← Book details Gadar Tsautsayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 51

Sashe 20

Gadar Tsautsayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushi ya yi,ya nuna motar gabansu,ya ce"Men!"babu musu sai ga zaratan jami'ansu sun fito su biyar,hannun ɗaya riƙe yake da Habu,ɗan autan maman Fauziyya,matar marigayi malam Tajo

Tana ganin Habu ta hau ihu ta nufi inda yake da gudu tana faɗin "ɗana!ku ba ni ɗana,shi kaɗai ne da Ni,don Allah ku ba ni,ku yi min duk abin da za ku yi min amma ku ƙyale min ɗana,shine rayuwata....."

Sam bata ankara ba har suka buga mata ankwa suka ja ta zuwa motar Haisam,tana ihu tana fizge-fizge,tana ji tana gani aka tafi da Mubarak, wanda bata san inda za'a kai shi ba, tsabar tashin hankalin da ta riski kanta a ciki kafin a je station É—in ma numfashinta ya É—auke

*BAYAN KWANAKI UKU*

*MALIYA ESTATE*

Izuwa yanzu gaba ɗaya ahalin Maliya sun samu labarin abin da yake faruwa a gari,wato dai yan jarida sun baza cewa wannan matashiyar yarinyar da ta addabi jami'an tsaro ta hana su saƙat take aikata abin da ta ga dama,ba kowa ba ce face ɗaya daga cikin ahalin a baya kafin ta hau GADAR TSAUTSAYI wadda ta kai ta halin da take ciki,wato Fatima Shaheeda,babbar ya a wajen uban wannan ahali wato Maliya family

Yan jarida sun nemi Alhaji Yusuf Maliya don jin ta bakinsa akan bayyanar sunan ƴarshi a matsayin mai aikata babban laifi a ƙasa,duk da yadda ya kasance mutum mai mutunci da ƙima a idanun mutane

Kai tsaye ya amsa da cewa tun kafin a zo wannan gaɓar ya daɗe da mantawa da ita a cikin ƴaƴanshi,ita ba ƴarshi ba ce, shiyasa ma ta daina amfani da sunan da ya saka mata,ta sakawa kanta wani

A ɓangaren Hajiya Zainab kuwa yau kwananta biyu a asibiti,tun da ta samu labarin nan ta shiga tashin hankali sosai,amma hakan bai yi wa abokan zamanta ba,suka yi ta yaɗa maganar suna yar mata da habaici,hakan ne ya hauhawar da jininta,wanda ya tilasta mata kwanciya jinya

Babbar yar Alhaji Ishaq, Maryam ce take kula da ita a asibitin,bayan ta samu sauƙi ta matsa a sallame ta,kai tsaye ta wuce gidan Hajiya Saudat

Hajiya Saudat da bata juma da komawa ba don ta huta ta bi ta da kallo, ganin lokacin d aka shirya sallamarta bai yi ba, ba tare da tunanin komai ba Hajiya Zainab ta zube a gaban Hajiya Saudat tana kuka mai tsuma zuciya

Kama hannunta ta yi, suka wuce zuwa bedroom ɗin Hajiya Saudat, Hajiya Saudat ta zaunar da ita a gefen gado tana kallonta, cikin kwantar da murya ta ce"a yi haƙuri,komai mai wucewa ne,komai idan aka koma ga Allah mai sauƙi ne, Zainab babu wanda ya isa ya ja da ƙaddara,idan kin yarda Allah ne mai yin komai ki gaya masa cikin dare da rana,yana kusa da ke,kuma yana ji kuma zai amsa kokenki

Ke ɗin mai haƙuri ce, Allahn da ya jarabce ki shine zai kawo miki mafita, ba'a fushi da yi da iyawar Ubangiji

Ki yi haƙuri Zainab,ki mayar da al'amuranki ga Allah"

Zainab ta share hawayenta ta ce"Hajiya ni ba wannan ne yake damuna ba,sai yadda kishiyoyi suka saka ni a gaba, kowacce da kalar maganar da take yi saboda abin da ya faru,wasu a cikinsu ma faÉ—a suke yi wa ya sani ko abin da Shaheeda ta yi tarbiyyar gidanmu ne?

