← Book details Gadar Tsautsayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 51

Sashe 14

Gadar Tsautsayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ɗaure fuska ta yi,ta ce"kin ga wata matsala ne, I'm okay mana"ta ƙarasa faɗa tana juyawa ta koma bakin window ɗin da take tsaye

"But kukan me kike yi?"Hanna ta jefa mata tambaya, Roxy ta juyo ta kalle ta tana faÉ—in "kuka kuma?"

Hanna ta ce ga hawaye nan a idanunki,kuka kike yi mana"Roxy ta yi É—an murmushi,ta juya ta sake fuskantar windon tana goge hawayen da ke fuskar tata, kafin ta ce"I need space,can we discuss leter?"

"But Carlos yana jiranki fa Roxy!

Why na?me yake faruwa ne?kina da wasu aminai bayan mu ne da ba za ki iya gaya mana matsalarki ba?

Please Roxy!"juyowa ta yi tana kallonta, kafin ta ce"kina da wata alaƙa da abin da ya dame ni ne?"Hanna ta girgiza kai,kai tsaye Roxy ta ce"so ba Ni waje!

Maganar Carlos kuma ki ce ya dawo anjuma,idan ya wuce anjuma kuma shi ya rasa, I'm leaving this country first to thing tomorrow morning "Hanna ta kalle ta kawai, kafin ta juya ta fice daga ɗakin don isar da saƙonta, Roxy ta faɗa kan gadonta ta lumshe idanunta,tana jin da zata yi kuka ma da ta rage raɗaɗin da yake taso mata

*DSS HEADQUARTERS, KANO STATE, NIGERIA*

"CSO Haisam Abdulmalik Madaka!

A last meeting da muka yi da kai mun yi magana,inda ka tabbatar mana za ka iya kama yarinyar nan ka dawo da ita,ta fuskanci doka,amma abin mamaki har yanzu shiru,babu wani feedback na a zo a gani,me yake faruwa ne?"

Haisam ya ɗaga kai ya kalli state director jiki a sanyaye,bai taɓa jin ya muzanta irin na yau ba,amma ɓacin rai da shan alwashin da yake ciki sun haura muzantar da yake jin ya yi

A hankali ya miƙe don bayar da ba'asi

"Operation É—ina ya yi failing,amma zan sake trying in sha Allah "

"Amma an ce ka bi ta har ƙasar Spain inda kuka saba harka da ita,me ya faru baka kamo ta ba?"

Kai tsaye ya ce"wani slide mistake ne ya faru,amma very soon zan yi fixing É—insa"

Shiru office É—in ya yi,sauran abokan aikin nashi suna jifansa da wani kallo,kafin state director ya cigaba da faÉ—in"yanzu ka yarda yarinyar tana da kaifin basira fiye da tunanin ka?"

Babu ko shakka Haisam ya jinjina kai

SD ya yi murmushin takaici ya ce"to yanzu za ka bar mu mu yi aikinmu ko?tunda zuwa yanzu ka gane ba gazawa muka yi ba,da kake neman nuna mana ba mu iya komai ba"

Haisam ya ce "I'm sorry sir!ko a baya ma ba raina iyawarku na yi ba,kawai dai ina da ƙwaƙwƙwaran sanin cewa zan iya kama ta,kuma...."

"Sai kuma gashi ta rusa kwarin naka!

Ko sai na gaya maka abin da ta yi maka,kowa ya ji sannan za ka bar cika mana baki?"

Shiru Haisam ya yi ba tare da ya yi magana ba, kanshi a ƙasa, SD ya ja tsaki ya ce"wannan operation ɗin ya bar hannunka,zan mayar da shi hannun wanda ya dace,kuma zai iya abin da ya dace

SO Shuaibu Ahmad musawa,kai za ka yi taking over na wannan aikin"Shuaibu ya dara yana faÉ—in "noted sir!"

A Ranar dai haka taron ya watse zuciyar Haisam sam babu daɗi,kuma kai tsaye ya nufi gida ba tare da ɓata lokaci ba

Yau bai nemi Amna ba,don ya san tana makarantar islamiyya,bai nemi mamynsa ba saboda ya san bata dawo daga aiki ba,bayan ya je masallaci ya yi sallar azahar ya koma gida ya kwanta akan gadonsa,yana cigaba da danne danne a wayarshi

Kira ne ya shigo,ya É—aga wayar yana faÉ—in "ya dai Saleem?"

