← Book details Gadar Tsautsayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 51

Sashe 40

Gadar Tsautsayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta shafa cikinta a hankali,ta yi ɗan murmushi jin yana motsi,ta ce"kai kaɗai gare ni a duniya yanzu,ina addu'ar Allah ya da ka zame min sanyin idaniya,ka zama duk abin da na rasa, ka share min hawaye, mamanka tana sonka ka ji masoyina, Allah ya kawo min kai lafiya"ta ƙarasa magana yana goge hawaye, zuciyarta tana sake karyewa

#Nusy_bee

Page 32

Tafiya ya cigaba da yi a hankali, lokaci lokaci tana share hawayenta,kafin ta koma gefe ta zauna ta yi shiru tana kallon masu wucewa da komawa

Tana nan a tsugunne har dare ya soma yi sosai,ga bacci,ga gajiya,ga yunwa, abubuwa sun yi mata yawa sosai, lokaci lokaci take share hawaye

Bata san inda zata dosa ba, ballantana ta san me zata yi, tana nan a zaune ta ji magana kamar daga sama

"Baiwar Allah lafiya?me kike yi a nan wajen?"

A firgice ta É—aga kai tana kallon mutumin da zai iya kai wa shekaru arba'in ko ma fiye,amma sai ta kasa ba shi amsa,ya sake tambayarta "baiwar Allah na ce lafiya?

Me kike yi a nan da wannan tsohon daren?"

Goge hawayenta ta yi ta ce "ni baƙuwa ce,ban san inda zan je bane,garinmu ana tashin hankali ne,an kashe mijina gashi bani da kowa"ta samu kanta da yin wannan ƙaryar

Duk da cewa ba shi da tabbas na maganarta amma ya tausaya mata sosai,ya ce "to Allah ya kawo mana É—auki,tashi ki shiga a daidaita sahuna gata nan,sai na kai ki gidana, zamanki a wajen nan a matsayinki na mace hatsari ne"Shaheeda ta rissina tana godiya,ta shiga a daidaita sahun tashi,ya tayar suka bar wajen

Wata ƴar ƙaramar unguwa ta masu ƙaramin ƙarfi ya nufa da ita,a ƙofar wani tsohon gida suka yi parking, Shaheeda ta fara bin gidan da kallo,a ranta tana tsarkake Ubangiji,dama akwai irin waɗannan mutanen masu rayuwa a irin wannan gidan a duniya?

Bata sake tsinkewa da lamarin Ubangiji ba sai da ta shiga gidan,É—akuna ne a jere,kusan guda shida,amma da alamu wannan mutumin ba shi kaÉ—ai bane a gidan,don ta ga wasu maza guda biyu, É—aya ma suna tare da matarsa,da alamu su ma mazauna gidan ne

Wasu É—akuna ya nufa a cikin É—akunan gidan,ya shiga wani da sallama

Matar da take zaune tana gyarawa wasu yara shimfiÉ—a ta É—ago tana kallonsu tana faÉ—in"sannu da zuwa!

Ka daw....."maganar ta maƙale a bakinta ganin Shaheeda a bayanta, wadda ta yi tsuru-tsuru kamar a ce mata 'kyat'ta zura da gudu

Mutumin bai tankawa matar ba,ya dubi Shaheeda da kulawa ya ce"mata Æ´an mata shigo,ga waje ki zauna "babu musu Shaheeda ta shigo cikin É—akin, sannan ta zube a gaban matar tana gaishe ta

A yatsine matar take kallonta da cikin jikinta, kafin ta amsa da" lafiya "Sannan ta miƙe ba tare da ta sake kallon sashen da suke ita da mijin ba ta fice daga ɗakin,shima kuma babu ɓata lokaci ya bi ta, Shaheeda da take zaune ta bi su da kallo duk jikinta a sanyaye

Su kuwa suna shiga É—aya É—akin da ya zama na kwanansu ta dubi mijinta da ya shigo ta ce"baban faruku wacece wannan yarinyar da kuka zo tare?a ina take?"

Baban faruku ya samu waje ya zauna,ya dube ta ya ce"haba Rabi, menene abin É—aga hankali ne? zauna sai na gaya miki ko?"babu musu rabi ta zauna,baban faruku ya gaya mata komai da Shaheeda ta gaya masa

Shiru ta yi na É—an lokaci tana kallonsa, kafin ta ce"to yanzu da ka kawo ta ya kake ganin za'a yi da ita?

