← Book details Gadar Tsautsayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 51

Sashe 51

Gadar Tsautsayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

A ina ta cigaba da rayuwa?ta haihu?me ta haifa? tabbas ya tuna Æ´an sanda sun fitar da rahoton cewa da É—anta aka yi mata tarko, kenan wannan É—an na Arnold ne kenan?

Ya aka yi yan sanda suka san da zamansa da za su yi mata tarko da shi?

A ina ta ajiye shi take kasuwancin nata?ko da shi take tafiya?ya dafe kai cikin ruÉ—ewa, gaba É—aya sabgar nan tana kulle masa kai, gashi an hana shi ganinta ballantana ya je ya ji dukkan bayanai daga gare ta,har da tambayar ina yaron ya shiga?

Kwantar da kanshi ya yi a jikin kujerar da yake zaune ya lumshe idanu, tabbas Shaheedansa tana cikin matsala,amma matsalar da yake hangowa a gaba ta fi wadda ake ciki yawa

*RANAR KOTU TA BIYU*

A yau kam kotu ta cika ta tumbatsa fiye da zaman baya,kuma yawancin mutane dalilai biyu ne ya kawo su,na farko ganin hukuncin da kotu zata É—auka akan Shaheeda,na biyu kuma ganin Alhaji Sa'idu Wada, kamar wancan karon, yau ma Muyassar ya samu zaman kotun, Hakazalika Haisam da tawagarsa

Bayan an shigar da Shaheeda don fara zama,a can ta hango Oga boss da Azeema a cikin mutane,suna haÉ—a idanu da Azeema ta ga hawaye sun fara wanke mata fuska,ta yi murmushi tana girgiza mata kai

An fara zama kamar dai wancan karon,an sake karanto gaɓar da aka tsaya a zaman baya, Shaheeda ta sake tabbatar da cewa eh lallai ta aikata, sannan alƙali ya buƙaci ganin Alhaji Sa'idu Wada,a nan yan sanda suka tabbatar da cewa ya bar ƙasar tun kafin a gama zaman baya, da alamu ma a shirye yake da hakan

Hakan ya sa alƙali ya bayar da umarnin gani da kamu a duk inda yake, sannan ya duƙa ya cigaba da rubuce-rubucensa,kotu ta yi tsit tana jiran hukuncin da za'a yankewa Shaheeda, wadda a wannan lokacin da za'a tsaga jikinta bai zama lallai a ga jini ba saboda yadda ta daskare tana jiran ikon Allah, duk da cewa a yanzu ta samu nutsuwa da kwanciyar hankali sosai sakamakon karatun alƙur'ani da take yi a yawancin lokuta

Alƙali ya ɗago ya fara magana "kotu tana tuhumar Shaheeda da safarar miyagun ƙwayoyi,wanda ta amsa ta yi hakan da kanta, sannan tana tuhumarta da sata ta yana,wato yahoo,bayan ta yi hacking asusun mutane

Don haka kotu ta yanke mata hukuncin shekaru bakwai a gidan gyaran hali bisa samunta da laifin safarar miyagun ƙwayoyi, rangwamen hukuncin ya samo asali ne saboda halin rayuwa da ta samu kanta,da kuma wanda ya zama shine mai alhakin hakan

Na biyu kuma kotu ta yanke mata hukuncin ɗaurin shekaru uku a gidan kaso bisa samunta da laifin satar kuɗaɗen mutane ta yana wato Yahoo, sannan kotu ta ƙwace dukkan abin da ta mallaka na dukiyarta da kadarorinta,idan bata yarda da hukuncin ba,tana da damar ɗaukaka ƙara zuwa kotun gaba nan da kwanaki talatin"daga nan ya buga guduma,mutane suka miƙe suna faɗin "koooootuuuuuu!!!!"

Tirƙashi!!!

(Yanzu wani wasan zai soma!!!"

*Wannan shine ƙarshen book one,akwai ragowar chakwakiya masu ɗimbin yawa a gaba,ni kaɗai ce nake tunanin akwai wani abu tsakanin prisoner ɗin da wanda ya yi arresting ɗinta?😁baya ga haka shin ya rayuwar Shaheeda zata kwashe a prison tsawon shekaru goma?

Ga Ummeey da ta kasance abar tausayi kuma wadda take cikin ƙunci da damuwa,shin damuwar tata zata tafi a banza ne ko zata samu sakamakon haƙurinta?

Nice dai Nusaiba Ibrahim Rimi (Nusy bee)ku kasance da ni a littafi na biyu don jin yadda zata kaya

Book one shine Free, Book 2 Paid ne both Whatsapp and Arewa pen,ga mai buƙata ya tura #500 kacal ta wannan account number 8125952284 Nusaiba Ibrahim Rimi moniepoint,sai a tura shaidar biya ta wannan number 08125952284,kada ku sake a yi babu ku,ina iyalan Roxy da na yallaɓai CSO Haisam ne?

Sai na ji ku.

#Nusy_bee
Chapter 51 · 0% Book details