← Book details Gadar Tsautsayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 51

Sashe 49

Gadar Tsautsayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Har cikin kanta ta ji wannan tuhumar da ake yi mata,tashin farko Ummeey ce ta faÉ—o mata a rai,ta fara tunanin ya zata ji idan ta ganta a wannan halin?tabbas bata yi mata adalci ba, kafin ta gama tunanin aka bayar da umarnin a kawo ta zuwa kusurwar tuhuma,babu musu Æ´an sanda suka rako ta,ta sunkuyar da kai,har yanzu jikinta yana rawa,duk da jarumtar da ta aro

Lawyern gwamnati ne ya fara miƙewa ya gabatar da kanshi,bayan ya gaida alƙali "sunana barrister Sulaiman Yusuf,ni ne prosecutor da yake ƙalubalantar wadda ake ƙara"ya koma ya zauna

Barrister Hibba ta ɗaga kanta, cikin izza da take shigarta a duk lokacin da ta samu kanta a bakin aiki,ta miƙe a dake ta ce"sunana BARRISTER HIBBA IBRAHEEM AIYO,nice lawyern wadda ake ƙara"

Alƙali ya ba wa lauyoyi damar magana, barrister Sulaiman ne ya fara miƙewa ya ƙarasa kusa da Shaheeda da kanta yake ƙasa,ya ce "kotu tana buƙatar jin ainihin cikakken sunanki"

Bata amsa ba, kamar yadda bata motsa ko da kanta da yake sunkuye ba,har sai da barrister Sulaiman ya sake maimaita mata tambayar

Kanta a ƙasa ta amsa"sunana FATIMA SHAHEEDA YUSUF MALIYA!"

Take kotun ta É—auki hayaniya sosai,sunan Yusuf Maliya da Shaheeda ta ambata a matsayin mahaifinta ya ba wa mutane da yawa mamaki,ko da yake akwai masu zargin Alhaji Yusuf Maliya shine mahaifinta,amma ya fito ya yi hira da Æ´an jarida ya barranta kanshi da ita,har wasu suke ganin kamar tana amfani da sunansa ne don tabbatarwa,amma sai barrister Sulaiman ya ce"kina nufin ke yar Alhaji Yusuf Maliya ce?mamallakin MALIYA GROUPS OF COMPANIES?"

Kanta tsaye ta amsa masa da faÉ—in "eh,kai tsaye ma na ce nice babbar Æ´arshi"

Barrister Sulaiman ya jinjina kai ya ce"dama haka na iya faruwa. To Malama Shaheeda!kotu tana tuhumarki da laifin safarar miyagun ƙwayoyi tsawon shekaru uku,da satar kuɗaɗe ta yana wato Yahoo, menene gaskiyar maganar?"

Shiru ta yi da farko, jikinta a sanyaye, kafin ta ɗago a hankali suka haɗa idanu da barrister Hibba, Hibba ta jinjina mata kai alamun ƙwarin gwiwa,don haka ta fara zayyano bayani kamar haka"eh haka ne!

Amma ba shekara uku bane, shekara É—aya ne!"

Shiru kowa ya yi yana kallonta da tsananin mamakin jin abin da ta faÉ—a, barrister Sulaiman ya ce"amma menene hujjarki ta cewa shekara É—aya ne?bayan kowa ya san shekaru uku kika É—auka kina aikata wannan laifin?"

Shaheeda ta gyara tsayuwarta ta ce"shekara guda na É—auka ina aikata wannan laifin saboda wata larura da ta same ni, wadda ya zamto bani da mafita sai hakan, tsawon shekaru biyun kuma nemana ake yi kawai ina guduwa,amma ba aikata laifi ba"

Barrister Sulaiman ya jinjina hakan cikin tsantsar mamaki, kafin ya ce"amma kuma duniya ta shaida cewa kin cigaba da aikata miyagun laifukan,har ma ana kyautata zaton jami'an tsaro sun kama ki ne bayan tarko da suka yi miki, menene gaskiyar wannan maganar?"

Ita kanta Shaheeda ta yi mamakin wannan ƙaryar da ta ji an yi mata,kuma zuwa yanzu ta sake tabbatar da maganar barrister Hibba da take ce mata ba don a ƙarfafa doka aka kama ta ba,sai don wani ƙudiri na dabam,don haka kai tsaye ta buɗe baki da niyyar magana,amma sai barrister Hibba ta riga ta

"Objection ya mai shari'a!

