← Book details Gadar Tsautsayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 51

Sashe 24

Gadar Tsautsayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Har ƙasa ummeey ta kai ta gaida innayyo, wadda ta amsa ciki-ciki,ta dubi Hajiya Sa'adatu da fara'a tana faɗin "maraba da zuwa Hajiya!

Sannunku da zuwa"

"Yawwa sannu! yarki ce ta É—ago mu ai"ta bata amsa kai tsaye

Hajiya Zainab ta samu kujera ta zauna tana kallon Shaheeda da ta zauna a kan carpet É—in parlourn ta ce"kayya! Allah ya sa dai lafiya"

"Duk wani abu da ya danganci wannan iblishiyar Æ´ar taki ai ba na lafiya bane Hajiya Zainab, Allah ya kyauta dai"da sauri Hajiya Zainab ta kalli Shaheeda, wadda ta yi tamkar bata ji abin da Hajiya Sa'adatu ta ce ba,itama ta ja bakinta ta yi shiru

Alhaji Yusuf da ya gama amsa waya yanzu,ya dawo da hankalinsa kan mutanen parlourn yana kallon Shaheeda da ta takure waje ɗaya kanta a ƙasa,ya ce"ke Shaheeda ba ki iya gaisuwa bane?"

Babu musu ta fara gaida innayyo, innayyo ta yi mata banza,bata damu ba ta gaida Hajiya Sa'adatu,caraf Hajiya Sa'adatu ta ce"Shaheeda ai ni yanzu ai ban isa komai ba,tunda ban wuce ki kalle ni ki zage ni ba"

Ko a jikin Shaheeda, Abba ya dube ta cikin fushi ya ce"wato Shaheeda nunawa duniya kike yi mu mutanen banza ne ko?

Mahaifiyar tawa da Æ´ar'uwata za ki je har gida ki zaga?"

Hankali kwance ta riƙe haɓa ta ce"tooo! Abba yaushe aka yi haka kuma?

Kowa fa ya san ba na zagin babba,kuma kai ma ka san haka Abba "

"Au ƙarya aka yi miki tabbatacciya?"a cewar innayyo cikin fushi, Shaheeda ta yi kamar bata ji ta ba, innayyo ta cigaba da magana a fusace

"Wato dai ba ki da ishashshiyar tarbiyya,na yarda da hakan tabbas,ke kuma jarrabawar da kika samu kenan,rashin tarbiyya,amma wallahi Zainab ba ki kyauta mana ba wallahi"

"A'a fa innayyo!babu ruwan uwata,ya kamata ku rinƙa adalci,ba komai zai faru ku rinƙa ɗaukar alhakin baiwar Allah ba"

"Ke Shaheeda! Shaheeda!!a gabana kike ƙaryata mahaifiyata?

Irin rashin albarkar da kike yi kenan?"

Kai tsaye ta ce"yi haƙuri Abba, Allah ya huci zuciyarka"

Hajiya Sa'adatu ta ce"shegiya Æ´ar banza annoba!"

"A'a fa Mummy,da ubana dai gashi kina gani, sannan kuma idan ni Annoba ce....."dukan da Abba ya kai mata ne ya sa ta yi shiru tana shafa fuskarta da ta sha mari, Abba cikin fusata ya ce"jaira kawai mara kunya,tashi ki bani waje "babu musu ta miƙe ta fice daga sashen hankalinta a kwance

Tana fita gaba É—aya parlourn aka mayar da akalar faÉ—an kan Hajiya Zainab da take zaune cikin fargaba,babu kalar maganar da innayyo bata faÉ—a mata ba, don ma dai Alhaji Yusuf yana tausarta, kuma ya hana Hajiya Sa'adatu magana

Ranta a ɓace ta koma sashenta,kai tsaye ta nufi ɗakin Shaheeda wadda tuni ta manta abin da ya faru ma, chat ɗinta take yi da ƙawayenta tana sanar musu lokacin tafiyarta zuwa Belgium,sai ga ummeey ta banko kofar

Tashi zaune ta yi tana kallonta, kafin ta nemi ba'asi Ummeey ta fara sauke mata mari a fusace,sai da ta yi mata biyu sannan ta fara masifa cikin fitar hayyaci

"Shaheeda kashe ni kike son yi kenan?

