Sashe 37
Gadar Tsautsayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Better!"a cewar Hajiya Mariya, sannan ta É—auki handbag É—inta da labcoat É—inta,ya dubi Nimra ta ce"sai na dawo"ta fice daga É—akin
*HAISAM*
Zama ya yi a office ɗin sa yana nazarin abubuwa da yawa,na farko labarin Roxy,bata kai ƙarshen labarin ba,amma daga yadda ya ga yanayinta har ya fara fargabar abin da zata ce masa a gaba, musamman game da iyayenta da danginta
Ga lamarin auren da ta yiwa kanta,ya yarda laifinta ya fi yawa,amma tun daga farko ya ga laifin iyayenta,sam sam bai kamata su nuna mata ƙarfi a wajen hana ta auren masoyinta da liƙa mata auren cousin brother ɗin nata ba
Sai maganar rayuwarta tare da Arnold,ta ba shi tausayi sosai, musamman yadda ta yarda da Arnold amma ya yaudare ta,kuma hakan ya karya mata zuciya sosai,a ƙarshe duk da yadda ya zama a gare ta ya kasance abin dogaronta,ya mutu ya bar ta
Ko daga nan ta tsaya ya samu amsar dalilin da ya sa ta zama Æ´ar ta'adda, tunanin mace ba shi da tsawo sosai,kai ko da ace namijin ne mummunan halin da ta shiga daga wannan zuwa wannan zai iya sauya halayensa zuwa wani mutum dabam
Yana nan zaune Musa ya shigo bayan ya yi masa izini,ya É—aga kai yana kallon Musa,,Musa ya gaishe shi cikin girmamawa yana sara masa,cikin sanyin murya ya ce "ka haÉ—a min zama da team É—in mu da muka yi operation na kama yarinyar nan"
"Sir wacce yarinya kenan?"
Haisam ya sauke numfashi ya ce "Shaheeda"
"Ko dai Roxy yallaɓai?"rai a ɗan ɓace ya ce" ba dai ka gane ba?
To sai ka yi min abin da na saka ka ko?"babu musu Musa ya sara masa, sannan ya fice daga office É—in
Bayan mintuna goma suka hallara gaba É—aya su shidan, Haisam ya yi shiru yana nazarin ta inda zai fara
Dakewa ya yi ya fara magana ganin gaba ɗaya sun ba shi attention,ya fara da faɗin "a ƙarshe dai ga Roxy ta shiga hannunmu,ina godiya da dukkan waɗanda suka taimaka min ma kama ta
Sannan abu na gaba,a cikin mu shidan nan akwai wanda Roxy ta siya don ya faɗa mata sirrinmu, kuma ta yi nasara,ta siye shi ya fitar mana da sirri,a ƙarshe ta yi nasara akaina a karo na farko,sai dai a karo na biyu ban yi wautar sanar da kowa shirina ba,kuma cikin hukuncin Allah sai gashi na kama ta ba tare da wata matsala ba
Ban damu da sanin wanene baren a cikinmu ba, abu daya zan faÉ—a muku kawai, shine ko ma wanene ya kiyayi gobe, saboda muddin zai cigaba da fitar min da sirri to tabbas zan gano shi watarana,kuma abin da zai faru zai ba ku mamaki
Na sallame ku"yana kai wa nan ya mike ba tare da ya sake kallonsu ba ya fice daga office É—in
Sai da ya kammala abubuwan da zai yi,da lussafe-lissafensa sannan ya miƙe ya fice daga office ɗin, kai tsaye ya faɗa mota ya nufi jail ɗin da aka rufe Roxy
Yau ma dai kamar kullum sai da ya nuna ID card É—insa sannan aka shigar da shi,aka fito da Roxy wadda gaba É—aya ta yi wani irin sanyi
Kallonta ya yi sosai, cikin kwantar da murya ya ce"kuka kika yi?"
A hankali ta É—ago ta kalle shi, cikin sanyin murya ta ce"bani da dalilin kuka ne?"
Haisam ya ce"of course kina da dalilin yin kuka,amma sai nake ganin kamar kukan ba mafita bane ko?