Ka san dai É—akunan da ka kama mana guda biyu ne,kuma É—aya nawa É—aya na yarana,don haka a bayyane yake bata da wajen kwanciya a gidan nan,sai kuma maganar matsayi,a matsayin wa ka kawo ta gidan nan?"

Shiru baban faruku ya yi na wasu mintuna kafin ya ce"ai ba zama zata yi mai tsawo ba,na ga tana buƙatar neman taimako ne,ga dare, na san za ki taimaka kasancewarta mace shiyasa na kawo ta,kuma ba a matsayin kowa ba sai na baiwar Allah musulma mai buƙatar neman taimako, shine za mu taimaka mata kawai"

Rabi ta haÉ—e rai ta ce "to ta zauna,amma ba daÉ—ewa zata yi ba, sannan kuma ban yarda da mu'amala tsakaninku ba,kuma na É—an lokaci ne zata tafi,ni ba don cikin jikinta ba ma da sati guda zan É—ebar mata ko ta tafi ko na kore ta wallahi "

Murmushi ya yi ya ce"to babu matsala in sha Allah,amma yanzu ki ba ta abinci idan akwai"Rabi bata kalle shi ba ta ce"babu,sai dai ko naka"kai tsaye ya ce"a ba ta nawa babu matsala,kin ga ta fi ni buƙata saboda abin da take ɗauke da shi"rabi ta kalle shi tana taɓe baki sannan ta miƙe tsaye ta ɗauki kwanon dambun da ta yi ta fice don kai wa Shaheeda

Shaheeda tana zaune ta takure kamar mai jin sanyi, zuciyarta cike da fargaba,sam bata ga laifin matar nan ba idan ma korarta ta yi ko ta hantare ta,ita da mahaifinta ma ya kore ta,ya nuna baya buƙatarta?

Ta goge hawayenta tana gyara ƙafarta da ta yi tsami, kafin ta yi wani yunƙuri sai ga Rabi ta shigo tana sallama ciki-ciki

Shaheeda ta amsa murya a sanyaye, rabi ta kalle ta a fizge,sai da gabanta ya faÉ—i,don kyan yarinyar ya ba ta tsoro, a ranta ta ji dole ma ta saita mata hanya nan ba da jumawa ba,kar mijinta ya sauya tunani akanta

A sanyaye Shaheeda ta sake gaisheta,ta amsa da "lafiya,ga abinci nan ki ci,idan kin gama ci ga buta can sai ki yi alwala ki yi sallah,ya sunanki ne ma?"

Shaheeda ta yi shiru na Æ´an seconds, kafin ta ce "sunana Fatima"

"To ya yi kyau Fatima"ta jefa mata wani tsohon labule duk ya yi ƙura,ta ce"kyau shimfiɗa a can wajen,daga bakin ƙofa, saboda kin ga babu waje"Shaheeda ta ɗauka tana faɗin "to na gode aunty"rabi ta kalle ta ta taɓe baki sannan ta fice daga ɗakin

Alwala Shaheeda ta ɗauro,ta zo ta tayar da sallah,ta rama magriba da isha'i da bata yi ba, sannan ta zauna ta fara cusa abincin,su da daɗin da dambun ya yi mata,abinka da mai ciki,amma ta kasa cin shi sosai, ragowar sai rufe shi ta yi ta koma ta kwanta a takure,bayan ta shimfiɗa labulen da aka ba ta, saboda tsananin gajiya da nauyin jiki irin na mai ciki cikin ɗan ƙanƙanin lokaci bacci ya yi awon gaba da ita

A ɓangaren Ummeey kuwa,da ƙyar ta danne kukan da take yi ya shiga sashenta,kanta har wani jiri yake yi ta lalubo wayarta,babu ɓata lokaci ta dokawa Hajiya Jamila kira

Bugu biyu ta É—aga da sallama, Hajiya Zainab ta amsa tana faÉ—in"Hajiya Jamila kina nan?"

Hajiya Jamila ta yi shiru na É—an lokaci tana nazartar muryar Hajiya Zainab, kafin ta ce"me yake faruwa ne Hajiya Zainab?

Ko dai wannan matsalar ce?"

