← Book details Diya Mace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 41

Sashe 13

Diya Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani bangare su ka shiga,sai ga su tsaye
cikin falo mai dauke da bangare biyu, Sani
ya fara sallama,dan kallan kauye Hajjo har
da tuntube da wani flower pot da ke aje
gefe guda.

Hankali dai!wata murya mai
tarin nutsuwa da sanyi ta daki kunnen
Hajjo,tini idanun Hajjo su ka shiga neman
mai murya.

Babban falo ne mai dauke da bangare biyu
wanda gilashi fari ya raba,na fari an ma sa
ado da fararen kujeru masu kyau da
kayatarwa,ga lallausar carpet da ke
shimfide kalar ganye a kasan kujerun,sai
kuma dayan bangaran falon da ke dauke da
wasu irin kujeru kanana sosai ga kuma
wasu kanana tintin da ke watse amma cikin
tsari,idan kana zaune cikin bangaran za ka
iya ganin abun da ke faruwa a cikin dayan
bangaran ba tare da na wancan bangaran
ya lura ba.

Dan haka har Hajjo ta gama
kalle kallen ta ba ta ga kowa ba,sai da su
ka fito.

Dattijuwa ce wayayyiya fara sol,kakkaura
mai kyauwun gaske,idanun ta sanye da
farin gilashi ta fito,biye da ita danta ne mai
kimanin shekara talatin aduniya,kamar shi
daya da ita,hatta yanayin tsayin su daya,ba
dogo ba ba kuma gajere ba,shima ya na da
dan jiki,da ka gan shi ka ga magidanci.

Dattijuwa ta na fara’a ta ce wa’alaikumul
salam Malam Sani,yau ka so ka makara,ta
bi Hajjo da kallo,gaban Hajjo ya fadi,ba
shakka muryar ta ce wanda ta ji,kwarjini ta
ma ta matuka,bare kuma danta da ke ma ta
kallon kurilla.

Sani ya durkusa yanda ya saba ya gaishe
da Dattijuwar,bayan sun gama gaisawa su
ka gaisa da dan na ta wanda sani ya kira
da suna Jabir.

Ganin haka Hajjo ma ta
gaida su,sai a sannan Sani ke ma Hajiya
bayanin dalilin makarar ta sa,ya tsaya
tahowa da Hajjo ne….

DEDICATED to The Women Of Virtue
(group)
[2:54pm, 5/27/2015] Khadija Sidi:
DIYA MACE
Dattijuwar ta ce ah ku shigo daga ciki
mana,abokiyar debe min kewar kenan?

Jabir ya ce ban tari numfashin ka ba
Mallam sani,amma wannan ai ta yi yarinta
da yawa,wacce fa za ta taya Hajiya aiki fa
aka ce,wannan ko ai ba ta wuce a yi renan
ta ba itama!

Kuma wai goyo na ke gani a
bayan ta..Gaban Hajjo ya fadi,Malam Sani
ya budi baki zai yi magana Hajiya ta katse
shi da fadin kyale shi Mallam Sani,karaso
ciki,ai na ce da ku zan iya zama na ni kadai
na ku ka takura sai an samo min kuma ka
fara sara tin kan su zauna,shigo abun ki
yarinya.

Hajiya ta wuce ta zauna kan
doguwar kujera shi ma Jabir din kasa ya
samu gaban ta ya zauna.

Sani ya aje
Ghana must go din Hajjo daga gefe,shi ma
ya sami matsuguni,yayin da ita kuma Hajjo
kici kici ta sauke fantekar da ke kanta
kasa,sai kuwa Inna ta tsala kuka alalle
Hajjo ba za ta zauna ba,itama Hajjo ji ta yi
kamar ta tsala na ta kukan ganin yanda da
ga Hajiyar har Jabir su ka zuba ma ta
ido,ta ce wayyo ni Inna dan Allah ki taimaka
min ki yi shiru!

Jin haka sai Hajiya ta
dara,ta ce sinto ta mana,ki ba ta ruwa ta
sha kin san akwai zafi kila ma yunwa ta ke
ji ki ba ta nono!

