Sashe 22
Gadar Tsautsayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shaheeda da ta yi tsammanin wani abu dabam, saboda sanin halin Arfa,ta yi fari yadda ta saba ta ce"thanks"
Muyassar da yake kallonta yana murmushi ya raɗa mata a kunne"ƙwaila ƙanwar bera!"
Diddira ƙafa ta fara yi na shagwaɓa, Muyassar ya riƙe hannunta yana murmushi,sauran ƙawayenta kuma suna dariya,ya ja hannunta suka koma kan yanka cake ɗin
"Muyassar wajenka na zo fa!"s cewar Arfa tana danne ƙuncin da take ji a ranta game da wannan tsinanniyar yarinyar da ta addabi kowa,a cewarta
Kafin ya yi magana Shaheeda uwar tsiwa ta kalle ta tana murguɗa fuska ta ce"sai dai fa ki yi haƙuri ki jira, yanzu yana cikin lokacin ƙanwarshi ne abin sonshi,amma idan mun gama zan bar miki shi"ta ƙarasa maganar tana murmushi
Cikin ɓacin rai Arfa ta dube ta tana faɗin "ke ban yi miki magana,ko shi ba shi da baki ne?
To bana son rashin kunya,dama an gaya min cewa ba ki da kunya,idan kika yi min sai na zane ki wallahi"
Shaheeda ta gatsine fuska ta ce"tabÉ—ijam! wallahi mai dukana a yanzu sai dai ruwan sama,gidan ubana fa kika zo kina son ki janye min yayana sannan kike maganar dukana, wallahi wuce nan,ki tafi,idan kina da muhimmanci a wajensa zai zo inda kike"Muyassar ya dubi Shaheeda wadda sam bai yi mamakin rashin kunyarta ba in dai ita ce, fuska a haÉ—e ya ce"Shaheeda kar na sake jin bakinki"
Yana kai wa nan ta cafke da faÉ—in "sai in yi mata shiru ta yi ta gaya min son ranta?"
Muyassar ya ce"amma ai ta girme ki ko?to bana son rashin kunya,idan ba haka ba kuma za mu raba hanya da ke"ya dubi Arfa ya ce
"Madam a ɗan ba mu waje,ki zauna wajen su Mamie,idan na gama in sha Allah zan shigo "ta bi shi da kallo cikin ɓacin rai, Shaheeda ta faki idanun Muyassar ta yi mata gwalo
Rai a ɓace Arfa ta koma sashen yayarta ta gidan,wato Hajiya Ruƙayya, wadda ta yi ɗaiɗai a parlounta tana ba wa cikinta haƙƙinsa,tana shiga ko sallama bata yi ba ta samu waje ta zauna idanunta yana tara ƙwalla
Hajiya Ruƙayya ta ɗago tana kallonta da mamaki, kafin ta ce"ikon Allah!
Arfa yaushe kika zo?"
Ƙwallar idanunta ta goge ta ce"ban daɗe da zuwa ba aunty"
"To kukan me kike yi daga zuwa?"
Hawaye suka sake zubowa Arfa,ta dubi Hajiya Ruƙayya ta ce"aunty wallahi na tsani yarinyar nan,kin san ina tsananin son Muyassar,nema take yi ya shiga tsakanina da abin da nake so,amma wallahi zan sauke mata dattin da yake cikin kanta,gashi shima sai ya yi ta bin ƙaramar yarinya tana saka shi yin abubuwa kamar wani mara hankali,aunty wallahi ba zan iya zuba idanu ina kallonsu a haka ba, salon ta ƙara girma ma a ce za'a haɗa su aure"
Hajiya Ruƙayya ta ce"don Allah daina wannan tunanin,idan shi mahaukaci ne uwarshi ai ta san me take yi,don haka ki kwantar da hankalinki,ki ci gaba da neman soyayyarshi,idan ma ya ƙi yiyuwa ni sai na yi wa uwar Magana, yadda na shigo gidan nan ke ma ta matsa miki hanya ki shiga gidan ɗanta,ba wani wayo gare ta ba"
Arfa ta goge hawayenta ta ce"amma aunty wallahi bana ƙaunar yarinyar nan,sam bata da tarbiyya,ta raina mutane,ga haushin yadda take mannewa Muyassar kamar wani ubanta "
Kar ki damu, za'a yiwa tufkar hanci,amma tabbas sai kin mallaki Muyassar Arfa"
#Nusy_bee
Page 18
Hankalin Arfa ya kwanta sosai,don ta san wacece yayar Tata Hajiya Ruƙayya,har ma ta saki jiki ta ci abincin da masu aiki suka jera mata
Da daddare ta shirya cikin ƙananan kaya da suka bayyanar da surar jikinta ta tafi sashen Muyassar,wanda ya dawo nan tun bayan kammala karatunsa na tertiary da ya yi a abroad, Abba ya buɗe masa babban Company ya naɗa shi CEO
Yana zaune yana duba wasu file yana shan green tea É—in da ya sa a dafo masa ya ji knocking,da farko ya yi tsammanin Shaheeda ce, wadda ta ce zata kawo masa abincin da ta dafa masa,don haka ko kallon sashen bai yi ba ya ce"come in!"
