← Book details Diya Mace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 41

Sashe 19

Diya Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ji ya yi an taba kafadar sa ance
ai sai dai diyar ta girma ta zama uwar,dan
tin zuwan Child abuse gidan nan kamannin
ta haka su ke ba ta canza,kawai dai ma su
ido ke gani….hakan ya tabbatar ma sa a fili
yayi maganar ba cikin ran sa ba,ya juyo ya
na dariya,ya ce kwarai kuwa ma su ido da
baki irin su Jabir ba,duka dariya su ke su
ka rungume juna cikin musabaha.

DEDICATED to The Women Of Virtue
(group)
[7/25, 5:13 PM] Salmah Ateeku: [6:38pm,
6/5/2015] Khadija Sidi: DIYA
MACE
Jabir na dariya ya ce da Hajjo kamar fa kin
ruda kanin nawa,cikin girmamawa da kuma
jin nauyin maganar Jabir ta gaida Khalid,ya
amsa idanun sa kanta.

Jabir ne ya janye
shi ya na fadin wallahi child abuse din nan
ta ka ce ka ma bar kokanto yaro!

Ta na jin
shi ya na wlh Jabir kada fa ka matsa min!

Sai na fadawa Nabeela abunda ka fada min
rannan!

Shegen maza!

Ta ciyo Jabir na
zagen Khalid,ga dariyar su na tashi kamar
su kadai ne a gidan.

Hajjo ta saki ajiyar zuciya,damuwar da ke
kwance cikin ranta ce ta taso,gaba daya ji
ta ke ranta a dagule,ya za ta haifi diya ta
na gudun ta?

Su ma su rikon ta ba su
sheda ma ta wacce mahaifiyar ta ba?

Me
ma su ke nufi ne?

Kai lokaci ya yi da za a
dawo ma ta da diyar ta gaskiya!

Da wannan
tunanin ta cigaba da wanke wanken
ta,tsabar bacin rai ma ta kasa katsewa ta
je su gaisa da Hauwa.

Sai da ta gama tsaf.

Can falo kuwa Hajiya zaune tare da su
Khalid ana hirar ya bayan rabuwa,Jabir ya
tafi gidan sa.

Tin fitowar su hankalin sa ke
kan hanyar fitowa daga kitchen,Allah Allah
ya ke ya kara sa Hajjo a idon sa,ya ga
baiwar Allah,kamar da diyar ta kamar an
tsaga kara,kawai dai dan ita yar fara ce,ita
kuma uwar wankan tarwada,da kuma ita
Innar yarinya ce da sai ma ace yan biyu
ne.bini bini Hajiya sai ta kalli Inna ta ce
yarinya fa ta zama budurwa,yanzu wa zai
kalle ta ya ce mahaifiyar ta ce ta haife ta,ai
sai dai ayi zatan yaya da kanwa ne.

Khalid
ya ce wlh kuwa,ni kai na na yi mamaki
kwarai da na ga uwar!

Ita dai Hauwa da
anyi maganar Hajjo gaban ta faduwa ya
ke,duk da dai ta san Neenan ta ta ba diyar
ta ba ce,amma ba ta ji za ta iya rabuwa da
ita,shi ya sa ma ko zancen Hajjon ba ta ma
ta,kunga karfin hali barawo da sallama.

Hajjo ta fito fuskar ta dauke da
murmushi,da Khalid ta fara hada ido saboda
dama dai shi ne ya kasa ya tsare ya ke
jiran tsammanin sake ganin ta.

Ta yi saurin
janye idanun ta da ga na shi gaban ta na
faduwa,wajan Hauwa ta karasa ta na
maraba sannun ku da zuwa,ita ko Inna da
ta ga haka sai ta koma gefan Khalid.

Hajiya
ta ce aw ku ga yar butan uwa!

Uwar ta ki
ki ke gudu?

Hauwa ta ce ina ruwan Neenan
Mama,kin san ba ta san ta ba.

Maganar ta
yiwa Hajjo daci,amma sai kawai ta boye,ta
ma dauke kai daga kan Innar.

Bayan sun
gaisa ta tashi ta ba su wuri,wanda hakan
be yiwa Khalid dadi ba,ita kuwa Hauwa
hakan daidai ya ma ta.

