← Book details Gadar Tsautsayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 51

Sashe 36

Gadar Tsautsayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana zuwa daf da ƙofar sashen nashi ya hango Nimra a tsaye a wajen, murmushi ya yi,ɗazu ya sa aka zo aka canja makullin sashen,don haka yanzu dole ta jira idan ba ya nan,ya gaji da yadda take shigar masa sashe kamar wasu dabbobi ko marasa addini

Ita kuwa yaron hannunsa ta bi da kallo da wani irin yanayi a fuskarta,bai kalli sashen da take ba ya zo zai shige sashensa, ranta a ɓace ta ce"excuse me!

Ina Amna É—in?"tambayar tata sai ta ba shi dariya,amma bai yi ba,kuma bai kalle ta ba ya shige part É—in sa,ya biyo shi a baya tana faÉ—in "bacci yake yi kuma za ka É—ago shi?

Ba zai tashi ba?"banza ya yi mata,yana shigewa sashensa ya mayar da ƙofa ya rufe

Yana kwantar da Haisam akan gadonsa ya fara jin bugun ƙofa na hauka kamar za'a karya ƙofar,har sai da Mubarak ya firgita,ya tashi yana ƙoƙarin fara kuka, Haisam ya lallaɓa shi ya samu ya koma sannan ya tashi ya nufi bakin ƙofar inda ake ta bugun

Bai yi mamakin ganin Nimra ba a tsaye tana ta huci, abin ma sai ya ba shi dariya,ta dube shi ta ce "yau kuma?abin da wulaƙanci ya zo?ka san ina biye da kai shine za ka mayar da ƙofa ka rufe?
Meyasa kake yi min irin wannan wulaƙancin ne?don kawai ina sonka?"hawaye Masu zafi suka zubo mata,take kuma ta fashe da kuka sosai

Ɗan ƙaramin tsaki ya ja,ya ce"Nimra,kin san yadda aikina yake,kin san ina buƙatar hutu da kwanciyar hankali da dogon nazari akan aikina, menene dalilin da ya sa kike so ki ƙara ba ni ciwon kai ne?

A tunanina ke ma mai taimaka min ce na samu nasara akan aikina, menene dalilin da ya sa ke ce kike saka ni wasa da aiki?

Look Nimra,akwai gobe,akwai jibi,akwai sauran kwanaki,za mu iya zama mu yi maganar da kike so,amma yanzu bacci ya kamata na yi please "

Nimra da take jefa masa wani kallo ta ce"to kai da kake buƙatar ka kwanta ka huta me ya haɗa ka da yaro karami? meyasa ba ka bar shi a wajen mai rainonsu ba?tun farko na menene alaƙarka da yaron da kake ƙoƙarin fifita shi akan kowa?"

#Nusy_bee

Page 29

Kallonta kawai Haisam yake yi a wulaƙance har ta gama jero masa waɗannan tambayoyin, kafin ya sake kallonta ya ce"yanzu dare ya yi, kamar yadda na gaya miki ina buƙatar Hutu,duk lokacin da na samu dama sai na ba ki amsoshin tambayarki,amma kafin nan kar ki sake buga min ƙofa Please, respect yourself,good night"yana kai wa nan a maganarsa ya mayar da ƙofar ya rufe ba tare da ya sake sauraren abin da zata ce ba

Cikin dare Mubarak ya farka yana ta kuka yana kiran Mama,da ƙyar Haisam ya iya tashi yana lallaɓa shi,amma ya ƙi komawa baccin,sai kuka yake yi sosai,jikinsa ya ɗauki zafi zau,hankalinsa ya tashi sosai

Lokaci ɗaya kuma numfashinsa ya fara neman harɗewa,ƙirjinsa ya rinƙa ɗagawa sosai,dole ya shirya ya canja kaya,saɓa shi a daren ya fita da shi zuwa asibiti

A can asibitin yana zuwa likitoci suka yi gaggawar karɓarshi,kai tsaye aka ba shi gado aka tura shi emergency saboda lokacin da Haisam ya isa asibitin Mubarak ya fara kakkafewa,hakan ya tayar da hankalin Haisam sosai

Ya kai aƙalla awa guda kafin likitan da ya karɓe shi ya fito, yana duban Haisam ya ce"officer biyo ni office za mu yi magana"babu musu Haisam ya miƙe jikinsa a sanyaye,ya bi bayan likitan suka nufi office ɗin likitan

Sai da suka zauna likitan ya dube shi,a sanyaye ya ce "officer patient É—in naka bai ci abinci ba,kuma gashi akwai alamun ba'a ba shi kulawa sosai game da ciwonsa,me yake faruwa ne?"