Barrister Sulaiman yana so ya ɗora ƙarfin zargi akan wadda ake tuhuma bayan ta musanta hakan,mai Shari'a ya kula da hakan"babu ja mai Shari'a ya yi masa gargaɗi,ya bayar da haƙuri sannan ya cigaba da tambayoyinsa

Ya sake duban Shaheeda ya ce"kina da hujjar abin da kika faÉ—a? na cewa kin dakatar da duk wani aiki da kike yi a tsawon waÉ—annan shekaru?"

Shaheeda ta jinjina kai ta ce"eh!

Ina da hujja "

Barrister Sulaiman ya ce"menene hujjarki?"

Shaheeda ta ce"tun a lokacin da aka kama ni a Abuja na dakatar da komai,sai dai Alhaji Sa'idu Wada, tsohon minister a wancan lokacin ya buƙaci na cigaba da yi masa aiki,na fara na ɗan lokaci,daga baya da na ga na tara abin da nake nema,dama ba gaya maka akwai dalilin da ya sa nake yi,sai na daina komai

To saboda na yi masa bore na ce ba zan cigaba da yi masa aiki bane sai ya sa aka fara bibiyata don a kama ni "

Barrister Sulaiman da yake aika mata wani kallo ya ce"wanne Alhaji Sa'idu Wada kike nufi?"

"Alhaji Sa'idu Wada dai wanda ka sani,kowa da yake nan wajen ya sani,wato tsohon ministan ilmi"

Take waje ya kaure da hayaniya,don dama wasu mutanen suna zarginsa da aikata ɓarna,wasu kuma sun yi mamakin bayyanar sunansa a cikin maganar,sai da alƙali ya buga guduma sannan aka yi shiru, barrister Sulaiman ya ce"ko kina da shaidar hakan?"kai tsaye ta ce

"Eh,na turawa lawyerna, barrister Hibba Aiyo evidence,zata nunawa kotu"ita kanta bakinta rawa yake yi ta ƙarasa, saboda bata san me barrister Hibba ta taka ba ta ba ta umarnin ta faɗi haka

Alƙali ya buƙaci barrister Hibba ta fito,ta miƙe ta fito daga wajen zamanta,gaba ɗaya kallo ya koma sama,don an tabbatar da cewa barrister Hibba bata bari a yi nasara akanta tun tana matashiya,har zuwa yanzu da girma ya fara cim mata,ta taso ta dawo gaban alƙali ta fara magana

"Ya mai shari'a,kafin na gabatar da hujjojin Shaheeda a gaban kotu zan so kotu ta ba ni dama na yi mata wasu ƴan tambayoyi"alƙali ya bata izini,ta rissina ta ce"na gode ya mai Shari'a "ta dubi Shaheeda ta ce"a bayananki na ɗazu kin shaidawa kotu cewa akwai dalilin da ya sa kika faɗa harkar safarar ƙwayoyi da Yahoo, shin za ki iya sanar da kotu wannan dalilin?"

A hankali ta jinjina kanta, sannan ta fara ba da labarinta a hankali,bata dakata ba har sai da ta kai ƙarshen labarin, kafin ta kai ƙarshe kusan rabi da quarter da suke kotun sai da suka zubar da hawaye

Bayan Shaheeda ta kai ƙarshen bayanin barrister Hibba, wadda ita zuwa yanzu ta daina kuka akan irin wannan case ɗin ta ɗauko laptop ɗinta ta danno wasu hotuna da Roxy da Alhaji Sa'idu Wada suke tattaunawa,har ma da CCTV footage da ta samu oga boss ya samar Mata na lokacin da Alhaji Sa'idu Wada yake tattaunawa da Roxy,ga bayanai nan raɗau sun fito,ga muryarshi ga hotonsa

Tuni kotu ta sake kaurewa da hayaniya,mafi yawa suna tsinewa Alhaji Sa'idu Wada da suke ganin a matsayinsa na ministan ilmi abin da ya dace shine ya tallafi Roxy ta yi karatu ya daƙile wannan sana'ar tata,to amma bayan munin abin da ya nema a wajenta har ma ya nemi ya yi haramtacciyar tarayya da ita,hakan ya sa mutane suka fara tsine masa,da yawa kuma suka fara yabawa Roxy saboda yadda ta nuna kai tsaye cewa ba zata siyar da mutuncinta akan wani kuɗi ba

