← Book details Gadar Tsautsayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 51

Sashe 33

Gadar Tsautsayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A wannan tsukin ne cikinta ya kai watanni shida,kuma a waɗannan watannin ko sau ɗaya bata taɓa yarda ta haɗa jiki da Arnold ba,shima kuma tunda ta haƙura da yin azumi ya daina karantar ta ta dole

Tuntuni suka raba É—akin kwana,yana É—akinsa itama tana nata

A wannan halin ne tana zaune a ɗakinta ta ji muryar Arnold da kamar muryar mace,da sauri ta leƙo tana kallonsu gabanta yana faɗuwa, yarinyar da ganinta baturiya ce yar asalin ƙasar Spain ɗin,kayan da suke sanye a jikinta ya tabbatar da wacece ita

Da sauri kuma a firgice ta ƙarasa inda suke tana kallon yarinyar idanunta a rufe da kishin da har yanzu bai rabu da zuciyarta ba, dukkansu tsayawa suka yi suna kallon ta, cikin harshen dutch ta ce"Arnold wacece wannan?"

Kai tsaye ya ce"ita É—in budurwata ce,akwai wani abu ne?"

Shaƙe shi ta yi ta ce "budurwarka?ko karuwarka?

Ta fice min daga gida ko na illata ta,ta fice min ko na kashe ta!"

Arnold ya ƙwace wuyan rigarsa yana aika mata da wani kallo ya ce"da gaske kike?

Ta fice miki daga gida?ko kin manta ba wajenki ta zo ba?wajena ta zo?

Ai ba don ke ta zo ba, don ni ta zo,ta zo ne don ta yi min abin da ke ba kya yi min,don haka ba ki isa ki hana ta shigowa ba"ya ture Shaheeda gefe ya kama hannun budurwarsa da sam bata ma san me suke cewa ba kasancewar ba da Spanish suke magana ba suka shige É—akinsa

Abubuwa suka sake taruwa suka yi wa Shaheeda yawa,ga damuwa da ta yi mata yawa amma bata da mutum ɗaya da zai ba ta shawara,kullum cikin kuka da tashin hankali,a yanzu Arnold ya daina damuwa da ta ci abincin ma ko ba ta ci ba, tuni shan ƙwayoyin saka baccinta suka ƙaru,ta zama kusan kowanne lokaci tana cikin shaye-shayen ƙwayoyin don ta hana kanta damuwa

Cikinta yana da watanni bakwai yanzu, gaba ɗaya ta rame ta yi baƙi sosai, tamkar ba Shaheeda yar ƙwalisar Ummeey ba,sam fara'a da walwala sun kaurace mata, dama ita sam ba shiga sabgar mutane take yi ba, mijinta kawai ta sani,ko da yake saka ta interaction da abokansa dama can bata wani sakar musu fuska ballantana yanzu da ta san wanene ainihin wanda take kallo a matsayin mijin nata

A yanzu ta sake tabbatarwa Arnold ba musulmi bane,kuma addinin nashi na Christianity É—in ma ba damuwa ya yi da shi ba,don ita idan banda ya faÉ—a ma cewa zata yi bashi da addini

A yanzu Arnold ya daina ɓoye mata shan giya ko neman matan da yake yi,dama tuntuni ya daina attempting ko da taɓa ta ne kamar yadda ta buƙata,amma idan ya ga dama zai kawo ko ma wacece ya so,su yi abin da suka ga dama ko da a parlournsu ne,ba a ɗaki ba, sai dai ita ta tashi ta ba su waje

A baya Shaheeda tana cikin tashin hankali da taraddadin abin da zata je ta gayawa iyayenta game da wannan auren kasadar da ta yi wanda ya zame mata GADAR TSAUTSAYI da ya jefar da ita zuwa ga kwatamin dana sani,da wanne idanu zata kalli Ummeey da abbanta?akwai mutanen da suka so ta,suka nuna mata ƙauna,ta ba su kunya, irin su Muyassar,akwai mutanen da irin wannan faɗuwar tata suke jira,irin su mahaifiyar Muyassar, kakarta da sauran matan gidansu,ta san wadannan mutanen sun yi farin ciki sosai, Allah sarki!ko a wanne hali mahaifiyarta take ciki?

