Sashe 21
Gadar Tsautsayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Allah ya taimaka ya faɗa hannun na gari, alhamdulillah uwar riƙon nashi sai da ƙyar ta yarda da ni tunda na ambaci ɗaukar yaron na zo yi, sai da na yi mata bayanin wacece ke,da manufar da ta sa kika jefar da yaron ba ta kirki ba ce, sannan ta ba ni shi,a yanzu kuwa ba za ki sake ganinsa ba,zan ɗauke shi na mayar da shi inda zai yi rayuwa irin wadda kike yi,ko kina ganin za ki yiwa Allah wayo, shiyasa kika ɗauke ɗanki kika kai shi matsera wajen tarbiyya,ke kike lalata na wani?kina son shi har haka kika kasa tsayawa ki yi masa tarbiyya?a maimakon haka ma sai kika canja suna,kika canja addini don ki fi jin daɗin aikata ɓarnar da kike so?
Ina jiran ba'asi Shaheeda!!"ya ƙarashe a ɗan tsawace, ranshi a ɓace, saboda ya ji zafin yadda ta wulaƙanta rayuwar yaronta fiye da komai
#Nusy_bee
Page 17
A hankali ta sunkuyar da kanta,hawayen da ya cika kwarmin idanunta suka zubo, cikin wata iriyar murya mai cike da raÉ—aÉ—i ta fara magana
"Da ace kuskuren da na aikata a baya an same ni ne da irin wannan tambayoyin, ba'a watsar da rayuwata an ƙyamace ni ba,da wataƙila yanzu ina rayuwa a cikin farin ciki, wataƙila a gidan aurena, tare da ɗana,ko ma ƴaƴana,da rayuwata bata kasance cutarwa ga wani ba,da ta kasance mai amfani da alkhairi ga rayuwar mutane
Amma ina!bakin alƙalami ya bushe,abin da alkalamin ƙaddara ya rubuta akaina babu makawa sai ya faru, wannan abu ne wanda ya kasance a rubuce tun kafin zuwana duniya
Batun Mubarak kuwa,ban rabu da shi don bana son shi,ko don na fifita rayuwata ta duniya akanshi ba,asalima Mubarak shi kaÉ—ai ne abin da nake da shi a duniya wanda nake tunawa ina da shi raÉ—aÉ—in da zuciyata take yi ya ragu,don haka wannan hanyar ita kaÉ—ai ta rage min da zan tseratar da shi daga halaka
Sannan maganar addini kuma,ban taɓa tunanin canja addini ba, don na canja suna hakan ba yana nufin na chanja addini ko ina wasa da nawa addinin ba
Tabbas ina shaye-shaye,amma ba na wata alfasha bayan wannan,asalima na tsani aikatawa,shaye-shayen da nake yi ma ina yi ne don na gusar da damuwar da nake ciki ne,kuma a silar hakan na fara safarar miyagun ƙwayoyi "
"Menene gaskiyar Maganar da ake faÉ—a na cewa kina yin Safarar muggan makamai?
Ban ji kin yi batun ba"
Kai tsaye ta ce"wannan ba gaskiya bane,amma idan ba ka yarda ba gani a hannunku,za ku iya bincike akaina "
Haisam ya ja numfashi sannan ya sake faÉ—in"har yanzu ban ji wani dalili mai girman da zai iya sakawa ki aikata irin wannan mummunan aikin ba Shaheeda,ko ma me kika aikata ba za ki iya neman yafiyar iyayenki ki koma gare su ba"
Ga mamakinsa sai ya ga ta yi ƴar dariya,ta dube shi sosai ta ce"na san mahaifiyarka ta rasu Allah ya ji ƙanta,amma mahaifinka yana raye,shi ɗin ya kasance yana zama ya yi shawara da kai,ya baka dama ka kare kanka idan ka yi masa kuskure ko ka zo da wani baƙon abu,to ka ƙaddara ba kowanne uba bane yake kasancewa irin mahaifinka "
"Still I can't get you Madam! tukunna ma,duk me ya kawo wannan matsalar?"
A hankali ta ce"ba komai bane ya yi silar tarwatsewar farin cikina sai faɗowar ARNOLD cikin rayuwata, wanda ya zama GADAR TSAUTSAYI da ta jefa ni ga tafkin ibtila'in da har yanzu nake ninƙaya a cikinsa"
Kallonta yake yi sosai,ya ce "wanene kuma Arnold?
