Sashe 47
Gadar Tsautsayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da kika san da haka,na cewa ƴaƴanki suna jin maganarki ai da ɗan naki ya yi nisa shi za ki tunkara ki ce ya dawo,ba ni za ki zo kina zaƙalƙalewa ba,ƙaddarar Shaheeda kuwa idan Allah ya so zai iya mayar da ita ba komai ba,ni fatana koda yaushe Allah ya shiga rayuwarta ya zama gatanta "
Wani kallo Alhaji Yusuf ya yi mata, cikin ɓacin rai ya ce "wato kina nufin da na ce a manta da ita a gidan nan ba ki manta ba kenan ko me?"miƙewa ta yi tana kallonsa cikin idanu ta ce
"Ko zan manta komai,ai ba zan manta cewa Shaheeda ce ta mayar da ni uwa,nake tuna cewa na haihu ba tare da na ji zafin wani gori ba,a lokacin da kowacce uwa take ƙyamatar na nuna ɗanta na ce nawa ne a lokacin ne nake alfahari saboda na tuna cewa ina da Shaheeda,kuma ban taɓa nadamar haifarta ba,don haka ka ma cire a ranka cewa akwai ranar da zata zo har ta wuce ban yiwa Shaheeda addu'a ba,ko kuma ban ji ta a raina ba"
Arfa da Hajiya Ruƙayya da mamaki suke kallon Hajiya Zainab wadda iya tsawon zamanta a gidan ba'a taɓa jin ta mayarwa da wani amsa ba saboda tsananin haƙurinta,amma sai gashi yau ga tana mayar da magana
Hajiya Sa'adatu ta kama haɓa da mamaki tana kallonta ta ce"ke yanzu idan banda rashin kunya da rashin ɗa'a irin na wasu mutanen yanzu har Shaheeda ta kai a yi tutiya da ita?
Wallahi ni dai a nawa ganin da haihuwar irin su Shaheeda gwara zama babu haihuwar ma gaba É—aya,me ake da É—a irin Shaheeda,haka kawai a haifarwa duniya Annoba?"
Hajiya Zainab ta yi murmushi ta ce"idan kin tashi haihuwa ki haifo limamin harami bisa wayonki da dabararki,Ni wannan ba matsalata ba ce
Allah shine ya san hikimar ba ni Shaheeda ba tare da yan'uwa ba, sannan ya jarrabe ni da halayenta,amma a hakan na godewa Allah,kuma har yanzu ban cire rai zata zamar min abar alfahari ba watarana,ban cire rai zai sake haÉ—a mu ba"daga haka ta juya da sauri ta fice daga parlourn tana mayar da zazzafan hawayen da ya fara cika mata idanu,da wanne zata ji ita kuwa?
Da halayen Shaheeda?ko da baƙin cikin korar da mahaifinta ya yi mata wanda shine tushen komai,ko da abubuwan da aka ce ta aikata?ko da kamun da aka yi mata?ko da wadannan surutan da ake yi mata,da baƙaƙen maganganun da ake gaya mata dare da rana
Daga sashen Alhaji kai tsaye parking space ta nufa ta shiga motarta ta tayar ta fice daga gidan,tana tafiya a mota tana share ƙwalla, aranta tana ambaton dukkan sunan Allah da ya zo mata rai
Kai tsaye gidan Hajiya Saudat ta nufa,a bakin gate ta tsaya ta kashe wayar ta sannan ta shiga cikin gidan,a ranta tana ganin gwara ta ba wa kowa hutu kawai, ita ma ta samu nata hutun
*ROCKY ESTATE*
Sai da ya yi sallar isha'i sannan ya shiga sashen Nanny ɗin su Amna,yana shiga da sallama Amna ta taso da gudu ta ɗane shi tana murna,ya rungume ta yana murmushi,ya mayar da kallonsa ga Mubarak wanda yake raɓe a gefe guda
Sauke Amna ya yi, Nanny tana faɗin "Barka da zuwa ranka ya daɗe"ya yi murmushi ya ce"Barka dai Nanny,ya na ga yallaɓai a zaune ya takure?"