Hawaye suka zubo mata,ita kaɗai Ummeey ta haifa,bata da wata sanyin idaniya sai ita,ta san ta yi kukan rashinta har hawaye sun ƙare mata,a fili, cikin harshen Hausa da ta daɗe bata yi ba,ta ce "Allah sarki Ummeeyna!

Ki yafe min!ki yafe min Ummeey!!na san alhakinku ne yake ya bibiya ta har yanzu,na san alhakinku ne ya hana ni jin daɗin rayuwa,na bijire muku, kuma gashi a ƙarshe ina karɓar sakamako mafi muni da ciwo,ku yafe min"ta sake rushewa da kuka sosai tana dafe kanta,ita kaɗai ta san yadda take ji,da mummunan halin da take ciki

Tana nan a zaune,bata san ma lokacin sallar maghriba ya yi ba, sai duba agogo ta yi ta ga lokacin sallar isha'i ne,ta miƙe jiki a mace ta nufi ɗakinta don ta yi alwala ta yi sallah

Ko da ta idar da sallar ma kwantar da kanta ta yi a jikin gadonta tana cigaba da zubar da hawaye, idanunta sun kaÉ—a sun yi jajir,gaba É—aya ji take yi ta rasa hope, tunaninta ya koma kan yadda zata bar Spain ta koma ga iyayenta ta nemi yafiyarsu

Motsin da ɗan cikinta ya matsa mata sosai da shi ne ya sa ta miƙe cikin sanyin jiki ta nufi kitchen don samarwa kanta abin da zata ci ko babu yawa,don rabonta da cin abinci tun karin safe, shima kuma ɗan kaɗan ta iya ci

Yanzun ma da ƙyar ta samu ta sha tea ta sake komawa parlourn ta zauna tana tunanin irin rayuwar da ta yi a baya,da yadda ta jefa kanta a kogin danasani

Tana nan zaune Arnold ya shigo yana tangaɗi,da alamu giya ya sha ya yi mankas,ita mamaki ma abin yake ba ta,zai ƙaraci shaye-shayensa sannan ya hau titi ya ce zai yi driving

Tana ta kallonsa yana ta tamɓelensa a tsakar parlourn kafin ya tunkare ta,kamar ba mai ciki watanni bakwai ba ta yi wuf ta matsa,ya sake tunkaro inda take,ta sake matsawa tana watsa masa wani mugun kallo,kafin ta ce "wai menene haka?

Me giyar ta gaya maka yau ne da kake zuwar min haka?

Bana so!"

Yana tangaɗi ya ce "na gaji!na gaji da hana ni kanki da kike yi, Fatima bana buƙatar wata mace a duniya idan ba ke ba,don haka yau dole ki ba ni haɗin kai"

Tsaki ta yi ya juya zata shiga cikin ɗakinta,ya damƙo ta, tuni ta manta da wata kasala da nauyin jiki ta fara yunƙurin ƙwatar kanta, ganin ba zata iya ƙwatar kanta ba ya sa ta ɗaga flower vase ta rotsa masa a kai,tuni jini ya wanke masa kai,ita kuma ta samu ta gudu zuwa ɗakinta

Sai da ta rufe É—akin sannan tsoro ya É—arsu a ranta,ganin jini yana gudana akan Arnold, jikinta ya fara rawa,ta samu waje ta takure,ta zauna tana tunani

A haka bacci mai nauyi ya É—auke ta,mai cike da mafarki iri-iri marasa daÉ—i

Can cikin baccinta ta ji ana buga ƙofar,a firgice ta tashi zaune,da gaske ne bugu ne,kuma muryar mutane take ji,da alamu ma ba iya Arnold kaɗai bane, tsoro ya ɗarsu a ranta,ta leƙa ta window a hankali

Gabanta ya faÉ—i ganin Æ´an sanda,ta yi saurin saka hijabinta ta fita a tsorace tana kallonsu

