Sashe 29
Gadar Tsautsayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Duk abin da yake faruwa Ummeey tana kallo,amma bata magana,sai dai can ƙasan ranta ita kaɗai ta san me take ji saboda tashin hankali,amma ta miƙa lamuranta ga Allah kawai,kuma ta ja bakinta ta yi shiru
Tsawon sati biyu babu wani canji,gaba É—aya Shaheeda ta lalace ta fige ta fita hayyacinta,ba damuwarta karatun da Abba ya hana ta ba, damuwarta raba ta da Mubarak É—inta da ya yi, wanda ya zama wani sashe na rayuwarta
Sai da ta yi watanni uku da dawowa sannan ta koma hayyacinta,shima ta zama silent bata yawan magana, Muyassar kuwa tuni suka yi uwar watsi saboda haushinsa da take ji saboda shine silar rabuwarta da abin da take so,a cewarta
Shima bai damu ba,ya koma don cigaban karatunsa ya ba ta waje don ta sake hutawa
A lokacin ne Abba ya ba ta Sabuwar waya da sabon layi, sannan ya shaida mata zai mayar da ita makarantar BUK don ta cigaba da karatunta,amma ya yi mata gargaÉ—i akan kule-kulen maza,da kuma focusing akan karatunta
Sannan ya ƙara da faɗin "maganar mijin aure kuma na riga na zaɓar miki, Muyassar shine mijinki,bana son na sake jin kin kula wani,tashi ki je, Allah ya yi miki albarka"ta miƙe jiki babu ƙwari ta tafi bayan ta yi masa godiya
Tana komawa ɗaki ta yi murmushi tana kallon wayar hannunta, ba tare da ɓata lokaci ba ta hau jera numbern da take ta ajiya a ƙwaƙwalwarta tsawon watanni, lokaci guda kuma ta wuce zuwa banɗakinta da yake cikin ɗakin
Tana rufe ƙofar daidai da fara ringing da wayar da ta kira ta yi,ƙirjinta ya tsananta bugu,duk da cewa banɗakin babu zafi amma haka take sharce gumi, lokaci guda kuma kamar an tsayar da jinin jikinta ta ji ya ɗaga wayar
"Hello!"
"Mubarak!"ta faÉ—a muryarta tana rawa,kuka yana kubce mata
Sai da ya yi shiru na wasu sakwanni, kafin a hankali ya ce "Shaheeda!
Shaheeda ke ce?"ya furta cikin harshen dutch
Ƴar dariya ta yi tana goge hawaye ta ce"Mubarak a ina ka san sunana Shaheeda?"
Murmushi ya yi sosai,ya ce"a wajen yayanki, yanzu dai ba wannan ba, kina ina ne?
Me yasa kwana biyu na ji ki shiru?"
Tana kuka ta tsara masa abin da ya faru, shiru ya yi na É—an lokaci,a hankali ta ce"ba zan iya rayuwa babu kai ba Mubarak,ina sonka,kai ne rayuwata,kai ne farin cikina,kai ne komai nawa,ka taimake ni na same ka kar na rasa ka, Please Mubarak"
Mubarak ya ja ajiyar zuciya mai nauyi ya ce "to yanzu menene abin yi?
Ya kamata na zo na samu Daddy na yi masa magana,ya ba ni aurenki "
Girgiza kai Shaheeda ta yi ta ce"ba zai yarda ba, Abbana ya ce ya ba wa yayana Muyassar ni,ya yanke ba zai taɓa komawa baya ba, in dai aka tafi a haka na tabbatar ba zan same ka ba"
Mubarak ya ce"to yanzu ya ake ciki?"
