← Book details Gadar Tsautsayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 51

Sashe 41

Gadar Tsautsayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ba ta can?"ta faɗa a ɗan tsorace,bata jira amsarshi ba ta miƙe da sauri ta fice daga sashen ta nufi sashen Abba

Sai da ta je ta samu tabbacin cewa tun da ta fita Shaheeda ta fita, a lokacin kasa nuna kararta ta yi,a gigice ta dubi driver tana faÉ—in"don Allah kai ni na duba Æ´ata,kar ta faÉ—a wani halin,don Allah mu bi hanya yanzu......."

"Zainab!"ta ji muryar Abba a fusace

Juyawa ta yi a gigice tana kallonsa,sam bata kula da jama'ar gidan da suka taru suna kallonta ba, Abba ya dube ta fuska a ɗaure ya ce"ban hana ki nemo ƴarki ba ki riƙe abarki,amma ki zaɓa ko aurenki ko ƴarki,daga sanda kika fita daga gidan nan da niyyar kin tafi neman ƴarki daga lokacin ki saka a ranki kin datse igiyar aurenki da kanki,zaɓi ya rage naki "yana kai wa nan ya kewaye ta ya bar wajen

Hajiya Ruƙayya da abin yake yi mata daɗi ta dubi Ummeey da take daskare a wajen ta ce"Allah ya kyauta dai!

Dama bahaushe yana cewa rana dubu ta ɓarawo ɗaya ta mai kaya,banda haka da ta yaya za mu san masu zuga yara suna lalacewa a gidan nan?

Allah ya kyauta"Hajiya Atika ta taɓe baki tana faɗin "Ameen dai"suka fara watsewa daga wajen suna kama gabansu

Da ƙyar Ummeey ta ja ƙafarta ta koma ɗakinta,tana zuwa ta zube a tsakar dakin tana mayar da numfashi, ƙasa-ƙasa ta samu zarafin ambaton"Inna lillahi wa inna ilayhi rajiun!!!"

Shikenan ta sani a yanzu,ta rasa ƴarta,komai ya ƙare mata, Allah ya kawo mata dauki

Tana jin wayarta tana ringing amma ta kasa É—agawa, saboda tashin hankalib da take ciki,duk da cewa ta san Hajiya Jamila ce ya kira akan batun Shaheeda

💫

Shaheeda kuwa saboda tsabar gajiya tunda ta kwanta bacci bata iya tashi ba sai da washegari Rabi ta shiga ɗakin tana tayar da yaranta don su yi Sallah,ta tashi da ƙyar,ta ɗauki buta don ta je ta yi fitsarin da ya matse ta a mara

Bayan ta yi Sallah tana zaune ta yi zuru,yaran da ɗaiɗai da ɗaiɗai suke zuwa suna gaishe ta,ta amsa tana murmushin yaƙe

ÆŠaya daga cikin yaran, wanda ta ji ana kira da faruku,da alamu shine babban shine ya kawo mata abincin karyawa,kunun gero ne da yar tsala,shima wannan abincin ya shiga ranta sosai,don haka ta ci da yawa,dama gashi da yunwa ta tashi, kamar ba ta ci abinci ba

Wajen ƙarfe bakwai da rabi yaran suka fice zuwa makaranta, Shaheeda ta kwanta ta lumshe idanu kawai tana tunanin yadda rayuwa take wujijjiga ta

Baban faruku ne ya yi sallama ya shigo É—akin,ta tashi zaune tana amsawa,ya shigo sosai ya samu waje ya zauna, Shaheeda ta rissina ta gaishe shi

Ya amsa da sakin fuska, sannan ya dube ta da kulawa ya ce "Ni zan fita aiki,ga wannan"ya miƙa mata ɗari biyar,ya ce"na san ba za ki rasa abin da kike sha'awa ba,sai ki siya ki ci ko?"Shaheeda ta karɓa tana rissinawa, cikin sanyin murya ta ce"na gode Allah ya saka da alkhairi"baban faruku ya amsa da Ameen sannan ya fice daga ɗakin

Wajen ƙarfe sha ɗaya na rana,a lokacin bacci ya fizge ta, cikin baccin ta rinƙa jiyo hirar matan gidan

"Umman faruku wai wacece wannan matar da na ga sun zo tare da baban faruku juya?baƙuwa kika yi ne?"umman faruku ta taɓe baki ta ce "wacece ni?

