Sashe 6
Diya Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ai ko da gudu Hajjo ta biyo bayan
shi,ta ja kofa ta ki buduwa,tayi kuka,tayi
kuka har da birgima kamar za ta shide.
Sai
bayan isha’i ya shigo,ya tadda har ta yi
bacci wahala,be damu ya tada ita ta yi
sallah ba ko ta ci abunci,ya tsallake ta nan
inda take kwance a kasa bakin kofa ya
dauko tuwan sa miyar kuka da ta ji
daddawa,ya ci ya koshi,ya wanko hannu ba
tare da kuskure baki ba,bare sauya kaya,tin
babbar rigar jiya ce jikin sa,ya haye gado
ya saki gabba da su labba ya fara
munshari..
DEDICATED to The Women Of Virtue
(group)
[11:04am, 5/5/2015] Khadija Sidi:
DIYA MACE
Washagari da sassafe,kafin ma Garbati ya
tashi Iyalle ta zo ta buga mu su kofa,tini
Hajjo ta tasha ta na murje ido,shi ko
Garbati da ko sallar asuba be tashi yayi ba
da kyar ya tashi ya na gunguni,ganin ya
nufo kofa Hajjo ta matsa da saurin ta,be
ma lura da ita ba ya bude kofa ya na fadin
wai menene Iyalle!
Ita kanta Iyalle sai da ta
ja baya jin yanda Garbati ke tashi,gashi da
yayi magana sai ka ji kamar za ka sume.
Iyalle daga baya baya dai ta ce Hajjo na zo
tashi ta fara shirin hada mana karin
kumallo ai ba kai ba.
Ya fara ware ido,ke
Hajjo,ya ki ki bita dallah!
Dama ita Hajjo
burin ta ta fita,da saurin ta ta fito,Garbati
ya ja kofa ya rufe ya haura gado ya ci gaba
da bacci.
Iyalle ta dubi Hajjo maza wanko
ido ki zo ki sa min hannu wata rana ma ke
zan sakarwa,Hajjo da ke yarinya ce me san
aiki,sam ba ta sa kiwa,bare kuma an ceto
ta daga warin Garbati,ta ce toh,bara na yi
sallah,banyi magariba da isha’i da asuba
ba.
Iyalle ta ce maza je ki dungura ina jira.
Hajjo ta ce toh.
Ta dau buta ta yi bandaki.
A dakin Iyalle ta yi sallah wai gudun kar ta
tada Garbati,wato Iyalle mace ce mai
shegen san lallaba yaran ta,amma na wani
ko oho.
Ta na Sallah Alhaji Baso ya fara
wai ina kokon ne?
Iyalle ta leko ta ce ke ki
fa yi sauri dallah,Mallam ina zuwa be sauka
ba tukun.
Da sauri Hajjo ta idar,ta na ganin
Mairo da kande sai baccin su su ke,haka ta
fita ta fara tular aiki ba kakkautawa,duk da
ba ta iya ba,amma Hajjo akwai saurin
dauka,wuyar ta a koya ma ta,shikenan.
Ranar dai Hajjo ba ta sami hutu ba,hatta
wanki ita ta yiwa Iyalle,ta na ta zuba ido ko
Indo za ta zo shiru,tin tana kuka har ta fara
sabawa da rayuwar da ta tsinci
kanta,kullum cikin aiki,ta zame mu su
kamar baiwa,ta ma fara tunanin Innarta ma
ta yada ita,ga Warin Garbati na bata wuya
duk da kowa da gadan sa amma daki daya
su ke.
Wasa wasa haka rayuwar ta ta
kasance,gashi har ta cika wata dakin mijin
ta.
Iyalle ta tura Garbati wajan wani
malamin sauro ya na karbar ruwan
rubutu,wai dan ya kafe Hajjo,ya kuma
mallake ta dan ta na jin maganar sa,duk
daren Allah sai Garbati ya tisa ta gaba ya
bata ruwan rubutu ta sha,idan ta ki sha ya
nuna zai buge ta,haka dai sai ta karba ta
sha,idan ta yi karfin hali ta tambaye shi na
menene sai ya ce maganin dangana da
hana yawo ne,tin abun ya na damun ta har
ya zame ma ta jiki.
