Sashe 3
Gadar Tsautsayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Farin ciki sosai ya bayyana a fuskokin yaran,amma babu wanda ya samu zarafin magana tunda har zuwa yanzu Abba(Alhaji Yusuf Maliya)bai ba su damar yin magana ba,kamar yadda tsarin family ɗin yake,wato yaro baya taɓa yin magana sai ya sami umarni daga wajen babba
Alhaji Yusuf maliya ya mayar da hankalinsa ga yaran da za su tafi karatun,su huɗu ne,bayan Amina da Iman da Surayya akwai Salim da Mufeed yaran Alhaji Rufa'i,amma da yake su maza ne,kuma matsalar da aka samu a baya ba daga mazan aka samu ba shi yasa ba'a damu sosai da nasu ɓangaren ba
Alhaji Yusuf ya dubi yaran,a nutse ya kira sunayensu É—aya bayan É—aya,suka amsa cikin girmamawa, cikin nutsuwa ya fara bayani
"Ku ba ni hankalinku nan
Kun san tsarin, musamman ku yan mata,a Maliya family ba'a barin mata su fita don zuwa wata ƙasar karatu, saboda kowa ya san abin da hakan ya janyo mana
Sai dai wannan karon za mu dage mu bar ku ku fita waje don karatu,ba don komai ba,sai don muna kyautata muku zato
Zainab da Surayya za su tashi zuwa ƙasar US nan da kwanaki takwas in sha Allah,inda Zainab za ta karanci medicine ita kuma Surayya zata karanci business administration, Saleem da Amina za su tafi Turkey inda Saleem zai karanci medicine, Amina zata karanci engineering, Mufeed kuma zai tafi Spain inda zai karanci SOFTWARE ENGINEERING!"
Ambatar software engineering kawai da Abba (Alhaji Yusuf Maliya)ya yi ya sa ɗakin ya yi wani irin shiru,tuni wasu zuƙata suka tsinke,wasu kuma suka shiga kokwanto da fargabar kar a sake afkawa GADAR TSAUTSAYI makamanciyar ta baya,ta rufta da su a karo na biyu,a wannan karon kuwa sun san kafin su dawo daidai za'a ɗauki lokaci mai tsawo
Alhaji Yusuf Maliya shi kanshi ya ji wani canji,amma ko a fuska bai nuna ba,ya cigaba da jawabinsa cikin nutsuwa
"Don haka ina yi wa kowanne yaro fatan alkhairi,ina fatan Allah ya kai ku lafiya ya ba ku abin da kuka je nema
Nasiha ta kuwa bata wuce ku ji tsoron Allah ba, ku kama mutunci da ƙimar kanku musamman ma ku mata,ku yi abin da ya dace,kar ku ga cewa ba ma kallonku,kar ku manta cewa mahaliccinku yana kallonku,kuma a kowanne lokaci za ku iya ganinmu mun kawo muku ziyara,da wasa muka ga wani abu wanda bai yi min ba zan ɗauki matakin dakatar da karatun ne kawai, wannan gargaɗin ba iya mata kawai nake yi wa ba, har da ku mazan!"
Cikin girmamawa suke jinjina kai,s hankali kowa a cikinsu yake daukar alwashin kiyaye dokokin da aka kafa musu, Alhaji Yusuf Maliya ya cigaba da bayani
"Duk wani abu da kuke buƙata an kawo,ku duba,idan akwai abin da ba ku gani ba to sai ku yi min magana a kawo"Mufeed ne ya fara rissinawa yana faɗin"to Abba mun gode, Allah ya saka da alkhairi "sauran ma suka rissina suka yi godiya, Alhaji Yusuf ya ce"Masha Allah!
