Sashe 23
Diya Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yanda Hauwa ta ganshi jike rai a
bace ta san ba lfy,ta yi kokarin jin
musabbabin bacin ran na sa,ya ce da ita ta
dan bar shi ya na so ya ji shi kadai,ta ce
toh,Allah ya kyauta.
Ta ja diyar ta ta bar
shi ya ci kan sa,binibini sai ka ji ya ja
tsaki,mtws!
Ranar dai haka ya kwan da
takaicin Hajjo wanda hakan shi ne karo na
biyu.
Washagari da sassafe sai ga Khalid a
kumurya.
A tsakar gida Sani ya sa ma sa
kujerar da ya ke bawa bakin sa na albarma
ya zauna.
Bayan ya gaisa da Indo,ya ke ce
ma ta ta fa dan so ta yi kama da Hajjo,dan
dai ta fi Hajjon kyau,dadi har ran
Indo,kyakkyawa kamar Khalid ya ce ta na
da kyau.
Zaman shi da Sani ya ke fada ma
sa dalilin zuwan sa,so ya ke a kai shi gurin
iyayen Hajara.
Sani ya ce toh fa.
Ai
mahaifiyar Hajara Allah ya ma ta rasuwa
shekara goma sha uku kenan.
Khalid ya ce
Allah sarki,Allah ya ji kanta,sunan ta Neena
ta ci kenan shi ne Hajara ke kiran ta Inna.
Mahaifin ta fa?
Sani yayi jum.
Khalid ya ce
ya ka yi shiru ne?
Sani ya ce ai abun
ne,toh mahaifin ta na nan,gidan nan gaba
ne ba nisa.
Khalid ya ce toh mashaAllahu
za ka iya raka ni gun sa?
Sani ya yi
jugum,kamar mai shawara.
Khalid ya ce kar
ka damu,tsakanin mu ne,ko matar ka ban
so ta san za mu wajan na shi,sai nan
gaba,da alkhairi na zo,kamar yanda na ma
ka bayani a baya auren Hajara zan yi.
Sani
ya ce ba komai,sai na raka ka din.
Sani ya
ce da Indo su na zuwa,su ka fita ba su
zame koina ba sai gidan su Hajjo.
Gidan ya
koke ya lalace kamar ba Jama’a ciki,wai
kuma a haka Mudi ya yi aure ya aje matar
shi ciki haka shi ma Ayuba shi ma da matar
sa cikin gidan.
A waje su ka tsaya,su ka
tura yaro ya mu su sallama da Baba,Yaro
na shiga ya fito ya ce ai ga Alhaji Mamman
din nan soro sai nishi ya ke ina ga ba shi
da lfy ne.
Godiya su ka ma yaro,tare su ka
kutsa cikin soron,sai kuwa ga Baban nan
kwance a wulakance sai nishi ya ke,be ma
san wa ke tsaye kan sa ba.
Subhanallahi,tare su ka yi saurin durkusawa
gaban Baba,Sani ya na fadin yaushe kuma
haka ya faru?
Ko da wasa ba mu ji rashin
lfyar ba!
Shi kuwa Khalid ran sa ne ya dada
baci da al’amarin Hajjo,ya Baban ta mahaifi
na nan kwance cikin wannan
wulakantacciyar rayuwa ba gata,amma ita
ko a jikin ta, ta na likita,haba wannan wata
irin duniya ce haka!
Ya kalli Sani ya ce
bayan Hajjo da Indo bai da wasu ‘ya’ya ne?
Ya ce akwai Mudi da Ayuba,nan su ke
zaune da matan sa.
Khalid ya leka ya sami
yaro ya ce ya yi sallama da Mudi ko
Ayuba,dan tin zuwan su ba wanda ya
leko,da sun zo da wani mugun abu ne da
tuni sun aiwatar.
Yaro ya dawo ya ce ba sa
nan,sai matan su.
Khalid ya ce ace su su
leko.
