Sashe 26
Gadar Tsautsayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sosa kyakykyawar sumarsa ya yi ya ce"aure wai Mummy na ta ce zata yi min,ni kuma I'm not ready gaskiya, shiyasa zan koma, beside ina da wadda nake so,ita kuma zata ba ni wata"
Murmushi Shaheeda ta yi ta ce"alright!
All the best! Allah ya taimaka,ni zan shiga ciki to"suka yi sallama,ta nufi hostel shi kuma ya nufi komawa hotel É—in da ya sauka
#Nusy_bee
Page 21
Washe gari Muyassar ya dawo,sun daÉ—e suna hira kafin ya yi mata sallama, Shaheeda tana murmushi ta ce"to yaya!
Yanzu sai yaushe?"
Muyassar ya ce"to kin ga dai yanzu karatu zan koma in sha Allah,ba zan ce kai tsaye ga lokacin da zan zo ba,amma kuma in sha Allah zan yi ƙoƙarin sake zuwa very soon,ke dai ki dage da karatu kawai, in sha Allah wannan little engineer ɗin sai ta zama hasken da zai haska Maliya family"
Murmushi sosai ta yi,ta ce"yayana abin alfaharina, Allah ya tabbatar da bakinka,ina matuƙar son na ga na amsa sunan nan"tana murmushi tana juya kai ta ce"zan buɗe Company na kaina,zan zama shahararriyar yar sarrafen computer,zan ƙirƙiri apps da yawa waɗanda za su taimaka a harkar internet,kuma....."
"To sarkin soki burutsu, Allah ya taimaka ya ba da sa'a kawai, I can't wait na ga wannan ranar "ya ƙarasa yana murmushi
Ba su daÉ—e ba sosai suka yi sallama,ta koma hostel shi kuma ya tafi
Kwana biyu zuciyarta ta kasa sukuni saboda wannan matashin Guy É—in da ta gani, wanda tun ranar da Muyassar ya zo bata sake ganinsa ba
Ta rasa yadda aka yi zuciyarta ta damu da tunaninsa,abin yana matuƙar damunta, har abin yake so ya shafi karatunta
Kusan watanni uku kenan, karatunsu ya miƙa sosai,kuma suna daf da fara jarrabawar second semester, wadda daga ita ne zata tafi hutun session,zata koma Nigeria,gaba ɗaya yanzu bata da nutsuwa, kullum cikin karatu take da nazari,ita ce searching, practical, group discussion da sauransu
Tana zaune a inda suke zama don karatu, hankalinta ya raja'a sosai,sai ga wasu samari sun zo sun zauna a kusa da ita suna kallonta cikin sigar rashin mutunci
Sau ɗaya ta kalle su,ta cigaba da abin da take yi, ɗaya daga cikinsu ya ja mayafinta, ɗayan kuma ya ja handout ɗin hannunta ya yar a ƙasa, ganin abin nasu ba na ƙare bane sai ta miƙe,amma sai suka hana ta wucewa
Kuka ta fashe da shi,suka kama dariyar izgilanci suna ta dungure mata kai,ta durƙusa a wajen tana kuka
Ji ta yi sun yi shiru,tana ɗagowa ta ganshi yana miƙa mata hannu, ba tare da ya jira komai ba ya kama hannunta ya ɗaga ta suka bar wajen,bata yi masa musu ba ta bi shi tana kallonsa
Wani waje dabam ya kai ta ya zaunar da ita,ya dube ta fuskarsa babu walwala, cikin yaren Dutch ya ce"ki rinƙa kiyayewa,ba su da kirki,za su iya yi miki wani abu da bai dace ba,ke mace ce,kar ki sake zuwa can"
Jinjina kai ta yi a hankali, cikin sanyin murya ta ce"na É—an kauracewa mutane ne saboda na samu damar karatu sosai"
Shafa kanshi ya yi yana lumshe kyawawan idanunshi,ya ce"ya kamata ki kiyaye,ba a ko'ina za ki iya zama ba,sai anjuma"ya juya zai tafi,ta yi masa murmushi tana faÉ—in "na gode"ya É—aga mata hannu ba tare da ya yi magana ba ya bar wajen
Duk da yadda tunanin Guy ɗin da ko sunansa bata sani ba ya so ya hana ta sukuni amma ta dage da ƙarfin hali ta cigaba da karatunta,har ƴar rama ta yi,su Alice da Olivia har sun gaji da tambayarta me yake damunta