ÆŠaya daga cikinsu ne ya gaishe ta cikin harshen Spanish, sannan ya ce "Madam mijinki ne ya yi hatsari a mota yanzu,mun yi gaggawar kai shi asibiti,a can yana ta kiran sunanki,a takaice dai yanzu, mijinki Arnold Liam Lambert yanzu ya riga mu gidan gaskiya,amma kafin ya rasu mun ga ciwo a kanshi,kuma ya tabbatar da cewa ke kika ji masa, don haka yanzu za ki bi mu zuwa office É—inmu,za mu tsare ki har sai an gama bincike,sannan sai mu ga abin da ya dace"

#Nusy_bee

Page 27

Kallonsa ɗan sandan da yake yi mata bayani kawai take yi numfashinta yana ɗagawa sama-sama, dishi-dishi ta hango ɗaya daga cikinsu yana ƙoƙarin buga mata handcuff,daga nan bata sake sanin inda kanta yake ba

A hankali ta fara buÉ—e idanunta,tana rufewa tana buÉ—ewa, lokaci guda kuma komai da ya faru ya dawo mata fes

Labari aka kawo mata na cewa mijinta Arnold ya mutu,kuma ana zargin da saka hannunta a mutuwarsa,a firgice ta yunƙura zata diro daga kan gadon, ƴar sandan da take tare da ita ta dakatar da ita gudun kar ta illata kanta, ga cikin da yake jikinta

Kuka sosai ta fashe da shi mai ban tausayi, duk yadda likitocin suka so ta kwantar da hankalinta ta daina kukan hakan ya gagara,ba wai mutuwar Arnold ce kawai ta taɓa ta ba, sai tonuwar asirinta, ina ma a yanke mata hukuncin kisa a ce ita ta kashe shi,ina ma ta zo haihuwa ta mutu,ina ma zuciyarta ta buga ta bar duniya,irin tunanin da ta rinƙa yi Kenan tana rera kuka cikin tashin hankali da gigita

Kwananta biyu aka sallame ta,kuma kai tsaye aka nufi station da ita,a can ta wuni,duk irin tambayoyin da aka yi mata ta kasa ba da amsa

Diego shine ya tabbatar da cewa Arnold giya ya sha,a buge yake lokacin da ya yi hatsari,kuma tabbas hayaniya ta haɗa su da matarshi Fatima shiyasa ma ta gudu ɗaki,sai dai ba ita ba ce ta ji masa ciwo,kamar yadda suke tunani, sunanta kuma da yake ambata yana da alaƙa da kewarta da yake yi ne

Da wannan bayanin Diego ya samu ƴan sandan suka saki Shaheeda,gashi kuma dama ba a son ransu suke riƙe da ita ba saboda cikin jikinta da kuma kukan da take yi, wanda duk wanda zai ganta zai tabbarwa kanshi na baƙin ciki ne

Diego shine ya cigaba da kulawa da Shaheeda har ta samu sauƙi,da farko ya kan zauna ma ya yi ta ɗebe mata kewa,ya kawo mata abinci,ya hana ta shan ƙwayoyin da take sha cikin dabara da hikima, don sun fara illata ta da ɗan cikinta,daga baya ma sai ya kawo mata ƙanwarshi Martina don ta rinƙa ɗebe mata kewa

Shaheeda ta yaba da karamcin da ya yi mata sosai,har hakan ma ya rage mata raɗaɗi mai yawa daga zuciyarta,ta yi iya ƙoƙarinta ganin ta rabu da damuwa kamar yadda Diego yake so

Kwanan Arnold tara da rasuwa mahaifiyar Mrs. Andrea Lambert ta iso ƙasar Spain,a ranar Shaheeda ta ga wulaƙanci ta ga tozarci, Arnold shi kaɗai ne ɗa a wajen Mrs. Andrea Lambert,kuma a saboda Shaheeda ya gudu ya bar gida,babban abin da ya fi yi mata ciwo ma shine kasancewar Shaheeda musulma,hakan ne ya sa ta sake zargin eh tabbas ita ce ta kashe mata ɗa

A ranar ta kore ta daga gidan,duk da halin jinya da kuma nauyin ciki bai saka ta tausayawa Shaheedan ba,haka tana kuka ta ɗauki iya abubuwa masu muhimmanci da zata buƙata ta bar gidan, zuciyarta cike da tunanin inda zata je,don lokacin Martina tana makaranta,gashi bata san gidansu ba
Chapter 33 · 0% Book details