Sashe 16
Gadar Tsautsayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ba'a juma da fara game ɗin ba Haisam ya cinye ta,ta kama kuka har da shura ƙafa tana faɗin sai an sake,ai bata shirya ba, Haisam yana murmushi ya ce"babu abin da za'a sake,ai ke kika ce a yi, leave me alone Madam!"ta faɗa jikinsa tana kukan shagwaɓa
Nimra ce ta shigo sashen nashi da sallama,ya É—aga kai yana kallonta gami da amsawa
Nimra ƙanwar Hajiya Mariya ce,wato matar babansa,kamar yadda ta saba yau ma sanye take da kayan da suka ɗame ɗan siririn jikin nata,sai ƴar light make up da ta yi wa fuskarta,da mayafin da ta saƙala a kafaɗarta
#Nusy_bee
Page 13
Sau ɗaya ya kalle ta ya ɗauke kai yana ɗan taɓe baki, yarinyar sam bata burge shi saboda yadda bata da kamun kai sam,shi kuma a duniya ya tsani mace mara kamun kai
"Hi!"ta faÉ—a tana murmushi sosai,ba ta ba shi damar magana ba ta cigaba da magana tana kallon Amna
"Amna babu magana ko?"Amna ta kalle ta ta ce"good morning aunty!"tana murmushi ta ce"No I'm your Mummy,not aunty,kin ji?"ita dai Amna bata yi magana ba sai kallonta take yi
Ɗan murmushi ta sake yi,ta dubi Amna da ta sake lafewa a jikin mahaifinta ta ce"ki je wajen Hajiya Mamie kin ji?ko wajen Nanny,za muyi hira da Daddy"babu musu Amna ta miƙe daga jikin mahaifinta ta fice daga sashen tana waigen ubanta
"Good morning love!"É—aga kai ya yi yana kallonta,tsawon shekaru biyu kenan,tunda suka rabu da mahaifiyar Amna take bin shi da sunan neman soyayyarshi,sai dai sam yarinyar bata burge shi ko kaÉ—an, saboda bata da kamun kai,bata da wadatacciyar tarbiyya
"Aiki nake yi, can you please excuse me zuwa anjuma??"
Kwaɓe fuska ta yi,a shagwaɓe ta ce"kai my baby boy!
Aren't you happy of seeing me?"
Ɗauke kai ya yi yanayin fuskarsa yana canjawa,ya ce"aiki nake yi ne,bana son a rinƙa interrupting ɗina "
"Amma na ga kuna hira da Amna time É—in da na shigo"
Wani banzan kallo ya watsa mata ya ce"kishi kike yi da ita?"É—an murmushi ta yi ta ce"no ba haka nake nufi ba,ya uwa zata yi kishi da Æ´arta?
Kawai dai ina son ka ba Ni time ne,ka ga don kai kawai na zo gidan nan"bai amsa ta ba,ya cigaba da danna system É—in shi
Ganin ya yi banza da ita ya ƙi saurarenta sai kawai ta fashe da kukan kissa,ya ɗaga kai yana kallonta gami da sassauta fuskarsa,a hankali ya ce
"I'm sorry please,amma me ya faru da za ki yi kuka?me na yi miki?"
Goge hawayenta ta yi ta ce"ba ka yi min ba,ka ƙi yi min dai"
Ya sake dubanta sosai ya ce"me na ƙi yi miki?"
Ta karyar da kai ta ce"ka ƙi ka kula ni,ka share ni,bayan na shafe tafiya na zo don na ganka kai kaɗai,amma ba za ka iya ba ni time ɗinka ba?even a little?
Nima na ji ina da matsayi ko yaya ne a wajenka?"
Cikin kwantar da murya ya ce"okay na fahimce ki
Yanzu don Allah ki ba ni wasu Æ´an mintuna na gama da wannan file É—in da nake dubawa,idan ya so sai mu tattauna"
Kwantar da kanta ta yi a jikin kujerar da take zaune ta ce"alright!
I'm waiting"ya sake dubanta,ranshi ya fara ɓaci ya ce "I need space Nimra,idan kuma ba haka ba sai na bar miki gidan"
Cikin sanyin murya ta ce"But na ce zan jira ka ai, ka gama sai mu yi magana "cikin ƙosawa ya ce"okay!
