Sashe 13
Gadar Tsautsayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
C-C-M!!! Ka je ka cigaba da bincike akan waɗannan letters ɗin da ka fara before,ina ga da ka gano ma'anarsu da ba ka sake attempting shiga gona ta ba, David,yi masa allurar nan"babu ɓata lokaci David ya yi masa allurar,a take kuma jikinsa ya saki,wani bacci mai nauyi ya yi awon gaba da shi
A ranar Roxy ta bar Spain zuwa Mexico,inda ta gama shirin sake order na wasu kayan,daga nan zata sake komawa Nigeria don ta rabawa distributors dinta
Har ta bar Spain ranta yana a ɓace saboda ji kimarta da take jin Haisam ya taɓa,ta yi wasa da manyansa,shi wanene da yake jin zai iya biyo ta har inda take ya ce wai zai kama ta,ta ja tsaki ya fi sau a ƙirga
*HAISAM*
Yana zaune a garden ɗin da yake kusa da masaukinsu ya yi shiru yana kallon waje ɗaya,amma da alamu hankalinsa ba ya kan inda yake kalla, tunani yake akan wulaƙanci da tozarcin da Roxy ta yi masa,wanda tun da ya zo duniya ba'a taɓa yi masa makamancin irin wannan cin mutuncin ba
Bayan Roxy ta gama yi masa bayanin da ya zauna masa akai,don tabbas zai yi amfani da su ya karya alkadarinta,ta sanya aka yi masa allura,ta saka aka cire masa kaya aka bar shi daga shi sai shortneakers,ko arzikin singlet babu, sannan aka kawo shi gefen gari aka ajiye shi cikin dare
Sai da ya samu ya koma masaukinsa,ya sake lalubensu Awwal,Awwal ya shaida masa cewa lokacin da suke cikin magana da shi,ba su san abin da ya faru ba suka ji network ɗinsa ya katse, ƙarshe sun yi laluben duniya ba su same shi ba
Tunda yake a wajen aiki ba'a taɓa yi masa illa an lalata masa aiki irin wannan karon ba,sai yanzu ya gane dalilin da ya sa Roxy take ba wa jami'an tsaro wahala, tamkar wadda aka yiwa training,tana aiki da lissafi sosai
Amma kuma wannan abu da ta yi masa shine ya sa yake jin dole ma ya kai ta ƙasa ko ta wanne hali,zai san yadda zai yi da ita
Miƙewa ya yi ya fice daga garden ɗin,a ranshi yana raya ta hanyar da zai bi ya rusa wannan yarinyar da ya kira annoba
Da yamma ya kammala komai da shi da team É—inshi,suka bar Spain zuwa Nigeria
*KANO*
"Arfa!ba Ni wayata!"
"Wacece wannan da kake kallon hotonta?
Malam ka gaya min ko ka ga bala'i a gidan nan wallahi!"
"Arfa na ce ki bani wayata ko?"ya faÉ—a cikin É—aga murya
"Wacece wannan da kullum kake kallon hotonta?
To wallahi ba zan bayar da wayar nan ba sai ka gaya min wacece!
Okay!na gane!wato yanzu hotonta kake kalla ko?wato ina murnar na rabu da ƙaddara amma ashe tana liƙe da ni ko?ko tsine maka aka yi ne da har yanzu Kai kake sonta bayan kowa ya kama kanshi kanta?"
"Oh seriously!ashe dai kin san wacece kike wahalar da kanki wajen tambaya?ba ni wayata dalla malama!"
A maimakon ta ba shi wayar sai ta buga ta da ƙasa,sakin baki ya yi yana kallonta cikin mamaki da takaici,ta yi ta buga wayar da ƙasa har ta yi kwatsa-kwatsa da ita, sannan ta ɗaga jajayen idanunta ta ce"Muyassar!
Na fi ƙarfin ka ci amanata saboda kilaki,ragowar arne!!!"
Da wani irin ɓacin rai da hargowa ya ce"Arfa!
Watch your tongue!ina yi miki gargaɗi da babbar murya kar na sake jin kin kira ta da kilaki,akwai kilaki da ta wuce ki ne? wadda ta gama tambaɗewa kafin a cuce ni a liƙa min?"
