← Book details Diya Mace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 41

Sashe 2

Diya Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ba
dai haka ta so ba,ta ce toh,ta karasa ta
dauko koko da kwanan numame ta ya haye
kan tabarmar da ke shimfile karkashin
bishiyar mangaro ya yayi rumfa a tsakiyar
gidan.

Babban gida ne mai dauke da
dakuna shida a jere,sai kuma guda daya
mai ciki da falo,shi ne wanda Baba ke
kwana ciki,sai daya na Inna da Hajjo,na
biyu na Mudi da Ayuba,daya dakin
girki,daya kuma dakin aje kayan abunci duk
da ba aje mu su kayan abuncin ya ke ba,sai
kuma dayan dakin da ke kulle cike da kayan
takarce har da wani tsohon gado mai
rumfa.

Da ke Inna mace ce mai tsaftar
gaske kullum gidan tsaf sa shi.

Sai da ta fara kai loma sannan ta daga ido
ta kalli Inna ta ce laa Inna wankin ki ke
ashe,ni da na ce zan na taya ki.

Inna ta
dara,Hajjo hankali,ke tin shigowar ki ba ki
lura da wankin ba sai yanzu?

Baki cike ta
ce eh wlh Inna,bara na gama sai na sa mi
ki hannu,Inna ta ce a gama lfy auta.

Inna!

Hajjo ta kwada ma ta kira,na’am
auta,menene kuma?

Hajjo ta ce ni ma dan
Allah ki ce da Baba ya sani makarantar
gaba da firamari kamar yanda ya sa su
Mudi da Ayuba…..ba za a saki din ba!

Baba
ya fito a fusace,ya ci ado da babbar rigarsa
aska shida,ashe ya na daga daka ba ta sani
ba.

A fusace ya ke duban Hajjo da tini ta sha
ruwan jikin ta,ta yi tsumu tsumu.

Shegiyar
kaya,ke dubanni nan!ke wacece da za a
saki makarantar gaba da firamari?

Inna ta
dauke kai ta ci gaba da wankin ta,ba da ke
na ke magana ba!

Ido na shirin kawo ruwa
ta ce ni Hajjo ce…

Baba ya ce Hajjo me?

Hajjo ta ce diyar ka mutum!

Ungu nan!

Ya
ma ta daguwa!

Hajjo diya mace ba diya ta
ba za ki ce!

Ke diya mace ce,su Ayuba da
Mudi maza ne shiya na sanya su
makaranta koba komai idan su ka gama ma
amfana da su,ke kuwa fa?

Ita diya mace
jidali ce,a haifo uban ku yayi dawainiya da
ku,mu aurar da ku mazajen ku su yi
dawainiya da ku,ku tsufa ‘yayan ku su yi
dawainiya da ku,shegiyar kaya na ki na yi
asara,bazan sa ki a makarantar ba!

Da ma
ki ka samu na.sanya ki firamari din?Har
kina sa bakin magana dan kin ga ban buge
ki jiya ba ko?

Ya kama kunnen ta sai da
Hajjo ta dan yi kara dan zafi,in kara gani
kin maimaita abunda ki ka min jiya sai na
lahira ya fi ki jin dadi!

Ya saki kunnan,Hajjo
ta durkushe ta na kuka,ko a jikin sa,hannu
ya sa a aljihu ya fiddo da damin kudi,ya
zaro naira hamsin ya karasa wajen Inna ya
na fadin ke Amenatu ungo nan kudin
cefane,sai Allah ya dawo da ni,na tafi daurin
auren Garbati dan Alhaji Baso,ta dago ta
karba tare da ma sa fatan dawowa lfy,ya
fice ya na baza babbar riga.

Inna ta dubi
Inda Hajjo ta ke durkushe ta na kuka,tace
maza tashi diyar albarka ka karasa cin
tuwan ki,kar su Mairo su shigo su cinye mi
ki fa!

Hajjo fuskarta cike da hawaye ta ce Inna
dama ni ma namiji ce kamar su Mudi da
Baba ya soni ko da dan gutsire ne!

Inna ta
baro wajan wankin ta zauna kusa da
Hajjo,ta ce kul Hajjo,na godewa Allah da
yaiyo ki diya mace,kin san darajar ‘ya’ya
mata kuwa?