Kuma menene ya haÉ—a rayuwarki da shi?"
Lumshe idanu ta yi ya buÉ—e tana kallonsa, kafin ta ce"kana da lokaci?"
Ya jinjina kai ba tare da ya yi magana ba,itama ta jinjina kai ta ce"good!
To saurari labarin Shaheeda;
*WAIWAYE.........*
*WASU SHEKARU A CAN BAYA*
Hausawa na cewa dare mahutar bawa,amma ga Shaheeda wannan maganar a yau dai ba haka take ba, wannan daren ya kasance dare ne mai cike da É—imbin alkhari ga Shaheeda, daren farin ciki da annashuwa saboda alkhairin da zai same ta gobe
Kasancewar ta yi nasara a jarrabawarta ta kammala secondary school,bayan an yi daga da Alhaji Yusuf da beloved yayanta Muyassar,a ƙarshe dai ya yarda zata je Belgium don cigaba da karatunta na tertiary inda zata karanci software engineering, course ɗin da take so kamar ranta
Ummeey sam bata yi farin ciki da wannan zuwan ba,amma ko da ta yiwa Abba Magana faÉ—a ya hau ta da shi sosai,har sai da ta yi nadamar yi masa magana
Ta shiga damuwa sosai, saboda bata da abokin hira a gidan sai yarta da mijinta da ba ita kaÉ—ai ce da shi ba,to yanzu kuma Æ´ar tata ma zata sake yin nisa da ita
Amma ita Shaheeda ko a jikinta,don dama akwai ƙuruciya sosai a kanta, kasancewar gobe ma zata yi birthday party ɗin da yayanta abin sonta Muyassar ya haɗa mata
Tana nan zaune tana nazari,ganin nazarin ma ba zai yi ba sai ta miƙe tana murmushi ta nufi locker ɗinta,in da ta ajiye yar ƙaramar jotter ɗinta da ta yi list ɗin yadda shagalin nata na gobe zai kasance, bisa jagorancin yayanta abin sonta Muyassar, wanda duk abin da take so sai ya yi kokarin samar mata,ko da a ce kowa ba ya so a gidan kuwa
Muyassar shi kaÉ—ai ne sanyin idanunta a gidan, kasancewar sauran al'ummar gidan suna jin haushinta saboda bayyanannen bambancin da yake tsakaninta da yaran gidan a wajen mai gidan
Kan gadonta ta koma ta kwanta,ta buÉ—e jotter É—in tana kallon kyakykyawan rubutun nata tana murmushi
"Ashe cake ɗin biyu ce ma,da babba da ƙarama,to zan gayawa yaya Muyassar ko ba'a siyo wata ba a siya min manya, don na san halin Ummeey na ba bari zata yi a kawo min cake ɗin nan ba,ba bari zata yi na yi birthday ɗin nan yadda nake so ya tafi ba
Allah ya sa dai ta bari a yi casu,don wallahi tunda ta hana kama hall na san akwai abin da bata so a yi, uhm!
Ummeeyna sai ita,ina sonki Ummeey na"ta ƙarashe maganar tana murmushi sosai
"Wai Shaheeda dama har yanzu ba ki kwanta ba?
Me kike yi haka da kika kai har yanzu idanunki biyu?"
"A firgice Shaheeda ta kalli Ummeey da ta leƙo ɗakin ta same ta a zaune akan gadonta tana murmushi tana sambatu tana kallon jotter, Ummeey bata damu da yadda take da kame-kame ba ta ce"maza a kwanta,sai da safe"daga haka ta juya ta fice daga ɗakin
Ita ma Shaheeda kwanciya ta yi tana murmushi,a hankali ta furta "zan yi kewarki Ummeeyna, Allah sarki ni,zan koma rayuwar wajen da ban san kowa ba,kuma babu wanda ya san ni,gashi kuma babu yayana Muyassar abin alfaharina,kuma uban gidan fita kunya"ta yi Æ´ar dariya tana rufe jotter É—in
Washe gari da safe Muyassar ya zo don ya kai ta super market don ta karasa siyayyar da ba'a yi ba ta birthday É—in, Muyassar ya dube ta yana faÉ—in "a'a!