Rannan ta hada zufa da tsakar rana ta na
ta wanke wanke,ba kowa a gidan sai ita
kadai,an tula ma ta aiki,kamar daga sama
ta ji sallamar Indo,ta daga ido ta ga Indon
ce,sai ta saki kwanan da ta ke wankewa ta
zuru wajan ta a guje,tana fadin wayyo Indo
sai yau za ki dawo!
Ganin yanda Hajjo ta
rame ta yi baki ya dagawa Indo gankali,har
ta rungumeta Indo kallan ta ta ke,ta ce
Hajjo sai ka ce da ke ake miya wannan
rama taki?
Ina mutan gidan?
Hajjo ta ce
sun fita,daga ni sai baban su Garbati,kuma
sun hana ni fita,Garbati ya ce duk randa na
sake fita sai ya kusan kashe ni.
Kashe ki?
Indo ta kama baki,ta ja hannun Hajjo su ka
yi daki,ga dai dakin tsaf da shi Hajjo ta
gyara ko ina,sai dai kuma dakin gum ya ke
da warin Garbati,Indo ta zauna tare Hajjo
bakin gado,ta ce Hajjo ya dakin na ki wari
haka?
Hajjo ta ce kayan wankin Garbati
ne,idan ya sa kaya ranar juma’a baya
sauya su sai wata Juma’ar in yayyi wanka
dama juma’a juma’a ya ke wanka,toh
kayan na sa can bisa kyaure su ke warin….
DEDICATED to The Women Of Virtue
(group)
[11:04am, 5/5/2015] Khadija Sidi:
DIYA MACE
Indo ta dafe kai ta ce hoo Hajjo zama da
kazamin miji sai hakuri,Hajjo ta ce wlh ba
na san shi Indo,na fi san zama da Inna
ta,dan Allah ki mu su magana su bar ni na
koma gida.
Indo ta ce ki yi hakuri Hajjo,ki yi
hakuri,sai da na biya ta wajan Inna kafin na
zo,ta fito da kayan kamshi,su kananfari,jitta
da dai sauran su,ta mikawa Hajjo ta ce ga
tsarabar Inna.
Hajjo ta ki karba,ta ce Inna
ba ta so na,ta ki cewa a mayar da ni ta
kuma ki zuwa.
Hankalin Indo ya dada
tashi,nan ta ci gaba da ma ta bayanin Baba
ne ya hana Inna zuwa,ita din ta na kewar
ta,sannan ta hakura ta karba.
Indo ta
tambaye ta ya zaman ta a gidan,ta na jin
dadi kuwa?
Nan ta kwashe komai da take
ciki,har da ruwan rubutun da Garbati ya ke
bata,Indo ta ce oh ya Allahu,Allah sarki
Hajjo shi ya sa na ga kin zama shiru shiru
haka,asirce ki ya ke,so ya ke ya maisheki
baiwar sa nan gaba,kai wannan akwai
azzalumai,nan gaba ya baki kar ki sha,ki
faki idon sa ki zubar,kin ji ko?
Hajjo ta
gyada kai alamar eh.
Indo ta ce wannan
duk aikin ke kadai ki ke yi Hajjo?
Wlh da
sake,da gida zani amma na fasa wajan Inna
zan koma dole a kwatar mi ki hakkin ki!
Tashi mu je na taya ki aikin!
Hajjo ta ce
laaa zan iya,ai har na fara sabawa,har fa
girki na ke,da na sa hannu na ke gama
komai.
Cikin tausayawa Indo ta ce Hajjo
Allah ya zama gatan ki,mu je na taya ki dan
Allah.
Hajjo ta wuce Indo biye da ita.
Ta sa
ma ta hannu su ka gama aikin gidan tas.
Kamar yanda Indo ta fada,wajan Innar ta
koma,jin halin da Hajjo ta ke ciki ran Inna
be so ba,amma sai ta buye ta ce in banda
abun ki dan an sakarwa Hajjo aiki wani abu
ne?