Baki bude Jabir ya ke
duban ta dan har yanzu be gama gasgata
zatan shi na Inna diyar Hajjo ba ce,sai da
ya ga ta sinto ta da rawar,ta sanya ta cikin
mayafi ta fara ba ta nono.

Ya ce kai jama’a
wlh Hajiya diyar ta ce kuwa.

Hajiyar dariya
ta yi ta ce toh da diyar ka ce?

Ta ce
shekarar ki nawa?

Ta tambayi Hajjo,Hajjo
ta ce shekarata goma sha uku…..Jabir ya
ce tashin hankali!

Hajiya kuwa ko a jikin
ta,ta ce Allah sarki,ni ma ina da shekara
sha uku na haifi diya ta ta fari sai dai ba ta
zauna ba,bayan shekara daya kuma na haifi
Sabir yayan Jabir…ita dai Hajjo uhum kawai
ta ke cewa ta na yake.

Hajiya ta ce da Sani
ai ba matsala Hajjon ta ma ta.

Jabir ya ce
Hajiya yarinya ce ga goyo,maimakon ta
taya ki aiki ai sai dai ma ta saki,mai
wannan yarinyar za ta iya fisabilillahi?

Ta na gani za a ma ta biyu babu ba ta san
sanda ta ce na iya ko wani aiki yasin!

Ko
aikin gidan su Garbati ma kaf ni na ke
yi,Baban Aisha shi ne sheda ta ko?

Ta dubi
Sani idanun ta cike da magiyar ya sa baki.

Sani ya ce kwarai kuwa,ai ba da ganan ba
idan dai aiki ne Hajjo ba ta da san jiki…

Hajiya ta ce bare ma ba wani aiki a gidan,ni
ce fa dal sai Auta,shi ma din be fiya zama
ba bare ma auren sa ya matso,to indai zan
zauna da yar aiki toh Jabir da wannan diyar
zan zauna,ta yi min ni dama dan ni ake yi
ko?

Jabir ya gyada kai tin da Hajiya ta
dage,toh lalle hakan za a yi.

Ya ce toh zan
fadawa Sabir an samu,nawa za a ke biyan
ta?

Hajiya ta dubi Hajjo ta ce yarinya ya
sunan ki ne?

Hajjo ta ce Hajara,amma Hajjo
ake kira na.

Hajiya ta ce toh Hajjo nawa ki
ke so a biya ki?

Hajjo ta dubi Sani,dan ita ba ta ma san
nawa za ta ce ba.

Sani ya gyada ma ta
kai,sannan ta ce ko nawa ne Hajiya zan
karba.

Hajiya ta ce ah ah gwara dai ki fada
kar a kware ki Hajjo,kin san dai kwana za ki
na yi,kuma duk wata za a ke baki kudin
ki,kuma ni da kike ganina ban da matsala
musammam idan ki na da tsafta,za ki ji
dadin zama da ni.

Hajjo ta ce Hajiya ni kam
wlh ko nawa ne Allah sa albarka.

Hajiya ta
ce toh shikenan tin da kin ki ki fada,kin ga
ko an kware ki ba laifin mu.

Sani ya ce
kwarai kuwa.

Hajiya ta ce da Jabir sai su
yanke nawa za su ke biyan ta,daga yau za
ta fara aiki.

Sani ya koma kan aikin shi,ita ko Hajjo
dakin da za ta ke kwana Hajiya ta kai
ta,daki ne mai hade da ban daki a ciki,ga
wani sanyi mai dadin gaske da ke ratsa
Hajjo wanda ta gaza gane sanyi daga ina
ya ke busowa gashi dai zafi ake bare ta ce
ta taga ne aka salima tagogin a rufe su ke.

Hajjo tsaye ita da Inna tsakar dakin,wannan
daki ai yayi a hada nawa da na Iyalle da na
Baban Garbati!

Wannan girma ai anyi asarar
fili!

Haka dai tai ta tabe tabe da kalle
kalle,hatta bandakin abun kallo ya zame ma
ta,ita kuwa Inna sai gwaran cin ta take.