Ka ga yar gatan Abba masoyiyar Ummeey,kuma ta hannun damar yaya Muyassar,ko na ce zuciyarshi"
Murmushi ta yi tana faÉ—in "capacitated babban yaya!
Jiya na yi kewarka fa, wayyo Allah yau za'a sha shagali"
"Haba shagali ai abin sai wanda ya gani, yanzu dai da me da me kike buƙata?"ya faɗa yana kallonta cikin kulawa gami da buɗe mata ƙofar motarsa
Shiga ta yi tana faɗin"mu je dai kawai,sai na ga wasu abubuwan zan tuna,amma dai new teddy mai kyau dai kar ka manta, sannan ka roƙi Ummeey ta ɗaga min ƙafa wannan karon na sha shagalina da teddyna,da ita ma zan tafi can Belgium in sha Allah "ta ƙarasa faɗa tana fari da idanunta
Abin ya bawa Muyassar dariya,ya yi dariya sosai yana kallonta,ya ce"oh Allah!
Wato dai duk inda ƙwaila take sai ta nuna hali,ina ke ina ɗaukar teddy bear har wata uwa duniya saboda Allah?"
Kwaɓe fuska ta yi tana harararshi, ya yi ƴar dariya,ya sani ta tsani ya ce mata ƙwaila,a fusace ta ce"yau nake cika 16 years amma kana ce min ƙwaila,na kammala secondary school zan tafi University kai ma dai ka san na wuce ƙwaila ko?"
Murmushi ya yi yana faÉ—in"au!
Na manta fa,hakane ko?ashe an kusa shiga class, inyeeeee "murmushi Shaheeda ta yi tana fari,yadda ta yi farin ya ba shi dariya,amma sai ya yi fuska,don ya san idan ya yi dariyar zata iya saka masa rigima
Sun yi sayayya sosai,wani abin ma shine yake cewa ta É—auka, kamar yadda aka saba yau ma sai ya ja ta don biya,a raunane ta kalle shi ta ce"yayana ka ga kudin da yawa, kuma jiya Abba ya bani kuÉ—in amfani,why not ba za ka biya rabi ba nima na biya rabi?"
Kallon banza ya watsa mata sannan ya wuce ya biya kuɗin ba tare da ya yi mata magana ba,aka fito musu da kayansu niƙi-niƙi
Suna fitowa ta daka tsalle ta rungume shi tana murna tana faɗin"yayana na gode,na gode sosai, Allah ya biya ka"lumshe idanunshi ya yi ya buɗe,a hankali ya raba ta da jikinsa, saboda halin da ya ji tana ƙoƙarin ta jefa shi,a hankali ya ce"ke fa ba kya girma cutie,wuce mu tafi gida,kin ga lokaci yana ƙara ƙurewa"
Bata yi musu ba ta faÉ—a mota,ya tayar suka wuce gida
Taron ya ƙayatar sosai, don Muyassar ya tsaya mata,duk da a babban parlourn Alhaji Yusuf (Abba)aka yi, Muyassar ɗin ne kawai ya halarta sai ƙawayenta da ƴan makarantar su,amma babu wasu ƴan dangi ko ɗaya da suka halarta
Ana daf da tashi daga taron ne Arfa ƙanwar Hajiya Ruƙayya ta zo,dama wani lokacin ta kan zauna a gidan,tana fakewa da wajen yayarta ta zo,amma a zahiri ba haka abin yake ba,wajen Muyassar take zuwa,don ta ganshi,don shi ko kallon banza ba ta ishe shi ba ballantana ya kula ta
Kai tsaye kuma babban parlourn da ake gudanar da shagalin birthday É—in Shaheeda ta nufa,tana shiga ta bi parlourn da kallo,gashi nan an yi decorating wajen,har da golden numbers 16
Taɓe baki ta yi,kai tsaye ta nufi wajen Muyassar da yake tsaye da Shaheeda suna yanka cake ta biyu suna murmushi,tana isa wajen hankalin kowa ya dawo kanta
Ta ɗan yi ɗan murmushin yaƙe tana kallon Shaheeda da ta zuba mata idanu ta ce"happy birthday!"