Kallonsa Haisam ya yi a sanyaye,da farko kasa magana ya yi,sai daga baya da ƙyar ya iya faɗin "wanne irin ciwo ne haka? I'm sorry yaron baƙo ne"

Likitan ya girgiza kai ya ce "yana da matsalar asthma,kuma ta taɓa masa huhu sosai,ta kai wani mataki wanda dole sai an saka masa idanu sosai

A yanzu dai ba ya cikin matsala in sha Allah,amma ya kamata a ba shi kulawa sosai, saboda gudun matsala"

Haisam ya yi shiru,gaba É—aya kanshi a kulle,dama yaron nan yana da asthma ne ko kuma daga baya ya same ta?

Cikin jimami da tausayawa ya girgiza kai ya ce"Allah ya ba shi lafiya, shikenan,in sha Allah za'a ba shi kulawa sosai,na gode sosai doctor"doctor ya ba shi hannu suka yi musabaha sannan ya mike ya fice daga office É—in cikin yanayin damuwa

Washe gari wajen ƙarfe tara na safe aka ba wa Mubarak discharge letter, Haisam ya ɗauke shi yadda ya saba suna hira suka nufi gida

Yana shiga sashen Nanny ya samu Amna a zaune,tana ganinsu ta taso da gudu ta rungume shi tana faɗin "Daddy ban ganka ba,na duba kuma ban ga ƙanina ba,ina kuka je?"

Janye ta ya yi gefe,ya ce"ba shi da lafiya Amna, idan kina yin magana da ƙarfi za ki saka masa ciwon kai,yau me kike yi har yanzu ba ki tafi makaranta ba?"

Yar dariya ta yi ta ce"Daddy ai yau da gobe Friday muna hutun mid-term holiday,babu school"Haisam ya jinjina kai, sannan ya ƙarasa kan kujera ya kwantar da Mubarak da yake ta bin su da kallo

Nanny ce ta fito, cikin girmamawa take faɗin "barka da dawowa yallaɓai"

"Barka dai Hajiya,ya aikin,ya fama da yaran kuma?"

Nanny ta ce"alhamdulillah,ashe mutumina ba shi da lafiya haka?"Haisam ya ce"wallahi fa,ashe wai ciwonsa na asthma ne ya tashi,amma yanzu alhamdulillah da sauƙi"cikin tausayawa Nanny ta ce"ya Salam!

Allah ya ba shi lafiya ya tashi kafadunsa"Haisam ya ce"Ameen,bari na je,zan wuce wajen aiki ne "Nanny ta ce"to Allah ya bada Sa'a yallaɓai "ya ce "Ameen "ya fice daga sashen

A gaggauce ya kammala komai ya fito cikin shigar suit baƙaƙe,sai addu'a yake yi Allah ya sa kar ya haɗu da Nimra, don ya makara,amma ina!

Yana fitowa suka yi kiciɓus,ya ja baya a firgice,daga baya ya ƙaƙaro murmushi yana faɗin "good morning Nimra "

Kallonsa kawai take yi tana nazartarsa, fuskarta a É—aure ta ce"good morning,Ina zuwa haka?"

Kai tsaye ya ce"aiki mana!ko kin manta yau ina da zuwa wajen aiki?"

Gyara tsayuwa ta yi tana yi masa wani irin kallo ta ce"ka san da haka ai ka ƙi kwana a gida,gashi ka yi min alƙawarin za mu yi magana da kai, meyasa yanzu ka zama mai alƙawari da saɓawa ne?"

