← Book details Gadar Tsautsayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 51

Sashe 2

Gadar Tsautsayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana tafiya ta zura hannunta a wata kusurwa ta kujerar da take zaune,a take ta fito da wata ƴar ƙaramar takarda kalar yellow,kuma ba tare da ɓata lokaci ba ta buɗe takardar tana kallon rubutun

'OLD VENUE,BY 3:AM'

Haka kaÉ—ai aka rubuta a jikin takardar ta ninke tare da cusa ta a aljihu ta É—aga kai tana kallon waitress É—in da take dawowa É—auke da tray na abin da ta saba yin order duk sanda ta shigo restaurant É—in

Shawarma ce sai mint tea,ita mint tea ɗin ta sha sannan ta miƙe bayan ta biya Bill ta fice daga restaurant ɗin ba tare da ta sake kallon wani ba,da yawan ma'aikatan suka bi ta da kallo suna ƙusƙus na halin wannan matar mai jiji da kai, tunda suke da ita sai dai ta shigo ta yi order,a Kawo Mata ta ci ta tafi, bata yiwa kowa magana,bata amsa gaisuwar kowa, babu wanda zai iya shaida muryarta,hakan ya sa wasu suke tunani wataƙila kurma ce bata magana

Ita kuwa tana fita ta faɗa motarta,sai da ta rufe baƙaƙen tinted glasses ɗin sannan ta ɗauko wayarta ƙirar lastest iphone ta daddanna sannan ta kara a kunnenta tana zare scarp ɗin kanta

"Hello!"muryar mace ta amsa bayan an É—aga wayar

Hannu ta saka tana gyara zaman dogon gashin ta, cikin muryarta mai cike da izza da jan aji ta furta "old venue,by normal time"daga haka ta kashe wayarta ba tare da ta jira amsar ɗayan ɓangaren ba

Daga nan ta tayar da motar, ba tare da ɓata lokaci ba ta bar bakin wajen, kamar walƙiya ta fice daga layin

Bata yi tafiya mai nisa ba ta tsayar da motar a kusa da wani ƙaton gate, cikin wani irin yanayi akan fuskarta take kallon gate ɗin gidan, abubuwa da yawa suna dawo mata kai,ta girgiza kai tana ɗan murmushi wanda ya yi kama da mai ciwo sannan ta tayar da motarta ta yi gaba,a ranta tana jin duk abin da ta yi bata yi kuskure ba,akan daidai take,don haka bata nadama

*ALHAJI YUSUF MALIYA RESIDENCE, MALIYA ESTATE,KANO STATE*

Ƙaton parlour ne wanda ya wadatu da kayan ƙawa da ado na zamani, parlourn ya yi shiru tamkar babu wata halitta mai rai a cikin parlourn

Sai dai kuma É—auke yake da ilahirin jama'ar da ke cikin katafaren mansion É—in, wanda ya kasance mallakin Alhaji Yusuf maliya,wato mai gidan

Alhaji Yusuf maliya shahararren dan kasuwa ne,mamallakin MALIYA GROUPS OF COMPANIES da MALIYA MOTORS,duk wanda yake cikin Maliya family, waɗanda aka haɗa su a cikin Maliya estate to mai arziƙi ne,daga lokacin da aka haifi jariri za'a ware masa wani kaso a matsayin hannun jarinsa,yana kai wa wasu shekaru a damƙa masa

Iyali ne masu cike da haɗin kai da ƙaunar juna,duk da cewa ko da akwai ɓarakar ba'a bari ta bayyana, saboda tsananin zafi da tsatstsauran hukunci da zai fuskanta daga wajen shugaban wannan family

Alhaji Yusuf maliya shine babba a wannan family,yana da ƙanne biyar,uku maza,biyu mata, Hajiya Sa'adatu ita ce wadda take bin sa, wadda a wannan ƙaton family aka santa da Mummy,babbar ƴar kasuwa ce, sannan yar kasuwa,mammallakiyar Maliya plaza da Maliya shopping complex,tana importing da exporting na kaya sosai

Mai bi mata shine Alhaji Rufa'i, wanda yaran family suke kira da abbeey,yana da Company na shigowar spare parts na motoci, sannan yana da manyan shaguna a kasuwanni a ciki da wajen Kano,sannan shi É—in babban jami'in custom ne,sai na uku Alhaji Aliyu,shima kamar sauran ya kasance ma'aikaci ne,yana aiki da NNPC,sannan yana da babban Company na sarrafa abinci,sai na hudu, lieutenant colonel Habib, soldier ne,kuma É—an kasuwa