Bayan tashin Hajjo, Hajiya ta bijiro mu su
da maganar Inna,hankalin Hauwa ya tashi
gudun kar Inna ta gane zancen da ake ta ce
da ita ta Neena tashi ki je daki ki kwanta
abun ki.

Tana tafiya Hajiya ta ce kun dai
san ya kamata ba sai an fada mu ku
ba,amma na ga alamar ba ku ma shirin yin
abunda ya kamata,kamata yayi ayau dinnan
ku taho da komai na yarinyar nan ku
damkata hannun mahaifiyar ta,ta mu ku
kara ai.

Idanun Hauwa yayi rau rau zai
kawo ruwa,Khalid ya gyara zama,ya ce
dama Hajiya za a yi hakan,dama so mu ke
mu gama settle….ah ah!

Hajiya ta katse
shi,yarinyar nan fa alkunya ta ke mu ku,it is
high time auta,ku dawo ma ta da diyar ta.

Khalid ya sosa kyeya,idanun sa kan Hauwar
shi,ganin yanda gaba daya ta sauya yanzu
yanzu sai ta ba shi tausayi,dole ya nemo
mu su mafita.

Ya ce toh Hajiya ta,yanda ki
ka ce haka za a yi,ta ma yi kokari ai,amma
dan Allah ki ba mu zuwa sati na gaba sai
mu dawo da ita din.

Hajiya ta ce ko ku
fa,Allah ya nuna mana,ya ce amen.

Farin cikin Hauwa ya gushe,daurewa ta yi
kawai har su ka gama wuni a gidan,amma
kowa ya san ta na cikin damuwa.

Suna
komawa gidan su kuwa,ta samu ta kebe da
Khalid sai kuka.

Kuka sosai ya ma kasa
rarrashin ta dan tuni ta riki ta shi,sai da
kukan na ta ya tsagaita,kwance cikin sa ya
ke ba ta baki,haba baby-luv,toh menene na
kukan?

Ta na ajiyar zuciya ta ce ya bazan
yi kuka ba?

Kasan matsala ta Khalid,kasan
ba na haihuwa ba zan taba haihuwa ba ma
wasu likotocin da ba su iya magana ba su
ka ce….shhhhh ya toshe ma ta baki da dan
yatsa,ya ce kema kin ce wanda ba su iya
magana ba,ki sa Allah a ranki baby-luv,shi
kadai ne mai iya bawa bawan sa kyauta
sanda be yi zato ba,shi zai ba mu
haihuwa…Hauwa ta ce haka ne,ban fidda
tsammani ba duk da kowani indication ya
nuna kishiyan haka,amma Beb idan aka
dauke min Neena ban san inda zan sa rai
na ba,ya zan yi da rayuwa ta,na riga na
saba yarinyar ta shige jiki na.. shiru ya yi
daga bisani ya ce ba yanda za mu yi,dole
mu mayar ma ta da diyar ta,kar ki
damu,Allah na sane da mu.

Nan fa sai
Hauwa ta kara fashewa da kuka,tin ya na
rarrashi,har ya kyale ta,kusan kwana ta yi
ta na kuka,wai za a raba ta da diyar da ke
kiranta Momma.

Washagari abun duniya ya ishi Khalid,shi
ma din tafiyar Neena na damun shi,babu
yanda zai yi ne kawai,da ga shi har matar
ta shi babu mai walwala,zuciyar sa na sake
sake kala kala,hez 37 yanzu,Hauwa
31,amma ko kwai be taba ajewa ba,shekaru
na ja,tsufa da mutuwa na gabatowa,shin
rayuwa za ta yiyu a haka kuwa?

Da sam
haihuwar ba ya gaban shi,sai yanzu da ya
manyanta ya fara damun shi,duk da kuwa
be taba nunawa baby-luv din ta shi ba.

Da
yamma ta yi sai ya wuce gidan Hajiya,ganin
ta tare da Hajjo zaune cikin dakin Hajiyar
sai abun ya bashi sha’awa,ita Hajiyar ma
kenan da Allah ya ba ta haihuwa,dan dai
kawai ba ta da diya mace ji soyayyar da ta
kewa Hajjo da ta yi kusan rabin rayuwar ta
a hannun ta,bare shi da be san dadin
haihuwa ba,sai akan Neena,wacce tin ta na
shekara biyu ta ke tare da shi.