Mai gidan dai,nima tare na gansu ai"

"Mai gida kuma umman faruku?

Ƙanwarshi ko yar ɗan'uwanshi?"

"Mhm!ke ma dai kuma faÉ—a maman jidda, wallahi babu É—aya,a hanya ya ce ya tsinto ta"

"Kan uban can!sannu umman faruku!

Wallahi kaf duniya babu wanda ya isa ya yi min haka, tabÉ—ijam!"a cewar É—aya matar

Maman jidda ta ce "maman Ahmad ni ba wannan nake tunani ba, wallahi na fi zargin ƙarya take yi,karuwa ce kawai,ko wadda idanun ba su gama buɗe idanu a yawon dandi ba,mu je mu tuhume ta ya rantse abin da ta faɗa gaskiya ne,idan bata rantse ba wallahi mu fatattake ta, saboda tsaf sai ta lalata mana mazaje wallahi,ba zai yiwu muna zaman lafiya da mazanmu ba daga taimako a ɗauko mana masifa

Ni bari ma ku gani, wallahi ba zan yi sanya ba"ta miƙe ta nufi ɗakin da Shaheeda take ciki da Adams, don har wani zafi take ji a ƙirjinta,ji take yi ma kamar ta ga mijinta tare da wata macen,ko ma ya ce zai aure ta, dama ta fi sauran matan gidan zafin kishi

#Nusy_bee

Page 33

Maman Ahmad da umman faruku ma ba su yi sanya ba suka rufawa maman jidda baya zuwa É—akin da Shaheeda take, Shaheeda kuwa wadda take jin duk abin da suke cewa tuni ta tashi zaune tana jiran shigowarsu,ko ma me za su yi mata su yi mata,ita yanzu ta daina tayar da hankalinta akan ko menene ma zai same ta rayuwa,gwara ta koyawa zuciyarta dakewa da juriya

Ko sallama maman jidda bata yi ba ta bankaÉ—a labule ta shigo tana aikawa Shaheeda wani mugun kallo, Shaheeda ta dai ko motsawa daga inda take zaune bata yi ba,sai idanu da take ta bin ta da shi,babu jumawa Kuma sai ga umman faruku d maman Ahmad su ma sun shigo É—akin

Da wani mugun kallo maman jidda take kallonta, kafin ta ce"wacece ke?

Daga ina kike?

Ina kika samu cikin jikinki?ina buƙatar ki gaya min gaskiya, sannan kuma ki rantse min da Allah cewa gaskiya kika faɗa idan har kina son ki cigaba da zaman gidan nan"

Ita dai Shaheeda ko motsi bata yi ba, asalima bata da niyyar motsin,maman jidda da ta fi su fusata ta ƙaraso inda Shaheeda take ta ɗauke ta da wani mari,sai da ta tintsira

Gigicewa ta yi,don marin ya shige ta,amma saboda taurin kai bata yi magana ba sai hawayen da ta fara zubarwa

Maman Ahmad ta kalle su tana faÉ—in "maman jidda rabu da ita,amma mu fincike ta mu jefar a bakin titi idan bata tashi ta bar mana gida ba

Matsiyaciyar yarinya tun kina Æ´ar mitsitsiyarki amma kin san makirci?kuma kin san ki kwanta da namiji?"

Har yanzu kuka Shaheeda take yi, kuma babu niyyar tashi,a fusace maman faruku ta fincike ta,ta ƙanƙame jikinta tana runtse idanu,amma hakan bai hana su fincikarta ba,a fusace maman faruku take faɗin "yau ko gidan ubanki ne nan ɗin sai kin bar shi wallahi,shegiya munafuka"ganin za su illata ta ya sa ta miƙe tana kuka ta gyara zaman hijabinta,ta kalle su ta ce"Allah ya ba ku haƙuri"sannan ta goge hawayenta ta nufi hanyar waje

Maman Ahmad ta watsa mata mugun kallo ta ce "Ameen!sai a bi wani sarkin kuma, shegiyar yarinya kalle ta kamar ta Allah"maman jidda tana huci ta ce"haka suke ai,su yi maka lumbu-lumbu su shiga jikinka su cuce ka su bar ka da wayyo Allah, irin wannan kyasa-kyasan da ake samu akan irin waɗannan mutanen ai suna da yawa,shine ba za muyi hankali ba?kuma sai abin ashsha ya faru mu ɗorawa ƙaddara?"

