← Book details Gadar Tsautsayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 51

Sashe 50

Gadar Tsautsayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hanan ta riƙe hannunta, cikin lallashi ta ce"Na'ima,duk lalacewar iyaye fa iyaye ne, ba'a taɓa fushi da su,sai dai a yi ta haƙuri ana nuna musu hanya, ba'a fito na fito da su,yin hakan kuskure ne,kuma ba'a gyara kuskure da kuskure,ki yi duba ga maganata please "

Na'ima ta taɓe baki, Allah ya sani tana jin ciwon halayen mahaifiyarsu,mace mai tsananin son kanta da ƙyashi,tana jin haushin yadda take dakile Abba tana shigarwa Ummeey hanci da ƙudundune,mace ta gari, wadda a kowanne lokaci take sha'awar zama mai irin halayenta

Daga nan Na'ima chanja topic ta yi,amma har yanzu a ranta tana jin Shaheeda ta yi daidai,kuma zata iya zama irinta,banda haka ma sai ta san yadda aka yi yayanta ya aure ta

*ROCKY ESTATE,KANO STATE*

"Ikon Allah!anan nake jin son zuciya, wadda hausawa suka ce ɓacinta"Hajiya Mariya ta dubi Nimra mai wannan maganar tana riƙe haɓa,ta ce"me kika gani?"

Nimra cikin ɓacin rai ta ce"wannan shari'ar da aka canjawa ma'ana mana, wallahi ko kaffara ba zan yi ba duk abubuwan da aka gabatar ba haka suke ba,haka kawai an wani rage mata laifi,an shirya ƙarya da sharri an saka babban mutum kamar Alhaji Sa'idu a matsala?

Gaskiya wannan yarinyar masifa ce,kuma in sha Allahu ba zata gama da duniya da lafiya ba"ta ƙarasa magana cikin ƙunan rai

Hajiya Mariya da take kallonta ta ce"ke menene matsalarki da ita ne?"

Nimra ta ce"ya Haisam ya damu da ita da yawa,bana son na zarge shi akan wani abu dabam, Allah Allah nake yi ta zo ta amshi É—anta,ni da ban ga kamannin halfcast a tare da shi ba ma da na ce É—an na Haisam ne,ta shiga rayuwarsa da yawa,babu wata criminal da ya yi chasing da nake ganin yana kallon hotunanta yana murmushi sai ita,why?duk saboda ta yi laifi ne ko me?"

#Nusy_bee

Page 40

Hajiya Mariya ta yi murmushi ta ce"oh Allah!

Nimra meyasa abin da ya zama damuwa da wanda bai zama ba duka saka shi kike yi a ranki?

Ba kya tsoron wani ciwon na zamani?

Ki kwantar da hankalinki ki cirewa kanki damuwa,tunda ya zaɓe ki a matsayin macen da zai aura ai komai mai sauƙi ne

Allah na tuba ko da a ce ya ce zai aure ta ne ke ba mace ba ce?ba ki san yadda za kiyi kissa irin tamu ta mata ki mayar da abin tarihi ba?

Ni ba ki ga yadda nake zaune a gidan ubansa ni kaÉ—ai ba?ko an gaya miki haka kawai a banza nake zaune?"

Nimra ta jinjina kai, Hajiya Mariya ta ce"ko ke fa!

Mace da ta isa bata taɓa yin hayaniya akan namiji,idan kika ga mace tana hayaniya akan namiji to kucaka ce"

Nimra ta yi shiru tana jin huɗubar yayar Tata,kuma tana shiga kanta,a ranta ta ƙudurce tabbas sai ta koyawa Shaheeda hankali muddin bata fita sabgarsu ita da Haisam ba

*HAISAM*

Sun sake tattaunawa sosai shi da barrister Hibba,duk da ya ji relief na alamun cewa za su yi nasara a zaman kotun to amma ya ji babu daɗi da barrister Hibba ta tabbatar masa ko yaya ne zata yi zaman kaso,amma ganin babu wata mafita sai wannan ya sa ya haƙura

Bai koma gida ba sai wajen ƙarfe takwas na dare,kuma kamar yadda ya saba yau ma sashen Nanny ya nufa

Ya sha mamaki da ya shiga sashen ya ga Nimra a zaune tana kallon cartoon tare da su Amna,amma fa Amna ce a kusa da ita, Mubarak kuwa yana kusa da Nanny wadda take goge musu kaya zata jera musu a wardrobe

Da fara'a ta fara gaishe shi da yi masa sannu da zuwa,ya amsa fuska babu yabo babu fallasa, Amna ta miƙe ta tafi da gudu ta ɗane shi,ya ɗaga ta ya sauke, sannan ya kira Mubarak,ya taso fuska babu yabo babu fallasa,ya ɗaga shi ya dire yana murmushi, kafin ya ce"abokina ya ne?

