Sashe 45
Gadar Tsautsayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Alhaji ya yi murmushi ya ce"oh na gane! Æ´ar kasuwa kenan"murmushi kawai Shaheeda ta yi, Alhaji ya cigaba da faÉ—in"idan ba za ki damu ba zan iya ganin ki zuwa gobe?"sai da ta É—an yi shiru tana nazari, kafin ta ce"eh babu damuwa,turo min location É—in"daga nan suka yi sallama
Tana kashe wayar ta bawa su Oga boss labarin yadda suka yi, Oga boss ya ce "to ki je,amma fa ki yi taka tsantsan,ko ma na raka ki kawai"Shaheeda ta ce"ba sai ka je ba,nima ya kamata a ce na kai lokacin da zan iya ƙwatar kaina,zuwa anjuma in sha Allah zan je"Oga boss ya ce"to shikenan babu damuwa, Allah ya tsare,sai ki kula "Shaheeda ta ce"babu matsala "
Ai kuwa bayan magriba ta shirya ta tafi location É—in da aka tura mata, ba'a bar ta ta shiga ba sai aka yi mata iso, Alhajin ya ce a bar ta ta shigo
Ta yi mamaki mai tsanani ganin mutumin, Alhaji Sa'idu wada, ministan ilmi na lokacin,bata nuna masa a fuska ta yi mamaki ba ta gaishe shi,ya amsa yana murmushi, sannan ya sa aka gabatar mata da kayan sha,har da tukunyar shisha da ƙwayoyi
A yatsine ta kalli komai ta ɗauke kai,ta ce"Alhaji ai ni bana cikin yanayin yanzu,kai dai ka gaya min abin da kake buƙata,ma gani,idan ina iyawa na yi, idan bana iyawa kuma na kama gabana "Alhaji yana murmushi yana shafa gemunsawya ce"haba zazzafa za ki iya mana
Yanzu dai bari na fara ta kan abu na farko,an ce ke ɗin mai siyar da ƙwayoyi ce,kina da kwastamomi a hannu,don haka nake son mu yi magana,ina son a rinƙa shigo min da ƙwayoyi daga waje,har ma da cocain da sauran kayayyaki,amma ke nake so ki zama agent,idan kika yi haka zan yi miki biya mai kyau,sai adadin miliyoyin da kike so zan ba ki,kuma zan tsaya miki kar wani jami'in tsaro ya yi nasara akanki
Sai kuma abu na biyu, yarinya tun sanda na fara ganinki na ji kwaɗayinki, shine nake so idan zai yiwu a bani dama,na yi miki alƙawarin miliyoyin kuɗi idan hakan ya samu,zan mallaka miki irin gidan da kike so,mota kuwa sai wadda kika zaɓa,amma menene ra'ayinki?"
#Nusy_bee
Page 36
Wani banzan kallo Shaheeda take aika masa daga inda take zaune, fuska a É—aure, cikin fusata ta fara magana
"A harkar business ka gan ni,ka yi business da ni,idan da ace zan yi karuwanci ba sai ka gaya min ko yaudare ni da wasu ƴan kuɗin ka ba,idan kuɗi ne ko ban siyar da ƙwaya ba ina da hanyar samunsu,don haka hattara!
Ka yi abin da ya kawo ka kawai,kaya ne kake so,idan ka shirya a shigo maka ko a fitar maka da kaya,ka kashe waccan mummunar aƙidar taka to Shaheeda tana maraba da kai"ta miƙe a fusace zata fita
"A haba kyakykyawa!haba kyakykyawa!ya da haka ne?
Don Allah ki yi haƙuri,na rusa waccan maganar, na ɗauka ke ma ƴar hannu ce,amma yanzu na gane,zauna mu yi magana"tana daga tsaye ta ce"yi maganarka ina jin ka"ya marairaice ya ce"don Allah ki yi haƙuri ki zauna"babu musu ta zauna tana aika masa da wani mugun kallo
Yana murmushi ya ce"haba kyakykyawa!don Allah ki saki fuskarki, wallahi ba kya yin kyau a haka,haba kyakykyawa "É—an sakin fuskar ta yi,amma bata yi murmushi ba,ta sake faÉ—in"yi bayani,ina jin ka"babu musu ya fara bayani
"Akwai kayana a Columbia,ina so su shigo Nigeria,kuma ke nake so ki shigo min da su, don Allah bana son a samu matsala "
Babu bata lokaci ta ce"consider it done in sha Allah, menene ƙimar kayan?