Hajjo diya mace ce,aiki ga diya mace ai
taimako ne,kin ga za ta tashi a kwararriyar
mace mai himma,kuma zancen asirce ta
Indo ba su isa su yi ma ta abunda Allah be
kaddara ba,wannan shiru shirun da ki ka ga
Hajjo ta zama wlh adduar uwa ce,nutsuwa
ta ke kasencewar adduar da na ke ma ta na
Allah ya nutsar min da diya ta gidan mijin
ta,adduar iyaye ga ‘ya’yan su karbabbiya
ce,dan ko asirin Garbati ya ci Hajjo,to
kadan zai yi tasiri kanta,zan kuma ci gaba
da ma ta addua,kuma ki na yawan zuwa ki
na duba ta dan Allah,ba komai ai diya mace
dama da aiki aka san ta.
Jiki a sanyaye ta
ce toh Inna,Allah ya sa mu dace,Inna ta ce
ameen,Allah ya ci albarka.
Indo ta ce
amen,gami da mikewa ta ce Inna bara na
koma toh.
Inna ta ce a sauka lfy,Allah ya
tsare,ta ce amen amen.
Washagari da wani irin matsanan cin ciwan
mara Hajjo ta tashi,haka a daddafe ta dinga
yin aiki,duk da Iyalle ta lura da haka,sai ta
yi kamar ba ta gani ba,sai Mairo ce ma ta
zo fita dandali ta ga Hajjo durkushe gaban
murhu ta ce ke Hajjo mene wai?
Baki da lfy
ne?
Ta dago idanun ta sun kada ta ce
Mairo kasan ciki na ciwo,Mairo ta ce sannu
toh!ta kama hanyar ta ta fice.
A haka tai ta
fama da hura wuta ta na gyarawa Iyalle har
Iyalle ta gama girkin ta,Hajjo ta yi shara ta
yi wanke wanke…
DEDICATED to The Women Of Virtue
(group)
[1
[16/10 21:44] .: 05am, 5/5/2015] Khadija
Sidi: DIYA MACE
Ta na gamawa ta koma daki ta
kwanta,ciwo ya ki ya barta,daga bisani
kuma ta ji kamar wani abu na fita daga
jikin ta,ta nan kwance ta ki motsawa sai ga
Kande ta shigo ta na fadin Hajjo wai me ke
damun ki ne?
Hajjo ta ce kasan ciki na ke
min ciwo,yanzu na ji kamar wani abu na
fita daga jikina,kande ta ce mugani?
Dan
matsa na gani,ko da ta matsa Kande ta ga
halin da Hajjo ta ke ciki,ita ma Hajjo sai a
sannan ta gani,sai ta sa kuka.
Kande ta ce
menene na kukan?
Ai al’ada ce,kowace
cikakkiyar diya mace ta na yi,ke ma yau kin
zama cikakkiyar diya ma ce,hukunci ya hau
kan ki,ki bar kuka,ita dai Hajjo ta ki ta yi
shiru,gani ta ke mutuwa za ta yi,da kyar
Kande ta shawo kanta,ta ce auduga ake
siya ake sawa,ko kuma kyalle,itama ba ta
da audugar,Hajjo ta kawo kyalle mai kyau
sai ta koya ma ta,cikin kayan Hajjo ta sami
wani dankwalin ta,ta yanka,sai da ta kai
ma ta ruwa bandaki,sannan ta gwada ma
ta yanda za ta sa kyalle,dake ciwan diya
mace aka ce na diya mace ne,Kande ba ta
nuna kyama ba,taiwa Hajjo kara kafin ta
fito ta cire zanin gadon da Hajjo ta bata ta
wanke ta shimfida ma ta wani,sai da ta
tabbatar Hajjo ta yi tsaf,ta ba ta Panadol
sanan ta ce da Hajjo ta kwanta kafin
Garbati ya dawo sai ta tambaye shi ya
bada kudin auduga ta siyo mata,Hajjo ta na
fama da ciwan mara,ta ce ma ta toh
kawai,idanu runtse.
Ko da Garbati ya dawo Kande ta fada ma
sa halin da Hajjo ke ciki,ya ba da kudi ta
siyo ma ta auduga,sai ya kalle ta yace yo
wani kudi zan ba ki?
Ina na gan sa?
An
fada mi ki tsintar su ake a kasa?