← Book details Gadar Tsautsayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 51

Sashe 1

Gadar Tsautsayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

💫❣️*GADAR TSAUTSAYI*💫❣️

✍️Alƙalamin Nusaiba Ibrahim Rimi (Nusy bee)

Marubuciyar;

Matar khalees
Barrister Hibba
Siraɗin uƙuba
Kaddararmu ce ta zo a haka
Masarautar Kaizur

And now

GADAR TSAUTSAYI

SANARWA!

Littafin GADAR TSAUTSAYI ƙirƙirarren labari ne,ga duk wanda ya hali ko suna ko gari ya zo daidai da shi,to a rashin sani ne🙏

GARGAÆŠI!

Littafin GADAR TSAUTSAYI mallakin Nusaiba Ibraheem Rimi (Nusy bee)ne,ban amince a chanja ko a juya min littafi na ta kowacce fuska ba

Haka nan ban amince a karanta min shi a YouTube channel ba sai da izini na

*BOOK ONE*

Page 1

*DSS HEADQUARTERS,KANO STATE, NIGERIA*

Ƙaton office ya yi shiru tamkar babu wani mahaluki a ciki,baka jin ƙarar komai sai na kaɗawar AC ɗin da sanyinta ya wadaci katafaren office ɗin,tamkar dai babu wani mahaluki a cikin office ɗin

Sai dai mutane ne sun kai goma sha biyu a zaune a jere akan kujerunsu, waɗanda suka kasance manya manyan masu riƙe da muƙami kala-kala a fannin nasu na ƴan sanda,ɗaya daga cikinsu, wanda ya kasance shine shugabansu,wato S.D Ibrahim Haruna yalwa yana tsaye yana fuskantar su fuskarshi babu alamun walwala,da alamu shine cheif officer ɗinsu,kuma yana yin wani bayani ne suna saurara

Sake jan numfashi ya yi, cikin ɓacin rai ya cigaba da magana

"Wannan abun kunya ne a gare mu,a ce wai wannan Æ´arinyar da da yawanmu mun haife ta amma ta gagare mu a cikin garin nan

Gaba daya ta lalata mana gari,ta lalata mana matasa, lafiya ƙalau zata yi order na kayan maye ta shigo da shi Nigeria,ta rabawa distributors dinta ta koma inda ta fito,amma an rasa wanda zai iya kama ta a cikinmu?

Me hakan yake nunawa kenan?ba mu da amfani ko yarinyar bayanmu ta fi ƙarfinmu?

Na gaji da ji da ganin gazawarmu hukumarmu akan yarinyar nan, tabbas wannan gazawa da abin kunya ya yi mana yawa,kuma wannan abin kaico ne"

ÆŠaya daga cikinsu ne ya É—aga hannu cikin girmamawa, chief officer ya ba shi izinin magana, cikin sanyin murya ya ce"sir!

Yarinyar nan fa ina zargin akwai waÉ—anda suka tsaya mata a sama, shi yasa take cin karenta babu babbaka,har ta kasa kamuwa kuma ta cigaba da samun confidence na aikata abubuwan da take yi "

Cikin ɓacin rai state director ya dube shi,kai tsaye ya ce"babu wanda ya tsaya mata,ita ta tsaya da ƙafarta,kuma ta hana mu tsayawa,kuma ba zan fasa faɗin cewa mun aikata abin kunya ba,da muka gagara samun nasara akan yarinya ƙarama irinta "

Shiru office ɗin ya ɗauka kowa yana saƙa da warwara,don dai an san maganar state director gaskiya ce,shekaru biyu kenan ana chasing wannan matashiyar yarinyar amma an kasa yin komai akanta, dole su san abin yi ko hukumarsu ta zama abin dariya a wajen al'umma

A hankali ya lumshe kyawawan idanunshi ya buɗe,ya ɗaga kanshi a hankali ya kalli hoton yarinyar da yake kafe a ƙaton majigin da yake office ɗin,fara ce tas, tamkar wadda bata da alaƙa da Africa,kanta an yi kitson attachment kalar blue da ya sauka har ƙugunta,sanye take da riga da wando da ya kama ta,kanta ɗore da hat fara kalar kayan jikinta,sai jaka da ta rataya ta daidaita zamanta a gefen cikinta, idanunta sanye da bakaken glasses,amma hakan bai ɓoye ɗan ƙaramin murmushi da yake kwance akan kyakykyawar fuskar tata ba

A hankali ya ɗaga hannunsa,har yanzu idanunsa ƙyar akan hoton nata,har zuwa yanzu ya kasa gane dalilin da ya sa wannan ƙaramar alhakin ta saka hukumarsu ɗan ƙaramin hauka,kuma har yanzu sun kasa zuwa ko kusa da inda take ballantana su yi tunanin kama ta

State director ya dube shi ya ce"C.S.O HAISAM ABDULMALIK MADAKA!