Ke yanzu ba za ki zame min sanyin idanu ba?ke kenan a cikin neman masifa,kawai burinki ki ganni ina ɓacin rai? da gaske annoba kike son zame min?

To wallahi idan kika cigaba da yi min wannan halin sai kin fasa tafiyar, tunda da alamun ma idan kin je can abin da za ki rinƙa yi kenan, shashasha kawai!"ta fice cikin ɓacin rai

Ƙwalla ta fara taruwa a idanun Shaheeda tana ƙoƙarin mayarwa, ɗabi'arta ce tun tana ƴar ƙaramar yarinya bata taɓa yarda ta yi faɗa ta yi kuka ko da ace an yi galaba akanta, yanzu kuma kuma bata kuka akan duk wani mutum da ta tabbatar ta fi shi gaskiya

Wayarta ce ta yi ƙara, ganin Muyassar ne sai ta ɗaga ta kai kunne tana sauke numfashi, Muyassar yana jin yanayinta ya kwantar da murya ya ce"da wani abu ne Shaheeda?"

"Ummeey ce ta mammare ni saboda su innayyo sun ce bani da tarbiyya na ce ina da ita"

"Kayya!ke ma bakinki ba ya bari ki ci riba,kai mata wayar mu yi magana"a kufule ta ce"itama tana da waya"

Ƴar dariya Muyassar ya yi,ya ce"haka ne,to bari na kira ta"kafin ma ya rufe baki Shaheeda ta kashe wayar ta

Muyassar kuwa haƙuri ya yi ta bawa Ummeey yana gaya mata gaskiyar abin da ya faru lokacin da Shaheeda ta je gidan, Ummeey ta ce"ni ba wani abu nake jiyewa Shaheeda ba,mace ce, watarana zata yi aure,zata tafi gidan wani da wannan tsinin bakin ne?

Ga taurin kai da gardama har ta yi mata yawa tun tana ƙaramarta, gashi sam bata da kunya ta yi ta ja min magana,ya kamata ka rinƙa yi mata faɗa "Muyassar ya rissina kamar wadda take gabanshi ya ce"in sha Allah Ummeey zata daina, yarinta ce kawai"

"To Muyassar, Allah ya sa hakan"

Muyassar yana É—an murmushi ya ce"Ameen Ummeey "

Washe gari da neman magana Shaheeda ta tashi, saboda baƙin cikin abin da aka yi mata jiya, shiyasa yau take neman wanda zata huce akanshi,don haka bayan ta gama karyawa ta koma wajen lambun gidan ta zauna

A wajen lambun gidan sashen Hajiya Atika, wadda suke kira da Ammi yake,kaf gidan ta fi kowa yara,kuma ta fi son yara

Tana zaune tana jin waƙar Alingo ta p-square tana bin waƙar Safwan ya zo zai wuce,yana ganinta ya yi murmushi ya ce "su yaya Shaheeda yan ƙasar Belgium"

Yana direwa ta É—ora"su Safwan yan zaman gida Nigeria "

Safwan ya ce"ai nima Ammi ta ce ina kammala karatun secondary za'a kai ni ƙasar waje na yi karatu "

Shaheeda tana murmushi ta ce"ai dole ka je yaro tunda kishiyar gidanku ta je,kai dai ka buɗe ƙwakwalwar ko sau ɗaya ne don ka samu Sa'a ka tafi,ka san Abba ba ya biyawa daƙiƙi kuɗin makaranta har ƙasar waje,amma ni ka ga mahaifiyata na biyo"da kallo Safwan ya bi ta, kafin ya ce "ai nima ba daƙiƙi bane,kuma nima mahaifiyata na biyo"

Ƴar dariya ta yi ta ce "kayya!yaro man kaza,kai dai je ka,kar allura ta tono garma"babu musu Safwan ya wuce zuwa sashensu

Ƴan mintuna da shigarsu sai ga Ammi ta fito riƙe da hannun Safwan fuskarta a ɗaure, hankali a kwance Shaheeda ta ɗaga kai ta kalle ta, Ammi ta ƙaraso tana faɗin "ke Shaheeda! menene manufar tambayoyin da kika saka yaron nan a gaba kina yi masa?

Wanne irin sakarci ne hakan?"

Yatsine fuska ta yi tana yi mata kallon hadarin kaji ta ce"tambaya kuma?