Akwai ciwo sosai,duk wani haushin Alhaji da suka ji a baya a yanzu suna hucewa a kaina,ga maganar da ya je ya yi da yan jaridu, Hajiya,ba zan ɓoye miki ba,na ji ciwon wannan maganar,ya nunawa duniya ko babu Shaheeda zai rayu, Hajiya ba ni na ce akai Shaheeda makaranta ba, asalima wallahi ban goyi bayan hakan ba,ya zan yi?

Hajiya ki ba ni shawara, zuciyata kamar zata fashe "

"Haƙuri autar Hajiya, haƙuri, addu'a,istigfari,sallar dare,miƙa lamura kacokan ga Allah, sanyawa a zuciya cewa Allah ne mai yi,kuma shine mai jarabtar bawa, kazalika shine mai warware matsaloli,za ki ji zuciyarki fes zainabu

Ki duba cewa,ban taɓa haihuwa ba,amma a yanzu ko wata mai ƴaƴa goman ba zata gwada min farin ciki da cin moriyar yara ba, akwai wadda ta haihun,amma kuma bata ci moriyar yaran ba,duk wanene mai yi? Allah

Don haka yanzu ki tuna,akwai Allah,idan kika miƙa komai ga Allah,hakan ya isa"

Hajiya Zainab ta goge hawayenta, cikin sanyin murya ta ce"in sha Allah Hajiya, Allah ya yi mana jagora "

Hajiya Saudat ta dafa kanta ta ce"Ameen autar Hajiya!

Allah ya albarkaci rayuwarki! Allah ya share miki hawaye, Allah ya zama gatanki auta "

"Ameen hajiyata, Ameen, Hajiya yunwa nake ji"

Hajiya ta yi murmushi ta ce"mu je ki ci ɗanwaken da na saka a yi min"babu musu suka miƙe suka fice zuwa dinning area

Da kanta ta bawa Zainab abincin,tana ba ta tana janta da hira, wadda ta sa ta manta da damuwar da take ciki,suka sha hirarsu abin su

Hajiya Zainab bata tafi gida ba sai da Alhaji Yusuf ya zo ya É—auke ta da kanshi, Hajiya Saudat bata nuna masa damuwar komai ba,a mota ma suna tafiya yana ta kwantar mata da hankali cikin dabaru da hikima

*MUYASSAR*

Ɗaga kai ya yi yana kallon Arfa da take ta waƙa cikin farin ciki, cikin ƙosawa ya ce"Arfa na gaya miki kina damuna,ba ki bar ni na yi abin da yake gabana ba kin wani sako ni a gaba da waƙe-waƙen banza da na wofi,bana son sakarci fa!"

"Sakarci?"ta faÉ—a tana fashewa da dariyar rainin hankali, ta ce "oh Allah!

Wato sakarya ce ni,to ita kuma yar safarar cocain mecece ita?jan wuya?"

Shiru ya yi bai ba ta amsa ba,ta É—aure fuska gami da jan tsaki,ta ce"Allah wadaran naka ya lalace!

Na godewa Allah da ya sa uwata ta gari ce da ta ba ni tarbiyya,gani nan a ɗakin aure ba a gari ina gantali kowa yana tsine min ba, lalacewar tawa bata kai jami'an tsaro su rinƙa bi na muna tsere da su ba, saboda ina yaɗa baɗala a bayan ƙasa,wa ya sani ma ko iya nan ɓarnar ta tsaya ko ta wuce haka?mu dai Allah ya tsare mu daga aikata irin wannan mugun aiki "

Miƙewa Muyassar ya yi don ficewa daga ɗakin,don ya fara gajiya da irin wannan surutan na Arfa,don shi har yanzu bai ji soyayyar Shaheeda ta yi rawa a cikin zuciyarshi ba,ji yake yi waɗannan zantuttukan da Arfa take yi tamkar ana zuba masa ruwan dalma a cikin zuciyarsa,amma sai Arfa ta tare masa hanya

Calmly ya dube ta ya ce"Arfa ba ni hanya,zan wuce "

"Ba za ka wuce ba, saboda ina zargin waccan tsinanniyar tunda aka kama ta ka gigice,wa ya sani ma ko kana zagawa kuna haɗuwa? wataƙila ma ɗan da aka ce an yi mata tarko da shi naka ne,wanda kuka samu a rariya!"

