← Book details Diya Mace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 41

Sashe 25

Diya Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Khalid
ya na murmushi,ya nuna motar sa ya ce je
ka duba bayan motar can,amma ka
tabbatar diya ta ba ta tashi ba.

Suraj ya
juyo ya kalli Hajjo,ta girgiz kai ta ce ba
gaskiya ba ne,kar ka je…ya juya ya nufi
motar,ko da ya leka sai ga diya kwance ta
na ta baccin ta,ya bude motar ya kalli
fuskar Neena sosai,tamkar Hajjo ya ke
kallo,dan dai wannan fara ce kuma yarinya
ce shakaf da sai ya ce yar biyun Hajjo ce!

Abun da ya zo ran sa shi ne kanwar Hajjo
ce,duk da dai Hajjo ta fada ma sa ita ce
auta,Allah kasa kanwarta ce addu’ar da
yayi a fili kenan,Hajjo is too young to b her
mother.

Ji ya yi kamar ya tada Neena,sai
kuma ya fasa ya dawo wajan su Hajjon da
tuni idanun ta ya kawo ruwa.

Hajjo ta ce let
me explain plsssss Suraj.

Khalid na gefe
murmushi fal fuskar shi,yau dai kam tarkon
da ya sa ta kam katan zaki ba kurciya ba.

Suraj ya ce Hajjo,tambaya daya zan mi ki,ki
kuma gaggauta fada min gaskiya,aaa ko ah
ah,waccen diyar da ke kama da ke sak,diyar
ki ce?

Ya Allah ka sa ta ce ah ah!

Kallan
Hajjo ya ke kamar rayuwar sa depend on
her answer.

Hajjo ta yi kasa da ido,ji ta ke
kamar kasa ya bude ta shige ciki,abun
kadan da ya kamata ta fada ma sa tuntuni
ya zama babba.

Suraj ya ce ke na ke
sauraro Hajjo!

Murya a kasa ta ce eh
Ameena diya ta ce…

DEDICATED to The Women Of Virtue
(group)
[11:55pm, 6/5/2015] Khadija Sidi:
DIYA MACE
Juyawa ya yi ba tare da sake furta komai
ba ya shige motar sa.

Hajjo na fadin dan
Allah ka tsaya na ma ka bayani Suraj!

Tuni
ya figi motar sa ya tafi.

Cikin tsana Hajjo
ta ke kallan Khalid,ta ce dan me ya sa
haka?

Me na tsare ma?

Me na taba ma ka
da na cancanci wannan hukunci daga gare
ka Khalid?

Ya ce marry me,jst marry me
suger!

Ni na san da ‘ya’ya na cikin ki,kuma
bazan bari ba sai inda karfi na ya kare,sai
kin haifa min su Suger….kallon sa ta yi irin
kallan da ake yiwa wanda su ka sami tabin
hankali,ta ce Allah ta baka lfy! ta juya ta
shige gida a fusace,ta na ji ya na kwalla ma
ta kira ta ma sa banza,ta na shiga gida ta
karasa daki da gudu sai ta fashe da kuka.

Indo ta shigo da sauri ta na fadin lfy!

Lfy
Hajjo!

Me ya faru!

Cikin kuka Hajjo ta ce
Indo Allah ya raba ni da Gatbati tin da
dadewa amma yanzu ya hada ni da Khalid!

Ya matsa min,ya isheni!

Na tsane shi!

Na
tsane shi fiye da yanda na tsani Garbati tin
da ya raba ni da Suraj.Kai gaskiya wannan
bawan Allah ya yi lefi,amma zauna bar
kukan,zauna ki bani lbry.

Ba ta dena kuka
ba har ta gama ba wa Indo labari tin daga
sanda Khalid ya dawo har zuwa yau da ya
raba ta da Suraj,me san ta dan soyayya ba
dan ya na so ya aure ta saboda wani
bukatar shi na daban kamar Khalid ba.

Indo
ta ce toh ki yarda ki aure shi mana
Hajjo,menene a ciki tin da ya na kaunar
diyar ki…bazan aure shi din ba,ni bazan
taba auren mutum mai ji da kai da dagawa
irin Khalid ba!

