Sashe 11
Gadar Tsautsayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wata sabuwa!duk da haihuwar da matan suka yi a kusan lokaci ɗaya hakan bai saka ya iya haɗa soyayyar Shaheeda da ta kowanne yaro ba,hakan ya tayar da rikici, musamman ma da matan gidan suka ƙara hayayyafa,amma ita Ummeey ko ɓatan wata bata sake yi ba tun bayan haihuwar Shaheeda
Hakan yana damunta,amma ta miƙa lamarinta ga Allah,ta rungumi ƴarta tilo ta cigaba da kulawa da ita
Shaheeda tana da shekaru bakwai yaya Saude, wadda ake kira da Hajiya Saudat a yanzu ta koma Egypt da zama, saboda wani ɗan ƙanin mijinta da ta riƙe, ya yi mata komai,ya mayar da ita uwa, kasancewar ya rasa iyayensa tun yana ƙarami
Ba su cika gaisawa ba sosai, saboda a can baya babu waya sosai,sai dai bayan wasu shekaru masu yawa sun dawo, inda suka samu mummunan labarin abin da ya faru da Shaheeda, yanzu haka ma ba'a san inda take ba,yaya Saude ta yi kuka sosai,ta ci burin ina ma ana dawo da hannun agogo baya?da ta dawo da baya ta dawo a ƙasar don ta ɗauki Shaheeda, wadda har zuwa yanzu kukan da ta fita tana yi ya kasa barin tunanin mahaifiyarta
To daga lokacin da Hajiya Saudat ta sake komawa Egypt bata sake waiwayar Nigeria ba sai yanzu, wannan kenan
✨💫
A daidai katafaren gidan da Alhaji Abubakar, ɗan rikon Hajiya Saudat ya gina mata Hajiya Zainab ta yi parking, ba tare da ta iya jiran mai gadi ya buɗe gate ba,ta ƙwanƙwasa ƙofa,yana buɗewa bata tsaya amsa gaisuwarshi ba ta wuce cikin gidan
A ƙaton luxury parlourn ta iske dattijuwar tana shan kayan marmarin da mai aikinta ta yi mata blending,tana shiga bata yi wata-wata ba ta faɗa jikinta ta fashe da kuka
Ɗan murmushi Hajiya Saudat ta yi,ta ɗago ta tana faɗin "za ki ƙarasa jikin tsufa autar Hajiya,zauna mu yi magana, wannan kukan ba shi da amfani,ya kamata ki san zuwa yanzu kin girmi kukan banza Zainab"
#Nusy_bee
Page 9
Hajiya Zainab ta gyara zamanta tana goge hawayenta, cikin karyewar murya ta ce"na rasa yadda zan yi miki bayani ne yaya Saude
Abubuwan sai sake lalace min suke yi,ina kewar ƴata, aƙalla ko da a ce ina jin motsin ta zan ji sanyi
A silar wannan abu da ya faru har yanzu ina fuskantar dariya da izgilanci da gori daga wajen kishiyoyi har ma da ƴaƴansu,ga ki ba kya nan yaya Saude,ina cikin wani hali"ta ƙarashe hawaye yana zubo mata sosai
Abin ya taɓa Hajiya Saudat sosai,amma sai ta yi murmushi cikin dattako,ta kama hannunta ta miƙar da ita tsaye,kai tsaye suka nufi dinning area, Hajiya Saudat da kanta ta zuba mata abinci,dama ta saka an dafa abin da ta san ta fi so,sakwara da miyar egusi,ta tura mata gabanta tana faɗin "bismillah auta ta!"