A buÉ—e yake a gare shi cewa bayan yaran Roxy da suka raina masa hankali akwai wanda ya ci amanarshi a cikin nashi yaran,a dalilin haka ya sa ya ji sam ba zai sake yarda da su ba, gashi kuma yana zargin a cikin hukumarsu akwai masu fitar musu da sirri

A dalilin haka ya saka Saleem ya yi masa bincike akan Roxy, Saleem ba jami'i bane,mutumin gari ne, ko zurfin karatu bai yi ba, iyakar shi diploma a fannin political science,amma sama ta ka Allah ya ba shi ilmin computer da na sarrafa harshe,ga wayo da hikima da dabara, Haisam ya ja shi a jiki, kasancewar shi yana da alaƙa da shi ta wajen mahaifiyarsa,ya ba shi jari, sannan idan yana son yin bincike mai wahalar irin wannan Saleem yana taimaka masa su warware shin

Daga ɗaya ɓangaren Saleem ya amsa yana faɗin "Barka da warhaka Oga!ya aiki?ya fama da mu kuma?"

Haisam ya ce"alhamdulillah Saleem,ya batun aikin da na saka ka?"

Saleem ya ce"Oga ai na jijjiga da abin da na gano game da yarinyar nan,a kaf abubuwan da ake zargi babu wanda yake a yadda ake kallonshi"

"I don't get what you are saying Saleem?"Haisam ya tambaye shi

"Da farko dai,na fara bincike akan wadannan letters É—in da take amfani da su,kuma na gano ma'anarsu"

Da sauri Haisam ya ce "I'm all ears Saleem,me suke nufi?"

Saleem ya cigaba"wadannan letters ɗin ba ƙungiya ba ce,kuma ba wata alama ba ce,barazana ce kawai sai kuma yin wani abu da ta san zai ɗauke hankalin mutane

Yawan amfani da su da take yi ga mutum a yayin da ya shiga gonarta shi zai saka mutum ya fara zargin wani abu a ƙarƙashin waɗannan letters,bayan kuma a zahiri babu komai a ciki,ta yi amfani da su ne don ta rainawa mutane hankali

A taƙaice dai NOCCM full meaning ɗin shi shine NO ONE CAN CATCH ME!

Kalmomin ba na wani abu bane sai na fariya kawai, shine abin da na samu game da kalmomin NOCCM

Sai kuma abubuwa da yawa da na gano,amma kafin nan ita wannan yarinyar tana da wani tarihi da yake É—auke da wani tabo, kusan dai na ce shine silar faÉ—awarta halin da take ciki

Sannan kuma akwai sirri sosai a tare da ita wanda na yi nasarar ganowa, shine MUBARAK!

MUBARAK kuma ya kasance........"

"No Saleem,na san wannan cigaba da gaya min abubuwan da ka gano"babu musu Saleem ya saki batun Mubarak ya cigaba da bayanin abubuwan da ya gano game da Roxy, wanda har ya yi bayani ya gama Haisam yana É—an murmushi

Sai da ya gama tsaf Sannan Haisam ya ce"na gode Saleem,zan kira ka leter "bai jira amsar shi ba ya kashe wayar

Gyara kwanciyarshi ya yi yana murmushi sosai,a hankali ya furta"Roxy!or whatever your name is, your end has began!"ya janyo laptop É—insa ya buÉ—o wasu hotuna yana kalla yana murmushi

*NNAMDI AZIKWE AIRPORT,ABUJA, NIGERIA*

Miƙewa ta yi don zuwa wajen da Bolt ɗin da ta tsare yake,kuma ba tare da ɓata lokaci ba ya ɗaga suka nufi suleja

A can suleja bayan ta sauka kai tsaye ta kunna kai gidan da ta nufa, Amra da ke zaune tana shan kayan mayenta,gefenta wani saurayinta ne,ta É—ago tana kallonta cikin mamaki

Waje ta samu ta zauna tana kallonta, kafin ta daga gira,alamun kallon fa?