"Arfa!ko ki ba ni hanya na wuce ko na sauke miki mari!"

"Idan ka fasa marina ba ka haifu cikin Umar da Sa'adatu ba!"bata rufe baki ba Muyassar ya sauke mata mari,bata gama gane kanta ba ya sake sauke mata wani sannan ya hankaÉ—e ta gefe ya nufi hanyar fita

"Kan uban can kayyasa!ni ka mara?

Muyassar Allah ya isa na,mugu azzalumi macuci,matsiyacin namiji, wallahi na yi nadamar aurenka,kuma kai ma na yi alƙawarin sai ka yi nadamar sanina,kuma ...."

"Yadda kika yi nadamar aurena haka nima na yi nadamar aurenki, kin ga babu amfanin zaman nadama,don haka ki je na sake ki Arfa!!!"yana kai wa nan ya fice daga gidan da sauri,yana jin kururuwa da ihu da fizge-fizgen Arfa amma ko kallon hanyar bai yi ba,ya faÉ—a mota ya fice daga gidan

*HAISAM*

"Daddy yaushe za ka dawo?"

Kallonta ya yi yana murmushi ya ce"ba zan juma ba in sha Allah,ki yi min addu'a sweetheart!"

"Allah ya dawo da kai lafiya, Allah ya ba da Sa'a daddyna!"

"Ameen mummyna!

Much love"ta yi kissing É—in shi a kumatu,shima ya yi kissing É—inta ya ja mota ya fice daga gidan

A bakin jail ɗin ya tsaya,ya nuna ID card ɗinsa,ba tare da ɓata lokaci ba aka ba shi hanya ya wuce da wayarsa a hannunsa

Yana zuwa ya bayar da sunan criminal ɗin da yake son gani,babu ɓata lokaci ma'aikatan suka tafi don kiranta,shi kuma ya zauna a inda aka tanadar masa

Babu jumawa aka gabato da Roxy,kanta a ƙasa, idanunta sun canja da alamun ta sha kuka sosai,sai dai babu alamun karaya a tare da ita,ta samu waje ta zauna,amma still kanta a ƙasa, idanunta a kan hannayenta da suke ɗaure da handcuff

Murmushi ya yi sosai,ya ce"Barka dai!

Sunana CSO Haisam Abdulmalik Madaka,Ni jami'in tsaro ne na farin kaya,wato DSS

Tsarina ne muddin na saka abu a gaba tabbas sai na cimma shi, musamman idan ya zamana an wulaƙanta ni

To!yau ga ni ga Roxy, wannan fitacciyar wanted É—in, wadda take rayuwa cikin kwanciyar hankali tana gwara kan jami'an tsaro,amma sai ga ta a hannun waÉ—anda take rainawa hankali,malama Roxy Barka da zuwa komar Haisam!!"

Kamar ba zata yi magana ba,sai kuma ƙasa-ƙasa ta ce"ina ɗana?"

"Ban ji ba sosai, maimaita"ya faÉ—a yana aika mata wani kallon rainin hankali

ÆŠaga kai ta yi ta kalle shi,a hankali ta ce "cewa na yi ina É—ana mubarak?

Wanne laifi ya yi maka ka kama shi?"

Wata Æ´ar dariya ya yi ya ce "laifin da Amna ta yi kika saka aka yi musu barazana,ko ba ki san kukan Æ´ata yana tayar da bala'i bane?kuma muddin ta yi kuka sai na rama mata?"

Hawaye suka zubo mata ta ce"to ba gani ba?ka rama akaina mana!

Menene dalilin da ya sa zaka rama akan wanda bai takawa kowa komai ba?"

Haisam ya ce"ita Amna me ta yi miki kika razana ta?"

Tana goge hawayenta ta ce"ban yi da zummar na cutar da ita ba, ko da ban haihu ba na san zafin É—a, ballantana É—an da iyayensa da suke nuna masa soyayya ba sa raye"

"Ban ga alamun kin san zafin É—a ba Shaheeda,da ace kin san zafin É—a da ba ki jefar da naki don wani ya tsinta ba,ba ki ji tsoron abin da zai same shi ba?
Chapter 20 · 0% Book details