulunci ana tauye mace kenan?

Da gaske ne bata da ikon yin abin da take so sai namiji?"

Shaheeda ta yi saurin girgiza kai,ta ce"aure a musulunci yana nufin namiji ne shugaba, shugabancin nashi bai tsaya iya bayar da Umarni ba,har ɗauke dawainiyar auren duka,don haka ya wajaba ga macen ta yi masa biyayya a abin da bai saɓawa Allah ba,to tun fari idan ta auri wanda ya kasance ba musulmi za'a iya samun gagarumar matsala, shine dalilin da ya sa"

Arnold ya jinjina kai a sanyaye,ya ce"na fahimta

Yanzu menene abin yi?

Fatima kin san ina sonki sosai,kuma ba zan iya rasa ki ba,kuma bana fatan na ga wannan ranar a rayuwata,ki taimaka min Fatima,kar ki guje ni "

Shaheeda ta girgiza kai tana goge hawayenta ta ce"ba zai yiwu ba na gaya maka, muddin ba ka musulunta ba na tabbatar ba zai yiwu na aure ka ba"

Shiru ya yi na wasu seconds, kafin ya ce"to idan na musulunta zan iya?zai yiwu ki aure ni?"
Chapter 27 · 0% Book details