← Book details Gadar Tsautsayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 51

Sashe 19

Gadar Tsautsayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Idan ban da shi wawa ne ko babu mata a duniya me zai yi da wannan fanÉ—ararriyar yarinyar? wadda a yanzu ma babu tabbacin ko tana raye?

To ki ja masa kunne, wallahi tallahi, muddin magana makamanciyar wannan ta sake zuwa inda nake akan yaron nan to tabbas sai na shayar da shi mamaki,sai na É—auki mummunan mataki akansa

Ku bani waje zan huta"babu musu suka miƙe ɗaya bayan ɗaya suka fice, zuciyar Hajiya Ruƙayya da ta Arfa fes

Kai tsaye harabar gidan Hajiya Sa'adatu ta nufa,wajen parking space,anan ta iske Muyassar yana zaune,amma kallo É—aya za'a yi masa ya bayyanar da damuwar da yake ciki, sai dai sam bata kula da hakan ba,tana zuwa ta sauke masa mari mai kyau, kafin ya ankarar ta sake sauke masa wani

Dafe kuncinsa kawai ya yi ba tare da ya É—ago kanshi ba, Hajiya Sa'adatu ta cigaba da magana a fusace

"Wallahi ba ka isa ba Muyassar! ba'a haifi yaron da zai bijire min haka ba, wallahi ko bayan raina ka auri yarinyar nan Allah ya isa ban yafe maka ba,kai ko labari na sake jin ka kalli hotonta sai na tsine maka!!

Kai in banda abin namiji me za ka yi da Shaheeda ga Arfa kana da ita?asalima ga mata nan birjik a gari ko da kana sha'awar ƙari,amma idan na sake jin batun Shaheeda to lallai sai ka gane kuskurenka,tabbas sai na ba ka mamaki,dalla shiga mu tafi"babu musu ya buɗe motar jiki babu ƙwari,itama ta shiga baya,ya tayar suka bar wajen

*ROXY*

Yau kwana biyu kenan da tura Azeema gidan Amra da ta yi don rama abin da Amra ta yi mata,a ɗaya ɓangaren kuma tana samun sauƙi sosai,don zuwa yanzu hannun ya yi sauƙi sosai

A yau ta shirya zuwa kano,amma kafin nan tana buƙatar ganawa da Amra tukunna,don haka ta shirya cikin wasu expensive track suit,irin wanda take yawan sakawa,ta sanya baƙin sketchers,ta ɗaura scarp akan dogon gashin ta sannan ta fice zuwa gidan Amra

A hanya tana tuƙi tana kallon numbar David wadda tsawon kwanaki kenan yanzu idan ta kira ba ta shiga,ta rasa inda ya jefa wayar tashi

A ƴan mintuna ta isa gidan Amra saboda gudun da take yi,ba tare da damuwar komai ba ta kutsa kai gidan tana gyara zaman baƙin spec da ta sanya ya rufe mata ƙwayar idanunta

Murmushi ta yi ganin Amra a kwance an rufe mata ƙunar da wani yalolon mayani,tana sauke numfashi a hankali,ga wata ƴar'uwar cin mushenta da alamu ita ce take dawainiyar jinyarta,gefe kuma ga Hassy nan a zaune itama tana yin nata alhinin

Da kallo suka bi Roxy gaba É—ayansu, ba tare da damuwa ba ta dubi Amra ta ce"ya jikin?"

Cikin Muryar kuka ta ce"ke ce kika turo su ko?

Dama wallahi ke nake zargi, tsinanniya kafira, Allah ya tsine miki albarka, shegiya arniya"

ÆŠan murmushi mai sauti Roxy ta yi,ta samu waje ta zauna ta ce"ashe kin gane kenan

To ina fatan wannan jinyar ya zamar miki ishara ya hana ki aikata fasikanci har abada,dama na san ba za ki je asibiti ki zauna ba, saboda kin san me kika yi,ni lokacin bari na ƙasar ma ya yi,sai na ce Allah ya ƙara afuwa"

Miƙewa tsaye ta yi,ta yi taku biyu sannan ta waigo tana kallon Amra fuska babu yabo babu fallasa ta ce"Gobe ki sake yunƙurin aikata hakan, musamman da wayo da dabara kamar yadda kika yi min,amma kuma kar ki manta,a duk lokacin da kika yi yunƙurin aikata fasikanci Roxy zata zamo a tare da ke,ta tarwatsa mummunan nufinki,sai anjuma ko?"tana kai wa nan ta fice daga parlourn,babu wadda ta iya sake yi mata magana a cikinsu,har Roxy ta fice