Ni?kuma a ina ma tambaya ta zama laifi?na tambaya an ba ni amsa, menene abin da ya kawo tuhuma kuma?"

"Ke yarinya!

Dama ana faɗin ba ki da kunya ba ki da tarbiyya,to ni na fi ƙarfin in yi da ke sai dai da uwarki,yar banza mara mutunci "

"A'a ni ɗin dai,nice nake da lokacinki,amma dai ita waccan da kike ambata ki bar ta ta ji da abubuwan da suke gabanta, ƙasar waje ce dai sai na je,duk da zuga da busa da zungure da hankaɗe da ake yi wa malam Yusuf,babu mai shiga tsakanin hanta da jini,ni da ubana kenan"ta miƙe tana waƙar hanta da jini ba sa rabuwa ta wuce sashensu zuciyarta fes

Hajiya Atika ta bi ta da kallo tana auna mata zagi,amma ita ko a jikinta, tunda dai ta samu inda ta juye nata ɓacin ran ai shikenan

Yau ma dai tana zaune bayan isha'i tana game a laptop É—inta da Muyassar ya siya mata sai ga Ummeey fuskarta a haÉ—e,ta É—aga kai tana kallon Ummeey gabanta yana faÉ—uwa,a duniya babu mutumin da take tsoro,take shakkar ta ga sauyin fuska a tare da shi kamar Ummeenta,ko mahaifinta da ya kasance mafaÉ—aci bata damu da sauyawarsa ba kamar ta Ummeenta,don haka ta cigaba da bin ta da kallo gabanta yana faÉ—uwa

#Nusy_bee

Page 20

"Sannu da zuwa Ummeey"ta faÉ—a tana rarraba idanu

"Yau kuma me kika je kika jangwalo?

Dama ina ganin fitarki ta É—azu na san ba banza ba,ina kika je Shaheeda?"

"Ummeey lambu kawai na je,ce miki aka yi na yi wani abin ko?"

"Ban sani ba,tashi ki tafi ubanki yana son ganinki"babu musu ta saka hijabi ta fice daga É—akin, Ummeey ta bi ta a baya

Da sallama ta shiga parlourn abban nasu,shi kaɗai ne ya amsa, Ummeenta ta yi sallama itama, Shaheeda ta samu waje ta zauna tana kallon Hajiya Atika da Safwan ta gefen ido,saura ƙiris ta fashe da dariya ganin yadda Hajiya Atika take ta cika tana batsewa

Sai da ta gaishe su ɗaya bayan ɗaya, sannan Abba ya ce "Shaheeda wato iya shegenki ƙaruwa yake yi ko?"

"To fa!su Fatima iyayen laifi!Abba me aka ce maka na yi yanzu ?"

"Ƙaniyarki na ce!

Wato dai ba za ki fasa halinki ba ko?

ÆŠazu me ya haÉ—a ki da Safwan har kika zagi mahaifiyarshi?"

Kallon Safwan ta yi tana ƙwalalo idanu ta ce"innalillahi!

Abba zagi kuma?

Ka san dai bana zagin manya abba,zuwa ya yi fa yana gaya min magana akan zan fita ƙasar waje,kawai sai na ce masa ai ba'a kai daƙiƙai,ya ce ai shi ba daƙiƙi bane,na ce mu gani a ƙasa,shikenan fa!

Oh Allah!Abba ka gani ko?dama fa na ce akwai mutanen da suke baƙin ciki da tafiyar nan tawa a gidan nan,ga alamu nan dai muna gani"

Ummeey ta dubi Shaheeda cikin takaici,don ta tabbatar ba haka aka yi ba, saboda ba sabon abu bane a wajen Shaheeda cin zalin yara a gidan musamman Safwan,shi kuma kamar dole in dai ya ganta sai ya yi mata magana,amma kafin ta yi magana Abba ya yi abin da ya saba duk sanda aka yi case da Shaheeda a gidan

"Shaheeda ni nake so ta tafi karatu ƙasar waje,da kuɗina na biya mata, babu wanda ya isa ya sa na janye sai Allah, don haka bana son sake jin an taɓo ta da maganar tafiyar nan

Babyn abbanta!"ya faÉ—a yana mayar da hankalinsa ga Shaheeda,yana sakin fuska, Shaheeda ta yi murmushi tana faÉ—in"na'am abbana na kaina "
Chapter 24 · 0% Book details