Sai ga lantana matar Mudi ta leko da
daurin kirji ta na mita wai waye maigida
baya nan sa ya ce sai ya gan mu…Ganin
Sani tare da wani dandasheshen namiji sai
ta shanye maganar ta.
Yanda ya ganta
dukundukun,ga daurin kirji,Khalid ya ce
disgusting!
Ita ko sai ta fara hannu,hannun
ku,ashe Sani ne,ai daga Mudi har Ayuban
ba wanda ke gida,eh sun je samo mana na
afawa!
Khalid ya ce sun san da rashin lfyar
mahaifin su?
Lantana ta kalli inda Baba ke
kwance ta ce sun shi na mana,kullum cikin
ba shi jike jike su ke ai,Mudi ne ma ya
kawo shi nan ya kwantar,dudu ma kwanan
sa nan uku kwance ba,sai dai a tayar a
kwantar.
Rai bace Khalid ya ce Sani
taimaka min mu sa wannan bawan Allah
mota mu kai asibiti,wa’yan nan ba su san
darajar iyayen su ba,da ga su har matan na
su.
Lantana ce yo ai dai mun ma sa iya kan
kokarin mu mu dai,so ka ke mu sa zani da
majanyi mu goya?
Banza su ka ma ta,yayin
da su ka kama Baba,sai zarnin fitsarin da
yayi a kwance ya ke su sa shi mota.
Sai da
su ka biya gidan Sani,ganin halin da Baba
ke ciki Indo ta girgiza,Khalid ya ce ya aka yi
ba ta zuwa ganin sa har ya kai haka bai da
lfy?Indo ta ce wlh ta na zuwa duk da ko ta
je din fada ya ke ma ta wai ta na damun
shi da yawan zuwa,ko kwana hudu da ya
wuce ta je.
Tare su ka dunguma su ka taho
kano,Indo ta bar babbar yarta tare da yara.
Su na zuwa kano AKTH su ka wuce,nan da
nan aka kwantar da Baba emergency,darajar
Jabir tuni likitoci su ka rufa kan Baba su na
duba shi,abu na su.
Khalid da Sani,da Indo
su ka ja gefe,Har Khalid ya daga waya zai
kira wayar Hajjo,sai ya ja tsaki ya kashe,an
sha fada ma sa diya mace ta fi jin kan
iyayen ta akan maza,amma sam ya ga
bambamci gun Hajjo,hw comes?
Hw can
she be so cold to her biological father,ita ta
yaya ta ke so na ta ‘ya’yan su ji kanta har
su tausaya mana.
Kai daga dowowar sa
zuwa yanzu Hajjo ta tsaya ma sa a rai kan
abubuwan ta da dama.
Sani ya sallama,kar
Hajiya ta ji shiru,ya ce kar ya fada ma ta
sun kawo mara lfy,idan ya dawo zai ma ta
maganar,gudun kar Hajiya ta ji irin abun da
ya ke ji game da Hajjon.
Da wuri ta samu ta bar asibiti,hudu a gida
ta mata,ta yi saurin yin wanka ta shirya
cikin english wears riga body hug ruwan
goro,da kuma free skirt bski,sai ta daura
bakar sweater da ke garin ana sanyin
damina.
KB ne ya dame ta zai zo tin da ya
sauke ta jiya,ita kuma ganin kirkin da ya
ma ta dan a ramawa kura aniyar ta sai ta
yarda yau daya dai yazo.
Ta na kallan
kanta a madubi,ta dau humra ta na dan
shafawa jikin mayafin da za ta yafa wayar
ta ya fara kara,ta duba ta ga sunan KB sai
ta aje humran ta daga,ya ce gashi cikin
farfajiyar gidan.
Ta ce toh ga ta nan fitowa.
Ta kuma kalle kanta a madubi,ta yi kyau
kamar diyar turawa,ta sanya takalmi ta je
ta fadawa Hajiya za ta fita.