Kuka ya ƙwacewa Hajiya Zainab, cikin karayar zuciya ta ce"ta faru ta ƙare ma Jamila, Alhaji ya kori Shaheeda,ya ce ya cire ta daga cikin ƴaƴansa"

Hajiya Jamila ta ji dukan maganar,ta san dole abin zai yi wa Hajiya Zainab ciwo, ƴarta ɗaya, Allah ya jarabce su akanta,amma mahaifinta maimakon ya zaɓi ya gyara ya gwammace ya nunawa duniya cewa shi yana da wasu yaran ko da ace bata tare da shi,ya manta komai daren daɗewa matsayinta na ƴa a wajensa ba zai taɓa canjawa ba

Amma sai ta dake ta ce "to Hajiya Zainab ki kwantar da hankalinki,ki turo ta nan,ko da babu driver,baban nata yana cikin ɓacin rai ne,amma yana hucewa shikenan in sha Allah,komai zai daidaita ki kwantar da hankalinki "

Hajiya Zainab ta girgiza kai ta ce"ba za ki gane bane Hajiya, tunda ya nuna ba zai amshe ta ba to ta zauna, Alhaji yana da kafiya musamman akan ra'ayinsa

Kuma Allah ya gani tun sanda aka ce za'a kai ta makaranta ban so ba, saboda Shaheeda yarinya ce ƙarama,amma mahaifinta ya dage,ya ce ya ji ya gani,a ƙarshe gashi nan ni nake girbar shukar, ƴata ce ta lalace shi babu abinda ya yi masa zafi tunda yana da wasu yaran,Ni gani an bar ni a cikin tashin hankali da baƙin ciki,ko da wannan cikin ai ni nake ganin damuwa"

Hajiya Jamila ta girgiza kai ta ce"Hajiya bawa bai isa ya kauce ƙaddarar da Allah ya rubuta masa ba,ko ta wanne hali,da ni da ke da kowa ma mun san wacece Shaheeda mun san abin da zata iya da wanda ba zata iya ba,mun yi mata kyakykyawan zato, abin da ya faru ƙaddara ne da jarrabawa,mu san Shaheeda ba maza ta bi ba, aure ta yi, duk da cewa bata yi auren akan yadda ya dace ba,amma dai ba zina ta yi ba,ɗanta ɗan Sunnah ne,yaudarar da aka yi mata bata isa ta saka ɗanta ya zama shege ba, ki kwantar da hankalinki hajiya

Yanzu dai ki turo ta,ko da ma a ce Alhajin naku bai yarda ta koma gidansa ba ni zan riƙe ta ni da nawa Alhajin,kar ki damu Hajiya "Hajiya Zainab ta yi murmushi tana faɗin"na gode, sai,in sha Allah yanzu zan turo ta, sai kin ji ni Hajiya "suka yi sallama ran kowa a cikinsu babu daɗi

Tana sauke wayar Muyassar ya yi sallama, Ummeey ta ɗaga kai tana kallonshi ta amsa da murmushi a fuskarta,ya ƙaraso cikin falon yana kalle-kallen ta inda zai gano Shaheeda

Cikin girmamawa yadda ya saba ya gaida Ummeey, Ummeey ta amsa cikin fara'a tana faÉ—in"ango ya shirye-shirye?"Muyassar ya ce"alhamdulillah Ummeey

Ina Shaheedan?na ji abin da ya faru da ita,ban ji daÉ—in abin da ya faru ba,amma babu komai, za'a san yadda za'a yi kafin a samu Abban ya huce in sha Allah

Ki yi haƙuri Ummeey "

Ummeey ta sauke numfashi ta ce"babu komai Allah ya kyauta kawai

Shaheeda ai na bari ta a falon Alhaji,ban sani ba ko ta taho "

"Wai falon Abba?"ya faÉ—a yana kallonta da yanayin mamaki akan fuskarsa

Bata damu ba ta ce"eh can na baro ta, wataƙila ta shigo yanzu

Na yi magana da ƙawata ma,zan tura ta can gidanta kafin abubuwa su lafa a san yadda za'a yi"

Muyassar yana kallonta da yanayin mamaki da damuwa ya ce"amma kuma yanzu na baro wajen Abba,amma kamar bata can"
Chapter 40 · 0% Book details