← Book details Gadar Tsautsayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 51

Sashe 46

Gadar Tsautsayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gyara zama ta yi tana É—auke kanta,ta sauke numfashi ta ce"a duk lokacin da mutum yake ji ba zai iya aikata wani abu ba to bai same shi ba, ballantana ni da duk lokacin da na saka a raina zan yi abu to sai na yi shi

Kar ka manta nice na rainawa iyayena hankali,na auri wani ba tare da saninsu ba,na bi shi muka bar ƙasar baki ɗaya ba su sani ba,har yanzu a makaranta mataki na biyu nake,amma na yi abin da dubban masu Masters ba su yi ba da nasu,a taƙaice dai,duk wani abu da mutum ya saka kanshi to tabbas sai ya iya

Ni yanzu na san na gama tunda kuka kawo ni nan,mafi ƙarancin abin da zan iya fuskanta a kotu shine hukuncin ɗaurin rai da rai, saboda na san laifina babban laifi ne,abu ɗaya ne damuwata a rayuwa,shine ɗana mubarak"ta ɗago duk da babu alamun damuwa a fuskarta,amma ya gani a cikin idanunta,ta ce"a karo na biyu ina sake roƙonka,a wanne hali Mubarak yake ciki?

Kar ka manta na haife shi a maraya, wanda yake cikin ganiyar rashin gata,nima na yi masa laifi, saboda zaɓar duniya na watsar da shi na kama rayuwata,bai san daɗin iyayensa ba,bai san wani daɗi na rayuwa ba, musamman duba ga inda ya taso

Zan so a ce nan gaba ya samu farin ciki kamar kowa,ya samu ingantacciyar rayuwa, sannan kuma ya yi min addu'a "

Haisam ya yi murmushi ya ce"a matsayinki na wa zai yi miki addu'a?"

Ta kalle shi sosai tana ɗan murmushi ta ce"a ƙalla in samu darajar ɗaukar ciki da haihuwa mana officer "

Yana kallonta ya ce"ke mahaifiyarsa ce tabbas,ban isa na ce ba kya son shi ba, saboda na san ƙarya nake yi,amma meyasa za ki watsar da rayuwar tilon ɗanki ki kama rayuwar da kike so?

Na san dai babu jin haushin mahaifinsa a tare da ke, musamman da kika fuskanci laifinki ne "

Girgiza kai ta yi,ta ce"na kasa jurar hakan ne,matsayin Mubarak na ɗan Arnold, kamar yadda na gaya maka a baya idan na kalle shi ina tuna cewa Arnold ya yaudare ni,na aure shi na rabu da iyayena,amma shi ya watsa min ƙasa a idanu,ya tozarta ni,a ƙarshe a dalilin sa na shiga wannan rayuwar da nake ciki

Larurar Mubarak da ya gado daga wajen dangin babansa ta sake dasa min wani ciwo,hakan ya sa na zaɓi na nisance shi, gudun kar na illata shi akan laifin da ba nashi ba,kar na zalunce shi "

Haisam ya ce"ai kin gama zaluntar shi Shaheeda!

Tunda kika kasa zaɓa masa uba na gari, gashi a ƙarshe rayuwarsa ta koma wani sashen dabam na wahalhalu, meyasa kika yi hakan?"

"Wannan ƙaddarata ce da ban isa na tsallake ta ba a rayuwa,da a ce kowanne bawa shine yake tsarawa kanshi rayuwa da na tsarawa kaina yan'uwa daga mahaifiyata, waɗanda za su damu da ni ko da a ce ita mahaifiyar tawa bata kula ni ba,da ban tsarawa kaina soyayya irin wadda zata makantar da ni daga hangen abin da zai je ya dawo ba,da ban tsarawa kaina lalacewar rayuwata saboda abin duniya ba

A tsawon shekaru uku da na kasance a wannan halin sam bana cikin farin ciki,ko babu komai tsinuwar al'umma aba ce mai tasiri ga rayuwar mutum"ta ɗaga kai tana kallonsa, kafin ta ce"Ni yanzu abu ɗaya nake fata idan zai samu,a yanke min hukuncin kisa kawai,ina fatan hakan ya zama kaffarata "kukan da take riƙe da shi ya kubce mata