Amra ta yi dariya irin tasu ta yan maye ta ce"surprise!

Yaushe kika sauka a ƙasar?"Roxy ta mayar da kanta ga wayarta da take cirewa a flight mode ta ce"yanzu na sauka,ina sauka kuma na yo nan,ko gida ban je ba"

"Gaskiya ne tawan!

To ina su David É—in?"

Roxy ta yatsina fuska ta ce"suna can"

"Yaushe za su taho?"Amra ta sake jefa mata tambaya

Banza Roxy ta yi mata, saurayin Amra ya cewa Roxy "Hi beauty!"

Ɗagowa ta yi ya watsa masa wani kallon wulaƙanci sannan ta cigaba da danna wayar hannunta, kafin ta ɗago ta kalli Amra ta ce"ya ne?

Ina buƙatar hayaƙi fa,kin san kai kogo ne"

Amma ta ce"bari na ɗauko na haɗa miki welcome"ta mike ta fice daga parlourn tana faɗin "bad boy see you letter,ka ga ina da baƙuwa"bad boy ya miƙe yana faɗin "see you letter Hajiya ta,amma wannan baƙuwar taki zazzafa ce,ina son kayan idan babu damuwa "

Dakatawa Amra ta yi daga fita,ta juyo ta kalle shi tana faɗin"hattara dai! wannan kayan ya fi ƙarfinka "sannan ta fice daga parlourn

Shima bad boy ficewa ya yi daga parlourn yana faÉ—in"see you letter!"

A É—akin Amra kuwa,da sauri ta dauki waya ta danna kira,babu jumawa ta fara magana

"Hassy!

Tana nan fa "daga ɗaya ɓangaren Hassy ta ce"a haba!ki ce tana nan

To kwana zata yi?"

Amra tana leƙe ta ce"no ban tabbatar ba dai tukunna,amma kuma na san Roxy bata da alƙibla, yanzu zata iya chanjawa ko da ta yi niyyar kwana

Ita kaÉ—ai ta zo ba tare da mutanenta ba"

Hassy ta ce"daidai kenan,ki tsare mana ita,ko da a ce kin ga alamun zata gudu ki jefa mata ƙwayar nan da na ba ki a lemon ki ba ta,kin san yadda za kiyi dai,amma dai na kwaɗaitu da jikin yarinyar nan over,kuma na rantse sai na kwanta da ita,ina tsananin sonta,amma ita sai jiji da kai da wulaƙanci"

#Nusy_bee

Page 12

Kai tsaye Amra ta ce"noted!

Me za'a biya ni?"hassy cikin zaƙuwa ta ce"5m, yanzu ma zan tura miki ita ta account ɗinki"murmushi Amra ta yi ta ce"kuma bayan nan kafin ki yi komai ni zan fara gaskiya,don na juma sosai ina kwaɗayinta tana raina min hankali,don dai ƙarya take ta ce ita ba yar bariki ba ce"

Hassy ta ce shikenan babu damuwa,ga ni nan zuwa,ki tabbatar da cewa komai ya hau kan saiti kafin na ƙaraso "

Amra ta jinjina kai ta ce"babu matsala uwar É—aki"

Ƙwayar maganin da suka saba sakawa mutum a drink,su bugar da shi don biyan wata buƙata tasu,ko dai su yi masa sata,ko su aikata mugun ƙudurinsu ta ɗauko,ƙananan ƙwayoyi ne sosai,ta ɓoye su sannan ta fita zuwa ɗakin da shishar tata take

Yadda ta bar Roxy haka ta koma ta same ta,kanta akan wayarta tana dannawa,ta yi murmushi ta ajiye mata shishar a gabanta ta kama haÉ—awa tana faÉ—in "Barka dai Madam!

Ga mutuniyar tana yi miki sannu da zuwa"Roxy ta ɗago ba tare da ta yi magana ba ta kama pipe ɗin shishar ta fara zuƙa yadda ta saba tana cigaba da danna wayarta

Amra ta fice daga parlourn tana leƙen Roxy, tunani take yi ta inda zata fara ɗauke mata hankali

*MALIYA ESTATE, KANO STATE, NIGERIA*

*MUYASSAR RESIDENT*
Chapter 14 · 0% Book details