Sai autarsu Salma, wadda yara suke kira Aunty, yar jarida ce, sannan yar kasuwa ce kamar dai sauran yayyenta

Gaba É—aya su biyar É—in, Sa'adatu, Rufa'i, Aliyu, Habib da Salma sun kasance suna tsananin biyayya ga dokar Æ´aÆ´ansu Alhaji Yusuf,ko kara ya saka ya ce baya so kowa ya tsallaka to babu mai iya ko da matsowa inda karan yake,duk da cewa wannan tsatstsauran ra'ayin ya janyo wa ahalin wata gagarumar matsala wadda ta jefa su a cikin wani hali na wasu shekaru,kuma har kwanan yau an kasa samun mafita ga wannan matsalar

#Nusy_bee

Page 2

Matan Alhaji Yusuf maliya uku, Hajiya Zainab ita ce uwar gida,wadda yara suke kira da Ummeey, haihuwarta É—aya a gidan,ita ce babbar yar Alhaji Yusuf maliya, wato FATIMA SHAHEEDA,sai Hajiya Atika, Æ´aÆ´anta biyar,Safwan shine babba,sai Malika,sai Amina,mukhtar sai auta Fauziyya

Hajiya Ruƙayya ita ce matar Alhaji Yusuf Maliya ta ƙarshe, tana da yara uku, Zainab,mai sunan Ummeey, wadda ake kira da Iman,sai Nafisa, sai autanta Usman

Hajiya Sa'adatu, wadda ake kira da Mummy yaranta huɗu a duniya,Muyassar ne babba,ya kammala karatunsa na masters a ƙasar Britain,inda ya karanci civil engineering a jami'ar Harvard,ya fita da kyakkyawan sakamako,sai ƙannensa Hassan da Hussaini, wadanda suke jami'ar cologne suna karantar fannoni dabam dabam na lafiya,sai autarsu Na'ima, wadda take nata karatun a NUN da ke Abuja

Alhaji Rufa'i yaransa bakwai,uwar gidansa na da uku amaryarshi tana da huÉ—u,sai Alhaji Aliyu,shi kuma yaranshi tara, duka daga matarshi É—aya da suke zaune tare,sai auta Salma,mai yara biyu tal a duniya yan maza sakwanni, wadanda zuwa wannan lokaci dukkansu suna matakin farko a jami'ar Massachusetts da ke US

A bisa al'adar MALIYA family,a duk lokacin da za'a ƙaddamar da wani abu mai muhimmanci,ko wanda zai shafi al'ummar ahalin,ana haɗuwa a katafaren gidan Alhaji Yusuf Maliya, kasancewar shine shugaban ahalin,a matsayinsa na babba,kuma wanda yake gina ahalin a duk lokacin da aka samu wata ɓaraka, musamman da ya kasance mahaifiyarsu gaba ɗaya, Hajiya Zulayhat Maliya, wadda kafatanin ilahirin ahalin suke kiranta da hajiyya innayyo,ta kasance a gidansa,a sashe na dabam da aka ware mata

Kamar yadda aka saba yau ma sun taru a katafaren parlourn gidan,gaba É—aya iyaye da yaran,da alamu wani gagarumin abu mai muhimmanci za'a tattauna a kai

Parlourn ya É—auki shiru, Alhaji Yusuf Maliya ya ja numfashi a hankali, sannan ya cigaba da magana

"Sanin kowa ne a gidan nan,kun san abin da ya faru shekaru huɗu da suka wuce,wani tabo ya samu ahalin nan,girma da mutuncinmu ya zuba a idanun duniya,maƙiya sun yi farin ciki, masoya sun yi baƙin ciki

A wancan karon na É—auki hakan a matsayin tsautsayi,amma wannan karon ina ganin duk abin da ya faru dole ne mu bar shi a matsayin ganganci,duba da cewa ba shine karo na farko ba,amma menene shawararku akan hakan?"

