Sashe 6
Gadar Tsautsayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shiru Mama ta yi na some seconds, kafin ta ce"eh tabbas na tuna, Hajiya ya za'a yi na manta wadda ta yi min alkhairin da har yanzu nake mora?
Ai ni babu abin da zan ce miki ni da Habu sai fatan Allah ya biya ki da alkhairi, Allah ya saka miki da mafificin alkhairi"
Roxy ta yi murmushi tana faÉ—in "babu komai Mama,ina Habu da Æ´an'uwan nashi suke?"
Mama ta ce"ai da yake an saka shi a allo ne,suna makarantar allo,sai zuwa anjuma za su dawo"
Roxy ta yi É—an jimmm kafin ta ce"ba sa zuwa makarantar islamiyya ne Mama?"
Mama ta yi É—an murmushi ta ce "da dai suna zuwa,amma kin san abu na yau da gobe,sai abubuwan suka fara yawa, abinki da hannu É—aya, tunda kin ga mahaifin nasu ya rasu babu jumawa da tsintar Habu,to shine dalilin da ya sa suka koma allo kawai"
Roxy ta jinjina kai cike da jimami ta ce"Allah ya ji kan shi da rahama,to boko kuma fa?"
Mama ta ce"suna zuwa,habu ma ya fara zuwa wannan zangon da suka koma makarantar "
Roxy ta jinjina kai cike da gamsuwa ta ce "to Allah ya taimaka,zan samu ganinsa?"
Mama ta ce"eh sun kusa shigowa ma,ba za su wuce mintina goma ba, ƙarfe biyar suke tashi"
Roxy ta gyara zama ta ce"babu damuwa, bari na jira shi ya dawo,za mu gaisa"
Amra da take ta kallonsu cikin takaici ta dubi Roxy fuska a daure tana faɗin"Malama idan bata min lokaci za ki yi Just tell me,kin kawo ni wajen da za'a kashe ni da ƙazanta,ga warin talauci ya ko'ina,kin san ban saba rayuwa a irin wannan wajen ba,idan ke kin saba fine,but idan ba za ki taho ba ni sai na tafi "
#Nusy_bee
Page 5
Jiki a sanyaye Mama ta ɗago tana kallon Amra wadda ta yi maganar fuskarta a ɗaure,da alamun ɓacin rai ƙarara a kan fuskarta,don har ga Allah wannan mummunan gidan ya fara isarta,ga wari ga tsantsani da ya ishe ta,ta rasa yadda aka yi Roxy da ba ta Rayuwa a Nigeria ma ta san da irin wannan wajen a ciki
Kafin wani ya sake magana Roxy ta gyara zama tana murmushi ta ce"ba wani abu ai,komai ya yi gaba,amma idan aka koma baya za'a ga tushiyar dawa,ko na ce asalin ungulu,kusan kowacce mace a bariki musamman Æ´ar talaka za ki ga kuÉ—i ta zo nema ne, don bata sanshi ba,kuma tana son É—anÉ—ana daÉ—insa,to ba kowa bane ba ya iya jurar talauci ya shiga duniya,kin ga dai kamar Mama,uwa ta gari"ta karasa magana tana murmushi "
Kalaman Roxy kamar an watsa mata ruwan zafi a zuciya haka ta ji su,amma sanin halin Roxy na iya mayar da magana ya sa ta yi shiru,don sanin kanta ne Roxy sam bata da haƙuri,kuma bata da ɗaga ƙafa,muddin aka shiga gonarta,sannan ga tsananin wayo da hikima,ga basira, shiyasa take gudanar da rayuwarta yadda take so a ƙasashe zuwa garuruwa
Bata sake bi ta kan Amra ba, wadda ta yi kasaƙe tana kallonta,ta koma satar kallon Mama wadda fuskarta ta nuna alamun jin daɗin amsar da aka mayar mata sakamakon tsangwama da cin mutuncin da ta nemi ta yi mata
Hira suka cigaba da yi da Mama da Roxy, cikin hikima da wayon da Allah ya hore mata take jefa wa Mama tambayoyi game da Habu, bata yi mamakin jin cewa yana da larurar asthma ba,dama ta san da batun tun ba yanzu ba