Ka ci abinci kuwa?"Mubarak ya É—aga kai, Amna ta ce"Daddy É—azu ma ya yi kuka yana kiran mamana!mamana!!"ta faÉ—a tana kwaikwayon yadda Mubarak É—in yake faÉ—a

Murmushi Haisam ya yi,ya É—auki Mubarak da yake kallonta,yana faÉ—in "abokina yanzu fa kai babba ne,ya kamata fa a ce ka daina rigima"

Nanny ta yi Æ´ar dariya ta ce "tsokanarsa Æ´ar'uwar ta yi,shine dalilin kiran maman"

Haisam ya harari Amna,ta sunkuyar da kanta da sauri,ya ce"wato kuka kike saka friend É—in naki ko?

Sai na É—auke shi na mayar da shi tunda ba kya so"

Da sauri ta ce"I'm sorry Daddy ina so"ya ce"Weldon!

Sai ki daina tsokanarsa"ya kalli Mubarak ya ce"kana jin bacci?"

Mubarak ya gyaÉ—a kai a hankali, Haisam ya ce"yawwa mu boy!mu je mu kwanta ko?"nan ma ya gyaÉ—a kai yana kwantar da kanshi a kafaÉ—ar Haisam

Abin ya yiwa Nimra ciwo sosai,ganin ko kallo bata ishe shi ba,sai ta wannan matsiyacin yaron yake,a ranta ta ƙudurci sai ta raba shi da shi su huta, tunda gashi yanzu ma ko ta yar cikinsa baya yi

Har ya juya baya ta ce"Good evening yaya Haisam!"ya juyo ya ce"evening Nimra!"sannan ya kalli Nanny ya ce"Nanny na manta, Mubarak ya sha maganinsa kuwa?"

Nanny ta ce"ai bana yi masa wasa ko kaÉ—an Alhaji,na ba shi tun É—azu "Haisam ya yi murmushi yana sake rungume Mubarak ya ce"Weldon Nanny muna godiya sosai,sai da safe ko?"Nanny ta ce"Allah ya tashe mu lafiya Alhaji"

Amna ta É—aga masa hannu tana murmushi tana faÉ—in "Daddy Good night"ya ce"Good night angel"ta ce"Mubarak Good night"

Kamar yadda Nimra ta yi zato sai kuwa ta ga Haisam ya ja ya tsaya yana murmushi yana kallon Haisam,ya ce"ka ce"mata good night "da farko kamar ba zai faÉ—a ba,amma sai ya ce"good night!"da yanayin gwaranci a maganarsa

Dariya suka yi su duka banda Mubarak da Nimra, sannan Haisam ya fice daga sashen

Yana fita Nimra ta kalli Nanny ta ce"Nanny yaron ba shi da lafiya ne?"

Nanny cikin jimami ta ce"wallahi kuwa Hajiya!

Yaro abin tausayi,wai ciwon asma,jiya da numfashin ya riƙe ai sai da na kusa faɗuwa,don na ɗauka barin duniyar zai yi"

Nimra cikin fuskar tausayi ta ce"Allah sarki!

Allah ya ba shi lafiya"Nanny cikin jimami ta ce"Ameen Hajiya!

yaron abin tausayi wallahi,gashi sam ba shi da saurin sabo da mutane"

Nimra bata sake magana ba,ta cigaba da kallonta, ƙarshe ma da ta ga Amna ta fara jin bacci ta raka ta ta kwanta sannan ta miƙe ta fice zuwa sashen Hajiya Mamie

*MUYASSAR*

Yana tsaye a jikin windown ɗakin da ya kama a katafaren hotel ɗin yana leƙen titin da yake bayan hotel ɗin,gaba ɗaya duniyar ta yi masa zafi,damuwa ta ishe shi sosai,a yanzu yana jin ba shi da wani farin ciki ko walwala sama da mallakar abincin ruhinsa wato Shaheeda,amma jiya a gabansa aka gudanar da wata zazzafar shari'ar da yake kyautata zaton cewa Shaheeda ba za ta fita ba, sai ta yi zaman kaso