Shiga ta yi tana girgiza jikinta cikin salon jan hankalin ɗa namiji, yadda ta lafta turare da yadda ya ji ba'a yi sallama ba ya sa ya ɗaga kai da sauri yana kallonta,ya ɓoye mamaki da ɓacin ran da ya ji sun saukar masa a lokaci ɗaya ya bi ta da kallo, kafin ya dake ya ce"welcome!"
Murmushi ta yi ta samu waje ta zauna,ta zare siririn mayafin da yake kanta, dogon gashin ta ya sauka har bayanta,a hankali ta cire rigar da take jikinta ta after dress tana kallonsa tana murmushi
Fuska a É—aure yake kallonta, kafin ya ce"lafiya dai ko?"
Cikin narke murya ta ce "ziyara na kawo maka,na zo taya ka hira"
Taɓe baki ya yi sannan ya ce"na gode,amma da kin ɗan koma, kin ga aiki nake yi,idan na gama zan zo na same ki"
Tana shirin yin magana Shaheeda ta yi sallama,ya ɗaga kai yana kallonta yana amsawa da murmushi akan fuskarsa, ta ƙaraso tana gyara riƙon tray ɗin hannunta
Tashi ya yi ya amshi tray É—in yana murmushi yana faÉ—in "birthday girl!
Ya taron?"
Dariya ta yi ta ce "kai yaya!
Wani ma ya ji fa sai ya ce ba da kai aka sha shagali ba,ka cinye min cake,don ma dai kai ka siya"
Dariya ya yi ya ce"ba zan kula ki ba Fatsima,ya gajiya?"
Harararshi ta yi tana tura baki ta ce"nice Fatsima?"
"A'a ba ke ba,waccan"suka yi dariya a tare cike da nishaÉ—i
Zama suka yi suka fara cin abincin da ta kawo a tare, Arfa da ta ƙule ta bi su da kallo ta kawo wuya,ta dube shi cikin fushi ta ce"amma Muyassar wannan wanne irin wulaƙanci ne?
Na zo wajenka amma za ka bagarar da ni kana kula wannan yarinyar mara kunya mara tarbiyya!"
Muyassar ya dube ta,amma kafin ya yi magana Shaheeda ta yi shewa ta ce"cassss!
Wato ma nice mara tarbiyya ba ma ke ba ko?
Ko don an ce gwano baya jin warin jikinsa?"
Rai a ɓace Arfa ta kalli Shaheeda ta ce"ke yi min shiru kafin na ɗauke ki da mari,mara kunya mara tarbiyya kawai!"