Cikin damuwa Mama ta ɗora da batun "yanzu lokaci ne na damuna,ga yanayin zafi,ga kuma iskar gari,ciwon nashi yana yawan tashi,don ma wani lokacin sai mun haɗa da neman taimako a wajen mutanen arziƙi,kuma alhamdulillah ana samu,kin ga ko shekaranjiya da ciwon nashi ya tashi Musa ɗan maƙocinmu Malam Lado ne ya kai shi kyamis aka duba shi,ba ki ga magungunan da ya siyo ba,har da sabon abin zuƙar"
Roxy ta yi shiru na É—an lokaci tana jinjina kai,tana shirin yin magana sallamar yara ta katse ta
Mama ce ta amsa sallamar,suka shigo yaran
Su biyar ne,biyu mata sai uku maza babban da me bi masa maza ne,sai mata biyu da suke bi musu,sai ɗan ƙaramin su da bai fi shekara uku ba, wanda duk da wahalar rayuwa da ƙangin talauci da suke ciki bai hana kyawunsa bayyana ba, wanda ya zarce ya yi fintinkau wa sauran
Kallon kayan jikinsa take yi,rigar gwanjo ce,sai wando yadi,su ma dai ragowar yayyen nasa babu wani mai sutura mai kyan gani, duk da cewa tsaf tsaf suke,amma ƙangin talauci ya ɓoye kaso mai yawa na tsaftar ta su
Da girmamawa suka gaida Roxy da Amra, Roxy ta amsa tana murmushi tana tambayarsu sunayensu É—aya bayan É—aya,duk da cewa ta gane Habu,suka gaya mata É—aya bayan É—aya Sannan suka wuce don ajiye allunansu
A jikinta ta rungume Habu tana cigaba da yi masa wasa tana murmushi,shi kuwa sai bin ta da kallo yake yi, kasancewar ba shi da sabo,kuma bai santa ba, gashi kuma ba mai yawan magana ba
Ta ɗan juma tana wasa da yaron,ji take yi kamar kar ta rabu da shi,ita dai Amra tana tsaye akanta kamar wata sanda tana kallon su cikin takaicin wannan ɓata lokacin da Roxy take yi musu
Sun ɓata wajen awa guda a gidan,har hira Roxy ta yi da yaran matar kafin ta yi musu sallama,ta direwa matar 100k ta ce a mayar da yaran makaranta, godiya sosai suka yi mata,ta janyo hannun Habu tana murmushi ta ce "autan Mama in tafi da kai?"
Bai yi mata kara ba ya girgiza mata kai yana komawa jikin Mama ya rungume ta,suka yi Æ´ar dariya, Mama ta ce "ai shi wannan ba'a bayar da aron shi,na Mamansa ne,daga shi sai ita"
Roxy ta yi ƴar dariya tana faɗin "to yaran mamansa, Allah ya bar ƙauna tsakaninka da Mama,ga wannan ku sha Sweet kai da yan'uwanka"ta faɗa tana miƙa masa rafar ɗari biyar
Tsayawa ya yi yana kallonta, Mama ta ce"a haba!
Kin biya musu kuɗin makaranta yanzu kuma za ki ƙara wani kuɗin?
Don Allah ki bar shi, wallahi mun gode Allah ya saka da alkhairi"
Roxy tana murmushi ta ce"ayya Mama!abin da ba ki sani ba ni ƙawar Fauziyya ce kafin rasuwarta,mun haɗu da ita a secondary,a wancan lokacin Allah bai taɓa nufa na zo gidansu ba,amma bayan rasuwarta na ji ina sha'awar zuwa na ganku,sai na same ku a cikin jarrabawar ubangiji,kuma kin ga Fauziyya ta yi min babban taimako lokacin da tana makaranta,duk sanda na samu matsala a makaranta ita take taimako na ta fitar da ni daga ciki,ba zan manta halaccinta ba
Ni dai yanzu roƙon da nake yi miki shine ki ɗauke ni a yadda kika ɗauke ta"
Murmushi sosai Mama ta yi,tana tuna babbar Æ´arta Fauziyya, wadda ta rasu shekaru bakwai baya yanzu,a hankali ta ce"to Allah ya saka miki da mafificin alkhairi"
Roxy ta ce"Ameen Mama, Allah ya ji ƙan Fauziyya da baba, Allah ya albarkaci rayuwar ƙannenta
Wannan jihadi da kika yi Allah ya saka miki da alkhairi "
Mama ta yi É—an murmushi ta ce"har zuwa yanzu ba ki sanar da ni sunanki ba"
Roxy ta ce"kin manta sanda na zo wancan karon na gaya miki?