To tunda ba za ki tafi ba ni bari na ba ki waje, I told you since bana son musu"ganin yana ƙoƙarin miƙewa ya sa ta miƙe ba a son ranta ba tana murmushi ta ce"I will wait sweetheart!bye!"ta fice daga sashen
Tana fita ya miƙe da sauri,tuni ya ɗauki key din motarshi,ya fice daga gidan,don a rayuwarsa ya tsani a matsa masa
*ROXY*
A hankali take tafiya a gefen hanya,tana lumshe idanu tana buɗewa,da alamu har yanzu abin da ta sha bai gama sakinta ba, idanunta sun yi jawur, fuskarta a ɗaure tamau,alamun ranta a tsananin ɓace yake
Wayarta ta zaro,ta fara yunƙurin aika kira,bayan ya sakanni ta fara magana yanayin muryarta tamkar wadda take cikin maye
"Kana ina ne?"daga can ɓangaren Oga boss ya ce"ga ni a gida uwar ɗakina"
Kai tsaye ta ce"ka zo bayan gidan Amra,ina buƙatar ganinka"tana kai wa nan ta kashe wayar
Bata juma tana tafiya ba ta ji ana faÉ—in "wannan kamar wannan criminal É—in da ake nema!"
Ji ta yi É—ayan ya ce"a haba!
Ta yaya zata yarda ta fito ita kaÉ—ai a wannan lokacin?"
ÆŠayan ya yi shiru yana duba hotonta da yake wayarta, kafin ya ce"wallahi ita ce fa,ka ga hoton"ita dai ko kallon su bata yi ba,ta cigaba da tafiya abinta
Ji ta yi sun biyo ta suna faÉ—in "ke!tsaya!tsaya!!bari mu tabbatar,kar ki motsa,tsaya a inda kike"
Cigaba da tafiya ta yi a hankali har suka kusa cim mata,dayan ya ce "ki tsaya ko na yi harbi"
Cak ta tsaya a inda take,suka nufo inda take da gudu,amma kafin su ƙaraso ta shammace su ta saka gudu da tsananin ƙarfinta,suka rufa mata baya
Tsawon kusan awa guda tana ba wa yan sandan wahala,duk yadda za su kamo ta sun yi,amma ta ƙware wajen zilliya da rainawa yan sanda hankali,hakan ya fusata ɗaya daga cikinsu ya saita tsakiyar bayanta ya yi harbi,amma sai bai same ta sosai ba,ya same ta a kafaɗarta
Sai dai a maimakon ta tsaya sai shigewa wani lungu ta yi ta ɓuya,duban duniya suka rasa ta, babu yadda suka iya haka suka juya suka tafi
Ita kuwa Roxy bayan ta tabbatar sun tafi miƙewa ta yi ta cigaba da tafiya tana tangaɗi,ga mayen ɗazu har yanzu bai gama sakinta ba, saboda ƙwayoyin da su Amra suka zuba mata ba ƙaramin ƙarfi ne da su ba,ga jini da ya fara ɗibarta, saboda zubar jinin da take ta yi tunda aka harbe ta
Tun tana ganin gari yadda ya kamata har ta fara gani dishi-dishi,ga ƙarfin jikinta da yake ta ƙarewa,a hankali duhu ya rufe ƙwayar idanunta,duk da haka bata karaya ta tsaya ba sai da ƙarfinta ya ƙare duka,ita dai bata san lokacin da ta yanke jiki ta faɗi ba ma
*MALIYA ESTATE*
*UMMEEY*
Sauri sauri take yi don fita zata yi zuwa bikin ƴar ƙawarta Hajiya Jamila, Salma,amaryar ƙawa ce wajen ƴarta Shaheeda,sau tari idan ta ga yarinyar tana tunawa da ƴarta Shaheeda, saboda yadda halayyarsu ta zamo ɗaya,kuma manyan ƙawayen juna ne sosai
Ko lokacin da aka aiko mata da katin gayyatar bikin Salma ta yi kuka sosai,don ta tuna Shaheeda, wadda a halin yanzu bata da tabbacin tana raye ko ta bar duniya
Ƙoƙarin fitowa take yi daga ɗakinta sai ga Hajiya Sa'adatu ta danno kai cikin parlourn ta kamar wadda aka wurgo,sai huci take yi,da alamu ranta a ɓace yake, Ummeey ta kalle ta cikin faɗuwar gaba,ta ɗaure ta ƙaƙalo murmushi ta ɗora akan fuskarta tana faɗin
"A'a!
