Sashe 11
Diya Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shiru shiru an aika be zo ba,da Mudi ya
ga haka ya ce da Hajjo wani suna su Hajjon
su ka yanke za a sawa diyar ta su ne?
Dan
ya kamata a yi ma ta huduba Hajjo ta ce
ba su taba zancen ba,amma dan Allah ya
ma ta da sunan Inna,Ameena ta san shi ma
ba zai ki ba,Mudi ya ce toh a kawo masa
yarinyar,ya ma ta huduba da Ameenatu,Inna
ta tafi Inna ta dawo.
Washagari bayan Hajjo ta yi wanka ta
shirya,ta yi tsaf da ita,ta ciko sosai kamar
ba Hajjo ba.
Indo ce ke wa jariyar wanka,ta
ce Hajjo?
Hajjo ta ce ummm kin san kuwa
jiya ki ka cika shekara gomasha uku?
Hajjo
ta gyada kai kawai ba tare da ta ce komai
ba.
Har aka gamawa yarinyar wanka sai
cilla ihu take,dake yarinyar akwai kuka.
Indo
ta daura ta kan cinyar Hajjo,ta ce ki daure
ki ba ta tasha Hajjo,Hajjo ta yamutsa fuska
ta ce wlh da ta fara cikina ciwo ya ke,gashi
ba ta koshi,Indo ta ce ki yi hakuri Hajjo,ya
za ki yi tin da kin haifa dole ki shayar
ai,daure ki ba ta.
Hajjo ta turo baki ta sa
ma ta nonan a baki,caraf diyar Garbati ta
karbe ta fara sha kamar wacce aka koya ma
ta.
Sai da yamma su Iyalle su ka zo,sun zo da
sakon Garbati na a yiwa yarinya huduba da
suna Katime,sunan Iyalle.
Indo ce ta mu su
bayani cikin ba da hakuri akan yarinya da
aka ji shiru an ma ta huduba da suna
Ameena,an yi tunanin hakan zai yi daidai da
ra’ayin Garbati.
Toh ai ba komai,Allah ya
jikan Ameenatun,amsar da Iyalle ta bayar
kenan,amma sai da fuskar ta ta nuna ba a
mu su daidai ba,dan haka ba su jima ba su
ka tafi.
Har suna ya zagayo ba Garbati ba
alamarsa,ko ragon suna be aiko ba.
Mudi
da Indo da Ayuba sun yi cirko cirko a tsakar
gida,ana tunanin ko bin sawun Garbati Baba
ya shigo ya ce ya aka yi cirko cirko haka?
lfy?
Mudi ne mai bayanin,ya ce Baba muna
tattaunawa ne akan lamarin Hajjo,Allah ya
waye mu suna amma mai gidan na ta shiru
haka yan uwansa,ko rago ba su turo ba
bare kuma ayi batun abincin da za a bawa
yan suna.
Baba yace yo ba ku ku ka jawo
ba,ai na zuba mu ku ido ne kawai,yaro tin
da aka yi uku da rasuwar Ameenatu ya ce
mai dakin sa ta koma,ku ka kiya,ta haihu
ku ka ma ta huduba da sunan da kuka so
ba tare da kun jira shi ba,yanzu ga irin ta
nan,sai kusan yanda za ku yi dan na sadu
da Alhaji Baso dazu ya ke fada min an yiwa
Garbati ba daidai ba dan haka ya ce tin da
ku ka rada sunan ku siyi ragon suna,kuma
kwayar shinkafa tawa ban yarda a dafa dan
sunan asara ba,kun dai ji na fada mu ku!
Kuma gobe goben nan Hajjo za ta koma
dakin mijin ta,na gaji da hidama da ita da
diyar ta ai ta cinye ma hatsi!Ya shige ciki
ya barsu suna kallan kallo,Indo ta ce toh
kun ji fa,yaya kenan?
Ko dai cikin ragunan
da maigida na ya ke kiwo za mu ranci guda
a yanka?
Ayuba ya ce zai ba mu ne?
Indo
ta ce mai zai hana,ai Sani be da matsala.