Sai da alƙali ya buga guduma sannan aka yi shiru,ya ba wa barrister Hibba izinin cigaba da bayani

"Ya mai Shari'a,abu ne sananne a nan cewa Fatima Shaheeda ta aikata laifukan da ake tuhumarta tabbas,kuma daidai ne ta fuskanci doka,amma kuma ya kamata a ce wanda ya yi silar faÉ—awarta ciki shima ya fuskanci doka

Sannan ya mai Shari'a,duba da halin da Fatima Shaheeda ta shiga a rayuwa,muna roƙon wannan kotu mai adalci da ta yi mata rangwame,ko babu komai a ba ta wata dama a rayuwa"

Kotu shiru ta yi,kowa yana jiran abin da alƙali zai ce game da shari'ar da ake kan gabatarwa, wadda take a cukurkuɗe, alƙali ya juma yana rubuce-rubuce kafin ya ɗago yana gyara zaman glasses ɗin idanunsa,ya dube su ya ce"kotu ta saurari hujjoji daga dukkan ɓangarori,kuma ta yi dubanta don yanke hukunci,amma an ɗaga shari'ar zuwa takwas ga watan gobe,wato nan da sati biyu kenan

Kotu ta bayar da umarnin a cigaba da tsare Fatima Shaheeda ba tare da beli ba zuwa ranar, sannan ta bayar da umarnin a kamo tsohon ministan ilmi,wato Alhaji Sa'idu Wada,don tuhumarsa bisa ga laifukan da ake zargi ya aikata"daga haka ya buga guduma,mutane suka miƙe suna faɗin "koooootuuuuuu!!!"

Daga nan jami'an tsaro suka fito da Shaheeda barrister Hibba ta tare su, Shaheeda ta ɗago kai a sanyaye ta kalle ta, Hibba ta yi mata murmushin ba da ƙarfin gwiwa,amma zuciyar Shaheeda ta karye, hawaye suka cika mata idanu, Hibba ta goge mata hawayen, cikin kwantar da murya ta ce"khairan in sha Allah daughter!

Very soon za ki fita kin ji? Allah yana tare da mu gaba É—aya,ki daina zubar da hawayenki a inda bai cancanta ki yi asararsu ba"Shaheeda ta jinjina kai a hankali, Hibba ta dafa kanta, sannan ta wuce ta bar wajen, jami'an tsaro suka wuce da Shaheeda zuwa motar da za su kai ta gidan kaso,duk da Æ´an jarida suna ta jefo mata tambayoyi

*NILE UNIVERSITY NIGERIA,ABUJA*

Ɗan murmushi ta yi bayan sun kammala kallon yadda shari'ar su Shaheeda ta gudana, ƙawarta Hanan da take zaune kusa da ita suke kallon tare ta kalle ta ba tare da ta yi magana ba, tana murmushi ta ce"seriously Hanan I'm very proud of this lady, wallahi Abba ya yi asarar brainy girl irinta,ya kasa gane su Mommy da sauran matansa hassada suke yi masa na samun one in town irin aunty Shaheeda,i like her so much wallahi,ba ƙaramin daɗi na ji ba da aka ce ita ce wadda ta rinƙa jijjiga ƴan sanda,ko zuwa nan gaba na san sun gane cewa ba iyawarsu ba ce ta sa suka kama ta ba,ikon Allah ne kawai"

Hanan tana dariya ta ce"gaskiya Na'ima ba ki da mutunci, Mommyn kike cewa tana yiwa Abba hassada?"

"Let's keep joke aside Hanan,kin san wacece Mommy na, saboda yayan mamanki ta aura, which is our father,dukkanmu muna iya tuna yadda ta wahalar da dangin nan namu,da a ce mum É—inku ce ta wahalar da mu kamar yadda mum É—ina ta wahalar da ku da ba mu isa mu zauna a waje É—aya ba

I'm very sure su Mommy na sune suka janyo Abba ya kori Aunty Shaheeda

Kin san babban yayanmu Muyassar ya so ya aure ta,tun muna yara, Allah bai yi ba,su Mommy suka hana, suka aura masa wata matsiyaciya,for God sake Hanan na tsani yarinyar nan,bata da tarbiyya ko kaɗan,amma Mommy bata gani saboda tana sonta, shiyasa na zaɓi na koma wajen Mom ɗinki kawai na zauna,ko wajen Uncle Ismail (ƙanin babanta)"
Chapter 49 · 0% Book details