Murmushi ya yi a sanyaye tana girgiza kai, sannan ta ce"Shi kadai ne makami na a yanzu,akwai lokacin da nake ƙyamatarshi, saboda na ɗauke shi a matsayin raunin da zai karya ni,amma a yanzu kuma shine maganina, shine babban makamin da nake da shi"
Haisam ya girgiza kai ya ce"Roxy bai cancanci ta karaya irin haka ba"
Kai tsaye ta ce"Roxy dama can a karye take,dakiya da gujewa rauni ne ya sa ake yi mata kallon jaruma "
Haisam ya ce"yanzu kuma bai kamata ta rungumi raunin nan ba kuwa, saboda....."
"Saboda me?
Rayuwarta ta tsaya ko?ai na sani,babu babbar asararriya a duniya number É—aya kamar Roxy, saboda......"
"Zan iya samun cigaban labarin Roxy?"ya yi azamar katse ta da faÉ—in hakan yana kallonta,a ranshi yana danne yanayin da ta fara jefa shi
Murmushi ta yi,ta ce "menene abin jan hankali a labarin Roxy ne har haka da ya kasa gundurarka?"
Gyara zama ya yi, shima yana murmushi ya ce"Tun da na buƙace shi ke ma kin san dole zai yi min amfani,ke dai ki cigaba kawai"babu musu ta jinjina kai ta ce" haka ne kuma,to ga cigaban labarin Roxy........"
#Nusy_bee
Page 30
💫
A Murtala Muhammad airport da ke Lagos jirginsu Shaheeda ya sauka, tunda jirgin ya sauka gaban Shaheeda yake dukan uku-uku, tsananin firgici da tashin hankali ya bayyana akan fuskarta
Ta san su wanene iyayenta, musamman mahaifinta,ta san yadda yake da zafi,kuma ba ya É—aukar wargi,tana tsananin fargabar abin da zata je ta tarar
Hotel É—in da suka kama lokacin da za su tafi Spain ita ta sake komawa,ta kama É—aki don ta huta, gobe ta bi jirgi zuwa Kano
A wannan daren ko sau ɗaya bacci bai kawo mata farmaki ba,banda tashin hankali da fargaba, sai tunane-tunane da suka cunkushe mata ƙwaƙwalwa,a ranta tana addu'ar Allah ya ɗora ta akan Abba, Allah ya sa hukuncin da zai yi mata ya zamo da sauki
A ranar dare ya yiwa Shaheeda tsawo,duniyar ta yi mata ƙunci, fargaba ta mamaye mata zuciya, tunani da taraddadi suka cunkushe mata ƙwaƙwalwa,ji take yi a duniya ta fi kowa shiga mawuyacin hali,kuma ta fi kowa shiga tashin hankali
Washe gari ma ko ruwa ta kasa kai wa bakinta,jiki babu ƙwari ta yi booking jirgin da zai nufi Kano,kuma ba tare da ɓata lokaci ba suka hau zuwa kano
Ta kai a ƙalla awa ɗaya tana nazarin yadda zata tafi gida, kafin daga baya ta yi shahada kawai ta tafi, bayan ta sauka ma taxi ta hau zuwa Maliya estate,tana tafiya a taxi ɗin banda matsanancin tunani babu abin da take yi,sai share hawaye
A bakin maliya estate ta sauka daga taxi É—in,ta sallame shi sannan ta ja akwatinta,amma ta kasa motsawa ko nan da can
Kamar daga sama ta ji Muyassar yana faÉ—in "Shaheeda!
Shaheeda daga ina haka?"
A firgice ta ɗaga kai tana kallon Muyassar da yake ƙare mata kallo,jikinta babu inda ba ya rawa,amma duk da halin da take ciki babu abin da ta ji kunya da muzanta irin ganin ta da ya yi da tsohon ciki, musamman da ta kula idanunsa suna kan cikin nata yana kallonta da wani irin yanayi
Da ƙyar ta lalubo nutsuwa,muryarta na rawa,kanta a ƙasa ta ce"ina kwana yaya Muyassar"
Maimakon ya amsa sai ya ce"tsayuwar me kike yi anan?