Bayan sun kammala jarrabawa aka yi bikin fitar yan final year,an zaɓi wadanda za su yi speech a cikin ragowar ajujuwan,level one,two da three,a cikin waɗanda aka zaɓa a level one har da ita
Speech ta yi mai kyau akan abin da ya shafi course É—insu na software engineering, kusan kowa da yake wajen sai da ya burge shi, gashi da turanci aka yi, English accent É—inta ya burge kowa,ta sha tafi da hotuna kala kala
Abin da ya bata mamaki a waɗanda suka yi speech na ƴan level three har da wannan matashin,wanda ta ji cikakken sunansa ARNOLD LIAM LAMBERT, wanda hakan ya ƙara tabbatar mata da cewa ɗan ƙasar Belgium ne,ko kuma mazaunin ƙasar Belgium,a takaice dai haifaffen ƙasar ne
Shima ya yi speech mai kyau, yadda yake magana cike da jan aji da rashin son hayaniya ya yi matuƙar burge ta,don haka itama sai ta tsinci kanta a cikin masu tafa masa
An yi biki mai kyau,an ci an sha,an tashi taro kowa yana cike da farin ciki
Tana zaune a inda take zama sau tari, musamman idan tana karatu,yau ta buÉ—e wayarta tana chatting da yayanta Muyassar da Ummeenta,tana sanar musu da zata koma gida gobe,ta ji an ce "Hi!"
ÆŠagowa ta yi da sauri ta kalle shi,ya yi mata murmushinsa mai kyau,yana faÉ—in "good afternoon HERMOSA!"
"HERMOSA?"ta maimaita tana kallonsa,ya sake yin murmushi ya ce"HERMOSA means beautiful in Spanish,can I have a seat?"bata yi musu ba ta nuna masa waje don ya zauna,ya zauna yana kallonta
Cikin harshen dutch ta gaida shi,ya amsa yana murmushi,shima ya gaishe ta,ta yi murmushi tana kallonsa,ya ce"Good speech!"
Da harshen dutch ta ce"kai ma ai ka yi magana mai kyau da ma'ana, tunda da alamu wata shekarar ku ne wadanda za'a shiryawa wannan bikin"
Murmushi ya yi ya ce "na ji an ce ke ce mai overall a set É—inku,ina taya ki murna"
Kallonsa ta yi sosai ta ce"ya aka yi ka sani?"
Ya ce"a set ɗinmu ni nake yin overall duk shekara,na kan bibiyi masu yin overall duk shekara, wannan karon kuma sai ta faɗo akanki,na yi mamaki kasancewar ki yar Africa,hakan ya faranta min sosai,daga wace ƙasa kika zo?"
Kallonsa ta yi ta ce "kai É—an africa ne?'
Ya jinjina kai ya ce"mahaifina ɗan ƙasar South Africa ne, mahaifiyata ce ƴar Belgium,sai dai saboda domestic violence da ya faru da iyayen nawa tun ban san kaina ba mahaifiyata bata taɓa kai ni South Africa ba,a takaice ma,ban taɓa zuwa Africa ba"
Shaheeda ta jinjina kai ta ce"Ni kuma haifaffiyar Nigeria ce,yar asalin ƙasar Nigeria "
Ya jinjina kai yana murmushi ya ce"ya yi kyau
Kenan ke ma za ki tafi ganin gida ne?"
Shaheeda ta ce"gobe ma nake so na bar ƙasar nan zuwa Nigeria, na gama shirya komai"
Ya jinjina kai ya ce"fatan alkhairi,zan iya samun numbernki?"tana murmushi ta saka masa,ji take yi kamar ta yi tsallen murna,kuma ta kasa gane dalilin hakan
Washe gari jirgin su Shaheeda ya É—aga zuwa Nigeria,farin ciki da É—oki tamkar ta rufe idanu ta buÉ—e ta ganta a Nigeria,duk da bata so tafiya gaba É—aya ba saboda sabon abokinta Arnold
Tafiyar awanni bakwai ya kawo Shaheeda Nigeria daga Belgium, farin ciki kamar me don zata ga yan'uwanta,bata damu da yadda babu wanda ya zo daukarta ba,don Abba ba ya Nigeria,yana can harkokinsa na kasuwanci, Ummeey kuwa ba zuwa za ta yi ba ta sani, Muyassar ba ya ƙasar,a gidansu kuwa kaf babu wanda zai zo,don haka ko a jikinta ta hau taxi drop ta tafi gida
Da ihun murna ta shiga gidan na su, Ummeey dai ta kasa ɓoye farin cikinta,ta tafi da gudu ta faɗa jikin Ummeey tana murna, Hajiya Jamila da ta zamewa Ummeey ƴar'uwa tana kallonsu tana murmushi,ta ce"ba'a ganmu bane ɗaliban turai?"
