← Book details Gadar Tsautsayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 51

Sashe 38

Gadar Tsautsayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shaheeda kin san a halin da na samu kaina da na rasa ki a kusa da ni kuwa

Meyasa? meyasa za ki yi min haka?me na yi miki?"ita dai Shaheeda wannan karon babu baki,sai kukan da ita ma take yi cikin tsananin tashin hankali, fargaba da damuwa

Sun kwashi mintuna a haka, kafin Ummeey ta dubi Shaheeda fuska babu rahama ta ce"sai abu na gaba! wanene ya yi miki cikin jikinki?"

Muryarta a shaƙe saboda kuka ta ce"Arnold ne"

Shiru Ummeey ta yi gabanta yana faÉ—uwa,ta ce"wanene Arnold?"daidai nan Muyassar ya dawo parlourn da sallama, fuskarsa babu walwala

Kanta a ƙasa,tana jin wata muzanta da nadama, muryarta tana rawa ta ce"wanda na aura "

"Kika aura?"a cewar Muyassar yana kallonta da wani irin yanayi,"yaushe kuka yi auren?kuma wanene ya É—aura miki auren?"

Kanta a ƙasa ta goge hawayenta ta ce "kafin na tafi, wajen malami muka je aka ɗaura mana auren"

Shiru Muyassar ya yi yana bin ta da kallo cikin tsananin mamaki da takaici,ya ce"wanne malami ne haka da kuka je ya É—aura muku aure ba tare da ya yi tunanin abin da zai je ya zo ba"

Tana shashsheƙar kuka ta ce"ku yafe ni don Allah, Ummeey don Allah ki yafe min"

A fusace Ummeey ta kalle ta ta ce "tambayarki ake yi amma kin zauna kina shirme!kin san tsaf zan lakaɗa miki duka a gidan nan?ba ki san a ƙule nake da ke ba ko?"

Jikinta yana rawa ta fara ba su labarin abin da ya faru tana kuka,suka zuba mata idanu suka kallonta cikin tsananin mamaki,har ta kammala labarin,tun daga lokacin da suka yi aure da Arnold har zuwa lokacin da Diego ya saka ta a jirgi ta dawo Nigeria,da ƙyar ta kai ƙarshe kafin ta sake rushewa da kuka mai tsanani tana faɗin"don Allah Ummeey ki yafe min, zuciyata ciwo take yi min,don Allah Ummeey,zan mutu ki taimaka ki yafe min, Ummeey ki yi min addu'a don Allah,don Allah Ummeeyna"ta faɗa da ƙarfi cikin muryarta da bata fita sosai tana rungume Ummeey da ƙarfin tsiya, wadda itama zuwa yanzu kukan take yi sosai

Muyassar ne ya kama hannunta ya janye ta daga jikin Ummeey, wadda har yanzu bata yi wani yunƙuri ba, banda kukan da take yi kamar ranta zai fita,ya zaunar da ita yana faɗin "kukan ya isa haka Please,ki daina wannan kukan, abin da ya faru ya riga ya faru, Allah ya kyauta ya ba ki ikon cinye wannan jarrabawar,amma ke ma ya kamata ki daina taurin kai da gardama, Allah ya raba ku da abin da ke cikinki lafiya ya albarkaci rayuwarsa,ki kwantar da hankalinki kin ji?

In sha Allah komai zai daidaita,ki daina kuka"ya ƙarashe maganar yana goge mata hawaye

Cikin kuka ta ce"yaya ina tsoron abbana, Ummeey har yanzu tana cikin fushi da ni, tsoro nake ji yaya"

Muyassar ya ce"kin san dai ke favourite É—in abba ce ko?

To ki kwantar da hankalinki, in sha Allah ba zai ɓata miki rai ba, Ummeey kuma ki ba ta lokaci zata huce

Ya kamata zuwa yanzu a ce kin kwantar da hankalinki,kin fawwalawa Allah komai kin ji yar ƙanwata?idan ba haka ba kuma ba zan sake shigowa wannan sashen ba,idan ma na shigo to wajen Ummeey kawai na zo,ba wajenki ba"Shaheeda ta yi saurin goge hawayenta tana faɗin"na daina kukan yaya,na daina,amma don Allah ka cewa ummeey ta yafe min"Muyassar ya ce"ki kwantar da hankalinki,in sha Allah ta yafe miki ma,me za ki ci yanzu?"