Hajiya Sa'adatu, wadda ta kasance babba a cikin ƙannen Alhaji Yusuf Maliya ta gyara zama tana jan numfashi, sannan ta ce"Alhaji Ni ina ganin ba wata matsala ba ce hakan, musamman duba da nutsuwa da tarbiyyar yaran,abu ne mai wahala su manta da hakan idan suka samu kansu a baƙon waje

Kuma bugu da ƙari ya dace a ce an saka musu idanu, saboda su mata ne,kuma ita mace sai da sanya idanu,amma ni dai daga gare ni ina yi musu kyakkyawan zato,amma me kika ce Ruƙayya?"ta mayar da tambayar ga matar Alhaji Yusuf Maliya da suka fi shiri,wato Hajiya Ruƙayya, wadda yara suke yiwa lakabi da Mommy

Mommy gyara zama ta yi, sannan ta ce"to ni dai ba zan ce komai ba,amma kuma ga yaran nan za'a samu kyakkyawar amsa daga gare su "

Alhaji Yusuf ya dubi yaran,da alamu sun zaƙu a tambaye su ɗin,amma maimakon ya tambaye su sai ya mayar da akalar tambayar ga Hajiya Zainab (Ummeey)

A tausashe Ummeey ta dubi Alhaji Yusuf bayan ta gyara zama ta ce

"Alhaji a dai duba sosai,ka ga yara mata ne,kuma inda za su tafi babu wani babba a can

Idan da hali a nema musu makarantar a nan,babu laifi su koma gabanka a Abuja,ko su zauna a anan a gaban iyayensu,a ko'ina aka yi karatun ba wani abu ake nema ba sai albarkarshi

Idan muka yi duba a baya an yi irin haka,an samu sakamako mara daɗi,to mu bar wancan a matsayin ƙaddara,a wannan karon sai mu kiyaye,idan muka yi hakan sai Allah ya taimake mu"

Da sauri yaran suka kalle ta cikin wani irin baƙin ciki,don gani suke yi Ummeey hassada take yi musu tana son ta shiga tsakaninsu da burinsu,amma babu halin magana, musamman da ya kasance suna gaban Alhaji Yusuf Maliya, wanda ko manyan ba sa yin magana sai an nemi jin ta bakinsu

Sai dai kafin wani yunƙuri cikin ɓacin rai Hajiya Atika ta dubi Ummeey ta ce

"A'a Hajiya Zainab,wannan ba girmanki bane!wanne dalilin zai saka ki yiwa yara baki bayan ba sune suka yi miki laifi ba?

Ya kamata a rinƙa yi ana saran bakin gatari,don wannan abu bai dace ba gaskiya "

Tana rufe baki Hajiya Sa'adatu ta É—ora"kuma ban da haka ma Allah na tuba ai yaran sun samu tarbiyya sosai,ina su ina wannan abu saboda Allah?

Kawai dai kin san wasu mutanen, musamman waÉ—anda ba sune suka haifi yaro ba"

Ummeey ta girgiza kai ta ce"kayya!

Allah ya kiyashe mu da aikin danasani da ruÉ—in shaiÉ—an

Kun yiwa magana ta gurguwar fahimta, babu komai, Allah ya tsare su,ya kawo abin da aka je nema

Hajiya Sa'adatu É—a ai na kowa ne,da É—a da dukiya ba'a yi musu mugunta, saboda Allah ne kaÉ—ai ya san wanda zai more su"

Ganin abin zai zama na magana ya sa Alhaji Yusuf cikin É—aurewar fuska ya ce"ya isa haka!

Bana son na sake jin maganar nan ta cewa babu tarbiyya a gidan nan,hakan yana nuna na gaza ne, Ni kuma na san iya ƙoƙarin da na yi,a cikin matana babu mara tarbiyya,don haka haifar mara tarbiyya ba dai a gidana ba,sai dai idan abin ya zo da tsautsayi

Sannan ke kuma Hajiya Zainab,maganarki ta cewa a kula babu kowa da yake kallonsu ni na san me nake yi,ku dai ku yi musu addu'a kawai, Allah ya bada sa'a,ya kare su daga ruÉ—in zamani,ya sa a samo abin da aka je nema"kusan gaba É—aya aka amsa da Ameen

Iman da Amina,sai Æ´ar Alhaji Rufa'i Surayya,sune wadanda ake ta wannan tattaunawar akan tafiyarsu abroad karatu,amma iyalan sun kasance cikin shakku saboda tabon da suka samu a cikinsu wanda ba su san ranar da zai warke ba
Chapter 2 · 0% Book details