*KANO STATE, NIGERIA*

*HAISAM*

A hankali yake fitowa daga office ɗinsa,a yau ne ya shirya aikata aikinsa gaba ɗaya,a yi ta ta ƙare kawai,don haka daga nan ma gidan malam Tajo zai wuce kawai

Wayarshi ce ta yi ƙara, takaici ya kama shi ganin Nimra,ya ɗaga wayar ya kai kunne yana faɗin"I'm all ears Nimra "

Cikin shagwaɓa ta ce"I'm going back to Abuja, Please ka zo ka kai ni airport, Please Love!"

Cikin ƙosawa ya ce"Nimra meyasa kike son disturbing ɗina ne idan ina aiki?"

Cikin shagwaɓa Nimra ta ce"amma ai baka da lokacina,kai kullum kana tare da aiki, yanzu haka za ka rinƙa yi kenan ko nan gaba?"

"Okay wait, I'm coming "ya faÉ—a a gaggauce ya kashe wayar

Yana ɓacin rai yana jan tsaki haka ya koma gida, lokacin Nimra ta gama shiryawa,tana ganinsa ta taso da farin ciki tana faɗin "Aunty Mariya sai mun yi waya,bye!"ta ja hannun Haisam suka yi waje yana bin ta da kallon mamaki, ita kuma Hajiya Mariya sai bin su da kallo take yi tana murmushi

Har suka isa airport Nimra babu abin da take yi sai zuba surutu,shi dai jin ta kawai yake yi ba tare da yana gane abin da take cewa ba

Kafin su yi sallama sai da ta yi ta ɗaukarsu hotuna,shi dai ya biye mata don su rabu lafiya,bayan ta gama ya yi mata sallama, sannan ya shiga motarsa,ya tayar ya bar airport ɗin kai tsaye a unguwar da iyalan marigayi malam Tajo yake ya yi parking,a bakin ƙofar gidan ya yi parking motarshi yana ƙarewa gidan kallo,da tunanin ta inda ya kamata ya fara

Ganin zai ɓata lokaci ya sa ya yakice tunani ya ƙwanƙwasa kofar gidan,babban ɗan gidan ya leƙo,yana ganinsa ya rissina yana gaishe shi

Haisam ya amsa da sakin fuska, sannan ya ce"maman naku tana nan kuwa?"

Yaron ya ce"eh,bari na yi mata magana"

Haisam ya ce"okay to yi maza,ina jiran ka"yaron ya koma cikin gidan don sanarwa mahaifiyar tasu

Babu jumawa ta fito, Haisam ya rissina ya gaisheta yadda ya saba,ta amsa da sakin fuska sannan ta ce"bismillah!

Ashe kaine,yau dai don Allah ka taimaka ka shigo mu gaisa sosai"

Haisam yana murmushi ya ce"ai Mama yau maganar ma bata tsayuwa ba ce,mu shiga mu yi maganar,ina fatan dai yaran suna nan"Mama ta ce"eh duka suna nan, bismillah,shigo"babu musu Haisam ya bi bayanta,suka shiga cikin gidan

*UNKNOWN LOCATION,KANO STATE, NIGERIA*

*ROXY*

Isowarta gidanta na sirri kenan ko minti biyar bata yi ba,ta shiga wanka,bayan ta fito sanye da bathrobe,kanta naɗe da ɗan ƙaramin towel ta ga wayarta da take ɓoye da number ɗinta ta sirri tana haske, kasancewar kowanne lokaci wayarta tana silent

Bata kawo komai ba da farko, don ta É—auka Oga boss ne,amma bayan ta shirya a cikin riga da wando hoodie tana duba wayar ta ga sabuwar number

Tana kallo kiran ya katse wani ya shigo,ta dake ta É—aga wayar ba tare da ta yi magana ba

"Barka da wannan lokaci Madam Roxy!"ta ji muryar mutumin da ba zata taɓa mantawa ba ta doki dodon kunnenta

Da ƙyar ta dake,ta saita nutsuwarta saboda yadda gabanta ya yi masifar faɗuwa,ta dake ta ce "Barka!wanene kai?kuma daga ina?"