DEDICATED to The women Of Women Of
Virtue (group)
[1
[16/10 21:49] .: 1:15pm, 6/5/2015] Khadija
Sidi: DIYA MACE
KB zaune kan motar shi ya na jiran fitowar
Hajjo,wata mota ta shigo gidan,ta faka gefe
guda.
Ganin Khalid ya fito sai da ya sha
jinin jikin shi duk da dai ba su taba haduwa
ba,be kuma san wanene shi ba.
Shi ma
Khalid tin shigowar sa gidan ya gane
KB,dan haka kai tsaye wajan shi ya je,ganin
ya nufo shi KB ya sauko daga kan mota
tare da mi ka ma sa hannun tare da fadin
salama’alaikum,fuska murtuke ya amsa
wa’alaikumul salam.
Wajan wa ka zo ne?
KB ya dan yi jim sannan ya ce wajan Doctor
Hajara.
Khalid ya ce a matsayin ka na wa?
KB ya ce ban dai san kai wane ne ba,so dax
y zan amsa ma ka,a matsayi na na friend
din ta.
Khalid ji yayi kamar ya buge bakin
sa,ya ce matar tawa ce friend din ka?
KB
ya gyara tsayuwa,tare da fadin matar
ka,wlh ban san ta na da aure ba,ba ta fada
min ba,Khalid ya ce ba a daura ba ne,wata
biyu ya rage dax y ina ga ba ta fada ma
ba,so ka nemarwa kan ka arziki ka janye
kafar ka daga gidan kuma da ga wajen
mata ta.
Jin ba a daura auren ba sai
hankalin sa ya kwanta,ya ce ba
damuwa,sure bazan sake zuwa ba.
Khalid
ya ce madallah.
Ya juya ya na tafiyar nan
ta shi cike da takama ya shige gida,KB ya
ce ba shakka dan ma su gida,shi gidan ma
ya ke shiga kai tsaye,bara na ja rayuwata
na yi gefe guda!
Be san gidan su Khalid din
ba ne.
Ya shige motar sa ya ya fita lokaci
guda kuma Hajjon ta fito,sai gani korar
motar ta yi,cike da mamaki ba ta ma san
Khalid na tahowa ba ta ke fadin me zai sa
kuma KB ya tafi,bari na dauko waya na kira
shi.
Da jin kamshin turaren sa da ankarewa
da shi lokaci guda ne,ta daga kai ta kalle
shi.
Ya bi ta da kallo tin da ga sama har
kasa,har sai da ta kasa sakewa.
Fuska murtuke ya ce kar ki damu da ki kara
kiran shi,na sallame shi har a bada ba zai
sake dawowa gidan nan ba.
Maganar ta
bata ma ta rai matuka,har ta bude baki za
ta yi magana,sai ta kuma ta fasa ta juya da
niyyar komawa ciki,ya dada tsaida ta ta
hanyar fadin yaushe raban ki da Baban ki?
Dum maganar ta daki kunanta,ji ta yi komai
ya tsaya ma ta cak na dan sakanni,sanna
ta kara daga kafa ko taku uku ba ta yi ba
ta ji ya sake fadin diya mace da jin kai aka
san ta,musammam na iyayen ta,amma
yanda na ki lamuran su ke kin sa ina kokon
tan haka,ur father Hajara is very ill,shin ki
na neman albarka kuwa?juyowa ta yi a
hankali,dan bacin rai idanun ta har spark su
ke,ta sake bude baki da niyyar magana,sai
ta kasa.
Yanda ya ga ta na kallan sa kamar
kura ta ga nama,ga idanun nan na spark
dan masifa sai ta ma sa kyau,ya ma kusa
manta da bacin ran da ke tare da shi.
Juyawa ta sake yi,dan gani ta ke magana
be da amfani a yanayin da ta ke jin
kanta,lalle zaman ta a gidan nan ya zo
karshe!
Da wannan kudiri cikin ranta ta
shige ciki.