Kallon abincin Hajiya Zainab ta yi,tana shirin yin magana Hajiya Saudat ta ce"kin san bana san musu,na ce ki ci"bata sake yunkurin musantawa ba ta fara tura abincin da ƙyar,Hajiya Saudat ta fara ba ta labarin irin yadda ta yi rayuwa cikin farin ciki a Cairo
Tuni ƙunci ya fara kwaranyewa daga zuciyar Hajiya Zainab,tana murmushi ta ce"ki ce daɗinki kawai kike sha Hajiya
Gaba ɗaya kika manta da mu,kika bar mu da kujiba-kujiba"Hajiya Saudat tana murmushi ta ce"bari kawai auta,ai da an fita da Ni na zaga ƙasar zan fara tuna auta,sai na ji kamar na ce a zo a ɗauko min ke mu huta tare,mu ga gari,gari ya ganmu,abun sai wanda ya gani kawai"
Murmushi Hajiya Zainab ta yi tana faÉ—in "gaskiya dai sai wanda ya gani Hajiya
Lallai kin more,har wani jaja-jaja kika yi fa"
Hajiya Saudat ta yi ƴar dariya ta ce"ke ma dai gashi nan ai,ba ki yi duhu ba,sai wani ƙara murjewa da kika yi kika yi kyau,da alamu dai Yusufa yana kula da autar Hajiya"
Zainab ta yi yar dariya kawai,amma kallo ɗaya Hajiya Saudat ta yi mata ta gane dariyar ta yaƙe ce,sai dai ba ta tanka mata ba,suka cigaba da cin abincin tana ta tsokanarta
Bayan sun kammala sai da suka yi sallar azahar da lokacinta ya yi, sannan Hajiya Saudat ta ja hannun Hajiya Zainab zuwa É—akinta
Zaunar da ita ta yi, sannan cikin kwantar da murya ta ce"Zainab! fuskance ni mu yi magana!!
Haba Zainab! menene dalilin da ya sa a yanzu za ki nuna raki bayan hakan ba É—abi'arki ba ce?
Menene dalilin da ya sa za ki nuna rauni alhali ke É—in ba mai rauni ba ce?
Ganin hawaye a idanunki a yanzu a dalilin ƙaddarar da ta samu yarki ya sa jikina ya yi sanyi, nake jin kamar ba gaza akanki,kamar akwai abin da ban sauke ba,haka ne ko?"
Kuka ya ƙwacewa Zainab,tana kukan ta ce"yaya Saude na kasa jurewa ne,ƴata ta ɓata,a yanzu tausayawa nake buƙata, sannan kuma......"
"Kin iya addu'a?
Kin dogara da Allah?
Kin tabbatar shi zai iya yi Miki komai?
Kin nemi É—auki daga gare shi?
To ki koma ki jira sakamako, Allah baya taɓa bai wa bawansa wanda ya dogara da shi kunya
Ki zamo baiwar da ta dogara ga Allah,kuma ta tabbatar Allah zai yi mata komai,wallahil azeem babu wani bawa a duniya da zai iya yin galaba akanki ko da da magana ne
Addu'ar uwa akan ɗanta karɓaɓɓiya ce,koma ga Allah,dage da addu'a,ki yi ta gayawa Ubangiji,da izninsa za ku ga kyakykyawan sakamako mafi alkhairi da amfani,wani kuka da damuwa da saka takaici a rai duk ba naki bane Zainab"
Cikin rawar murya ta ce"amma Hajiya yadda suke nuna min fifikon ya'ya yana matuƙar damu na, kiri-kiri suke nuna min cewa ƴaƴansu ne,kuma tawa ƴar rashin tarbiyya ta yi aka kore ta, Sannan kuma ina yi musu hassada akan nasu yaran "
Ƴar dariya Hajiya Saudat ta yi ta ce"to sai me?
Ke dai har gobe ban ce ki cire hannu akan yaran ba, saboda ubansu bai taɓa nuna cewa ba naki bane, sannan a matsayin ki na babba dole sai kin ji kin kawar da kai,babu wanda ya rubuta ƙaddarar da zata same shi
Sannan batun rashin tarbiyya kuma su ma sun san ƙarya suke yi,kamar yadda ba ki da iko akan halayya da ɗabiun Shaheeda su ma ba su da iko akan halaye da ɗabi'un yaransu
Babu ruwanki da abin da aka ce, abin da za'a ce ko ake cewa,ki mayar da hankali akan me Allah zai ce?
Allah ya yarda da hakan?wanne sakamakon zan samu a wajen Allah?