Shaheeda ta ce"ban sani ba nima, makaranta ma an dawo da ni Nigeria "
Mubarak ya ce"zan zo Nigeria,zan zo har makarantar taku,za mu tattauna mu samo mafita "
Shaheeda ta jinjina kai ta ce"ina jiranka, Allah ya kawo min kai lafiya "
Ya jinjina kai yana faÉ—in"very soon "
Daga lokacin kuma Shaheeda da Mubarak suka ɗinke suka koma zuba soyayya sosai,amma a ɓoye, cikin ɗan ƙanƙanin lokaci ta mayar da jikinta,walwalarta ta dawo kamar baya
Cikin ɗan ƙanƙanin lokaci aka gama yi mata komai na komawa makaranta,inda zata cigaba da karatunta daga level two a maimakon level three,Sam hakan bai dame ta ba, musamman da ya kasance akwai wani gagarumin shiri da suka yi ita da Mubarak,duk da cewa duk sanda ta tuna da hakan jikinta yana yin sanyi
Allah ya taimake ta ta cigaba da zuwa makaranta,sai dai a ɓoye duk ranar da ta je makaranta sai sun haɗu da Mubarak,kuma da yake a Nigeria ne babu wanda ya damu da ya saka mata idanu
Game da Muyassar ma sun cigaba da zumunci,sai dai ba kamar baya ba,don da ya watsar da ita ma,daga baya ya dawo, kuma da ya ga ta sauko sai suka cigaba da zumunci, sai dai ya karance ta tsaf bata son batun aure ko soyayya ya gifta a tsakaninsu
Yau ma tana makaranta,tun sassafe da ta je bata shiga lecture ba,suna tare da Mubarak,ya dube ta ya ce"ina fatan kin gama shirya komai Fatima"
Ta girgiza kai, cikin sanyin jiki ta ce"ina sonka sosai Mubarak,amma ba zan ɓoye maka ba,ina son iyayena, mahaifiyata ni kaɗai ta haifa,ina tausayin ranar da zata buɗe idanu ta ga bana kusa da ita, kuma bata san inda na je ba,ji nake yi tamkar ban kyauta mata ba"
Mubarak ya dube ta sosai ya ce "to yanzu ya kike so a yi?ko aikinmu kike son ki dawo mana da shi baya?"
Da sauri ta girgiza kai ta ce "a'a ba ka fahimci me nake nufi ba,game da...."
"Relax Fatima!
Nima kar ki manta mahaifiyata ni kaÉ—ai gare ta,kuma ba ta amince ba kamar dai mahaifanki,amma na bijire mata na taho nan,duk da so da kewata da take yi,kuma hakan ba yana nufin bana sonta bane,amma kuma ina sonki
Ni ba zan raba ki da iyayenki ba,a madadin haka ma bayan auren za mu zo mu gaishe su mu nemi gafararsu,amma ya kika ce?"
A sanyaye ta jinjina kai,ya yi murmushi yana kallonta,suka cigaba da tsare-tsaren yadda za su yi aurensu su rayu cikin farin ciki da juna
A wannan halin ne Mubarak ya yi mata visa ta hanyar wani abokinsa Solomon ɗan ƙasar Nigeria,ya yi mata komai na ƙasar da suka zaɓa don tafiya,su cigaba da rayuwar su a can,wato ƙasar Spain
A ranar da suka shirya auren tun da safe ta sauka a makaranta,sai dai babu alamu na niyyar shiga lecture a tare da ita,tana zaune hankalinta baya jikinta tana jiran shigowar Mubarak
Can ta hango shi,ta miƙe cike da farin ciki,ya ƙaraso inda take yana kallonta yana murmushi,ya ce"ki zo mu tafi babu lokaci, Imam yana can yana jiranmu "babu musu ta bi shi,suka fice daga cikin makarantar
Kai tsaye wajen wani limami suka nufa,anan aka É—aura musu aure,bisa sadakin wani zobe na diamond da ya ba ta
Ta yi tsananin murna sosai na samun mallakin zuciyarta Mubarak,shima dai farin ciki kamar ya zuba ruwa a ƙasa ya sha,ya ɗauke ta ya ya mayar da ita makaranta
Sai dai kuma yana dire ta karaf! idanunta suka faɗa cikin na Muyassar! tashin hankali ba'a saka maka rana, tuni jikinta ya kama karkarwa,sai dai kafin Muyassar ya ƙaraso wajen Mubarak ya ja motarshi ya tafi, Muyassar ya bi motar da kallo ranshi a tsananin ɓace
Ƙarasowa ta yi tana murmushin yaƙe,ya watsa mata wani kallo ya ce"ke da wanene a cikin motar nan?"
"Am....dama....um.. wani course mate É—ina ne......"