"Muyassar!na za ka yiwa ƙazafi?don na kama ka kana kallon hotunan kilaki shine za kayi min ƙazafi!tsawon shekarun da muka ɗauka da kai baka taɓa tunanin ka yi min ƙazafi ba sai yanzu?
Innalillahi wa inna ilayhi rajiun!!
Allah ya yi min sakayya da kai,wa ya sani ma ko kaine ka fara nuna mata hanyar lalacewar shiyasa za ka......."
"Arfa!"ya daka mata tsawar da ta kaɗa ƴan hanjinta,yana huci cikin tsananin ɓacin rai ya ce"do your worst Arfa,ki yi duk abin da ya zo ranki, lokacin ki ne,amma kar ki sake kiran Shaheeda da karuwa,ba ki sani ba,bari na sake nanata miki,I LOVE HER!I LOVE HER MORE THAN HOW I LOVE MYSELF!
Kar ki sake haÉ—a wata ke da Shaheeda, Shaheeda ba sa'arki ba ce!!!
Ki yi duk abin da za ki yi, lokacinki ne,amma idan kika sake aibata ta komai zai iya faruwa, ciki kuwa har da tafiyarki gidanku, diot!!!"yana gama magana ya ja tsaki ya juya ya fice daga ɗakin cikin tsananin ɓacin rai,yana jin zuciyarsa tana tafasa,ya rasa wanne irin zafi yake ji,ji yake ya yiwa Arfa dukan mutuwa ma,ko zai samu ya huce wannan abin baƙin cikin da ta cusa masa
Ya sani soyayyar Shaheeda wani sashe ce ta rayuwarsa,da numfashinsa take bugawa,babu yadda za'a yi daidai da second É—aya ya iya mantawa da ita,ko ta bar tunaninsa,a kowanne hali,a kowanne lokaci da ita yake kwana yake tashi,ya sani soyayyar Shaheeda da ita zai bar duniya, kuma har zuwa yanzu ba ya jin ya karaya,yana da kyakkyawan fatan ko ba daÉ—e ko ba juma zai mallake ta a matsayin matarsa
Ita kuwa Arfa a wajen ta zube tana wani gunjin kuka mai motsa rai,ta daɗe tana zargin Muyassar yana tare da soyayyar Shaheeda,a da gani take yi ta haye,bata tare da kowacce matsala,amma sai ta tarfa Muyassar yana bacci yana sambatun kiran sunan Fatima Shaheeda,hakan ne ya tayar mata da hankali,ta so ta tuhume shi a wancan lokacin,amma ta san wanene Muyassar, mutum ne tsayayye wanda baya son wargi,hakan ne ya sa ta kasa fito masa gaba da gaba,ta fara bincikensa ta ƙarƙashin ƙasa
A yau dai ta kama shi red handed tana kallon hoton Shaheeda,hakan ya sa ta fizge wayar,har suka yi rikici ya kai su ga haka
Tana kuka sosai ta miƙe ta nufi inda wayarta take,tana ɗauka kai tsaye ta kira yayarta Hajiya Ruƙayya
Hajiya Ruƙayya tana ɗagawa Arfa ta fashe da kuka sosai, Hajiya Ruƙayya da take zaune tana cin abinci sai da ta kusa ƙwarewa,a ɗan firgice ta ce"Arfa lafiya dai ko?
Me aka yi miki kike irin wannan kukan?"
Cikin hargowar kuka ta ce"Aunty na gaji!na gaji wallahi,na kasa gane ɗabiun da abban Zuhra ya ɓullo min da su kwanannan,ashe wai har yanzu yana son wannan matsiyaciyar ƙaruwar yarinyar,don Allah Aunty ki yi wani abu akai, wallahi ina tsananin kishin miji na,ba zan iya haɗa shi da wata mace ba,don Allah Aunty na!"
#Nusy_bee
Page 11
Hajiya Ruƙayya da ta kusa ƙwarewa da bayanin Arfa ta yi saurin kora ruwa tana zare idanu,a ɗan firgice ta ce"ban...ban fahimta ba Arfa,ki yi min bayani yadda zan fahimta,me kike nufi da abin da kike faɗa?"