Miƙewa ya yi cikin jarumta jin zata karya masa zuciya,ya fara magana cikin kwantar da murya"ranar Monday za'a shiga da ke court,gobe idan Allah ya kai mu za mu zo da lawyer ɗin ki,in sha Allah komai zai zo da sauƙi,ina fatan don Allah kar ki yi mata taurin kai "a hankali ta jinjina kai, kafin ta ce"na yi maka wata tambaya amma har yanzu ba ka ba ni amsar da ta gamsar da ni ba

A karo na biyu ina roƙon ka ba ni amsa don Allah "

Kallonta yake yi ya ce"wacce tambaya ce?"

Sauke numfashi ta yi,ta ce"É—ana Mubarak,yana ina?

Sannan kuma a wanne hali yake ciki don Allah?"

#Nusy_bee

Page 37

Haisam ya yi ɗan murmushi ya ce"Mubarak yana hannuna a yanzu haka,idan za ki bar min shi ma ina so, because I love the boy so much,kuma ina fatan watarana mahaifiyarsa ta dawo gare shi ta cigaba da riƙe abinta"

Murmushi ta yi sosai,duk da hawayen fuskarta ta ce"na bar maka shi,kuma ina fatan watarana idan ya girma ka ba shi horo ya yaƙi mutane masu irin sana'ar da nake yi, maganar rainonsa kuwa kai ma ka san ba abu bane mai yiwuwa a gare ni a yanzu dai"

"Babu abin da ba ya yiwuwa da izinin Allah,ke dai in sha Allah za mu dawo mu tattauna akan batun shiga kotun

In Sha Allah za ki fita daga nan,kuma za ki sake ganawa da É—anki,amma ina so na yi miki wata tambaya É—aya"jinjina kai ta yi ba tare da ta yi magana ba

Kai tsaye ya ce "a Labarin da kika ba ni,ba ki sanar da ni cewa kin yi karatun addini ba, menene gaskiyar lamarin?"kai tsaye Shaheeda ta ce"na fara ba ka labarina ne tun sanda na kammala secondary,amma na haddace Alqur'ani tun ina SS2,na karanci littafai da yawa, dalilin haka ya sa na daina zuwa ma"

"To duk lokacin da kika ji damuwa da ƙunci,kin taɓa ɗauko Alkur'ani kin karanta?ko kin taɓa tashi cikin dare kin roƙi Allah ya duba ki ya ba ki maslaha akan matsalolinki?"shiru ta yi tana kallonsa, don tabbas bata taɓa yi ba,ya ce"to kin gani ko?

A duk lokacin da kika ce Allah zai yi miki to tabbas zai yi miki É—in,amma idan kika gwada dabara da iyawarki to tabbas Allah zai bar ki da iyawarki "
A hankali ta jinjina kai cike da gamsuwa,ta yi ɗan murmushi ta ce"na gode sosai da karamci,na gode,ka yi abin da iyayena ma suka kasa yi min"Haisam ya ce"babu ta inda iyayenki suka rage ki,sun yi dukkan ƙoƙarin da za su yi miki,ke ce a yanzu suke bi bashi"

"Ni kuma?ta yaya zan iya biyansu bayan ka san a yanzu tawa ta ƙare?"

"Weather taki ta ƙare ko kina da sauran dama lokaci ne zai bayyana haka,shekarunki nawa a yanzu, ashirin da nawa?"

Shaheeda ta ɗaga yatsunta guda uku ba tare da ta yi magana ba, Haisam ya zaro idanu yana murmushi ya ce"har yanzu ke ƙwaila ce Shaheeda,yarinya ce ke sosai,kin yi ƙoƙari sosai,na jinjina miki yadda kika rinƙa gwara kanmu da ƙananun shekarunki,I salute you Ma'am "ya faɗa yana sara mata yana murmushi

Sunkuyar da kanta ta yi ƙasa tana kallon handcuff ɗin hannunta tana murmushi ita ma, Haisam ya ce"alright then,ni zan tafi,sai na dawo zuwa gobe "ta sake yi masa godiya,suka yi sallama