Sauke ajiyar zuciya ya yi ya ce"yaron da muka zo da shi ne babu lafiya, shiyasa na kai shi asibiti"

"Allah ya ba shi lafiya,ina fatan ka mayar da shi ga iyayensa,tunda ka ga É—aukar alhaki ne barinsa a hannun wani a wannan halin,bayan ga iyayensa"

Kallonta ya yi fuska a É—an É—aure ya ce"yana nan,da wani abu ne?"

Taɓe baki ta yi ta ce"a'a,babu komai,kawai dai na yi mamaki ne, saboda Mamie ta ce har yanzu baka ce mata komai game da zaman yaron a gidan nan ba"

Haisam ya tsare ta da idanu ya ce"okay zuwa kika yi kika tambaye ta Kenan?"shiru ta yi kanta a gefe tana taɓe baki,ya yi ƙokarin sauke temper ɗin sa ya ce"bana son ki rinƙa yi min irin haka,tunda ni da kaina na ce zan gaya miki ki jira na gaya miki, meyasa kike yin abu tamkar wadda bata yi karatu bane?ko yaron nan akanki yake da zama ne?"

"I'm sorry "ta faɗa a daƙile,ya ce"sai na dawo, yanzu zan tafi aiki"yana kai wa nan ya kewaye ta ya wuce ya bar ta a wajen

Bin shi ta yi da kallo fuska a ɗaure, kafin ta koma cikin gida tana taɓe baki,ranta a ɓace, don haka kawai take jin ta tsani yaron,kuma bata yarda da zamansa ba,tana jin akwai ayar tambaya

Kai tsaye ta wuce sashen Hajiya Mamie, wadda itama take nata shirye shiryen don tafiya aiki,tana shiga sashen bata yi wata-wata ba ta faÉ—a É—akin yayar tata tana huci

Kallonta Hajiya Mariya ta yi, fuska a É—aure ta ce"ya dai?

Ya za ki faÉ—o min daki haka kamar wata karamar yarinya?"

Nimra tana huci ta ce"Aunty ki tambaye shi inda ya samo yaron nan, bashi da niyyar gaya min, kuma wallahi zuciya ta fara raya min wata ya yiwa ciki ta haifar masa,don dai gashi kin ce Æ´a É—aya suka haifa shi da tsohuwar matarsa,gata nan Amna "

Shiru Hajiya Mariya ta yi ba tare da ta yi magana ba,sai cigaba da gyara daurin ɗankwalinta da ta yi,sai da ta gama ta juyo tana kallon Nimra da saura ƙiris ta fashe saboda takaici,hankali a kwance ta ce "ina fatan dai ba shirmen naki kika je kika yi masa ba ko?

Menene abin da zai dame ki akan ƙaramin yaron da har yanzu ba ki da tabbacin Wanene shi?"

Nimra cikin ɓacin rai ta ce "shine abin da yake damuna aunty,ya gaya min mana idan yana da gaskiya,ita kanta Amna bana jin zan iya riƙe ta ballantana wani yaro da aka samo a kwararo,tsintacciyar mage"

Hajiya Mariya ta ce"ai kuwa idan da irin wannan zuciyar za ki zauna da namiji ina mai tabbatar miki ba za ki taɓa cin riba ba, ita mace ma da aka santa da kissa? da ace hakan kika yi masa da tuni ba'a wuce wajen ba?kina tunanin wannan rigimar da kika ɓallo da ita zai biye miki ne ko zai ji tsoronki?

To ba'a yiwa namiji haka,ki gyara yadda za kiyi mu'amala da shi,kar ki manta matsayin sa na mijinki ma gobe,kuma har yanzu neman soyayyarshi kike yi bai kai ga amincewa ɗari bisa ɗari ba,har yanzu abubuwan da za su faranta masa za ki koyi yi,ba wanda zai baƙanta masa ba

Idan kina da hankali kamata ya yi ki kwantar da kai akan batun yaron nan,ki ja shi a jiki,da kanshi zai sanar miki da ko wanene shi,ai nima ba son zama na yi da shi a gidan nan ba,amma da na kwantar da kai gashi nan ke shaida ce, yadda na mallake ubansa "

Nimra ta jinjina kai ta ce"I will try Aunty,da farko raina ne ya kai ƙololuwar ɓaci,amma yanzu na sauko,zan yi amfani da dabarunki in sha Allah"
Chapter 36 · 0% Book details