Nanny ta yi murmushi tana kallonsa ta ce"wai nan fushi yake yi saboda na ba shi magani,ka san baya son magani ko da wasa"Haisam ya yi ƴar dariya ya ƙarasa inda Mubarak yake zaune yana kallonsu, fuskarshi duk hawayen da bai gama gogewa ba,ya sa hannu ya ɗago shi yana faɗin "abokina ya dai?
Wa ya taɓa min abokina ne?me yake faruwa? Nanny ce ta ba ka magani?ba ka so ko?"ya gyaɗa kai fuskar nan a ɗaure, Haisam ya ce"ai tafiya ma zamu yi mu bar mata sashenta ko?"ya sake gyaɗa kai yana shagwaɓe fuska, Haisam ya yi murmushi ya ce"Weldon my friend,zo mu tafi ko?"Nanny tana murmushi ta ce"tafiya za kayi ka bar ni?"ya juyo ya kalle ta ya ɗauke kai, Amna ta ce"Daddy nima zan bi ku"
Daddy ya ce"ba yanzu ba tukunna, sai da safe sai ki zo, yanzu ki zauna a wajen Nanny "ya ja hannun Mubarak suka bar sashen
Ya É—an É—auki lokaci yana yi masa wasa,har shima Mubarak ya fara sakin jiki yana ba shi amsa,shi dai kallonsa kawai yake yi,ganin exactly fuskar Shaheeda, babu inda ya bar ta,sai hasken fata da ya fi ta
Wajen ƙarfe tara Haisam ya samu Mubarak ya yi bacci,ya kwantar da shi sannan ya miƙe ya nufi sashen iyayenshi,don Abba ya yi masa magana yana son su gana
A parlour ya same su a zaune,ya yi mamakin ganin Nimra da ya fara gajiya da É—an banzan nacinta,amma ko a fuska bai nuna ba, bayan ya gaida su abbansa ya nuna masa kujera yana faÉ—in"zauna Haisam "
Babu musu ya zauna, Abba ya ce"har yanzu baka cewa kowa komai ba game da yaron da ka kawo gidan nan,gashi mu kuma ba mu san shi ba"
Haisam kai tsaye ya ce"Abba ba ku sanshi ba,amma yanzu ya zama É—aya daga cikinmu, É—an criminal É—in da na kama ne, kasancewar ba shi da kowa sai na kawo shi ya zauna a cikinmu"
A kusan tare Nimra da Hajiya Mariya suka razana, Abba ya ce"menene hikimar hakan Haisam?na san dai baka yin abu sai da dalili"
Haisam ya gyara zama ya ce"haka ne Abba!
Akwai ƙwaƙwƙwaran dalili kuwa, saboda shi yaron ba shi da kowa,asalima"ya ba su labarin Shaheeda a taƙaice yadda za su fahimta
Abba ya tausaya mata sosai,su kuwa Hajiya Mariya da Nimra kallonsa kawai suke yi sun kasa magana, Abba ya ce"Allah sarki!
Dama a rayuwa ba kowa bane za ka ganshi da wani hali ya zama laifinsa ne,wasu trauma ce,wasu kuma dole ne,to ina yi mata fatan Allah ya fito da ita lafiya ta riƙe ɗanta,don bai kamata abu irin wannan ya shafi rayuwarsa ba
Allah ya kawo mafita,shi kuma yaron Allah ya raya shi ya yi masa albarka "
Haisam dama ya sani zai samu goyon bayan Abba, dattijo mai nutsuwa da hangen nesa,mai tsananin tausayi da mayar da duniyar ba komai ba, kafin Haisam ya sake magana Alhaji Abdulmalik ya cigaba da Magana
"Akwai kuskure sosai a tozarta rayuwar ƴa mace a lokacin da ta aikata kuskure,da ba'a tozarta ta ba an sallama ta da yanzu wataƙila ta zama wata mai amfani,amma hakan da aka yi mata gashi nan baiwarta ta zama barazana ga al'umma
Muna buƙatar yara irinsu a society ɗin mu,bai kamata mu yi musu haka ba"
Haisam ya yi murmushi yana gyara zama, kafin ya yi magana Hajiya Mariya ta kasa haƙuri ta ce"Haisam ni kuwa sai na ga kamar baka yi dabara ba
Me zai hana ka kai shi gidan marayu?amma menene amfanin kawo shi nan?mu da ba mu da alaƙa da uwar tashi?"