Kuma menene kasona na abin da zan samu?"
Alhaji ya ce"kayan sun kai ƙimar dala million hamsin,kuma kina da 5%"yatsina fuska ta yi tana yi masa kallon hadarin kaji,ta ce"albarka!"
"To kashi goma idan kin amince "miƙewa ta yi tsaye ta ce"idan ka shirya biyan kaso ashirin da biyar sai ka yi min magana "ta kama hanya don ficewa daga parlourn
"A haba yarinya ki duba mana!
Kashi ashirin da biyar ai da yawa fa,ribar me zan samu kenan?"juyowa ta yi tana kallonsa ta ce"Ni baka duba tsananin kasadar da zan É—auka ba?
Sai kai akan kuɗinka?to yadda kake son kuɗi haka na fito neman kuɗi,ya rage naka ka saki kuɗi ka samu kuɗi,ko ka riƙe kuɗi ka huta"ta juya hankali kwance zata fice daga parlourn
"Na yarda,na yarda,haba ranki ya daɗe"babu ɓata lokaci ta juyo ta samu waje ta zauna tana fuskantar shi
Da kanshi ya tsara mata yadda abubuwa za su tafi,kuma bata tafi ba sai da ya tura mata Miliyan ashirin na cin chewing gum
Bayan ta koma gida ta sanar da su Oga boss yadda suka yi,sun yi farin ciki sosai, Oga boss ya sake jaddada mata cewa ta kula, saboda irin su ba su da tabbas
Alhaji Sa'idu wada da kanshi ya haɗa ta da mutanen da za su taimake ta,wasu daga cikinsu yan sanda ne,har ma da ma'aikatan hukumar DSS,daga kan state directors zuwa kan masu muƙamai, ba'a maganar ma'aikatan customs da immigration wadanda suka zama sune manyan yaranta wajen shigar da kayan
Cikin nasara kuma ba tare da ɓata lokaci na ta fara aiwatar da aikinta,sai dai kamar yadda Oga boss ya bata shawara ta sauya sunanta daga Fatima zuwa ROXY
Banda waÉ—anda suka santa a baya,da waÉ—anda suke jikinta babu wanda ya san asalin sunanta,a tsawon shekara É—aya da fara wannan sana'ar tata ta hadu da mutane da yawa,ciki har da babban yaronta David, wanda yake taimaka mata a kasuwancin nata
Ta koyi dabaru kala-kala na rayuwa da gujewa jami'an tsaro,bayan ta tabbatar ta tsaya da ƙafafunta har gida ta je ta sanar da Alhaji Sa'idu wada cewa ta gama yi masa aiki,itama yanzu ta kama gashin kanta
Duk yadda ya so ta koma ta cigaba da yi masa aiki ta ƙi,hakan ya fusata Alhaji Sa'idu, babu ɓata lokaci ya bayar da hotonta a kama masa ita,don a lokacin ya kasa tantance wanne suna ne asalin sunanta
Ɗaya daga cikin jami'ai, wanda ya kasance ita yake yiwa aiki ne ya kira ta ya sanar da ita,hakan ya sa ta yi murmushi,kuma ta ƙudurce a ranta dole ne ta sake shiri
Shirin farko da ta fara yi shine gayawa duniya da take yi a sirrance cewa babu mai iya kama ta, saboda ta yi dukkan wasu dabaru don gujewa hakan,ta fara amfani da harufan NOCCM, waÉ—anda babu wani abu da suke nufi sai NO ONE CAN CATCH ME,kuma ta yi farin ciki ganin jami'an tsaro sun mayar da hankali don gane abin da haruffan suke nufi,ita kuma ta mayar da hankali don abin da yake gabanta
Daga nan barin ƙasar ta yi,ta koma Spain, inda ta cigaba da sana'arta cikin kwanciyar hankali ba tare da wata matsala ba