Gwara ma kar na yi auren
kwatata!!!

Ba fa so na ya ke ba,kawai dan
matar shi ba ta haihuwa zai aure ni,ga
machine ta haihuwa ya samu ba!

Ya aure ni
ya hada ni da matar nan ta sa kamar
balarabiya su ji dadin wulakanta ni,duk
lalacewar rayuwa ta Indo na fi karfin
wulakanci.

Cikin tausayawa Indo ta ce yi
shiru Hajjo,ki ta addu’a da istikara Allah ya
zaba mi ki ma fi alkhairi.

Hajjo ta ce babu
alkhairi a tare da Khalid…kul Indo ta katse
ta,ki dai yi addua na ce,zabin Allah ya shi
ne zabi,Allah ya zaba mi ki.

Hajjo ta ci
gaba da kukan ta.

Tin shigar Hajjo gida Khalid ya ja motar shi,
shi ma ya je yayi abunda ya kawo shi,wato
gaida Baba,har yau ma sai da ya tambaye
shi Hajjo,Khalid ya yi mamakin ta na garin
ma amma ba ta zo ta duba shi ba?

Halin
Hajjo sai ita.

Da kyar Neena ta yarda Baba
ya ruke hannun ta da ke Khalid tada ita
yayi da su ka isa gidan dan Baba ya ga
jikar ta sa.

Ita ko Neena ce wa ta yi sam ba
kakan ta ba ne,ita kakan ta na kano,wato
mahaifin Hauwa,da shi ta saba, har cikin
ranta tsoro Baba ya ke ba ta.Baba ya ce
Allah sarki mai sunan ki mutuniyar kirki,ba
dai ta cutar ba sai da a cuce ta,Allah ya ji
kanta da rahama.

Khalid ya amsa da amen.

Neena ce ta matsa su tafi,dan haka ba
dadewa su ka juyo abun su,zuciyatt sa cike
da tunanin ko wani Hali Hajjo ta ke?

Bayan ta sha kuka ta koshi ne ta yi kokarin
kiran wayar Suraj,amma a kashe.

Ta kira ta
Ayush ta ba ta lbryn abunda ke faruwa,ta
ce haba shi yasa Ya Suraj ke nema na,ya
zo da magariba ba na nan,kar ki damu zan
ma sa bayani inshaAllahu zai gane.

Hajjo ta
ce toh Allah ya sa.

Su ka yi sallama.

Sai a
sannan ta bude jakar ta,Jewellery ne ma su
kyan gaske Indian design,da kuma turare iri
iri,sai kuma takalma da pakistans na gani
na fada.

Hajjo ta yi ajiyar zuciya ta re da
fadin Allah sarki Suraj,Allah ya sa ka
gane,amen.

Suraj kuwa tin da ya je gidan su Ayus ba ta
nan ya koma gida ya kasa zama,abun da ke
daure ma sa kai shi ne ta yaya wannan za
ta zama diyar Hajjo?

Ai wannan ta yi rabin
shekarun Hajjo,ta yi yarinta a ce ta na da
diya kamar wannan,dama ba budurwa ba
ce?

Ta taba aure?

Toh ma ta ce Khalid
autan Hajiya ne,shin ta yaya ya zama
mahaifin diyar Hajjo?me ya sa ba ta taba
sanar da shi ba?da wannan tambayoyi ya
sake komawa gidan su Ayush cikin
daren,dan ba zai iya kwana ba su yi
maganar ba.

Ya ko ci sa’a ta na nan.

Ta ji
dadin ganin sa duk da ba dan ita ya zo
ba,dan case din sa da Hajjon sa ne.

Bayan
zaman su yay ta jero ma ta tambayoyi,har
dai ta banbance ma sa zare da abawa,ta
bashi lbryn yanda aka yi Hajjo ta ke da diya
kamar Neena,kuma Khalid ya kira kansa ne
mahaifin Neena ba dan komai ba sai dan
shi ne ke rukon Neena,kuma ya ke san
auran Hajjo.