Shaheeda ta girgiza kai ta ce"na ƙoshi yaya"

Muyassar ta É—aure fuska ya ce "okay ba ki huce ba kenan?"

Da sauri ta girgiza kai ta ce "a'a yaya,ka kawo min avocado,ina so zan ci"Muyassar ya yi murmushi yana lakace mata hanci yana faɗin "that's my little ƙanwa!

Sai na dawo,ki kula kin ji"ya miƙe ya fice daga sashen yana ɗaga mata hannu

Bayan fitar Muyassar aka fara zaman kurame tsakanin Ummeey da Shaheeda,sun kai aƙalla mintina goma kafin Shaheeda ta dubi Ummeey ta yi ta maza, cikin raunin murya ta ce"don Allah Ummeeyna ki yafe min

Kin ji Ummeey?ko zagina ne ki yi, Ummeey ki dake ni ko za ki huce,amma don Allah ki yafe min,ki yafe min don Allah,kin ga halin da ma shiga a sanadin fushin da kika yi da ni,don Allah ki yafe min na samu sassauci kin ji Ummeeyna?"

Duk da yadda zuciyar Ummeey take zafi,amma abinka da ɗa da uwa,sai ta ji zuciyarta ta karye, tausayin Shaheeda ya rufe ta,ta dube ta, cikin sanyin murya ta ce"Allah ya ƙara ganar da ke, Allah ya raba ku lafiya , Allah ya ba ki lafiya, tashi ki je ki yi wanka ki sauya kaya,me za ki ci?"

Murmushi ya ƙwacewa Shaheeda,ta rungume Ummeey tana faɗin "na gode Ummeeyna, Ummeey ko menene kika dafa zan ci, Allah ya saka miki da alkhairi Ummeeyna"daga haka ta miƙe ta shige zuwa ɗakinta tana farin ciki

Jikinta ya yi sanyi sosai lokacin da ta ga wasiƙar da ta rubutawa Ummeey a inda ta bar ta, Allah sarki Ummeey! yanzu haka don kar damuwa ta dame ta ne ta kasa shigowa ɗakin, Allah sarki Ummeey!ta goge hawayenta ta shiga wanka

A parlour kuwa Ummeey tana zaune sai ga Hajiya Atika kamar an hankaɗo ta, kallonta Ummeey ta yi gabanta yana faɗuwa,amma ta dake ta ƙaƙaro murmushi ta ce"a'a!

Maman Malika!ya yaran?"

"Yara alhamdulilla!sune suke gaya min wai Shaheeda ta dawo, menene gaskiyar maganar?"

Jikin Ummeey a sanyaye ta jinjina kai,ta ce"eh Shaheeda ta dawo,tana ciki ma, yanzu ta shiga"

Hajiya Atika ta jinjina kai ta ce "to kenan gaskiya yaran suka faÉ—a da suka ce ta dawo da tsohon ciki kenan?"

Ummeey ta kalle ta jiki a saɓule kafin ta yi ƙasa da kai, Hajiya Atika ta ce "tambaya nake yi Hajiya,da gaske ne?"

Ummeey ta ce"da gaske ne,ta dawo da ciki"Hajiya Atika ta rafka salati tana rike haɓa ta ce"oh Allah ka dube mu!

Wai cikin shege a gidan Alhaji Yusuf Maliya duk da tarin tsaro da tarbiyyar gidan?

To Allah ya sawwaƙe,da kika ce mata ta dawo yau ai alhajin nan da abin da bai wuce sati guda ba ma zai dawo,shi da kanshi ai zai yi abin da ya dace,don dai mu ma muna da ƴaƴa mata, gaskiyar magana kenan"ta juya fuuu ta fice daga parlourn

Ummeey ta bi ta da kallo kawai ba tare da ta iya ce mata komai ba,ta sani hakan zata faru, fiye da haka ma zata iya faruwa, gashi Hajiya bata nan ballantana ta tura ta gidanta,amma zata yi magana da Hajiya Jamila,zata je gidanta ta zauna,don ba zata iya wannan tashin hankalin ba,ba za'a yi haka da ita ba