*MALIYA ESTATE*

Izuwa yanzu al'amura sun sake rincaɓewa a gidan Alhaji Yusuf Maliya,don a wannan karon Ummeey ta kasa jure halin da ƴarta take ciki, da gaske ciwon da take ciki ya taɓa ta,kuma kallo ɗaya za'a yi mata a gane hakan

Hakan ne ya sa Alhaji Yusuf ya fita daga sha'aninta,don a ganinsa saboda Æ´arta tana son ta fara karya masa doka

Hakan ya sa ta fusata ta fara shiryawa don komawa gida,don ita ta gaji da wannan auren da tunda ta yi babu abin da take samu banda baƙin ciki da ɓacin rai

Tana shirin fitowa daga sashenta sai ga Hajiya Atika,tana yi mata wani kallo ta ce"Hajiya sai kuma ina?"

Bata amsa ba, Hajiya Atika ta sake faÉ—in"dama Alhaji ne ya ce na yi masa kiranki "tana kai wa nan ta juya ta bar wajen

Bata yi niyyar zuwa ba,amma sai ta canja ra'ayi ta tafi, tana zuwa ta samu Alhaji Yusuf a tsaye, fuskarsa a É—aure

Bata nuna ta gane halin da yake ciki ba ta ce"Barka da warhaka Alhaji"

"Samu waje ki zauna Zainab"ta manta rabon da ya kira ta da wannan sunan,amma ko a fuska bata nuna damuwa ba,ta samu waje ta zauna

Daga nan ɗaga waya ya yi ya yi kira,ana ɗagawa ya ce"Ruƙayya ku taho tare da Arfa,ki cewa Sa'adatu itama ta zo,ina buƙatar ganinta"sannan ya kashe wayarsa

Babu jumawa suka iso,sau É—aya Hajiya Zainab ta kalle su ta É—auke kai,daga amsa sallamar da suka yi ba ta sake magana ba, musamman da ta ga ko sashen da take ba su kalla ba

Alhaji Yusuf ya ɗaga kai ya kalle ta,a ɗan fusace ya fara magana "Zainab an kawo min ƙararki a gidan nan,ban san menene matsalar da take son ta canja ki ba,ko don kina ƙoƙarin ki nuna min ban isa da Shaheeda bane ya sa kike yin haka ban sani ba"

Hajiya Zainab ta É—aga kai ta kalle shi ta ce"Alhaji me kuma aka ce na yi?"

Alhaji Yusuf ya ce"ina Muyassar ya je?"

Hajiya Zainab ta dube shi sosai ta ce "Muyassar?

Alhaji ta ina zan san inda ya je?"

Alhaji Yusuf ya kalli Hajiya Sa'adatu,kamar jira take yi ta fara magana a fusace "ɗana tunda nake da shi ban taɓa ba shi umarni ya kauce ba sai akan ke da ƴarki,me kuka taka ne haka?

Da me kika fi sauran mutane ke da Æ´arki?

Har ga Allah zuwa yanzu na fara gajiya,na gaji da yadda nake tarbiyya kuna rusawa,don haka ki saka É—ana ya dawo gida kawai ya mayar da matarshi Kamar yadda kika saka ya sake ta,don na san ke ce kika saka shi ya sake ta sannan ya yi nisa da ita, saboda an kama gallafiriyar Æ´arki "

Kallonta kawai Hajiya Zainab take yi har ta kai aya, sannan ta yi murmushi ta ce"hattara dai Hajiya Sa'adatu!

Me É—a ba ya yiwa wani gorin lalacewar É—a idan da tunani, babu uwar da zata so É—anta ya lalace ko da ace ita lalatacciyar ce kuwa, kin ga......."

"Saurara Hajiya Zainab!

Ai lalacewa kuma sai dai ki ganta akan ƴarki wadda take zuba rashin tarbiyya da rashin mutunci tun tana ƴar ƙanƙanuwarta amma kin kasa tsawatar mata,idan ma wani asirin kika yi don lalacewar yayanmu to Allah ya mayar miki da masifar kanki,amma yayanmu sun fi ƙarfin lalacewa da ikon Allah "

"To madalla!
Chapter 46 · 0% Book details