Hajiya Sa'adatu yau ke ce tafe?
Maraba da zuwa"Hajiya Sa'adatu ta watsa mata wani mugun kallo ta ce "ai ke ce da sannu Hajiya Zainab!
Wai me yake faruwa ne? meyasa ba za ki bar ni haka na huta bane? meyasa kika zamar min masifa da bala'i a rayuwata ne?"Ummeey da ke tsaye tana kallonta ta safe ƙirji tana faɗin "subhanallahi!me ya kawo wannan maganar kuma?
Don Allah ki yi haƙuri ki zauna mu yi magana ta fahimta,me yake faruwa ne?"
Kai tsaye Hajiya Sa'adatu ta ce"ba zama ne ya kawo ni ba,dama na zo ne na gaya miki ki yi wa yarki gargaɗi akan ɗana,ta hana shi zaman lafiya da matarshi,an kawo min ƙararta,bana son hakan ya kuma faruwa
Haka kawai yanzu ta haddasa gaba tsakanin Muyassar da matarsa,ba zai yiwu na ɗauki ƴar mutane na ba shi sannan yarki ta hana su zaman aure ba,kar hakan ya kuma faruwa, bana buƙatar matsala a gidan ɗana
Ba sai an faɗa ba kowa ya san yarki masifa ce,kuma annoba ce,to bana buƙatar wani tashin tashina a kusa da ni"ta juya da zummar ficewa daga parlourn
Cikin karyewar murya Hajiya Zainab ta ce"Hajiya Sa'adatu ki fahimtar da ni,wacce Æ´ar tawa kike nufi?
Dama ina da wata yar ne ban sani ba?"
Kallon banza Hajiya Sa'adatu ta yi mata ta ce"wacce ya kuwa banda wadda ta janyo mana abin faÉ—a a family, Æ´arki Shaheeda?
Bana son abin nan ya kai mu gaban Alhaji, shiyasa na zo na gaya miki don ki ja mata kunne,ta fita harkar É—ana da gidansa, idan ba haka ba kuma komai zai iya faruwa,sai anjuma Hajiya "ta juya ta fice daga sashen zuciyarta cike da hassadar ganin Hajiya Zainab ta sake gogewa ta yi kyau kamar ba wadda take cikin damuwa ba
Zama Hajiya Zainab ta yi a hankali a gefen kujera cikin wani irin yanayi da ta kasa fassarawa, Shaheeda?ina suka ga Shaheeda?tana a wanne halin?
Ita a yanzu da zata ganta da bata san wanne irin farin ciki zata tsinci kanta ba,wai me yasa abubuwa suke ta faruwa da ita ne akan Shaheeda?
Ta goge hawayenta tana faɗin "ya Allah ga yata nan, Allah idan da rabo ina roƙonka ka dawo da ita gare ni, ya Allah kaine masani kuma mafi hikima, Allah ka yi min daga taskarka"
Kamar babu Abin da ya faru ta ƙarasa shiryawa ta fice don zuwa taron bikin yar su Salma,tana kallon su Hajiya Ruƙayya da Hajiya Atika suna magana,ta san mayar da yadda aka yi suke ya,bata ko yiwa sashen da suke tsaye kallo biyu ba ta shiga mota ta tayar ta fice daga gidan
*HOSPITAL*
"Amra wannan wacce mahaukaciyar yarinya ce kika haÉ—a ni da ita take neman rayuwa ta?
Daga nuna mata hanyar daÉ—i kuma sai ta nemi kisa?"
Amra ta kalli Hassy da take wannan maganar ranta a matuƙar ɓace ta ce"ai ƴarinyar nan ta yi min wulaƙanci,amma wallahi bata ci banza ba,sai na ganar da ita kuskurenta,kafirar banza ƙazama kawai "
Hassy ta sauke ajiyar zuciya tana taɓa bandage ɗin da aka naɗe mata kai,a hankali ta ce"yanzu tana ina?"
Amra ta taɓe baki ta ce"oho!
Na dai bar ta a gida bayan na dake ta, gobe ta sake yi min wannan iskancin
Itama karuwar ce fa,amma take nunawa duniya ita ba haka take ba