Hajjo sanye
da doguwar riga baka,ta rufe kanta da
mayafin rigar,daga gani fita za ta yi ko
kuma daga fitar ta dawo,ganin sa ta yi
saurin tashi za ta fita,Hajiya ta ce ina dawo
ki zauna,kin ga shigowar Khalid za ki sami
damar fita,zauna shima ya taya ni ai,Hajjo
ta koma ta zauna a takure.

Idanun Khalid
kan ta,shi dai mamakin girma,kyau da
wayewar ta ya ke,gaba daya ta canza
kamar wacce makirin mata ya kyera.

Ya
dan kalli Hajiya ya gaishe ta,sannan Hajjon
ma ta gaisheshi,yanda ta saba cikin
girmamawa.

Khalid ya ce Hajiya kamar ki
na zan taya ki,me zan ta ya ki?

Hajiya ta ce
jin ta baki Hajjo,sam na ga alama ba
zancen aure a gaban ta,ya kamata ta yarda
tsayayye ya fito.

Dim!

Ya ji wani irin
mummunar faduwar gaba,sai da ya koma
ya dan jingina da bango….

DEDICATED to The Women Of Virtue
(group)
[7:06pm, 6/5/2015] Khadija Sidi:
DIYAMACE
Ya gyara murya ya ce Hajiya ai gwara dai
kar a ma ta shisshigi,tin da ba yarinya ba
ce,auren nan ta yi na fari dama,kar a
azalzale ta a jira na gari ya zo sai ta tsayar
din.

Hajiya ta ce ahaf,kar ka mai da mu
baya kai kuma,wani na gari ya zo?

Ai tuni
Hajjo na da nagarin ta a hannu…da sauri ya
daga ido ya kalli Hajjo,wani abu ne ya
tsaya kamar kashi cikin ransa,well obviously
mace kamar Hajjo ya kamata ace ta na da
manema,plus shi ina ma ruwan sa ne?

Tambayar da yayiwa zuciyar shi kenan!

Ina
ruwan ta da kaduwa akan maganar child
abuse?

A zahiri tambayar Hajiya ya yi waye
shi na garin?

Hajjo ta saci kallan sa ta
wutsiyar ido,see dis man!

Ina ruwan shi da
ni da har zai na tambaya kan rayuwa ta!

Ni
fa shisshigi ne ban so,dan ya na ruke da
Inna ta be zama uba na ba!

Tafasar da
zuciyar Hajjo ke yi kenan.

Hajiya ba tare da
ta kawo komai ba cikin ran ta,ta ce wani
likita ne,Surajo,Jabir ma ya san shi,yaran
arziki wlh.

Ran sa idan yayi dubu ya baci,ya
kasa gane mai ke ma sa dadi,wai ma ina
ruwan sa ne!

Toh Allah ya sa a yi da mu.

Hajiya ta ce amen amen.

Hajiya bari na
tafi,dama gaishe ki na zo yi na yi da Jabir
zan dauko sa daga asibiti,akwalar motar ta
sa da ya kasa rage ciki ya sake ta kara
samin matsala.

Hajiya ta dara ta ce kamar
a kunnan sa.

Shi ma darawan yayi duk da
de ba dadi ya ke ji ba,ya ce kin san dai
gaskiya na fada.

Zuciyar Hajiya daya ta ce
in dai haka ne ka ragewa Hajjo
hanya…..Hajjo kamar ta kurma ihu,sam ba
ta san abunda zai hada ta da Khalid,da
sauri ta ce ah ah Hajiya ba ma sai ya rage
min ba sai na hau a daidaita sahu.

Hajiya
ta ce AKTH zai je,kin ga ina kundila ina
AKTH,ai ya fi sauki ya sauke ki..dan kar na
bata ma sa lokaci Jabir na jira Hajiya,Hajjo
ta kara kan bayanin ta.

Da ya fuskanci bin
shi ne ba ta so,sai ya ce no ba bata
lokaci,mu je na sauke ki kidin.
Chapter 19 · 0% Book details