Shin kana da wani hanzari ne?"

Wanda aka kira da C.S.O Haisam Abdulmalik ya miƙe tsaye cikin izza da yanayi na rashin son hayaniya, kyakkyawa ne fari,amma ba tas ba,suit ɗin da yake sanye da ita ta yi matuƙar amsar farar fatarsa

A hankali ya bi mutanen da suke zaune a office ɗinda idanu,da yawansu sun fi shi muƙami da matsayi a wajen aikinsu,a hankali ya kawar da kai, cikin yanayinsa na rashin son hayaniya ya fara magana

"Good evening Sir!

Good evening everyone!!

Ita É—in ba kamar sauran mutane ba ce,tana rayuwa tamkar a cikin iska, shiyasa kamunta zai bayar da wahala

Ko da ace babu wanda ya tsaya mata a zahiri to tabbas tana tare da masu tsaya mata a baɗini, saboda yadda take zuwa duk ƙasar da ta so,ta dawo Nigeria kuma ta cigaba da harƙallarta yadda take so ba tare da wani ya dakatar da ita ba"

S.D da ya zamo É—aya daga cikin waÉ—anda suka zubawa Haisam idanu suna ji da saurarensa,ya jinjina kai kafin ya ce"menene hujjarka na cewa akwai wanda ya tsaya mata?

Ka san kai jami'in tsaro ne, da tsayayyiyar hujja za kayi amfani don kar ka ruÉ—a kanka ka ruÉ—a mutane"

Haisam ya jinjina kai ya ce"a saboda hakan ne ma ya sa na gaza isa inda take har kwanan yau, saboda bani da wata rikaƙƙiyar hujja,amma kuma in dai ni jami'in tsaro ne na gaske watan watarana zan gano abin da yake ɓoye,don na tabbatar da cewa akwai waɗanda take yi wa aiki"

S.D ya sake jefa masa tambaya yana kallonsa"wa take yiwa aiki?

Kuma menene hujjarka?"

Kai tsaye ya ce"ba na ce ba dai yanzu,wa take yi wa aiki?zai iya zama kowa ma a ƙasar nan muddin babu Allah a ranshi,zai iya zama wani ma a cikin wannan hukumar tamu,zai iya zama a cikin ƴan siyasar ƙasarmu,kuma zai iya zama farar hula,amma kuma bincike ne zai nuna,kawai abin da na sani game da aikinmu shine,ka zargi kowa,amma kar ka ɗora laifi akan wani "
Da yawan mahalarta taron suka fara jinjina kawunansu cike da gamsuwa da bayanin C.S.O Haisam, State director ya sake dubanshi ya ce"to yanzu menene kake ganin mafita?

Me kake ganin za'a yi?"

Haisam ya shafa kanshi ya ce"a bani lokaci,zan yi bincike,kuma zan tabbatar na gano inda take kuma na kama ta da hannu na !!!"

Kusan gaba ɗaya mazauna office ɗin a zabure suka ɗago suna kallonsa, mamakin ƙarfin halinsa akan abin da 90% ɗinshi rashin yiyuwa ta fi yawa,amma C.S.O Haisam yana bayar da tabbaci akai, murmushi A.D Hamza Zubair ingawa ya yi yana girgiza kai yana kallon Haisam, cikin muryar dattako irin tashi ya ce

"Yunƙurinka da ƙwarin gwiwarka yana matuƙar burge ni jarumina

To amma wani hanzari ba gudu ba,ita wannan yarinyar dukkanmu nan a cikinmu babu wanda ya santa, ma'ana ya san wani abu akanta,babu wanda ya taɓa ganinta a zahiri,babu wanda ya san ko da sunanta,da abu ɗaya ake iya gane ta,shine haruffan N.O.C.C.M da take amfani da su, waɗanda har zuwa yanzu ba mu san cikakkiyar ma'anarsu ba, ballantana mu san yunƙuri na gaba,babu wanda ya san sunanta,babu wanda ya san inda take zaune, ballantana ya san inda zata je ko inda ta baro,a duk waɗannan,wacce alama gare ka wadda zata nuna maka wacece ita?