Wuce ki shiga ciki mana"shiru ta yi bata tanka ba,ya sake faÉ—in "wuce mu je na kai ki,kin zo kina tsayuwa a nan"ya wuce gaba,ta bi bayanshi jikinta a sanyaye,suka nufi cikin gidan
Shaheeda ta sake muzanta ganin duk ta inda suka wuce sai an kalle su kafin su isa sashen Ummeey,suna zuwa ta ja ta tsaya tana lafewa a jikin bango, Muyassar ya kalle ta yana faÉ—in "ya dai?
Ki wuce mu shiga ciki mana"
Hawaye suka zubo mata,ta ce "ka bar ni a nan kawai,ina tsoron Ummeey"
Yar dariyar takaici ya yi,ya ce"Shaheeda kenan!
Wasu abubuwan kafin mu aikata su za muyi tunanin yadda makomarmu zata zama ba sai mun aikata ba, yanzu misali, menene amfanin wannan abu da kike yi yanzu?
Ummeey mahaifiyarki ce,ke kaÉ—ai ta mallaka wadda zata kalla ta ji sanyi na cewa eh tana da zuri'a a duniya,amma ba ki tuna hakan ba kika yi abin da zata yi kuka, why Shaheeda?"
Ita dai Shaheeda bata tanka ba, sai kukanta da ya fara tsananta, Muyassar ya kwantar da murya ya ce"alright,komai ya wuce, na san ba za ki sake irin wannan aikin ba, Allah ya kyauta ya kiyaye gaba,tashi mu wuce ciki"babu musu ta miƙe, jikinta duk babu ƙwari suka nufi cikin sashen Ummeey
Ummeey tana zaune a parlour tana shan tea a hankali sai ta ji sallama,a gigice ta ɗago tana kallon Shaheeda wadda gaba ɗaya ta fita hayyacinta, Shaheeda ta kasa jurewa ta taho da gudu ta faɗo jikinta tana kuka mai gunji, Ummeey bata yi wani yunƙuri ba sai kukan da ta fashe da shi ita ma, tana bin tilon ƴar tata da kallo, wadda gaba ɗaya ta fice a hayyacinta tamkar ba dirarriyar ƴarta Shaheeda ba,mai kazar kazar da yawan surutu
Yanzu duk ta yi sanyi ta canja,ta rame sosai,mafi girman tashin hankalin da ta gani a tare da ita shine tsohon cikin da yake jikinta
"Ummeey don Allah ki yafe min!na yi kuskure!na bijirewa maganarki,a ƙarshe ban samu sakamako mai kyau ba,don Allah Ummeey ki yafe min,don Allah Ummeeyna"kunnuwanta suka ɗauko mata sautin Shaheeda cikin gunjin kuka
Da ƙyar Ummeey ta iya ɗaga harshenta ba tare da ta kalli Shaheeda ba,ta fara magana cikin karayar zuciya
"Shaheeda! Allah ne shaida,a tsawon lokaci tun da na haife ki ƙoƙarina shine na ba ki tarbiyya,bani da kowa a kusa da ni daga ke sai mahaifinki,ke ce kaɗai ƙwan da Allah ya ba ni, wanda nake saka ran samun walwala daga gare ta,amma a ƙarshe a dalilinki na yi nadamar haihuwa,wasu mutanen suna kuka saboda ba su haihu ba,wasu mutanen suna alfahari da ɗaya ko da yawa da Allah ya ba su,amma ga ni ina kuka saboda na haihu,ina nadama saboda ɗaya da Allah ya ba ni, meyasa Shaheeda?me nayi miki da zafi haka?"
Kukan Shaheeda ya tsananta, cikin kuka ta sake rungume Ummeey tana faɗin"don girman Allah Ummeey ki yi min rai, Ummeey ki yafe min, wallahi na yi nadama, ba zan sake ba,don Allah Ummeey kar ki juya min baya, wallahi ina sonki Ummeey,ke ce....."a fusace Ummeey ta hamɓare ta daga jikinta tana aika mata da wani mugun kallo,hawaye bai tsaya a idanunta ba ta ce"kina so na Shaheeda?a hakan? ƙarya kike yi!!!
Da kina so na da ba ki so raina ya ɓaci ba ko yaya ne
Shaheeda da kina so na da ba ki guje ni ba,da ba ki jefa ni a cikin baƙin ciki da tashin hankali ba!