Ai darajar diya mace da yawa
take Hajjo,yanzu in tambaye ki,da ki zama
kamar Inna da ki zama kamar Baba wanne
ki ka so?

Hajjo ta ce caf!

Gwara na zama
kamar Inna ta wlh,Inna ta rungumo ta
yauwa diya ta,shi ya sa na ke san ku,Baban
ma fa ya na son ki,har ya fi gutsire,kawai
baya nunawa ne.

Hajjo ta dara Allah Inna?

Shi ya sa ma jiya da ya dawo ya ga na yi
bacci be buge ni ba ko? .Inna ta gyada kai
kwarai da gaske,maza ci tuwan ki toh sai ki
zo mu yi wankin,ko kin fasa taya ni ne?

Hajjo ta ja kwanan tuwan ta, zan taya ki
mana Inna,bara na yi sauri na zunzunduma
loma!

Inna ta tashi ta na dariya,ta ce a dai
ci a hankali,ta koma kan wankin ta,ta bar
Hajjo ta na zunduma lomar kamar dai
yanda ta ce
DEDICATED to The Women Of Virtue
(group)
[12:11am, 5/1/2015] Khadija Sidi:
DIYA MACE
Babban Masallacin Kumurya,jama’a an
taru,Baba tare da aminin sa Alhaji Baso
baban ango zaune cikin masallaci suna
jiran waliyan amarya su karaso,shiru ba su
karaso ba,har rana na shirin takewa,Baba
ya dubi Alhaji Baso ya ce anya kuwa lfy?

Ka ga fa yanda aka shanya mu kamar
kayan wanki?

Alhaji Baso cikin damuwa ya
ce ni ma dai jiran ya fara damuna Alhaji
Mamman!

Daga can gefe su ka hangi
Garbati,yaci babbariga tare da abokansa.

Garbati kato ne mai girman gabobin
jiki,gashi dai yaro ne mai kimanin shekara
ishirin da biyu a duniya,amma sai kayi
zatan ya haura haka,fari ne mai zubin
gwabaye.

Kai Garbati,ya ka nan!

Alhaji Baso
ne yayi kiran sa,Garbati ya karasa da sauri
ya durkusa gaban su,gani Baba,Alhaji Baso
ya ce ya haka ne?

Ya da girman mu a gari
ana shirin maishe mu kanana mutum ne?

Mun tara Jama’a amma ba waliye na
amarya?

Cikin maganar sa irin ta
gwabaye,da karfi ya ke ya ce yo ni ma
Baba hakan na gani!har raina ya fara baci!

Aw Baba ka ga yayan Jummalan ma ya
karaso!

Ya yi nuni da wani matashi da ya
shigo,Illo ga mu nan!

Ya kwalla ma sa
kira,Illo ya karaso ya gaida su Baba,Baba
ya ce ya haka ku ka makara kuma?

Illo ya
durkusar da kai ya ce ai an sami matsala
ne daga wajan amarya,ta ce maganar aure
ba ta san shi ba,ta fasa auren
Garbati…..lahailahaillallahu Mahammada
Rasulillahi Sallallahu alaihi wasallam!

Su
duka su ka doka salati!Garbati ya fara
muzurai!

Alhaji Baso ya ce wannan ai
yashashshen zance ne!

Mu za a maida
kanana mutane!

Tintini ba ku san ku fasa
auren ba sai da mu ka tara jama’a!

Dan
Allah Mallam Mamman taya ni jin maganar
kananan mutanen nan!

Shi de Illo ya yi
kasa da kai kawai,Baba ya ce to a wani
dalilo yarinya ta fasa aure?

Illo ya ce a
dalilin kin ware ma ta gida ita kadai ba tare
da ya hada ta iyayen sa ba!

Zancen banza
zancen hofi!

Alhaji Basu ya dakatar da shi
ya na kumfar baki,an ki a ware ma ta
gidan!

An ki din!

Ta fasa auren dan
iyayenta!

Mu nan mu mu ka hana shi ware
ma ta gidan,tashi ka bamu waje!