Muyassar ya riƙe hannun Shaheeda da sauri yana faɗin"enough Shaheeda,bana son sake jin wani abu daga bakinki idan har na isa da ke,kuma idan har kina amfani da tarbiyyar da Ummeey ta ba ki"
Shaheeda ta jinjina kai cike da gamsuwa ta ce"kuma fa maganarka gaskiya ne babban yaya,idan ina da tarbiyya babu dalilin da zai saka na rinƙa kula karnuka suna yi min haushi,kai ma ya kamata ka san yadda za ka yi da su kar a gansu a tare da kai mutuncinka ya zube"
Muyassar ya dafe kai ya bi Shaheeda da kallo cike da takaici,bai yi mamakin wannan ɗanyen aikin nata ba in dai ita ce, abin da ya fi haka ma zata yi, saboda sam bata taɓa barin bashin magana a rayuwarta,bata da haƙuri ko kaɗan idan aka taɓo ta,a hakan ma don Ummeey tana tanƙwarata ne
A nutse ta juya zata fita, Arfa da ta je ƙarshe ta shaƙo mata wuya, ba tare da ɓata lokaci ba suka kacame da dambe,don duk da cewa Arfa ta girmi Shaheeda da wajen shekaru huɗu zuwa biyar hakan ba ya ba wa Shaheedan tsoro ko kaɗan
Da ƙyar Muyassar ya raba damben, sannan ya ja Shaheeda gefe ya rufe ta da faɗa
"Ba cewa na yi ki yi shiru ki wuce ba?
Ke dole dai sai kin nemi magana hankalinki zai kwanta? wai meyasa ba ki da haƙuri ne ko kaɗan?a haka kike son ki tafi Belgium ɗin da wannan shiriritar?
To su ba za su É—auka ba,idan kika yi musu wannan rashin hankalin zane ki za su yi,silly girl kawai!!"
Tana huci ta ce"amma yaya kana kallo ta rufe ni da duka ko?ko ni jaka ce irinta da zan rufe idanu ta rinƙa dukana?
Wallahi ko yanzu ta sake dukana sai na rama!"
Arfa da ke gefe tana mayar da numfashi,don bata saba dambe ba,ta ce"sai dai uwarki ce jaka,ba ni ba"
Babu ɓata lokaci Shaheeda ta ce"uwarki ta fi kama da jaka wadda babu abin da ta iya sai sakin ki kamar tinkiya kina liƙewa maza"
Muyassar ya buge mata baki ya ce "ba na ce ki yi shiru bane Shaheeda?"
Ƙwalla tana taruwa a kwarmin idanunta,amma don masifa da ƙi-faɗi ta hana ta zuba ta dube shi tana kumbura fuska ta ce"to ba kana jinta tana zagin uwata ba sai na zuba mata idanu?
To wallahi ta sake zagina sai na dake ta"
Muyassar ya dafe kai ya ce"Shaheeda wuce cikin gida,bana son ɓacin rai "babu musu ta wuce tana waƙar"mai wasa da maza karya! tunda na ganta na raina ta"
Girgiza kai kawai Muyassar ya yi, cikin ɓacin rai ya mayar da kallonsa ga Arfa wadda ta sake ƙanƙance idanu alamun Masifa, saboda waƙar da ta ji Shaheeda tana yi,amma kafin ta fara magana Muyassar ya daka mata tsawa
"What's wrong with you Arfa?
Kin zo kamar abin arziƙi kin kama dambe da Shaheeda?wannan wacce iriyar wauta ce?"
Cikin ɓacin rai ya ce"oh duk zagi da maganganun da ta gaya min ba ka gani ba sai nawa da na so sauke mata dattin kanta?"
Kai tsaye ya ce"na san me nake yi Arfa, lokacin da Shaheeda ta shigo parlourn nan ko kallonki ba tayi ba,amma sai da kika shiga sabgarta kika janyowa kanki magana"
Kuka Arfa ta saka ta ce"lallai ma Muyassar!
Wato goya mata baya za kayi ko?
Na gode!"ta miƙe a fusace ta bar wajen,shima ya ja tsaki sannan ya zauna don fara abincinsa da ya fara sandarewa
Ita dai Shaheeda bata sanar da Ummeey abin da ya faru ba,asalima ko a fuska bata bari wata alama ta bayyana ba, musamman ma da ta samu ta rama abin da Arfa ta yi mata, wannan ya fi komai yi mata daÉ—i
Ita kuwa Arfa tana kuka ta shiga sashen Hajiya Ruƙayya, Hajiya Ruƙayya ta ɗago daga sakawa Usman diaper da take yi ta zuba mata idanu da mamaki, Arfa tana shiga ɗakin ta zube a gefen gado tana gursheƙen kuka
"Me kuma ya faru?"