Ba
a jima ba sai ga Hajiya ta dawo dauke da
sinkin sabulun wanka,ta ce da Hajjo ta yi ta
kuma yiwa Inna,sai ta fito ta ci abunci ta
nuna ma mata gidan.

Hajjo ta karba tare da
ma ta godiya.

Sai dai wankan kusan gagara
yayi,da kyar ta samu ta yiwa Inna,ita kuwa
sai dan kwaskwarima ta yi,dan gani ta ke
da ta saki jikin a bandaki za ta ji ta a
kasa,ta fito ta na mita an bi an lallaye ban
daki da tangaran sai ka ce wajan hutawa!

In dai ba ka mutu ba ka sha kallo…..

DEDICATED to The Women Of Virtue
(group)
[3:09pm, 5/27/2015] Khadija Sidi:
DIYA MACE
Sati biyu Hajjo ta fara sabawa da rayuwar
gidan,haka kuma sannu a hankali Hajiya ke
nusar da ita yanayin yanda ya kamata ta
kasance a matsayin ta na diya
mace,uwa,kuma mai aiki,da ke Hajjon mai
saurin dauka ce hakan ya sa da an gwada
ma ta shikenan za ta dauka.

Hajiya kuma
ba ta da matsala,tausayin Hajjon ma ta ke
ji,sai ta ke tuno ma ta sanda ita ma ta ke
kamar ta,sai dai ita din da gatan ta ga
kuma soyayyar miji amma duk da haka ta ji
jiki bare kuma Hajjo ta take rayuwa daga
ita sai diyar ta ta.

Ga wata soyayya da ke
kulluwa tsakanin Hajiya da Inna,da ke
Hajiya ba ta taba samin diya mace
ba,wacce ta haifa din ba ta zauna ba,kuma
ta na sha’awa matuka,samin Inna kusa da
ita sai ya sa take kaunar yarinyar,ta na
yawan ma ta wasa,idan Hajjon ta na aiki
gun Hajiyar ta ke barin Inna,sai ka ji suna
ta dariya abun sha’awa.

Da yamma Sani zai koma Kumurya,sai
Hajiya ta ce ya aje Hajjo shagon da ake ma
ta din ki a tarauni,in ya so sai ta hawo
adaidaita ta dawo tin da Hajjon ta fara gane
gari,Inna goye a baya,Hajiya ta ba ta naira
dari ta ce idan ba za ta gane ba ta ce ya
shigo da ita ta kwanan magi.

A hanya Hajjo ta ke ta yiwa Sani
tambayoyi,ta ce ‘ya’yan Hajiya uku,amma
ita daya ta gani,ina sauran biyu?

Sani ya
na tuki ya ce ai babban dan na ta shi ne
Sabir,a Abuja ya ke zaune da iyalin
sa,matar shi daya da yara uku,suma duka
maza ne, can ya ke aiki karkashin company
da baban su mai rasuwa ya bari,shi mutum
ne mai hakuri kwarai da kawaici,be fiya
magana ba,da mahaifin su ya rasu bayan
an raba mu su gado sai suka hada karfi da
karfe su ka ci gaba da tafiyar da company
din,karkashin jagorancin Sabir,duk da be yi
wani karatu mai zurfi ba,a diploma ya
tsaya.

Hajjo ta ce menene diploma?

Sani ya
ce wani mataki ne na karatu na gaba da
sakandiri.

Hajjo ta ce ayyo.

Shi kuma Jabir
fa?

Sani ya ce Jabir shi ne dan Hajiya na
biyu,matar shi daya da yara biyu mata,na
ukun kuma ko yau ko gobe.

Mutum ne mai
haba haba da surutu,likita ne a asibitin
koyarwa na malam aminu kano.

Hajjo ta
kame baki likita?

Kai gaskiya ya burge ni
wlh.

To waye autan kuma?

Sani ya jinjina kai,yace wato sarkin kumbo
da kwalisa kenan,ga kumbo,ga kyawu,ga jin
kai,ga takama ga isa!

Caf girman kai
kenan?

Hajjo ta tambaya cikin mamaki.
Chapter 13 · 0% Book details