Kina rayuwa da mijinki lafiya ƙalau, don Allah ki yi haƙuri ki cigaba da yi masa biyayya, Allah ya tsare Shaheeda ya dawo da ita cikin aminci "a raunane Hajiya Zainab ta ce"Ameen Hajiya
A nan Hajiya Zainab ta kai yamma, kafin ta yiwa Hajiya Saudat sallama ta tafi gida, Hajiya Saudat ta rako ta tana cigaba da ba ta shawara, Kafin ta shiga mota
*IBIZA,BALEARIC ISLAND,SPAIN*
*PACHA IBIZA CLUB*
Kamar yadda ta saba a kowane lokaci dogon wando ne baƙi a jikinta, sai dai rigar yau T-shirt ce fara,kan nan nata babu ɗankwali,sai p-cap ɗin da ta ɗora kalar rigar jikinta white
Gabanta ƙatuwar tukunyar shisha ce ,irin wadda ta saba amfani da ita lokaci lokaci,tana ɗan jan hayaƙin shishar tana lumshe idanu tana buɗewa
A hankali ta ɗaga kai tana ƙarewa mutanen da suke cikin club ɗin kallo, musamman matan da suke kan dandali suna taka rawa a waƙar Despacito ta su Justin Bieber,a hankali ta mayar da kai ta kwantar a kan kujerar da take zaune tana lumshe idanunta
"Hi HERMOSA!"da a hankali ta buɗe idanunta da ya canja kala saboda hayaƙin shishar da ta bankawa cikinta,ta zuba su akan matashin baturen da yake tsaye akanta yana kallonta da murmushi a fuskarsa
"Leonardo! welcome!!"ta faÉ—a tana gyara zama
Waje ya samu ya zauna,ta miƙa masa hannu Kamar wanda za su gaisa,sai ya sa mata takarda a hannunta, sannan ya yi mata inkiya da idanu, ba tare da ta yi magana ba ta jinjina kai Sannan ta mayar da kanta ta kwantar a jikin kujerar da take zaune
Duk abin da yake faruwa yana daga can gefe yana kallonsu,ya tabbatar akwai abin da suke shiryawa a nan É—in,don haka sai ya zuba mata idanu ya ga gudun ruwanta
Ba ta juma a wajen ba ta miƙe don tafiya,shima sai ya fara yunƙurin miƙewa don barin wajen,dama gaba ɗaya ya takura da hayaƙin taba da na shisha, ga warin giya
Tana daf da shiga mota ta ji ya ce"hi!"
Juyawa ta yi tana kallonshi,ya yi kyau sosai a cikin wasu designer t-shirt da wando, waÉ—anda suka amshi farar fatarshi,yana murmushi cikin harshen Hausa ya ce"Barka da wannan lokaci babbar yarinya"
"Wanene kai?"ta jefa masa tambayar tana kallon cikin idanunshi
Murmushi ya yi yana ɗan buɗe idanunsa,ya ce"Nima ɗan Nigeria ne kawai, I'm very happy da na haɗu da ƴar ƙasarmu a wata ƙasar, that's why Babe"
"Wanene ya ce maka ni yar Nigeria ce?"ta jefa masa tambayar tana kallon cikin idanunshi
Kai tsaye ya amsa mata da faÉ—in "haba Madam!
Duk inda na ga É—an'uwa ai zan gane shi
Yanzu dai kaya nake buƙata,kuma ina da tabbacin zan samu a wajenki,ya za'a yi?"
Kallonsa ta tsaya yi kamar mai nazari ,ya yi É—an murmushi ya ce"kar ki damu babu mai jin me muke cewa,nan a Spain muke,ba Nigeria ba
Still shiru har zuwa yanzu bata da niyyar magana,ya yi murmushi sosai ya ce"ba ki yarda ba?
I'm MUBARAK!and you?"ya miƙa mata hannu don su gaisa
Daga inda yake yana iya kallon yadda ta razana da jin sunan,duk da kallon tsanaki da take bin shi da shi, wanda yake da tabbacin akwai abin da take son ganowa
ÆŠan murmushin da yake yi ne ya sa ta É—aure fuska ta ce"ka san ina siyar da kaya?amma ba ka san sunana ba?"
"Simple thing madam!
Na ga yadda kike naki business ɗin,kuma da yake mun saba da ƴan harƙalla a duk inda muka gansu muna gane su,ni dai sunana Mubarak,ke fa?"
Kawar da kai ta yi ta ce"tunda ka san aikina sai ka nemi sunan,na san za ka samu"daga nan ta haye kan bike ɗinta ta tayar,a ƴan mintuna ta bula masa ƙura ta bar wajen
Bin ta ya yi da kallo yana murmushi, kafin ya zaro wayarsa ya kira Awwal da suka zo ƙasar tare