Ta yaya za ka iya gane ta?

Akwai aiki a gaba fa!"

Kallonsa Haisam ya yi, cikin sanyin murya ya ce"I'm sorry sir!

Ni jami'in tsaro ne,a matsayina kuma bai kamata a ce kafin na fara aiki a ce na karaya ba,kafin na shiga aikin jami'in sirri na yi rantsuwar cewa zan kare ƙasa ta,zan yi chasing mai laifi,duk wayo,duk fikirarsa don na kamo shi,don haka ina sake roƙon a ba ni lokaci,wata guda kacal,as I said,I promise,zan kamo ta na gurfanar da ita gaban hukuma "

Shiru office É—in ya É—auka na É—an lokaci, kafin S.D ya dubi Haisam,ya ce"Best of luck Haisam!

Amma yanzu wanne taimako kake buƙatar a yi maka don kama ta?"

Haisam ya rissina ya ce"godiya nake sir!

Ina son a haɗa min team na mutum shida, wadanda suke ƙwararru kuma masana aikinsu, waɗanda ba sa wasa sam da aikinsu, wadanda suka samu kyakkyawan training sune za su taimaka min akan wannan aikin "

S.D ya ce"best of luck!

In Sha Allah za'a haɗa maka su,kuma an ba ka wata guda,za mu ga ƙwarewarka,fatan alkhairi "Haisam ya rissina yana faɗin"thank you sir!

Ni kuma na yi alƙawarin zan yi duk mai yiwuwa na ga ban bayar da kunya ga hukumarmu ba"S.D ya jinjina kai cikin kulawa,sannan suka cigaba da tattaunawa,ba su juma sosai ba suka ƙarƙare taron

*RED CHINA RESTAURANT, NASSARAWA GRA, KANO STATE, NIGERIA*

Ƙarfe biyar ne na yammacin ranar talata,garin ya ɗauki sanyi da danshi sosai sakamakon ruwan da ya ɗauke ƴan mintuna kaɗan baya,har yanzu akwai yayyafi kaɗan kaɗan,ga iska mai daɗi da ke busawa tana ƙara sanyaya yanayin garin

Motar ƙirar Lexus ce ta gama daidaita parking a bakin restaurant ɗin,sai dai na cikin motar babu alamun zai fito tsawon mintuna biyar da yin parking ɗin

Lokaci ɗaya ƙofar motar ta buɗe,a hankali aka zuro ƙafafu don fitowa daga cikin motar

Daga yanayin ƙafafun kawai za'a tantance na mace ne,duk da cewa dogon wando ne a sanye a jikin mamallakiyar ƙafar samfurin jeans,sai takalmi canvas,sai dai akwai sarƙar ƙafa a ƙafar hagu, wadda ta sake bayyanawa ƙarara cewa wannan ƙafar ta mace ce

Lokaci ɗaya ta fito gaba ɗaya, matashiyar budurwa ce wadda baza ta wuce shekaru ashirin da biyar ba, kyakkyawa ce sosai,fara ce amma ba tas ba,tana da diri amma bata da ƙiba sosai

Sanye take da riga mai ɗan kauri ta kamfanin puma,sai dogon wandon jeans,kanta ta ɗaura scarp da ya bayyana gashin goshinta da ya kwanta luf,ta sanya spec da ya cinye rabin fuskarta, hannunta riƙe da ƴar ƙaramar handbag fara,kalar rigarta da scarp ɗinta

Tsayuwar kusan minti ɗaya ta yi a wajen tana kalle-kalle fuskarta babu yabo babu fallasa,kafin daga baya ta nufi cikin restaurant ɗin tana tafiya a hankali kamar mai tausayin ƙasa

Kai tsaye wani table ta nufa ta zauna, waitress ɗin wajen ta ƙaraso, cikin rissinawa ta ce"good evening Ma'am!"

Kallonta ta yi fuska babu yabo babu fallasa, kafin ta yi mata nuni da hannu, waitress ɗin ta gane me take nufi, tunda ba yau ne karo na farko da ta saba zuwa tana bayar da umarni a haka ba,ta rissina sannan ta wuce don ta kawo mata abin da take buƙata
Chapter 1 · 0% Book details