Mudi ya ce ai Indo Mijin na ki ne balalle a
same shi ba.
Ta ce ya na gida,be tafi kanan
ba tukun,ku yi azama ku riske shi.
Su ka ce
toh su ka tafi,ita kuma Indo ta koma daki
wajan Hajjon da tun safe ta ke kuka,ga
Ameena da take kira Inna sam ba ta barin
ta ta sami bacci da daddare.
Ta ce Hajjo ki
rufa min asiri dan Allah ki bar kukan nan
haka.
Mu fatan mu a samu a yi yankar
nan,na so ace an mi ki wannan dinkin kafin
ki koma gidan ki amma Baba ya ce gobe za
ki koma,saboda haka bayan kin koma din
ma samu mu je asibiti a mi ki kin ji ko?
Komai zai wuce,yanzu Ina Inna?
Gaba shi
yau mun wayi gari ba ita ba,haka duk za
mu wuce komai mai wucewa ne ai.
DEDICATED to The Women Of Virtue
(group)
[7:16pm, 5/15/2015] Khadija Sidi:
DIYA MACE
Hajjo uhum kawai take iya cewa,ita kadai ta
san abunda ta ke ji.
Ba a jima ba sai ga
Mudi da rago,har da shinkafa kwana biyar
Sani mijin Indo ya hada su da shi.
Ba bata
lokaci aka yi yanka,Yan uwa sun ka fara
zuwa,da taimakon dangi aka sarrafa
shinkafar zuwa dafa duka,aka hada kunun
zaki…a haka da faci faci aka yi suna aka
gama da ke ba wani taro aka yi ba,dama ga
babu ga kuma rasuwar Inna.
Washagari Hajjo ta koma gidan ta,Mairo da
Kande kadai ke hidima da ita,su kan daukar
ma ta Innar na ta sosai,ita kuma Iyalle
bakin cikin ta na an ki a sa sunan ta,an sa
na Inna.
Shiko Garbati bakin cikin sa da
yawa,gashi Hajjo ta tafi ta ki dawowa sai
da ta haihu,gashi an sa sunan da ba shi ya
ce a sa ba,gashi diyar ta Hajjo kukan dare
gare ta,ta hana sa bacci,dan haka ko kallan
inda ta ke be taba yi ba bare ya dauke
ta,ko tsinke be taba siyawa yarinyar ba
kayan barka na yan uwa da abokan arziki
ake sa ma ta.
A haka Hajjo ta yi arba’in.
Da la’asar ta na sallah,Mairo ta goya ma ta
Inna, kwatsam sai ga Garbati ya
shigo,ganin Hajjon ta na sallah sai ya fara
bala’i,kut!
Ke Hajjo da ma munafunta ta ki
ke kin fara sallah ba ki fada min ba?
Munafukar aure!
Sallah ta ke amma sai da
gaban ta ya fadi,ta dade da fara
sallah,amma kiyayyar da ta kewa Garbati
ya sa tai ta buye ma sa,da ke shi din ma
ba zama ya ke ba,yanzun ma dubun ta ne
ya cika.
Ta tsora kwarai,ji take kamar tai ta
sallah har illa mashaAllah.
Garbati ya sami
waje ya zauna ya ce toh sai ki idar ki bani
hakki na,dan wlh bazan jira dare yayi
ba,munafuka kawai!!
Badan gaban Allah ta ke ba da taki
sallma,amma bayanda za ta yi dole ta yi
sallamar.
Ta ce yau fa na fara sallar,dama
zan fada ma…ya ce na ji toh gyara!
Hajjo ta
ce ka jira mana dare yayi,ya ce ban jira,ya
tashi ya sakace kofa,yayi wulgi da babbar
riga ya ce maza ki gyara na ce Hajjo!
Yanda ya ke so haka aka yi,amma fa ko da
ya gama biyan bukatar sa,sai labari ya
canza.
Rai bace ya ke kallan ta,murya a sama ya
ce Hajjo!
Wai ya na ji haka kamar kofar
gari?
Yaya haka ne?