Cikin kuka sosai Arfa ta ce"na gaya miki Aunty kama shi na yi yana kallon hotunanta,dama tunda muka yi auren ba wani ba ni hankalinsa yake yi ba, gaskiya Aunty da sake,ya kamata a san yadda za'a yi,don ba zan iya zama yana wulaƙanta ni akan wata kilaki ba"
Hajiya Ruƙayya ta numfasa ta ce"ki kwantar da hankalinki Arfa,da kin gaya min tun farko da tuni na yi wa tufkar hanci, yanzu ma dai bata ɓaci ba,sai na yi masa abin da ba zai sake sha'awar ko da kallon wata mace ba sai ke,ko da uwarsa ce kuwa,don ba zan ɗauki wargi irin haka ba"
Arfa ta ja numfashi tana faɗin "to na gode aunty,sai na ji ki"suka yi sallama, Arfa ta miƙe tana goge hawayenta
*TIJUANA, MEXICO*
*CLUB SAFARI*
A hankali take kwantar da kanta a bayan kujerar da take zaune tana sauke numfashi a hankali bayan ta gama zuƙar hayaƙinta na shisha, David da yake tsaye a bayanta ya sunkuyar da kanshi daidai saitin nata,murya ƙasa-ƙasa yana faɗin"Ma!
Are you okay?"
Shiru ta yi ba tare da ta yi magana ba,ba wannan ne karo na farko da David ya ganta a wannan hali, wanda har zuwa yanzu babu wanda ya san abin da yake jefa ta cikinsa
Kafin ya sake yin wani yunƙuri ta buɗe idanunta da suka sauya kala tana miƙa masa hannu,ya san me take nufi,a take ya zaro ƙwayoyin da take sha idan tana cikin wannan halin ya miƙa mata, ba tare da tunanin komai ba ta afa su gaba ɗaya,ta mayar da kanta ta kwanta tana sake lumshe idanunta
"Is everything alright ma?"ya tambaya a hankali
BuÉ—e idanunta ta yi, waÉ—anda suka sake birkicewa tana lumshe su,da muryar maye ta ce"I want..... let's go home.....ppplease!"
Ba tare da ɓata lokaci ba ya taimaka mata ta miƙe tsaye sannan suka fice daga club ɗin,bakinsa fal tambayoyi,ya san zuwa suka yi don su gudanar da irin kasuwancin su,amma ta shiga wannan halin, wanda ta saba shiga a duk lokacin da wani ƙunci ya mamaye zuciyarta, wanda har zuwa yanzu ba su san menene silar ƙuncin ba,don ko da wasa bata taɓa faɗawa wani ba
Washe gari Roxy tana tsaye a bakin window ɗin ɗakinta tana kallon shuke-shuken da suke bayan ɗakin nata, sai dai kuma hankalinta ba ya tare da ita,asalima ya luluƙa can tunanin baya
💫
"Yaya! wallahi ina sonshi!don Allah ka yi haƙuri ka ƙyale ni,idan ban aure shi ba zan iya mutuwa
Yaya saboda ni ya musulunta fa!yaya kar ka yi silar da za mu yaudare shi,bana son ya kalli musulmai a matsayin mayaudara,don Allah yaya ka yi mana addu'a, please yaya na!ta ƙarashe maganar tana haɗe hannayenta alamun roƙo
"A'a baby girl! don Allah kar ki yi min haka!
Na fara sonki tun ba ki san kanki ba,tun kina yar jaririya, wallahi sonki zai kashe ni,zai yi min illa,don Allah!don Allah baby girl!kar ki juya min baya ki auri wani, Please!!!"
"Please yaya!zuciya ta tana wajen shi,idan na aure ka ba zan so ka ba,ba zan yi maka biyayya ba,Ni tashi ce, zuciya ta tana gare shi, Please! please yaya!!"
"Baby girl!
Are you telling me kina son wani?da shi kadai za ki rayu?all in before my eyes?what the heck!!!
Baby girl wake up!nine fa yayanki,abin alfaharinki,abin sonki,amininki tun kina ƙarama,kin manta da haka?"
"I'm sorry yaya!stay in your lane,but I will never marry you, I'm not in love with you!"
💫
"Roxy are you okay?"da sauri ta juyo tana kallon Hanna da ta zuba mata idanu tana yi mata kallon tuhuma