#Nusy_bee
Page 38
Kallonta Haisam ya yi fuska babu walwala, kafin ya yi magana Abba ya ce fuska a É—aure "shine ya so hakan,ya kawo shi da radin kanshi don ya inganta masa rayuwa,idan zai yiwu ki bi shi da addu'a kawai,idan ba zai yiwu ba kuma ki yi shiru,amma ko da a ce kina so ko ba kya so yaron nan yanzu zai fara zama a gidan nan da izinin Allah"
Shiru Hajiya Mariya ta yi ba tare da ta yi magana ba,ita kuwa Nimra ji ta yi kamar ta kurma ihu
Haisam ya dubi Abba ya ce"na gode Abba, Allah ya saka da alkhairi
In Sha Allah zuwa next term idan an fara enrolling yara a makaranta zan saka shi a makarantar su Amna"
Abba ya jinjina kai ya ce"hakan yana da kyau, Allah ya taya riƙo, riƙon maraya akwai lada da alfanu mai tarin yawa ,fatan shi ne Allah ya raya shi ya albarkaci rayuwarsa "Haisam ya amsa da"Ameen "
Daga nan hira suka fara,suna tattaunawa akan abubuwan da suka shafi kasuwancinsu shi da abban, Nimra ganin ba'a yi batunta ba ya sa ta fara zungurin Hajiya Mariya, fuska a É—aure Hajiya Mariya ta dubi Alhaji Abdulmalik ta ce
"Ni ko Alhaji ba mu ƙarasa Maganar da muka fara kwanaki ba"
Alhaji ya dube ta ya ce"wacce maganar ce?"
Hajiya Mariya ta ce"maganar ya kamata a haÉ—a Haisam da Nimra aure mana,tunda dai yanzu ga ka ga ni,gashi kuma ga Nimra É—in kawai gwara a yi a gama ko?amma kai ya kake gani?"
Alhaji Abdulmalik ya kalli Nimra ya ce"da izininta kika yi wannan maganar?"Hajiya Mariya ta ce"da izininta ne,ka sake tambayarta ka ji"Alhaji Abdulmalik ya jinjina kai ya ce"to kai Haisam ya kamata ka ware lokaci ka san abin yi, tsawon lokacin da ka ɗauka baka yi aure ba ya kamata ko me aka yi maka zuwa yanzu a ce ka huce, riƙo a wajen ɗan musulmi ba shi da amfani sam, ballantana ma wadda ta yi maka laifin dabam da wadanda kake hukuntawa,ya isa hakanan Haisam "jinjina kai ya yi,a sanyaye ya ce"to shikenan Abba,komai ya wuce, Allah ya shige mana gaba ya yi mana jagora "
Alhaji Abdulmalik ya ce"Ameen Ameen!
Yanzu ga Nimra, menene ra'ayinka akanta?
Ka ga dai ita ka santa,kuma ina da yaƙinin ba zata ba ka matsala ba in sha Allah,kuma zata riƙe maka yaran da kyau,amma kai me ka gani?"
Haisam ya ɓoye mamakin rashin kunyar nan,ya ce"Allah ya zaɓa abin da ya fi alkhairi,amma ya kamata ta ƙarasa karatunta, idan ya so sai a yi maganar auren"
Cikin zumuÉ—i Nimra ta ce"za'a iya yi min transfer ma na dawo Kano,ba dole sai a Abujan zan yi karatun ba"
Haisam ya watsa mata wani mugun kallo,tuni ta nutsu, fuska a É—aure ya ce"za'a yi auren bayan ta kammala makaranta in sha Allah, Allah ya bada sa'a "
Abba bai damu ba ya ce"Ameen Ameen, Allah ya sa albarka "Haisam ya miƙe ya ce"sai da safenku"ya fice daga sashen zuwa nashi