Murmushi Shaheeda ta yi,ya durƙusa tana gaida su gaba ɗaya, Hajiya Jamila tana murmushi ta ce"ya karatun?
Kin yi kyau abinki,kin murje kin yi jiki kamar ba ke ba, Belgium ta karɓe ki alhamdulillah"
Cike da jin daÉ—i Shaheeda tana murmushi ta ce "alhamdulillah, Mummy ai karatun nasu da daÉ—i ba kamar a Nigeria ba"
Hajiya Jamila ta ce "kar dai ki bari Salma ta ji ki,kullum a cikin complain take yi karatu yana ba ta wahala"
Dariya Shaheeda ta yi ta ce"oh su Hajiya Salma manya, Ummeey bari na shiga ciki na yi wanka"daga nan ta miƙe ta shiga don yin wanka
Bayan ta kammala hutawa Ummeey ta umarce ta ta je ta gaida matan gidan, babu damuwar komai a ranta ta sanya dogon hijabinta ta fice daga sashen
Sashen Hajiya Atika ta fara zuwa,a matsayinta na babba a matan gidan,da sallama ta shiga,ta yi sallama ya kai uku amma babu amsa,duk da tana kallon Hajiya Atika a zaune tare da yaranta Safwan da Malika
Kutsa kai ta yi ba tare da damuwa ba,tana zuwa ta samu kujera ta kame ta zauna tana murmushi, kafin ta ce "sannu Ammi,ina kwana?'
"Wanene ya ba ki izinin zamar min a kan kujera?
Malama tashi min akan kujera"
Murmushi Shaheeda ta yi tana taɓe baki ta ce"Ni zuwa na yi mu gaisa,an daɗe ba'a haɗu ba
To ya muka same ku?ya yaran?ya gida?"
A kufule Hajiya Atika ta ce"ba'a gida É—aya muke da uwarki Zainab ba? Je ki tambaye ta mana,ko kuwa mu uban naki ya sa ki raina?"
Shaheeda ta girgiza kai ta ce"Ni yanzu na girmi faÉ—a,na bar wa marasa abin yi,kuma hankali dai daidai gwargwado na yi,na gaishe ki,bari na yi nan"
Hajiya Atika ta ce"gwara dai ki tafi kafin na naÉ—a miki shegen duka anan"
Shaheeda ta dakata daga yunƙurin fitar da take yi ta ce"a da ba'a daki Shaheeda ba sai yanzu da ta zama mutum?
Ai mai dukan engineer Shaheeda a yanzu dai sai dai ruwan sama"ta sa kai ta fice tana waƙa
Kai tsaye ta nufi part ɗin Hajiya Ruƙayya,tana zaune ita da ƙanwarta Arfa suna hira ƙasa-ƙasa,a ranta ta ce"munafurcin ya motsa kenan!"amma hakan bai hana ta kwarara sallama da ƙarfi ba
Da sauri suka ɗago suna kallonta fuska a ɗaure,babu damuwa ta ƙaraso parlourn ta zauna tana kallonsu tana murmushi
"Barkanku da dare,ya na same ku?ina wuninmu?"
"Ke tsagera,iskancin da kike yi idan kin ga a baya na ƙyale ki wallahi a yanzu kika kuskura kika ce za ki yi mana wani rashin tarbiyya sai kin gane kurenki "
Taɓe baki Shaheeda ta yi tana yi mata kallon banza, kafin ta ce"ke yanzu idan banda abinki wane ya ce miki idan kika ce za ki dake ni zan tsaya kamar itace ina kallonki?
To kaf danginku babu wanda ya isa na yi masa wannan alfarmar don ki ji da wai