Cikin ɗan ƙanƙanin lokaci maganar dawowar Shaheeda ta bazu a maliya estate,da yawa sai zuwa ake yi a ganta, musamman idan an faɗi da tsohon ciki ta dawo,babu wanda yake da tunanin ya tambaye ta daga ina ta samo cikin, banda wanda Muyassar ya yi mata,shi kuwa Muyassar ya ce mata kar ta damu da kowa, Allah ma ya sani ba zina ta yi ba,ba ɗan shege bane a jikinta don haka kar ta wani damu,idan ta haihu ma shine zai zama baban yaron

Hakan ya sa ta yi kuka sosai,ta yi nadama,amma ta san auren Muyassar ya fi ƙarfinta,don ta ji an ce watanni uku ne suka rage a yi aurensu da Arfa, wadda tun da Shaheeda ta zo bata ganta ba,alamun tana gidan iyayenta

Kwanan Shaheeda biyu da dawowa,da daddare suna zaune a parlour, Shaheeda tana cin avocado da yanzu ita ce abincinta,yau ma through out ta kasa cin komai saboda jikinta da ya motsa sai da Ummeey ta kai ta asibiti,ba su juma da dawowa ba ma

Wayar Ummeey ce ta yi ƙara,sai da gabanta ya faɗi ganin wanda yake kira, Abba ne

#Nusy_bee

Page 31

Kallon Shaheeda Ummeey ta yi, wadda take ta kallonta tunda wayar ta fata ringing,don ta gane abbanta ne ya kira daga yanayin ringing É—in, Ummeey ta É—auke idanunta saboda hango damuwa da fargaba da ta yi a idanun Æ´ar tata,ta É—aga wayar da sallama a bakinta

A gaggauce Abba ya amsa,ya kira sunanta "Zainab!"gyara zama tayi tana amsawa "na'am Alhaji"

"Menene gaskiyar maganar da na ji na cewa Fatima ta dawo gida?"

Sai da Ummeey ta kalli sashen da Shaheeda take zaune ta yi tsumu, sannan ta ce "eh haka ne,ga ta a gida"

Abba ya ce "to da kyau"kafin ta yi wani yunƙuri ya kashe wayarshi

Shiru Shaheeda ta yi tana kallon Ummeey,tashin hankali yana bayyana a kan fuskarta, cikin rawar murya ta ce"Ummeey me ya ce?"

Ummeey ta kalle ta da kulawa ta ce"bai ce komai ba,ki kwantar da hankalinki,babu abin da zai faru sai alkhairi in sha Allah,ke dai ki yi ta addu'a kawai,kin ji?"Shaheeda ta jinjina kai cikin sarewa, sannan ta miƙe don mayar da abincin zuwa kitchen,don gaba ɗaya ya fita a ranta,Ummeey ta kalle ta ta ce"ina za ki je?"

Shaheeda ta ce "na ƙoshi,zan mayar da abincin kitchen"Ummeey ta ce "to dawo ki zauna,idan kin manta bari na tuna miki,a dokokin da aka kafa miki ɗazu har da ta hana zama da yunwa,maza zo ki zauna ki ci"babu musu ta dawo ta samu waje ta zauna,ta cigaba da cusa abincin

Ummeey tana kula da yadda ta tsangwami kanta tun wayar da suka yi da Abba,don haka ta fara ba ta labarai masu É—ebe kewa,tun Shaheeda bata sakewa har ta fara

Washe gari da fargaba Shaheeda ta tashi, duk daily activities É—inta da ta yi a sanyaye,ita kanta a yanzu bata da burin da ya wuce Abba ya dawo ta san makomarta a gidan,ko dukan tsiya zai yi mata bata damu ba muddin zai yafe mata,ya bar komai ya wuce kamar Ummeey

Haka ta yini zullumi da fargaba har zuwa bayan la'asar,bata juma da idar da sallar la'asar ba ta ji alamun dawowar mahaifin nasu

Gabanta ya faɗi,ta yi tagumi tana jin yadda zuciyarta take lugude,bata taɓa tsammanin akwai wata rana a duniya da zata zo ta yi fargabar ganawa da mahaifinta ba, saboda irin yadda suka shaƙu, kuma suke tsananin son juna

Ummeey tana kule da ita, ganin tunanin ba zai ƙare ba sai ta dube ta ta ce"Shaheeda wai lafiyarki kuwa?tun ɗazu kina abu ɗaya? tunanin me kike yi ne haka?"
Chapter 38 · 0% Book details