Maman Ahmad ta gyara tsayuwa ta ce"an taɓa samun makamancin haka fa da ƴar babbar yayarmu,wai mijin ya taimakawa wata yarinya ya kai ta gidanta, shegiya ashe tana biye-biye, ƙarshe ta aure mijin ta kori waccan matar,daga baya ma ta yi mata asiri ta kusa haukacewa, Allah ya taimaka aka shawo kan abin"

Maman jidda ta riƙe haɓa ta ce"oh Allah!

Ki ce mutanen nan matsiyata ne,ki taimaka musu ki janyo su daga rana zuwa inuwa,daga sun ji sanyi sai su tura ki wuta, a'a wallahi,su yi zamansu a rana, Allah ya raba mu da mugun ji da mugun gani"ta fice daga ɗakin tana jinjina abin,su ma sauran matan suka fito suna kakabin lamarin Shaheeda, musamman yadda ta kafe ta ƙi magana,hakan ya tabbatar musu bata da gaskiya

Shaheeda kuwa tana fita ta goge hawayenta,kai tsaye ta nufi titi ta samu abin hawa,ta ce a kai ta kasuwar gwal,babu musu ya É—auke ta suka tafi

A hanya sai sauke ajiyar zuciya take yi, saboda ta ji daɗin abin da ya faru ma zata ce kai tsaye,jiya da ta rasa yadda zata yi,ga yunwa ga rashin matsuguni,kuma babu ko sisi a hannunta,sai Allah ya kawo mata baban faruku,a gidansa ta kwana kuma ta ci abinci,kuma a ƙarshe ya ba ta kuɗin da zata kashe, wanda ya zamar mata kuɗin mota

Yana sauke ta ta nemi inda zata siyar, kasancewar babu receipt ya sa ba'a siya da daraja sosai ba,don zoben ƙimarsa zata kai 600k saboda diamond stone da yake jikinsa,amma a 400k ya tashi,hakan bai dame ta ba,ta karɓi kuɗinta ta wuce kasuwa ta siya kayan jarirai, sannan ta samu laptop wadda bata gama shan jiki ba,da waya ƴar madaidaiciya ta siya, sannan ta wuce inda zata kama hotel

Mai sauƙin kuɗi ta kama na kwana uku,don ta san zai iya janta waɗannan kwanakin kafin ta sami gidan da zata zauna

Ai kuwa da ƙyar ta samu,don bata san kowa ba,sai da ta je gidan mai unguwar yankin,ta shirya ƙarya kamar yadda ta shiryawa baban faruku,mai unguwa ya tausaya mata,har ya ba ta dubu biyar,ta yi ta godiya

Gida ne madaidaici aka samar mata,sai dai ba ita kaɗai ba ce,gaba ɗaya gidan ɗakuna uku ne,wasu sun kama biyu ita kuma ta kama ɗaya,a ranar ta siya madaidaiciyar katifa da yan abubuwan buƙatu bayan ta siyar da ɗan kunnenta,duk da nauyin cikin jikinta ta miƙe zata fara gyaran ɗakin

Sallama aka yi mata,ta juyo tana kallon matar wadda ba zata wuce ta ba a shekaru,amma saboda talauci da babu gaba ɗaya ta lalace, ƙuruciyarta ma tana neman ta ɓuya, Shaheeda ta yi wa matar murmushi itama tana kallonta,matar ta ce"bari na taya ki ko?"

Shaheeda ta ce"na gode"daga nan suka mayar da hankali sosai ga gyaran ɗakin,amma matar ita ce ƙarfin aikin

Bayan sun gama Shaheeda ta yi ta yi wa matar godiya,matar tana murmushi ta ce"kar ki damu,ba komai,bari na zubo mana abinci"bata jira amsar Shaheeda ba ta yi waje "

Faten tsaki da yakuwa ne,ya burge Shaheeda,duk yadda ta so ta yi kara kasawa ta yi, saboda yadda faten ya rinƙa tsinka mata yawu,ai kuwa ta ci shi sosai,ta yi ta yiwa matar godiya, matar tana murmushi ta ce"ai ke ƴar'uwata ce,ya sunanki?
Chapter 41 · 0% Book details