"Karya kike yi Shaheeda!"ya faɗa cikin ɓacin rai yana ɗaga murya
Shiru ta yi tana haɗe rai, ranshi a ɓace ya ce "last question, Shaheeda da wa kike tare a cikin motar can?"
"Yaya na faɗa maka kuma ka ƙi yarda,na ce maka course mate ɗina ne fa,kuma...."
"Ƙarya kike yi Shaheeda!kar ki sake yi min ƙarya!!
A bar shi ma gaskiya kika faɗa, me ya haɗa ki da course mate ɗin ki har haka?ana yi muku lecture amma ke kina cikin motarshi?"ya sauke numfashi cikin ɓacin rai,ya dube ta fuska a ɗaure ya ce
"Bari na yi miki gwari-gwari don ki san cewa ni ba shashasha bane
Wannan kafirin saurayin naki ne Arnold,na san yana shigowa makarantar nan lokaci zuwa lokaci,kuma don ke ya zo ƙasar nan, to zan gayawa Abba gaskiya,tunda a nan ɗin ma ba ki fasa ba,gwara ya ɗauki duk matakin da ya so akanki sakarya! wadda bata san ciwon kanta ba!!!"
#Nusy_bee
Page 24
Cikin tashin hankali ta faɗi a gabanshi tana faɗin "don girman Allah yaya ka rufa min asiri don Allah yaya,na yi maka alƙawarin wallahi na daina,ka yi haƙuri yaya, Please yaya"
"Look!tashi Please,bana son wata magiya,bana son damuwa tashi mu tafi gida"
Tana kuka sosai ta ce"to don Allah ka yi haƙuri kar ka gayawa Abba, idan ka gaya masa na shiga uku,don Allah kar ka gaya masa Please"
Numfashi ya ja ya ce "to na ji,amma kuma da sharaÉ—i,kar na sake ganinki a wajen wannan É—an iskan"ta ce"eh wallahi,na yarda"
Ya ce"to wuce mu tafi"babu musu ta faÉ—a mota suka tafi
A hanya suna tafe yana lallashinta da yi mata nasiha,amma hankalinta baya kanshi,yana kan Mubarak da ya zama angonta,ranta fes,har suka sauka a gida
Da ta koma tunani ta rinƙa yi na yadda za su bi dabararsu ta yi aiki,su bar gari ba tare da wata matsala ba,amma sai ta turawa message na cewa zata neme shi,amma shi kar ya sake nemanta sai ta neme shi, saboda asirinsu zai iya tonuwa
Tana ankare da yadda Muyassar yake yawan saka mata idanu,ko tana makaranta, ko tana gida,don haka kawai sai ya yi mata zuwan bazata,bata wani damu ba,take nuna masa bata gane me yake yi ba
Ranar da suka shirya barin Nigeria gaba ɗaya jikin Shaheeda a sanyaye ta tashi, don sai da Ummeey ta kula da yanayinta, amma da ta tambaye ta sai ta ce babu komai,ta yi abubuwan da ta saba kafin ta tafi makaranta,amma kafin ta tafi sai da ta yagi takarda ta yi rubutu,tana goge hawaye ta ajiye akan dressing mirror sannan ta ɗan ɗebi wasu ƴan kayayyakin da take buƙata ta saka a jakarta sannan ta yiwa Ummeey sallama, ganinta da babbar jakar makaranta bai sa Ummeey ta kawo komai ba, saboda dama wasu lokutan tana ɗaukar babbar jaka
Tana fita suka haÉ—u da Muyassar ya shigo,da murmushi ta gaishe shi,ya amsa yana faÉ—in "student!
Ya karatun?"
Ta ce"alhamdulillah yaya,kai ka gama naka ko?"ya ce"na kammala,kuma alhamdulillah komai normal, makaranta za ki tafi?"ta jinjina kai ba tare da ta yi magana ba
Ya ce"okay bari na sauke ki ko?"babu musu ta shiga motar tashi suka fice daga gidan
Bayan ya sauke ta É—aga masa hannu ta yi ta shige aji,shi kuma ya tayar ya fice daga makarantar
Tana tsaye daga venue É—in nasu tana hangen motar Muyassar har ta daina ganinta,ta ba da wasu mintuna Sannan ta kira Mubarak ta sanar da shi