ÆŠan murmushi ya yi mai sauti,sannan ya ce" na san ba za ki manta ni ba ai,amma kuma bari na sake yi miki tuni

Sunana HAISAM ABDULMALIK MADAKA!kamar yadda kika sani, jami'in hukumar yan sanda na fararen kaya wato DSS, mai riƙe da muƙamin CSO

Akwai rahotanni masu yawa akanki,na cewa ke ɗin ƴar safarar miyagun ƙwayoyi ce,kuma cikakkiyar ɓarauniyar yana,wato ƴar Yahoo,don haka hukumarmu tana nemanki,tana buƙatar ki kawo kanki,amma a shawarce kenan"

Wani murmushi ta yi ta ce"okay!

Kun gaji kenan?kun gaza da bibiyata ne?kun kasa?shine kuke nemana?

To ku cigaba da jarrabawa, wataƙila a dace,amma kuma ka sani......."

Ya cafke Maganar da faÉ—in "NO ONE CAN CATCH YOU ko?

Mhm!anya kuwa?ko da ace an kama tilon É—anki MUBARAK?"

Cikin wani irin gigicewa da tashin hankali ta ce"what?what do you mean?

Ɗana?why?why?me Mubarak ya yi muku? don't try to make that mistake,zan iya kisa akan shi,kar ka taɓa min ɗana,shine kaɗai ya rage min, shine rayuwata,don Allah!!!"

"To malama FATIMA SHAHEEDA!

If you are ready then sai ki kawo kanki ga hukuma,Ni kuma sai na sakar miki É—anki,akasin haka kuma?"ya yi É—an murmushi ya kashe wayar

*To fa!dama Roxy ita ce SHAHEEDA?ita ce Æ´ar Ummeey wadda take kewa da bege a kowanne lokaci?wanne É—a kuma ake magana akai?dama tana da É—a?ya aka yi aka samu wannan kuskuren?to za mu ji dai,ku biyo Alkalamin Nusy bee a labarin GADAR TSAUTSAYI don jin yadda zata kaya*

#Nusy_bee

Page 16

Tashin hankali ba'a saka maka rana! faɗar irin halin da Roxy ta shiga ɓata baki ne,a haukace ta sake ɗaukar wayarta ta aikawa Haisam kira

Sai dai ya ƙi ɗagawa,bata sare ba, cikin ficewar hayyaci ta cigaba da yunƙurin kira,sai da ta yi kira goma,a na sha ɗayan ya ɗaga

Cikin tashin hankali ta ce"to ai ba ka gaya min inda zan same ka ba,ina zan kawo kaina É—in?"

Kai tsaye ya ce "ki yi tracking number na mana,ke ba software engineer ba ce?kuma a good tracker?try it mana"

Cikin tsananin rauni ta ce"ba zan iya ba,don Allah ka taimaka min,ka gaya min address ɗinka na yi maka alƙawarin zan kawo kaina,amma ina roƙonka kar ka taɓa min ɗana,shi kaɗai ne farin cikin da ya rage min a duniya,idan ka cutar min da shi ban san yadda zan yi ba"

Kai tsaye Haisam ya ce"to da kyau!

Zan tura miki address yanzu,ina buƙatar na ganki a wajen nan da thirty minutes,ko kuma wannan yaron ba za ki sake ganinsa ba har abada"

"Na yarda "ta yi saurin amsawa jikinta yana rawa

Kashe wayar ya yi,babu jumawa message na address ɗin ya shigo ,tana gani ta miƙe tsaye,ko ganin gabanta bata yi sosai ta ɗauki hanya,a wannan lokaci ko ita ba zata iya misalta irin tashin hankalin da ta tsinci kanta a ciki ba

Bata juma ba ta samu kanta a wani ƙaton fili da ba shi da nisa da gidanta, Haisam ta hango a kan motarshi a zaune yana murmushi game da tafa hannayensa,ta ƙarasa gabansa, cikin rawar murya ta ce"ina ɗana yake?"

Yana murmushi ya ce"mu gaisa mana, Roxy zan ce ne ko Fatima Shaheeda?the most smartest girl I have ever seen in my life?"

"I said where is my son Haisam?

Kar ka yi min wasa da rayuwar yaro!i can't tolerate it anymore!"ta faÉ—a cikin fusata da tashin hankali
Chapter 19 · 0% Book details