Sai da ta shirya cif sannan ta dawo Nigeria,ta saka idanu sosai akan dukkan wani jami'in tsaro da zai fara bincikarta,daga an fara bincikarta zata saka a bincika mata wanene jami'in,zata shiga rayuwarsa ta yi masa barazana,da haka zai yar da case É—in saboda tsoron abin da zai faru gare shi ko ga iyalinsa
A ɗaya ɓangaren kuwa bata fasa saka idanu ga ɗanta ɗaya tilo ba,kuma bata fasa zuwa wajen kantamemen gate ɗin MALIYA ESTATE ba,wani lokacin idan ta ga fitowar Abba ko Ummeenta tana yin kuka sosai, tana tsananin son su,amma yanzu sun yi mata nisa
Amma har zuwa yanzu zuciyarta baya karaya ba,kuma duk yadda take jin damuwa bata taɓa barin wani ya sani ko ya gane,ta cinye abarta ita kaɗai,sai idan abu ya dame ta ta sha kwayoyinta ta yi bacci
Da haka CSO HAISAM ABDULMALIK MADAKA jami'in tsaro na hukumar DSS ya shiga rayuwarta ya fara farautarta,da farko bata ɗauki case ɗin sa da zafi ba,ta ɗauka shi ɗin gama garin jami'i ne kamar sauran jami'an tsaron da suke farautarta,sai da ta yi kyakkyawan bincike akansa ta gane yadda take hatsabibiya haka yake da hatsabibanci,har ma ya fi ta, hankalinta ya tashi,ta yi dukkan mai yiwuwa don ta guje masa,ta yi masa barazana da iyalinsa,ta yi masa da ranshi amma duka a banza,a ƙarshe sai da ya san yadda zai yi ya ga bayan aikinta da ta gina tsawon shekaru uku
Wannan shine labarin FATIMA SHAHEEDA, wadda a yanzu take amsa sunan ROXY saboda yanayin aikinta ko sana'arta, abubuwan da suka faru da ita har ta tsinci kanta a cikin wannan halin
💫
Shiru ya biyo baya na yan sakwanni,kan Haisam a ƙasa,gaba ɗaya jikinsa a mace, kafin a hankali ya ɗaga kai ya kalle ta,sassanyan murmushi ta sakar masa,ya ɗaga gira alamar ya dai?ta girgiza kai ba tare da ta yi magana ba,sun ƙara jan wasu seconds ɗin kafin ya ce"na san lokacin da na je kama ki a Spain akwai wanda ya sanar da ke batun tafiyar a tawagata, wanda shine yake ba ki bayanai akaina da yunƙurina,shin za ki iya gaya min wanene shi?"
Sauke numfashi ta yi tana kawar da kai gefe, kafin ta ce"I'm sorry to say,ba zan iya gaya maka sunansa ba, saboda bana son ya rasa aikinsa,idan haka ta faru kuma ban san wanne irin criminal gobe zata haifar ba,ka bar shi a yadda yake,duk bala'i bai isa ya fito ya yiwa ƙasa zagon ƙasa Kamar yadda na yi ba"
Haisam ya ce"babu abin da zai samu aikinsa,asalima manya ba za su ji ba, maganar tsakanin ni da shi ne kawai"
Shiru ta yi tana kallonshi,ya yi murmushi ya ce"nima ba ki yarda da ni ba ko?"girgiza kai ta yi ta ce"A'a, kawai ina so na tabbatar da gaskiyarka ne, kamar yadda na faÉ—a maka bana fatan wani ya rasa aikinsa ta dalilina
Amma zan gaya maka,ba kowa bane sai abokin aikinka Awwal!
Ya daɗe yana yi min aiki,in fact,yana daga cikin yaran da state director na Kano State ya saka don su rinƙa taimakona "
A razane Haisam yake kallonta, kafin da ƙyar ya furta"You mean? State director da haɗin bakinsa a wannan badaƙalar?"
Jinjina kai ta yi, sannan ta ce"akwai bakinsa, amma shima Alhaji Sa'idu wada yake yiwa aiki,kuma bijirewar da na yiwa Alhaji Sa'idu ita ce ta janyo ya kware min baya ya fara farautata"
Haisam ya jinjina kai ya ce "Wanene ya ba ki dabarun gujewa jami'an tsaro?"