Sunana Zainab, kuma a yanzu ina jihar Kaduna ne da zama"
"Allah sarki!
A wanne gari kike a Kadunan?ai mahaifinsu ma É—an can ne"
Roxy ta ce"a cikin garin Kaduna nake,a unguwar dosa,to Mama za mu tafi,sai idan na sake dawowa "Mama ta fara yi wa Roxy godiya sosai,ita dai Amra har yanzu tana tsaye tana kallon Roxy da tsananin mamakin yadda halayenta da dabi'unta suke canjawa kusan kowacce daƙiƙa a rayuwarta
Babu abin da Roxy ta tsana a duniya sama da ƙarya, ƙarya ba ɗabi'arta ba ce ko kaɗan, kuma bata jituwa da mai yinta,amma sai gashi tana ta zubo bayanin da take da yaƙinin duka ƙarya ne,a gaban waɗannan mutanen da take kallon basu da maraba da bola a wajenta
Ba su sake É—aukar lokaci ba suka yi wa Mama da yaranta sallama suka fice daga gidan, zuciyar Amra fal da tambayoyi kala-kala
Adaidaita sahu ɗaya suka shiga,sai dai ba su yi nisa ba Roxy ta sauka,ta shige wasu lunguna ta ɓacewa ganinsu, Amra ta bi ta da kallo tana taɓe baki
*MALIYA ESTATE*
"Hooo Hajiya innayyo tamu,ko kewarmu ba ki fara yi ba ne?
Kar ki manta fa, tafiya za mu yi, Allah ne kaÉ—ai ya san lokacin da za mu sake waiwayar Nigeria"a cewar Iman tana rausayar da kanta tana yiwa innayyo magana, mahaifiyar Alhaji Yusuf Maliya
Wani kallo innayyo ta watsawa Iman, sannan ta sake jefawa su Surayya da suke dariya wani mugun kallo,ta ce"ko me za ki ce sai dai ki ce,duk wasu yan kayan da na siya saboda motsa baki kin sace kin cinye, to wannan ahir É—inki"
Zaro idanu Iman ta yi,su kuma su Surayya suka kwashe da dariya, Amina har da taɓawa iman kunne, Iman ta galla mata harara,sannan ta dubi innayyo ta marairaice tana faɗin "haba innayyo ta!
Daga yau ne fa, gobe iwar haka ma mun bar ƙasar miki ƙasar ma"
Innayyo ta taɓe baki tana girgiza kai,ta ce"Ni wannan karatu naku da sai an tafi wata uwa duniya ba wai ina son shi bane,kawai dai ban yi magana bane saboda na ga baban naku ya dage, sannan kuma akwai masu yi muku baƙin ciki da hakan,tabbacin alkhairi ne karatun kenan"
Tuni suka mayar da hankalinsu gaba É—aya kan innayyo, ba don sun yi mamaki da maganganun innayyo ba, dama sun saba da jin abin da ya fi haka daga bakin innayyo akan Ummeey, kasancewar kaf sirikanta babu wadda ta tsana kamar Ummeey,duk da biyayya da ladabin da take yi mata
Wannan sanannen abu ne a wajen iyalan Maliya gaba ɗaya,wani abin ma da ƙarin ƙiyayyarta baiwar Allah Ummeey take samu, inda kawai take samun sa'ada shine soyayyar da mijinta yake yi mata,duk da matansa uku kuma ita ce uwar gida amma soyayyar da yake yi mata dabam take