Hajjo ta mayar da
hijabin ta,ta takure gefe guda.
Ya ce ke
Hajjo ba da ke na ke magana ba!
Ya na ji
haka ne!
Murya kasa kasa Hajjo ta ce dama
da na haifi Inna ne aka ce na karu sai an
min din ki….kin karu?
Ana nufin kin yage za
a dinke ki?
Kai diya mace ta na yagewa ana
dinke ta kamar tsumma!
Wai wannan yar
mitsilar abar da ki ka haifa ita ta maida ki
sai ka ce kofar gari?
Caf da sake kuwa!
Wannan ai ba zan iya ba,wlh bazan iya
zama da mace wankakekiya haka ba!!!
Sauki zan yi!
Ke wlh na ma sauki,ki hade
kayan ki na sauki saki daya……!
DEDICATED to The WOmen Of Virtur
[7/25, 9:36 AM] Salmah Ateeku: [7:17pm,
5/18/2015] Khadija Sidi: DIYA
MACE
Hajjo ta daga ido ta kalli Garbati,maganar
ta sa ce ta ma ta ba za ta.
Ta ce kunne na
ke zagi ko kuwa dai sakin na ji?
Garbati ya
na hura hanci ya ce eh sauki na yi kofar
gari!
Hada na ki ya na naki,ki hada har
wannan abar da ki ka haifawa kan ki ki bar
min gida!
Wani irin farin ciki ne ya lullube
Hajjo,ji ta yi kamar an cire ma ta kaya,cikin
sauri kafin Gatbati ya sake shawara ta tashi
ta na fadin kai amma fa na gode Allah ya
saka da alkhairi.
Ya na huci ya ce idan ma
ba’a ki ke min amen,na dai ci moriyar
gangan,kar na dawo na same ki a gidan nan
wlh!
Ya fice tare da banko kofa.
Dan farinciki ta ma rasa da mai za ta
fara,Ghana must go din ta ta ja ta shiga
zufa komatsenta,sannan ta hade kayan Inna
cikin fanteka guda.
Ta fito da sauri neman
Mairo ta karbi diyar ta.
Mairo ba ta nan sai
dai Kande.
Saki?
Kande ta kame baki cikin
jimami,Iyalle ta fito jiyo maganar Kanden,ta
ce ya na ke jin batun da Allah ba ya so ne?
Wa aka sau?
Tana fara’a kamar wacce aka
yiwa albishir din hajji ta ce ni ce,wlh ni ce
dai Garbati ya sau…lahailahaillallhu!
Kai
Garbati ya isa maras hankali!
Ya sauki da
danyan jego??
Ba inda za ki….. gwiwowi
biyu a kasa Hajjo ta durkusa, ta na magiya
ta na tafa hannu,dan Allah dan annabi dan
ya rasulillahi Iyalle ki bari na tafi,wallahi na
rantse da Allah ya ce ya sau niii…sai ta sa
kuka.
Iyalle ta ce ah ah dai na kuka,ai sai ki
tafi din,za ki tafi,Allah dai ya sa haka shi ne
kairi.
Hajjo ta tashi ta na goge hawaye ta
ce amen,dan Allah ina Mairo ta kawo Inna
sauri na ke wlh,ai yanzu za ta dawo,Iyalle
ta ba ta amsa,makota na aike ta,jin
sallamar Mairo ta ce mata ga ta nan ma.
Cikin sauri tace Mairo sinto min ita tafiya
zan yi,ta sinto ta tana tambayar lfy?
Ina
Hajjo za ta?
Ita dai ta yi ciki da diyar ta ta
bar Kande na mata baya ni.
Sai ga Hajjo ta fito goye da Inna,fantekar
kayan Inna bisa kanta,ga Ghana must go a
hannu,ta durkusa gaban Iyalle ta ce toh
Iyalle a iya zaman mu idan na bata mi ki ki
yafe ni,sai kuma Allah ya sada mu da
alkhairin sa.
Iyalle ta tada ita ta na fadin ni
ce da neman yafiya Hajjo,a yayyafe mu.