Kuna iya tafiya,na sallame ku"babu musu suka miƙe ɗaya bayan ɗaya suka fice daga katafaren parlourn
Bayani Alhaji Yusuf ya cigaba da yi,da yadda za'a saka musu idanu,ya dubi Muyassar wanda ya kasance shine babba a cikin jikokin gidan ya ce "Muyassar ga ƙannenka nan,ka saka musu idanu,ka tabbatar da cewa ba su aikata wani abin ashsha ba,na san za ka iya in sha Allah"Muyassar ya rissina yana faɗin "in sha Allah Abba! Allah ya ƙara girma"
Alhaji Yusuf ya ce"to alhamdulillahi, Allah ya yi muku albarka baki É—aya,wani ya rufe mana taro da addu'a "Muyassar ya yi musu addu'a Kamar yadda aka saba,suka yi sallama,taron ya watse kowa ya kama gabansa
*ROCKY ESTATE,KANO STATE, NIGERIA*
A hankali motar ƙirar Audi A4 take shiga cikin estate ɗin bayan masu sojojin da suke gadin ƙaton gate ɗin estate ɗin sun ɗage shi,kuma kai tsaye ba tare da ɓata lokaci ba motar ta cigaba da tafiya a hankali don isa inda take nufa
A daidai wani katafaren gate motar ta yi parking,kuma cikin nutsuwa mamallakin motar ya matsa horn sau É—aya,jim kaÉ—an kuma aka É—aga gate É—in, motar ta shiga cikin harabar katafaren gidan a hankali
A parking space ya yi parking motar,tsawon mintina kusan biyar babu alamun zai fito,kafin a hankali ya buÉ—e motar yana mayar da wayarsa aljihu,da alamu kira ya gama amsawa
CSO Haisam Abdulmalik Madaka kenan,zaƙaƙuri,ƙwararre kuma nagartaccen jami'in tsaro na farin kaya (DSS) wanda Allah ya hore masa sanin makamar iko da zuciya,gami da dagiya a bakin aikinsa,mutum ne mai matuƙar ƙoƙari da ƙwazo
Shi kaÉ—ai iyayensa suka haifa Mahaifiyarsa Hajiya Rasheeda ta rasu,daga baya mahaifinsa ya auro Hajiya Malika, wadda ta haifi yara mata biyu, Hafsa da Haleema, Hafsa ta yi aure shekaru biyu baya,tana zaune da mijinta a Abuja,ita kuma Haleema tana Egypt inda take karantar pharmacy
Shekaru bakwai baya Haisam ya yi aure,amma saboda wasu matsaloli da suka Kunno kai a rayuwar auren nasu sun rabu da matar, yanzu haka Æ´arshi É—aya tilo mai sunan mahaifiyarshi, wadda ake kira da Amna tana tare da shi,sai dai ya É—aukar mata nanny,yar dattijuwa da take kula da ita
Kai tsaye ya nufi entrance É—in gidan yana tafiya a hankali,da sallama ya shiga katafaren parlourn wanda ya gaji da haduwa, Hajiya Malika, wadda suke kira da Mamie ta amsa tana É—ago kanta tana kallonsa, kafin ya yi wani yunkurin ko ya furta wata kalma Amna da take zaune a study table É—inta tana zane zanenta ta taho da gudu ta É—afe shi,yana murmushi ya rungume ta,a kunne ta raÉ—a masa
"I miss you Papa!"
"I miss you papa's baby!"ya faÉ—a yana murmushi
Itama murmushin take yi,ya sauke ta ya kama hannunta suka nufi cikin parlourn
Sai da ya fara shiga É—akin Mamie ya gaishe ta,ta amsa fuska a sake sannan ya ja hannun Æ´ar tashi suka nufi part dinsa
Tare suka ci abinci kamar yadda suka saba duk dare muddin yana gari,suna ci suna hira sosai,tana ta zuba masa shirme shi kuma yana biye mata, cikin dabaru kuma yana tambayarta game da darussanta na makaranta tana ba shi amsa
Rasheeda Haisam makawa (Amna) yarinya ce mai kaifin ƙwaƙwalwa da basira,a kamanni na fuska ta ɗebo mahaifiyarta,amma a halaye da ɗabi'u babu inda ta baro Haisam,akwai soyayya da shaƙuwa mai ƙarfi tsakanin uban da ƴarshi, shiyasa ko tafiya ya yi in dai ba aiki bane ya sha masa kai baya rabuwa da kiranta a waya
Bayan sun gama cin abincin babu jumawa bacci ya ɗauke ta,a hankali ya saɓa ta a kafaɗa,ya ɗauke ta ya fice zuwa part ɗin su
Sai da ya fara yin sallama a bakin É—akin nata, Nanny É—inta,da take kira da Mama tana zaune tana lazimi tun bayan ta idar da Sallar isha'i,tana ganinsa ta rissina tana gaishe shi,ya amsa yana gaishe ta sannan ya kwantar da Amna, ya yi musu bankwana ya wuce sashenshi
Kai tsaye bayan ya canja kaya zuwa na bacci ya wuce ɗakinsa da babu wanda yake shiga, ɗakin bincike ne,ko kuma ɗakin sirri,a wannan ɗakin shi da kanshi bai yarda da kanshi ba ballantana ya yarda da wani,kuma ba tare da ɓata lokaci ba ya mayar da dakin ya rufe
Kai tsaye computer É—in shi ya buÉ—e, ba tare da bata lokaci ba ya kunna,kuma kai tsaye ya shiga zuwa inda hotunanta suke,a nutse yake nazartar komai
#Nusy_bee
Page 3
A kaf cikin hotunan babu wanda aka yi a Nigeria,gaba ɗayansu daga ƙasashe ne kala-kala,wasu a Columbia,wasu a Mexico,wasu a Peru, wasu a Bolivia,wasu kuma a US
A nutse yake ƙare mata kallo cikin nutsuwa da nazari,har zuwa yanzu babu wanda ya san sunanta na gaskiya,a taƙaice ma, babu wanda ya san sunan nata, babu wanda ya san inda take, ballantana wani information game da rayuwarta
To amma kuma ai an san fuskarta,kuma tana shigowa ƙasar,to ya aka yi ta gagara kamawa?