Illo ya ce
na bar ku lfy,ya tashi yayi gaba ya bar su
cikin takaici,ga Jama’a an tara.

Baba ya dafa kafadar Alhaji Baso ya ce kar
ka damu,ba dai yau aka sa za a aura auran
Garbati ba?

Aure kam kamar an daura an
gama,kai Jama’a a saurara za a fara
abunda ya kawo mu,Garbati dai sarautar
Allah ya zubawa ido kawai.

Can gida kuwa Inna ta aiki Hajjo siyo
daddawa,dake Hajjo akwai san gudu,ta taho
a guje ga daddadawar ta a hannu,ba ta
ankara ba ta gwabje Idi dan makota ya
dauko tallar manja,tini farantin manjar ta yi
kasa,manjar ta zube malale a kasa,Idi ya bi
manjar da kallo ya ce kan uba!

Wlh sai an
biya ni ko na daki kudina!mahaukaciya
wacce ba ta san tafiya a hankali ba!

Jin
haka Hajjo ta dada zurawa a guje ta na
fadin ba sai ka biyo ni ka daki kudin na ka
ba in za ka iya kama ni!

Ai kuwa shi ma bin
na ta yayi,tsabar gudu ba ta hango Baba
tafe ba,da gudu ta shige gida.

Baba ya
shigo ya na fadin komai aka yi shegiyar
kayan nan wani masifar ta jangwalo ma na
ya sa take gudun fanfalaki haka!

Amenatu
ki na ina ne!

Inna ta fito daga dakin ta
yayinda shi ma Idi ya shigo a guje,ya tsaya
gaban Baba ya na haki.

Baba ya ce kai lfy?

Menene?

Idi da kyar ya ke magana dan haki
ya ce Hajjo ce ta baran min da manja ta ta
gudu,wlh sai ta biya ni!

Ko na daki kudi na!

Inna ta ce Hajjo kuwa?

Daddawa fa na aike
ta ta siyo min!

Baba ya murmusa,ya ce ni na ga abunda ba
ki gani ba,kai yaro nawa ne manjar ta ka ga
sadakin ta na biya ka a ciki!

Inna ta dafe
kirji SADAKI kuma!

Baba ya ma ta
banza,yayinda ya fito da kudi daga aljihun
sa,Idi ya ce dari uku ne,Baba ya dirga dari
uku ya mi ka ma Idi,ka ci sa’a yanzun nan
na karbi sadakin ta,da wlh sai dai ka daki
kudin na ka dan da kudi na dai ba zan cira
na biya ba.

Idi ya karbi kudi ya kama
hanyar fita ya na fadin Allah ya so ki
yarinya!

Inna ta ce Mallam magana na ke
fa,na ce wani sadaki ka ke magana akai
ne?

Baba ya ce sadakin Hajjo mana,Allah
ya yanke min wahala ai,yarinyar da Garbati
zai aura ta ce ta fasa auren,sai ni kuma na
samawa kai na sauki na Hajjo dan na fitar
da abokina kunya!

Inna ta fara salati ta na
sallallami,ta ce Mallam aure fa ka ce?

Hajjon nawa ta ke Mallam!kwanan nan fa
ta cika shekara goma shabiyu Mallam,Kai
kuji wani yashashhsen zance,Hajjon nawa
ta ke?

Zama zan yi da ita in ta dawainiya
da ita?kin manta motsin gado ce ba yarinya
ba,ina ma ta ke ne?

A gaban ido na ta
shigo a guje kamar walkiya!

Ke Hajjo ki na
ina ne wai!

Za ki fito ko sai na sabar mi ki!

Inna ta ce Mallam na ce da kai na aike ta
siyan daddawa…Baba ya ma ta banza,ya
cigaba da fadin Hajjo wlh na dirga uku ba ki
fito ba sai na mi ki dukan kawo wuka,ya
fara dirge daya,biyu….

Tim!kamar daga sama sai ga Hajjo ta diro
daga kan bishiyar mangaro,Baba ya ce
shegiyar kaya!

Ki ganta nan bishiya ta haye
kamar birinya,Inna kallan Hajjo da ta yi
tsumtsumu da ido ta ke cike da mamaki da
tausayi.
Chapter 2 · 0% Book details