Jikin sa ya yi sanyi ya ce amfanin bayani
kenan in a relationshp,sam boye boye be da
dadi,da ta fada min tuntuni da duk haka be
faru ba,wai dan ta taba aure ba ya na nufin
zan dai na san ta ba,I love her nd i wil
olways love her.

Ayush ta gyada kai ta na
murmushi,duk da kuwa maganar ta dan
taba zuciyar ta,ina ma ta ji wannan
maganar da ga bakin wanda ta ke so,kuma
ace da ita ya ke,da burin rayuwar ta ya
cika.

Bayan yayiwa yan gida sallama Ayush
ta raka sa har mota,ya ce gobe zai koma
ya sami Hajjo,amma kar ta fada ma ta,zai
ma ta suprise visit ne.

Ta na murmushi ta
ce ka gaishe ta,su ka yi sallama ya tafi ta
dawo gida zuciyar ta fal da san maso wani.

Washagari Hajjo na asibiti Hajiya ta yi kiran
wayar ta,ta ce idan ta tashi ta biyo gidan
ta za su gidan kanwar Hajiya su ga wasu
kayan kitchen da kanwar ta ta ta shigo da
su.

Da kamar ta ce da Hajiyar ba za ta
sami damar zuwa ba,sai kuma ta guji bacin
ran Hajiyar,dan ita ta tsaya tsayin daka
Hajjo ta fara siyan kayan aure tin da ta fara
daukan albashin ta,ta kuma sa Hajjo a
dashi na daidai yanda Hajjon za ta iya.

Duk
wata shawara ita take bawa Hajjo ita take
sa ta a hanya. ta amsa ma ta da toh,zan
zo Hajiya.

Bayan aje wayar ta ce ya Allah
kar ka sa na hadu da wannan dan anacen
har na je na tafi.

Kayan kitchen din ko sun mata,dan har
kwasar wasu ta yi,saboda ita ta gida ce aka
ma ta ragi.

Bayan dawowar su ta aje su
dakin da ta ke taro.

Ta ce Hajiya bara na
kama hanyar na tafi kar dare ya yi.

Hajiya
ta ce jira ma na Sani ya dawo sai ku tafi
tare.

Hajjo ta ce ay na zaci ya tafi,bari na
jira shi.

Nan su ka zauna ita da Hajiya suna
tadi,Hajjo na cin abunci.

Har ta gama shiru
shiru Sani be dawo ba.

Sai Sallaman Khalid
su ka ji,Shikenan gashi abun da na ke gudu
ya zo!

Hajjo ta fada cikin ranta.

Ba kunya
kamar babu lefin da yayiwa Hajjo ya raba ta
kusa da ita ya zauna kusa da Hajiyar
sa,bayan sun gaisa Hajjo ta daure ta gaishe
shi,ya amsa,tare da fadin yar kumurya ta
dawo kenan.

Hajiya ta ce ba dawowa ta yi
ba,Sani ta ke jira ya dawo su tafi,kuma na
ji ma wayar sa a kashe.

Khalid ya ce wani
Sani kuma da ya tafi tin bayan la’asar?

Hajiya ta ce haba dan Allah?

Ya ce wlh,sai
ma da ya biyo ta gida na da ke na neme
sa.

Hajiya ta ce Allah sarki na tsaida
Hajjo,rashin sani.

Kwayar idanun sa na
rawa ya ke kallan Hajjo da tuni ta ji komai
ya gama jagole ma ta,ga shi akwai wani
file da za ta yi submitn gobe goben
nan,kuma ta baro sa a gidan Indo. fuskar
sa cike da murmushin mugunta ya ce
Hajiya kar ki damu,dan dai nan da Kumurya
ai sai na kai Hajjon ta ki.

Da sauri ta daga
ido ta kalle shi,ya kashe ma ta ido,ta ce
Hajiya wlh na hakura zan kwana!

Hajiya ta
ce wa zai kawo mi ki file din da za ki yi
submitn goben?

Ta ce na kira Baban Aysha
ya taho min da shi.
Chapter 25 · 0% Book details