Sau uku yana zuwa don ganinta, amma abu ɗaya ake sanar masa shine babu wanda zai ga Shaheeda,daga jami'an tsaro sai lawyer ɗin ta, hakan ya sake tabbatar masa da case ɗin babba ne tun a wancan lokacin, wanda hakan ba ƙaramin ɗaga masa hankali ya yi ba

Duk wannan dambarwar ba ita ba ce ta dame shi kamar rashin damar auren Shaheeda, mafi girman tashin hankalin kuma shine rashin soyayyar da Shaheeda take yi masa, kenan hakan ya nuna cewa dakon wahala yake yi? Nooooo! Impossible ya san Shaheeda ko bata so shi ba yanzu zata so shi wataran

Arfa ce ya faɗo masa a rai,wani baƙin ciki ya tokare masa maƙoshi tuna yadda Arfa take ƙare masa zagi shi da iyayensa don kawai tana taƙama ba zai sake ta ba, saboda umarnin mahaifiyarsa, yanzu gashi nan ya sake ta ɗin,ta je can ta shirya duk makircin da zata shirya,shi yanzu ma nan da shekara guda ba za'a sake ganinsa ba, don yan kwanakin da ya ɗauka babu Arfa a tare da shi har ya fara samun nutsuwa ya dawo hayyacinsa

Kira ne ya shigo wayarsa,bai damu da ganin mai kiran ba ya É—aga wayar,kamar yadda ya zata kuwa haka É—in ne, Na'ima ce

"Yaya!kana tare da Ni?"

A hankali ya lumshe idanunsa ya buÉ—e ya ce"ina tare da ke Na'ima,ya school?"

"Yaya!ka kalli shari'ar su aunty Shaheeda kuwa?"

Muyassar ya ja numfashi ya fesar ya ce"na kalla Na'ima,in fact a gabana aka yi komai,sai mun dage da addu'a sosai, don Shaheeda tana cikin gagarumar matsala"

Na'ima ta yi murmushi ta ce"yaya kenan!

Kana kallon Shaheeda a matsayin wadda ta faɗi,ni kuma ina kallonta a matsayin jarumar da ta jijjiga ƙasa baki ɗaya da kaifin ƙwaƙwalwa da fikirarta, wallahi ko a yau aunty Shaheeda ta bar duniya tarihi ba zai manta da ita ba"

"Ke bana son shirme!

Ba fa abin a zo a gani ta yi ba, ƙwayoyi ta siyar, sannan kuma Yahoo girl ce, menene abin alfahari a nan?"

"Yaya yahoo ai na masu basira ne,Ni na yi mana,ko kai!

Sannan abu ka gaba kar ka manta yaya, manyan ƙasa waɗanda ya kamata su tallafi rayuwarta da sana'ar yi da ƙwaƙwƙwaran ilmi su ne suka ba ta hanya,ko na ce suka yi amfani da ita don aiwatar da wannan muguwar sana'ar,a wannan lokacin ahalinta sun watsar da ita,sun nuna ba sa buƙatarta, not even her,ko ni idan na gamu da wannan trauma ɗin ban ce zan iya riƙe kaina ba, musamman da ya kasance kana jin tarihin da ta bayar ai,ta ce ta nemi aiki a kamfanoni,amma ko'ina daga mai neman takardu sai me nemanta,kuma ƙarin alfaharin da nake yi da aunty Shaheeda shine rashin siyar da mutuncinta,ta yarda ta amsa sunan criminal amma bata yarda a yaga mata rigar mutunci ba,yaya aunty Shaheeda ta dabam ce "Muyassar da ya yi shiru yana sauraren maganganun Na'ima da ya ɗauka shirme ya ce"na ji Na'ima,Ni dai sai anjuma kar ki saka ni ciwon kai da wannan surutan naki "ya kashe wayar yana jin ta tana ƴar dariya

Sai kuma ya zauna yana nazarin maganganun ƙanwarshi Na'ima, ya tuna lokacin da Shaheeda ta dawo gida bayan rasuwar Arnold,da alamun nadama masu yawa a tare da ita,ga ciki,ga babu,amma hakan bai hana Abba ya kore ta ba, ba tare da tunanin a wanne hannu zata faɗa?ko wanne hali zata shiga ba?
Chapter 50 · 0% Book details