Ko dai da gaske ne zarginsa ya tabbata akwai masu taimakonta a manyan ƙasar?
To idan hakane,a shugabanni kenan?
Kai a'a!ko da a ce a shugabanni ne dole watarana zata zo hannu,sai dai a ce bayan an kamo ta a sake ta
To me yasa ba'a taɓa kama ta ba? wayo ta fi mutane ne?ko dabararta ta fi ta mutane,ko ma dai yayane dai ƙwaƙwalwarta ai guda ɗaya ce,kuma sauran mutane ma haka, yadda take yin tunani take tserewa su ma haka za su iya yin tunani su bi ta har su ƙure mata gudu don kamo ta
Wani hotonta ya buɗe, wanda take santa da baƙaƙen kaya,ta juya baya,haruffan N.O.C.C.M. raɗau a bayanta, wannan hoton idan bai manta ba ta turo musu shi da kanta,inda ta tura musu da adireshin inda take,amma da suka je can ba su samu komai ba sai wata takarda da ta sake maimaita waɗannan haruffan,N.O.C.C.M, waɗanda har zuwa yanzu babu wanda ya san me suke nufi
ÆŠan murmushi ya yi,a hankali ya ce"smart girl!
Ban taɓa ganin yarinyar da ta zubar da darajar jami'an tsaro ba sai ke,na jinjina miki,amma ina yi miki jajen lalacewar shirinki a duk lokacin da na waiwaye ki,kar ki bari na fara binki,don tabbas zan kama ki"ya mayar da computer ɗin ya rufe,ya miƙe a nutse ya fice daga ɗakin,kanshi q cushe,amma yana son ya yi tunanin ta inda zai fara cikin sauƙi
*UNKNOWN LOCATION*
Madaidaicin gida ne,flat mai 3 bedroom and parlour,sai dai haske bai wadace shi ba sosai
Fitowa ta yi daga ɗaya daga cikin ɗakunan gidan,shirye take cif cikin baƙaƙen hoodie riga da wandonta,a'a usual ta sanya scarp ɗinta, duk da cewa bai rufe dogon gashinta ba da aka gauraya shi da attachment kalar ja
Zama ta yi tana gyara takalminta samfurin sketchers,tana gamawa ta miƙe, maimakon ta nufi ƙofa sai ta daka tsalle ta kama garun gidan,babu ɓata lokaci ta haura, cikin nutsuwarta ta ƙarewa ko'ina kallo kafin ta dira,kai tsaye ta hau babur ɗinta samfurin bike,ta tayar ta bar wajen
Da wani tsananin gudu tamkar ba mace ba take tafiya,akan babur É—in,ta yi amfani da wani handkerchief ta É—aure rabin fuskarta
Da yan dabarunta ta kaucewa duk inda ta san da yan sanda har ta isa inda take son zuwa
Wajen ya fara shiga cikin jeji, ba tare da fargabar komai ba ta sauka a babur É—in ta wuce cikin wajen
Ta yi ƴar doguwar tafiya kafin da ƙafa ta isa inda take fatan zuwa